An gama yi mata gyaran jiki kenan, Arshaad ya zo.
Dama tunda ya kira ta yace ‘gashi nan zuwa’, tayi sauri ta tashi akan turaren wutan da take a kai ta fad’a wanka.
Tana cikin d’aura d’ankwalinta ta fara jiyo hayaniyar shi da su Sudais! Kasancewar a d’akin k’asa suke yin gyaran jikin.
Loose gown ce a jikinta kalar kwanduwar kwai mai haske, dan haka kawai ta d’an d’aura d’ankwalin ta zagayo da edges d’in ta bayan k’eyarta ta sake su suka zubo akan k’irjinta wanda hakan yayi kamar mayafi saboda d’ankwalin yana da d’an girma.
Waya ya fara mata dan haka tayi sauri ta fita, ta bar Sakina wadda ake k’arasa mata nata yanzu.
Bai ga fitowarta ba, dan haka ya sake d’aga wayar yayi dialing numberta ya kara a kunnenshi. Har ga Allah baya iya b’oye zalamarshi when it comes to Hudan! Y’ar tafiyar nan da yayi ya sanya ya sake fahimtar tsananin mugun k’aunarta da yake yi! Duk da cewa suna waya amman ji yake kamar yayi irin shekarar nan bai ganta ba! Ko dan tak’i yarda su yi video call ne may be shiyasa, he wonders why tak’i yarda suyi video call d’in. Sakina dai tace mishi gyara ake mata kuma in ya ganta idan ya zo ba lalle ya biya kud’in gyaran da kyau ba, ba yadda bai yi dasu ba amman fur itama Huda tak’i yadda ta bashi had’in kai ya gantan. Yana cikin wannan tunanin ya fara jiyo wani k’amshi mai mugun fitinannen dad’i, a take yaji jikinshi ya mutu!
A hankali yake jin k’amshin na sake shigar mishi hanci yana sake karad’e ko ina yana sake kashe mishi jiki..
Sai da ta kusan k’arasowa inda yake tukunna ya samu k’arfin jikin juyawa sakamokon jin takun tafiyarta wanda flat shoe d’in k’afarta ke badawa.
Yana juyowa suka had’a ido! Tsayawa kawai yayi ya kasa ci gaba da motsi, kamar wani statue.
“Ya Arshaad wayarka”. D’in da Sudais (waenda suke tare dashi a parlourn, d’an gefe kad’an da shi) yace masa ne ya d’an dawo dashi daga duniyar da ya lula. A hankali ya rik’o wayar wadda ta kusan zamewa daga hannunshi kafin ya iya cewa.“Lafiya, ya gida?”. Still yana kallonta.
Hudan ita kuwa kunyar kallon take ji, dan haka ta fara kame kame ta kasa cewa komai bayan gaisuwar da tayi masa. Sun yi kusan minti biyu a haka! Ganin bashi da niyyar d’auke idanunsa daga kanta yasa ta sake cewa ”Ya hanya? Ka dawo lafiya?”
“Alhamdulillah”. Ya ce kawai ya ci gaba da abinda yasa a gaba.
Wani irin kallo yake yi mata, tun daga kan y’an yatsun k’afarta har kan d’ankwalinta idan ya dire sai ya sake komawa daga inda ya faro kamar ya samu tv.
Ganin abun nashi ba na k’are bane ba yasa tace “Ya Arshaad dan Allah ka daina kallona”. Tana rufe fuskarta da tafin hannunta, a shagwab’a. Hakan da tayi kuwa ba k’aramin kyau ya k’ara mata ba.
Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin yace “Sorry na daina. Ina Sakina? Kice tazo ta karb’i tukuici mai tsoka.”
Ya fadi hakan a kasalance still bai daina kallon nata ba sai dai yanzu ya fara motsi ba kamar d’azu da ya k’ame ba. Cikin son kawo k’arshen kallon tace “Ana yi mata gyaran jiki, in ta gama zata fito.
Ka je kaci abinci yanzu, da kaina na yi maka girkin.”. Ta fad’a tana sunkuyar da kanta k’asa.
Wani sassanyan murmushi Arshaad yayi, yana mai jinsa a sama! Farin cikin da yake ciki yau anya zai iya misaltuwa kuwa? Cikin murmushin yace, “Anya Huda ranar da aka ce an d’aura mana aure ba zan mutu dan dad’i ba kuwa?”.Da sauri ta d’ago ta kalleshi, sai kuma ta tura baki ta kauda kai ta d’an b’ata rai.
Dariya yayi this time around kafin yace “Sorry tou, ba zan suma dan dad’i ba kuwa? Just looking at you fa da kuma jin wai kin yi min girki da waennan kyawawan hannayen naki! Wallahi ji nake kamar in yi ihu dan murna, Ina kuma ga in aka ce kin zama mallakina gabad’aya?”
Dariya ta d’anyi tana me sunkuyar da kanta k’asa, kafin tace “To muje kaci kar ya huce”.
Ya lura ta gaji da kallon shiyasa take ta so su bar wajen ta samu su daina facing d’in juna, dan haka yayi murmushi kawai kafin yace “Mu je tou”. A ranshi ya raya. ‘I can’t help it, ni kaina inaso In d’an janye idon but na kasa.’
Ita tayi serving nashi bayan sun isa dining d’in, kamar yanda yayi zato kuwa, tana gamawa ta nemi kujera ta hud’un wadda yake kai a side d’inshi ta zauna.
Dariya ta bashi dan haka sai da ya d’anyi dariyarshi tukun ya mik’e yaje inda take yace
“Tashi ki ga” Rau rau tayi da ido za tayi magana yace “Shiiii, taso”
A hankali ta mik’e ta bishi. Sai da ya zagaya d’ayan side d’in tukunna ya zaunar da ita a kujerar da take setin tashi. Kamar za tayi kuka tace “Ya Arshaad to kar ka kalleni”
Dariya yayi yace “Tou” kawai, ya zagaya ya zauna ya fara cin abincin shi
yana santi yana kallon nata da bata so.
Ko plate d’in abincin baya kalla, kawai spoon yake sakawa ya d’ebo ya kai baki, dad’i har kwanyarshi.
Suna a haka Sakina ta fito, jin an bud’e k’ofa kuma an nufo dining d’in ne ya sanya ya d’an
juya. Murmushi yayi kafin yace “Ta hannun dama! Kina da babbar kyauta yau.”
Cikin dariya Sakina ta k’araso suka gaisa tayi mishi sannu da zuwa.
Fitowar Abba wanda zai fita ne yasa tace musu “tana zuwa” tabi bayan Abban wanda ya nufi waje bayan sun gama gaisawa da su Arshaad d’in. Ganin ta biyo shi ne yasa ya d’an tsaya a y’ar varendar bakin main door d’in, tana k’arasowa Auwal shima yana isowa wajen! Ai kuwa ta had’e rai ta cuno baki ta d’auke kai. Shi kuwa Auwal gaba d’aya numfashinsa sama yaji yayi, da kyar ya samu ya seseta kanshi, ya shiga gaida Abba cikin nutsuwar da Abban bai tab’a saninshi da ita ba.
Murmushi Abban yayi bayan sun gaisa yace “wuta da auduga” yana kallon Sakinar da ta d’an kalleshi kad’an, kunya ce ta rufeta dan haka tace “Ya auwal Ina wuni”. Murmushi yayi wanda ya baiiyyana dimple da tsantsar kyawun fuskarshi, kafin yace “Lafiya, ya gida? Kwana biyu” Cikin takaici tace “Alhamdulillah”
Abba ne ya katsesu ta hanyar cewa “You were saying?” yana kallon Sakina had’e da kallon agogon dake d’aure a tsintsiyar hannunshi. Bataso yin maganar a gaban Auwal ba amman ba yadda ta iya, hakan yasa tace, “Um daman Abba, wai pre wedding picture nake so inyi surprising su Hudan da shi, In ba damuwa, please.” Dan k’uraa mata ido yayi, kafin yace “Okay, banda shirme.” Sannan ya juya har zai wuce sai kuma ya juyo yace, “Kina buk’atar cash ko?” Yayi maganar yana mai zura hannunshi a aljihu.
Dasauri Auwal yace, “No. Abba I’ll take care of it.”
“Okay” kawai Abban yace, dan sauri yake yi, yayi gaba ya bar su a wajen.
Murmushi Auwal yayi kafin ya dawo dai dai setin Sakina inda ta kawar da kai ta mayar da fuskarta ta, yace
“For this surprises sake za a d’an kula ni ko? Na wuni d’aya tak dai?
Ya k’arashe maganar yana karyar da wuyanshi sannan ya maida fuskarshi kalar tausayi.
Kallonshi tayi, bakinta na d’an motsi, tana son yin magana amman yanda idanuwanshi ya sarke da nata ne, ya sanya ta kasa cewa komai.
A hankali ya lumshe idanunsa ya sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciyar da har sai da ta jiyo hucin numfashinsa mai d’umi wanda ya had’e da wani calm scent da kuma k’amshin turarenshi.
Tana shirin d’auke idanunta daga kan kyakkyawar fuskarshi, ya bud’e idanunshi cikin hikima ya sake yin nasarar sark’e kwayar idanuwan nasu waje d’aya, a hankali taji yace “I love you!”.
Gabanta ne ya bada wani ‘Dumm!! Da masifar k’arfin da bata san dalili ba.
Da kyar ta aro jarumta ta yafa, da mugun k’ok’ari tayi nasarar zare kwayar idanunta a nashi k’irjinta na ci gaba da dukan uku uku. Harara ta zabga masa, ba tare da ta yarda ta sake kallon cikin idanunshiba had’e da yin tsaki sannan ta juya da mugun sauri zata shiga ciki..a ranta tana aiyyana. ‘Tabbas Auwal tantirin shed’an ne!’ Dan gashi yana k’ok’arin rusa mata tsari cikin mintunan da basu gaza ashirin ba.
Da kyar ya iya had’a kuzarin da ya bashi nasarar shan gabanta, ya tsaya a bakin k’ofar, dan ba k’adan ba jikinshi yayi mugun yin weak! Da sauri ya had’a hannuwanshi biyu waje d’aya kafin yace
“I’m sorry? so sorry ba zan k’ara ba. Please lets just.
Bari in kira wanda na san zai yi, a Kano yake yanzu nan zai zo, professional ne, okay?”
Ya k’arashe maganar da alamun serious a kan fuskanshi, yana mai d’aga mata gira duka biyu da d’an ware ido.
“Unhm”. Kawai tace sannan ta koma gefe tayi folding hannayenta tana kallon wani waje.
A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya, ya fara k’ok’arin dialing number mai hoton….
A gabanta suka yi waya sukai fixing time @5:00 pm Zai k’araso, nan da 2 hours kenan.
Suna gama wayar tace “thankyou” kawai sannan ta fara k’ok’arin wucewa.
A hankali yace
“Am, Sakina… i”.
Da sauri ta d’aga mishi hannu d’aya, alamar (stop). Kafin tace “Ya Auwal please. Ka kyale ni!
Ba na so!. I’m in a very serious relationship, besides ko ma bana dating d’in kowa I will never ever choose you! After what you did to Jalila kuma still ka ke dodging. Kullum ko sunan ka naji an kira abunda nake tunowa kenan! Ban shirya auren bazawari ba, ko da ace maza sun k’are ina rok’on Allah kar ya d’aura min k’addarar auren bazawari second hand.”
Auwal bai san san ya akai ba, amman tabbas kamar hawaye yake ji suna shirin zubo mishi.
Ita kanta Sakinar ta lura da yadda idanunshi suke kyallin hawaye. Jikinta ne ya d’anyi sanyi dan haka ta yi k’ok’ari ta danne ragowar maganganun da take ji suna taso mata.
A hankali yace, “Sakina na rantse miki da Allah a yanda nake jin ki a cikin zuciyata, ba abunda ba zan iya sacrificing akan ki ba, kuma babu abunda ba zan iya yi a kanki ba, zan iya chanja kaina in koma yadda kike so na zama, muddin zaki yarda da ni. I don’t know how why but ni kaina ina jin tsoron kalar k’aunar da nake yi miki! I just knew you but i have fallen head over heels.
Na tabbatar ba wanda ya tab’a yiwa wata kalar pure love d’in da nake yi miki. Ba wai wani abu daban ba kawai k’aunarki, yardarki, soul d’inki shi nake muradi.” Ya k’arashe maganar cikin karyewar zuciya.
Shiruu, tayi kawai tayi k’asa da kanta, bata k’aunar abunda zai sa ta sake had’a ido da shi.
A hankali tace “Ka rabu da ni! Dan Allah.”
Yana shirin yin magana Arshaad ya bud’e k’ofa Hudan na a bayan sa. Juyawa Auwal d’in yayi aka hau kallon kallo.
Arshaad ne ya katse shirun ta hanyar mik’awa Auwal hannu suka yi musabaha, a hankali Hudan ita kuma ta gaidashi.
Yana amsawa ya wuce ya nufi part d’insu yana ji kamar zuciyarshi zata fashe! Tabbas ya san ba komai ke binshi ba sai hakki..Hakkin y’an matan da ya yaudara, da waenda ya wulak’anta, da waenda yayi mocking soyayyar da suke yi mishi! Duk hakkin su ne yake binshi. Yayi mocking soyayya, ya yaudari dayawa ta hanyar kalmar soyayya, ya wulak’anta dayawa dan sun nuna mishi zallar soyayya, shiyasa shi kuma yanzu Allah ya d’aura mishi tsantsar so mai mugun zafi da azabtar da zuciya wanda ya san wadda yake yi wa ba lalle ta soshi ba, gashi yanzu ma direct ta fad’a mishi ‘she’s in a very serious relationship’ wanda hakan sai da ya kusan kasheshi ba tare da ta lura ba.Daman haka so yake? Dama haka mutum yake ji? Tabbas shi kam ya san ajalinshi..dan muddin Sakina bata yarda dashi ba akwai matsala! Ranar kuwa da akace ta auri wanda take ik’irarin suna tare d’in ya san a ranar zai bar duniya. Yana wannan lissafin da tunanin ya k’arasa b’angarensu, direct side nasa ya nufa, yana zuwa ya rufe ko Ina ya k’ara k’arfin ac ya zxube a kan kujera, ko d’aki kasa k’arasawa yayi.
Hudan ta bud’e baki kenan zata yi magana Sakina tayi sauri ta wucesu ta shige ciki.
Direct sama d’akin Hudan ta nufa, ta dad’e ta kusan awa d’aya tana juyi a kan gado ita kad’ai, daga baya ta hak’ura ta sauk’o. Suna zaune suna hira su Sudais suna gefe suna chess,tun da suka dawo daga karb’o gown d’in ta (Hudan) wadda delivery man ya kawo suke zuba idon ganinta amman bata sauk’o ba, Hudan taso zuwa amman Arshaad ya hanata. Sakina bata dace da Auwal ba at all, amman in haka Allah ya tsara basu da damar shiga tsakani, besides yayi mamakin changes d’in da yake gani a Auwal those days, maybe in ya samu wadda yake so ya aura a samu ya nutsu! Ko a office yanzu ya daina biye biyen matan da a daa yake yi kamar bunsuru. Arshaad, yana wannan tunanin yaji sauk’owarta dan haka ya juyo yana kallon yanda take tafiya a hankali kamar ba Sakina ba. Cikin kulawa yace, “Sai yanzu?”
Murmushi tayi ta ce “Bacci ne ya kwashe ni”
Shima murmushin kawai yayi, Hudan kuwa bata ce mata uffan ba. So take sai sun keb’e tukunna
dan tabbas In tunanin ta ya bata dai dai to Sakina tana k’ok’arin rufta kanta inda dai dace ba.
Suna zaune Auwal ya shigo, kujerar da Sakina ke kai 2 seater yaje ya zauna ya fara yi mata magana k’asa k’asa. Ga mamakin Hudan sai taga Sakinar ta biyeshi, suna ta k’us k’us daga baya kuma ta mik’e ta cewa Hudan “ta zo taji”, shi kuma ya mik’e ya juya ya nufi hanyar fita. Binta Hudan tayi, suna kaiwa hanyar bene ta rik’o hannun Sakinar wadda ta fara taka stairs. Juyowa tayi tana kallon ta, k’asa k’asa Huda tace
“Sakina kar fa ki biyewa Ya Auwal! Naga kamar ya fara cin galaba a kanki. Kin san Allah kuwa dan iska ne!
Ranar da muka je Munjibir park baki ga y.a”
Da sauri Sakina ta matsa kusa da ita ta sa hannuta ta toshe mata baki! Tun lokacin da Hudan ta fara magana taga tahowarshi, tana so ta hanata taga ya sa hannu ya d’aura akan lips d’inshi alamun tayi shiru yana d’an murmushi. Bama jin Hudan take yi sosai ba saboda gabad’aya hankalinta ya tafi wajenshi sai da taji tana neman b’aro musu aiki tukunna. Kallonta Hudan take, tana “hum um hum um”. Alamun ta saki mata baki. Ganin tak’i barinta ya sa ta sa hannu ta janye hannun Sakinar akan bakinta kafin tace “Dan na fad’a miki gaskiya shine kike k’ok’arin kasheni? Har da hancina fa kika toshe. Kin san Allah, tou su Ummu zan gayawa dan ba zai yiu inaji ina gani ki kula d’a is…” Da sauri Sakina tace “Shhh, behind u.”
Tsit! Hudan tayi kamar ruwa ya cinye ta, a hankali kuma ta juya. Karaff! Suka had’a ido da Auwal, yana d’an murmushi yana kallonsu. Hudan ta san gaskiya ta fad’a, amman sai ta tsinci kanta da jin mugun kunyar shi. Juyawa kawai tayi ta haye sama, Sakina kuma ta tsaya, ta fad’a mishi amsar abinda ya manta bai tambayeta ba, har ta kaishi ga dawowa.
Bata dad’e da shiga ba Sakina itama ta shigo. A parlournta ta sameta, dan haka ta zauna akan hannun kujerar da take kai kafin tace “Hudan, dan Allah ki daina had’a ni da wannan mutumin, na fad’a miki ba zan tab’a sauraron sa ba, infact kin san ina da wanda zan aura ko?. Kinaso ki san maganar me muke yi?”
Sai da ta d’an k’uraa mata ido, tukun tace “Eh”
Murmushi Sakina tayi kafin tace “Zo muje d’aki to ki shirya, in yaso muna sauk’a k’asa zaki gani. Kamar tayi mata musu, sai kuma ta mik’e ta bita.
Suna shiga taga Sakina tana ta fito da kayan kwalliya, aikuwa tace bata san zance ba! Dan in akwai abinda Hudan ta tsana to a shafa mata foundation da concealer, ji takeyi kamar anyi mata suminti a fuska, sometimes har numfashin ta take ji yana d’an yin sama sama, bata tab’a jin iskar gari sai ta wanke.”
Ba kalar rok’on da Sakina bata yi mata ba, amman furr tace “wallahi ba da itaba, ko me za ai sai dai ayi a haka” ita a tunanin ta ma ko wani get together su Sakinar suka had’a, dan tace mata surprise ne suka had’a musu ita da Auwal.
Abunda kawai ta tsaya Sakina tai mata shine, eye lining..da kyar ta yadda ta ja mata liner black a saman ido d’an kad’an, sannan tasa mata brown kwalli. Ko dan bata saba yin kwalliyar ba ga kuma gyaran jiki da ta sha! Ya sanya Inka kalleta ba lalle ka iya d’auke idonka lokaci d’aya ba. Ita kanta Sakina ta kasa yin shiru da ce mata ‘kin yi kyau’. Akwai wani sirrin da idanun Hudan yake dashi wanda bata tab’a gani a idon kowa ba, gashi kuma yau yasha liner da brown kwalli.
Wata zazzafar gown ta d’auko mata black, da ta ji silver stones, sai kyalli take yi. Tun daga k’irjinta zuwa k’asan mararta a tsuke ne daga nan kuma yayi wani irin bajewa har k’asa. Wani fitinennan tauban Sakina tayi mata wanda ya yi mata mugun kyau, sannan ta sak’ala mata wasu arnen silver sark’a da y’an kunne masu shek’i da abun hannunsu da zoben sai silver takalmi ta bata ta saka. Sannan ta d’auki set d’in kaya kala biyu suma duk English Wears kasancewar bata da wasu native masu kyau. Kafin tace “muje suna jira.”
Har ta kai k’ofa taji shiru, juyowa tayi tana kallonta tace “Me ne kuma?”
Hararar ta tayi tukun tace “A haka kikeson in fita da wannan matsarsen rigar?” Ajiyar zuciya Sakina ta sauk’e kafin tace “Hudan ana jiranmu, ga vail d’in nan a jakar nan na had’a In muka sauk’a sai in baki”
Ba don taso ba tabi bayanta suka wuce, dan ta san tunda ta nace tou ba zata bata ba sai sun sauk’an.
Ita kuwa Sakina batayi niyyar batan bane, ta gama rayawa a ranta ‘ko hoto d’aya ne sai anyi musu da wannan shigar’ ita tayi tauban d’in amman ba k’aramin tafiya yayi da imanin ta ba, dan haka bata ga dalilin da zai sa ta bata mayafi ta d’aura akai ba.
Suna sauk’a suka tarar da mai hoton har ya k’araso da yaranshi dan haka suka fara. Da kyar Hudan ta yarda ta tsaya aka yi kala uku da d’aurin daga su ta ware tayi rolling abunta. Styles Sakina ta dinga d’aukowa a insta tana nunawa. Auwal ne yaje har gida ya d’aukowa Arshaad kaya shima kala biyu!
Suite kalar kwanduwar kwai dark da kuma black d’in jamfa na yadi Suite d’in yayi using a last pics d’in da suka yi Ita kuma riga da skirt kalan suite d’in nashi tayi roling da black vail
Sunyi masifar yin kyau!.
Sai bayan Magrib aka kammala.Sun yi hoton har da su Sudais sannan aka yi da Auwal da su Sudais
Abun sai ya zama kamar event a tsakaninsu su shidda dan har drinks da snacks suka d’auko suka d’an cicci suka yi videos a wayoyinsu.
Masu hoto suna tafiya Abba yana dawowa..A parlourn ya samesu har Auwal suna zaune suna kallo.
Sai da mazan suka yi isha tukun suka zagaya gidan Daddy dukkansu aka yi dinner daganan kowa ya kama gaban shi bayan Arshaad ya karb’a ruwan adduar su.
Akwai maganar da yake so suyi da Aslam amman takaicinshi yake ji shiyasa kawai ya rabu da shi ya nufi gida. D’azu babu yadda bai yi da shi akan ya kawo mishi kaya kala biyu ba za ai pre wedding amman k’iri k’iri Aslam d’in ya k’i! K’arshema da yayi ta kiranshi k’in d’aukar wayar yayi.
A parlour ya ga Aaima ita kad’ai tana shan tea akan dining, har zai wuce ta kawai, sai kuma duk yaji ba dad’i tausayinta ya lullub’e shi, dan haka ya koma ya ja kujerar kusa da ita ya zauna.
Bata ce mishi komai ba ta ci gaba da kurb’an tea d’inta. Sai da ya zauna tukun ya fahimci ashe kuka take yi!
Dafe kanshi yayi ya furzar da iska kafin yace “Ok, I’m sorry! Kin b’ata min rain ne d’azu sosai Aaima.
Ba zai yiu ki tsani Hudan haka ba! Za a samu matsala..Hudan ta zame miki dole! Ki ajjiye duk issues d’inku da ita aside, ki manta ki yafe, She’s about to become my wife! Kar ki zama silar rusa zumunci da raba kan y’ay’anmu da naki in the future.”
Murmushin takaici Aaima tayi ta ajjiye cup d’in hannunta kafin tace “Do you know what the funny thing Is?” Bata jira jin mai zai ce ba, tace “Ya Arshaad ban ma san za ka yi aure ba! So i think ba ni ce zan zama silar raba zumunci ba! Kai ne! Infact ka riga ma ka raba dan wallahi ba k’aramin haushi na ji ba ba zan b’oye maka ba. Iya wannan banzatar dani d’in da kayi ya isa zumunci ya samu tangard’a!”
Cikin son fahimtar da ita yace “Aaima, an saka date d’in a k’urarren lokaci. I have a lot to discuss with you, inaso In ganar dake abubuwa da dama kafin In sanar dake shiyasa kika ga ban fad’a miki ba! Issues d’in are all tied up in na gaya miki zan yi aure dole za ki buk’aci Mammy! anan ne kuma za a samu case, na sani.
But I was planning inje in d’auko ki a week b4 daga nan in miki bayani ta yanda zamu fi fahimtar juna..
Mu uku ne kawai Aaima kece mace dan Allah kar ki fara irin haka tun yanzu, please..”
Ajiyar zuciya ta sauk’e, kafin ta kalleshi eye to eye, babu alamun wasa ko tsoro tace “Wallahi!! Muddin Hudan zaka aura to tsakanin mu ba zai yi kyau ba!.” Tana gama fad’in hakan ta mik’e ta bar mishi wajen a fusace…
Sai da ta kai stairs tukunna ta juyo tace, “Ya Aslam bashi da lafiya, Yana side d’insu ana k’ara masa ruwa.
Kaje ka kula da shi pls, shi kad’ai ne, ni kuma yak’i yarda In zauna da shi, sai amai yake yi.”
Har tayi gaba kuma sai ta sake juyowa tace “If Hudan permits.” Bata sake juyowa ba tayi sama abunta.
Ya dade a wajen, tukun ya mik’e ya je ya watsa ruwa ya sa pyjamas ya nufi gidan su Aslam d’in:
Direct d’akin sa ya wuce bayan ya bawa Gwaggo Asabe ruwan adduar.
Akan gado ya ga cannula da bandage da alamun wadda aka saka mishi ce ya cire! Yana shirin fara neman shi ya jiyo shi a toilet yanata shek’a amai. Toilet d’in ya nufa ya tura k’ofar ya shiga. Sai da gabanshi ya fad’i ganin yanda duk Aslam d’in ya fita daga haiyyacinshi cikin wuni guda tak!.
Taimaka mishi yayi suka fito bayan ya yi brush ya wanke fuskarshi. Yana kwantar da shi ya d’auki waya ya kira Doc. Bayan ya ajjiye wayar, cikin sanyin murya yaji Aslam d’in yace “Yanzu fa Doc d’in ya tafi, wanne kuma ka kira?”
Banza Arshaad yayi da shi kawai yaci gaba da had’a mishi tea d’in da ya fara.
After kamar 20min haka, Doc d’in suka shigo tare da Gwaggo Asabe. Sai da ta sa baki tukunna ya yarda ya tsaya aka sake duba shi, dan shi already ya riga ya san me yake damunshi tun kafin zuwan first Doc d’in
kuma baya so Arshaad d’in ya sani. Ba yadda ya iya shiyasa kawai ya kyalesu, bayan y’an gwaje gwaje Doc d’in ya tabbatar musu da ‘jininshi ne ya hau sai kuma fever mai zafi da ta ke damunshi.’
Gwaggo Asabe har da kukanta take ce mishi “Jikin Mommyn fa yanzu da sauk’i Alhamdulillah
Gashi kusan satinshi biyun a gidan amman shiru bata yi komai ba! Ta warke sosai fa, ita abun har mamaki ma yake bata, amman in ta tuna yadda aka duk’ufa akan neman lafiyarta ta hanyar kad’aita Allah shi kad’ai da taimakon ayoyin shi, sai ta ga ba abun mamaki bane ba!”
K’arshema cewa tayi “ya taso suje ko da ta window ne ya lek’a ya ganta, in ba fad’a maka akai ba ba zaka tab’a yarda ma ta tab’a yin rashin lafiya ba! Har waya fa suke yi da Dad”.
Shiruu, kawai Aslam d’in yayi a zuciyar shi yana godewa Ubangiji, sannan yana adduar Allah ya kawo ranar da zata warke baki d’aya su zauna inuwa d’aya shi da ita.
A d’akin suka zauna bayan Doc ya tafi, shi Aslam har haushi ma suka fara bashi dan sai kace wani jariri haka suka maidashi wai duk dan Doc yace kar a barshi da damuwa ko loneliness.
Sai wajajen 11 Arshaad ya k’arasa karatunshi shi da Aslam da Gwaggo Asabe tukun yayi musu sallama ya tafi bayan ya tabbatar Aslam din ya sha .
Dariya Arshaad yake bawa Aslam, shi ala dole fushi yake yi dashi wai akan yak’i fad’a mishi damuwarshi dan ko kallonsa ma baya yi amman kuma shi yayi jinyar shi yanzu.
Arshaad, ya fito kenan a babban parlourn suka had’u da Jalila, yayi matuk’ar mamakin ganin yanda ta rame. Bai kula ta ba ya d’auke kai kawai ya yi wucewarshi, ga mamakinshi shi kawai yaga tasha gabanshi ta tsaya.
Tamke fuska yayi kafin ya tsareta da lumsassun dogayen idanuwanshi cikin dakakkiyar murya yace
“Jalila!” Jin yanda ya kirata, da yanayin data ganshi ya mugun tsoratata dan haka ta kasa magana ta kasa cewa komai chaaan! Kuma sai ta hau kame kame tana wasa da y’an yatsunta “Em, Ya Arshaad wai dagaske Gwaggo Asabe take?” “Da gaske take me?”
“Maganar aurenku kai da Huda…” Sai kuma ta fashe da kuka.
Da mamaki yake kallonta kafin yace “Eh” Kawai ya juya ya fita dan ya san indai ya ci gaba da tsayuwa Inuwa d’aya da ita tou tabbas za a samu matsala! Ya san babu kyau ka tsani d’an uwanka musulmi but he cant help it! Wallahi tunda yake a rayuwarshi bai tab’a jin tsantsar tsagwaron tsana kalar wacce yake yi wa Jalila ba.
Da gudu tayi hanyar d’akin ta tana zuwa ta dannawa Umma kira! Ko gaisawa bata bari sun yi ba ta fara magana “Umma, Huda aure zatayi! Ya Arshaad zata aura. Umma wallahi mutuwa zan yi in ya aureta
Umma dan Allah kiyi wani abun, wallahi ina sonshi.”
Cikin katseta Umma tace “Dalla malama ki tsaya ki nutsu kiyi min magana yanda zan fahimceki”
Cikin kukan jalilan ta hau yi mata bayani tiryan tiryan akan yadda taji Gwaggo Asabe
suna maganar auren ita da wata mai aiki satin baya daya wuce data tambayeta kuma ta gasgata mata hakan
sannan yanzu ma Arshaad d’in ya sake tabbatar mata.
Cikin b’acin rai Umman tace “Kece ai Jalila da shegen son abunki! Nace miki ki kawo kud’i kin k’i ki bayar ya kikeso in yi? Babanku ma yanzu haka baya nan ya gudu saboda ba zai iya rayuwa ba Maryam ba!
Ga Ja’afar ba lafiya! Ga Junaidu ya b’ata! Matsalalo gasu nan burjik sunyi mana yawa ke kuma kin matse bakin aljihu ya kike so inyi???.
Ni kaina sai na mutu dan bak’in ciki in dai Huda ta auri Arshaad d’innan ba ke kad’ai ba!
Haba dan Allah mana sai kace su kad’ai Allah yake so?? Baban ta mai kud’i sannan ta auri mai kud’i!
Inaa, ba zai yiu ba gaskiya!”Umman ta k’arashe maganar cikin tsananin tashin hankali.
Cikin kuka Jalila tace “Umma yanzu meye abun yi? Dan Allah karta aure min shi wallahi Umma ina son Ya Arshaad sosai.”
Ajiyar zuciya Umman ta sauk’e kafin tace “Ki bani kud’i! Ki turo kud’i! Ki zuba mini ido kawai,
shine abun yi.” A hankali Jalila ta sauk’e ajiyar zuciya kafin tace “Tam shikenan,
Ta accnt d’inki ko?”. “Eh” Kawai Umman tace saboda tsantsar tashin hankalin da take ciki
ba zai iya barinta tayi magana sosai ba.
“Tam” kawai Jalila tace ta kashe wayar daganan ta tura mata ragowar kud’in accnt d’inta
da ta ishi Auwal, ya tura mata da kyar.
Bayan Arshaad ya tafi sun d’an tab’a hira tukunna Gwaggwo Asaben tace “itama bara taje ta bawa Mommy maganin nata ta sha ta shaafa dan yanzu ita take yi da kanta” Har ta yi gaba sai kuma ta juyo tace
“Ka zo muje kaga jikin nata mana”. Ahankali ya girgiza kai kafin yace “Gwaggo na san da sauk’i tunda gamu waje d’aya amman lafiya, kuma kin ce tayi garau yanzu to ai Alhamdulillah! Inaga ba sai na je ba, kar
muje a samu matsala.”
Shiruuu, Gwaggo tayi. Ita har ga Allah so take Aslam d’in yaje ya ga Mommy watak’il In ya ga ta warke shima ya samu ya rage damuwar da ta hau kanshi.
Amman tunda taga baya so bara kawai ta kyaleshi.
Ganin dayayi kamar bata ji dad’in musun da yayi mata bane yasashi mik’ewa kafin yace
“muje to”
Murmushi ta saki tace “Yauwa d’an albarka, muje.”
Itace a gaba shi a baya. Haka suka nufi saman ba don ranshi yana soba gashi k’irjinsa In banda dukan uku uku ba abunda yake yi. Wutar parlourn a kashe suka tadda, suna k’ok’arin kunna flash d’in wayoyin su haske ya gauraye ko Ina! Bata lura da shi ba tace, “Yanzun fa nake shirin kiranki na jiki yau duk shiru!
Sai kuma nace bara in yi wanka kafin ki zo, kin ga banma ida shiga d’akin ba naji motsinki.”
Tana maganar tana tahowa garesu. Aslam mutuwar tsaye yayi! Dukda a cikin zuciyarsa hamdala yake yi na ganinta a hakan, amma kuma bayaso suyi ido biyu dan bai san ya zata kaya ba! Hakan ne yasa shi fara ja da baya dan barin wajen Ita kuma kamar ance ta d’ago karaf! Suka yi ido biyu da ita. Ta k’uraa mishi idanu ko kiftawa bata yi tana kallonshi kamar da mamaki akan fuskarta…
Lura da hakan da Gwaggo Asabe tayi ne wadda itama ba k’aramin firgice ta shiga ba ya sanya ta daure taje ta fara jan hannunta tana “Muje ga tofin naki kisha In kin fito wankan sai ki shafa ko?”
A hankali suka ji Mommy tace “Aslam!” Aslam wanda already ya juya da niyyar tafiya har ya d’aga k’afar shi jin ta kira sunanshi ya sanyashi dakatawa ba tare da ya sauk’e k’afar shi ko ya juyo ba! Sai da ta sake cewa
“Aslam” Tukunna ya ajjiye k’afar ya juyo yana kallonta da idanuwanshi da suka rine lokaci guda!.
Dafe kanta tayi da k’arfi, ta runtse idanuwanta kamar mai son tuno wani abun. Ganin haka yasa Gwaggo Asabe ta sake kamo ta kafin ta ce mata. “Muje ki huta dan Allah” Sannnan ta baya ta yiwa Aslam d’in alamar ya tafi da hannunta.
A hankali Mommy ta bud’e idanunta tana sake kallonshi kafin tace “Asabe me ya faru da ni?
Kin ce nayi rashin lafiya meye ne ya sameni? Na shekara nawa?. Kinga fa Aslam, kina ganin abunda nake gani kuwa? Shekara ta nawa a kwance? Dan Allah kimi…..”
Gigitacciyar rungumar da Aslam wanda ba suba tahowarshiba, yayi mata ne ya sanya ta kasa k’arasawa…
Tana shirin yin magana taji Gwaggwo Asabe ta fashe da wani irin kuka mai ban tausayi cikin kukan banda kalmar “Alhamdulillah!” Ba abunda take ta nanatawa.
Da kyar Mommy ta iya b’amb’aro Aslam daga jikinta, a hankali da hawaye sharkaf akan fuskarta ta shafa fuskarshi wadda ta koma jajir kafin tace “Loosing memory nayi ko?” Ta fad’i hakan
tana mai fashewa da kuka.
Rasa wanda zai rarrashi wani akayi tsakanin ita da Gwaggo Asabe. Aslam kam banda ajiyar zuciya ba abunda yake sauk’ewa! Shi kanshi yau so yake hawaye ya zubo ta idanunsa amman abun ya gagara!
A hankali ya cika mata hannunta dake cikin nashi ya dan jaa da baya kafin ya seseta gabas ya durk’usa yayi sujjada! Da sauri itama Gwaggwo Asabe tayi sujjjadar, ita kam Mommy tsayawa tayi tana kallonsu tana hawaye da mamakin abunda ya sameta haka. Wani abun mamakin still shine yanda ta kasa tambayar inda Aslam d’in yake har sai da ya baiyyana a gabanta! Wanne irin loosin memory tayi haka ita kam? Aslam wanda ta san shekarunshi basu wuce 12 ba shine yanzu haka wanda ta tabbatar yafi 30!
Daman tun kwanaki 7 da suka wuce tayi noticing yanda Gwaggo Asabe tayi aging da kuma ita ma kanta!
Mai ya faru?
Wanne irin ciwo tayi haka? Innalillahi wa inna ilaihirrajiun Allahumma ajirni fi musibati.
Take ta maimaitawa cike da rud’ani da alajabi gaba d’aya kwanyarta ta cunkushe.
A hankali Aslam ya mik’e ya kama hannunta suka shiga d’akinta ya zaunar da ita kafin yace
“Ina yake miki ciwo, yanzun?” Murmushi tayi ta shafa fuskarshi a hankali tace “Ba ko ina”
Sai kuma ta sake fashewa da kuka. Hugging d’inta kawai yayi yana tapping bayanta.
A hankali ya d’auko wayarshi, ya hau kiran Dad video call, bai damu da time ba.
D’auka Dad yayi suka gaisa yana tambayarshi “ya shirye shirye na bikin su Arshaad?” A hankali Aslam yace “Alhamdulillah” Sai kuma ya gyara zamanshi ya matsa kusa da Mommy ya kamo hannunta cikin nashi ya d’an kalleta yayi murmushi yana ganin yanda ta k’urawa Dad d’in ido, kafin ya juyo ya kalli Dad shima yace, “Alhamdulillah Dad..” Bai ida rufe bakinshi ba, yaji Dad d’in ya saka kuka, cikin kukan shima yace
“Alhamdulillah!
Alhamdulillah!!
Alhamdulillah!!!”
Sannan yace “Aslam ganinan zuwa yanzun nan, in shaa Allah”. Da sauri Aslam d’in yace
“No dad, kabari sai gobe yanzu dar.” Kit! Dad ya kashe wayar ba tare da ta tsaya jin maganar Aslam d’in ba.
Anan aslam ya zauna, ya rik’e mata hannu gam kamar ance za a kwace mishi ita! Sai kallonta yake yana murmushi yana sauk’e ajiyar zuciya in yaji hakan bai mishi ba yasa hannu yai hugging d’inta.
Ita ma Gwaggo Asabe a daren ta kira Yaranta duk biyun ta fad’a musu halinda ake ciki, murna a wajensu ba a magana, suka ce “in shaa Allah, za su tambaya. Za su taho suma in shaa Allah.”
A haka Mommy ta sha addu’o’i ta shafa da hannu d’aya dan Aslam yak’i cikata, Gwaggo Asabe tana musu dariya tana kuka at the same time.
Ko cikakkiyar awa biyu Dad bai yi ba, sukaji tsayawar mota. Aslam ne yace “Oh Dad, dana sani da ban fad’a mishi ba. Waye ma ya d’auko shi a airport d’in sai Allah tunda gashi bai kira ni ba.”
Murmushi Gwaggo tayi kafin tace “ai ko kaine a matsayin shi na tabbatar sai ka zo”
Murmushi shima yayi kafin yace “Kuma fa hakane”
Cikin minti goma ya iso cikin d’akin! Yadda ya gansu a zaune ne yasa hawayen da yake ta koma run yaga ya danne suka samu nasarar zubowa. A hankali ya k’araso ya had’asu waje guda ya rungume. Shi kuka Mommy da kanta ya d’aure da komai kuka Gwaggo Asabe ma kuka. Da kyar Aslam wanda duk ya fi su son yin kukan ma ya samu ya lallashesu, daga nan aka hau murna k’arshe dai ba wanda ya runtsa a cikinsu har asuba.
Kafin gari ya gama wayewa kuwa, labari yaje kunnuwan kowa a estate d’in, har su Abba.
Daga masallaci Arshaad ya biyo Aslam suka zo tare dan ya ganewa idanuwanshi, ai kuwa shima har da kukan shi na tsananinfarin ciki.
Haka shima Auwal yazo da daddare tare da Daddy da Abba duk a b’oye kar e ya gansu.
Sun ji dad’in ganinta kuwa, sukayi barka suka tafi .
Mommy kuwa tunda aka bata labari sannan taga su Arshaad da Aaima yadda
suka girma da shi kanshi Aslam d’in, ta shiga alhinin ‘shikenan tayi missing teen age d’insu, da yanda suka taso kenan har abada?’ Gabad’aya tausayin kanta da Aslam d’in sai ya lullub’eta. Da kyar ta iya cin abinci, in banda kuka ba abunda take yi, tun ba ma da Dad ya gaya mata irin abubuwan data dinga yiwa Aslam d’inba, da irin rayuwar da yayi, gaba daya sai ta sake birkice musu, tana kuka tana cewa Aslam do yayi hak’uri ya yafe mata. K’arshe dai barin gidan ma yayi dan ba zai iya tsayawa tana kuka haka tana neman gafarar sa ba bayan ya san ba laifinta bane ba.
Dad kanshi kasa zama yayi sai gidan su Abba yaje, ya d’an zauna yana dana sanin fad’a mata d’in da yayi.
Sai dare aka samu damar kaita wajen Granpa, dan Gramma ita tunda taji labari ta taho itama suna tare ranar har dare. Ba yabo ba fallasa ya amsa gaisuwarta ya yi mata ya jiki. Ba abunda yake b’ata mishi rai irin yanda Gramma take ta faman yayatawa cewa “Ai Hudan ce ta bada shawarar yi mata sauk’ar Qur’ani kullum”. Har sai da ya kwab’eta ta hanyar cewa “Ta daina cewa ‘Huda’! Kawai ta dinga cewa
Allah ne ya bata lafiya ya warkar da ita.”
Gramma ta so yi mishi bayani, amman ganin kamar ranshi a d’an b’ace yake kuma ta son ba ya son jayayya yasa kawai tace “In sha Allah, Granpa. Zan gyara.”
Tun daga kan Gramma har Aaima ba wanda bai bada zakka da sadaka ba na ban mamaki! Sauk’a kuwa ba su daina ba ana kan yi dan Dad cewa yayi “zuwa k’arshen watan nan ma in Allah ya yarda aka kammala na Mommy to ba dainawa za ayi ba duk sati sai an yi sauk’a a cikin eatate d’in a tsakanin su, in shaa Allah”.
Yau kusan sati d’aya da warkewar Mommy, har su Hudan sai da suka zo suka yi mata sannu da barka a b’oye da daddare. Mommy tayi matuk’ar murnar ganin Sudais da Shuraim ita daman tana son twins, kuma tunda taji labarin suna da twins a family d’in taketa so ta gansu da su da Huda.
Tunda Mommy taga Huda Allah ya d’aura mata k’aunarta, especially ma da taji gudummawar data bayar akan rashin lafiyarta. Tayi mata godiya yafi a k’irga!
Ita kam Hudan wani tsoron Allah da girman zatin shine ya sake shigarta, tana tunawa ko 2 month ba ai ba ta ganta a hargitse amman kalleta yanzu garau! Tabbas a rayuwa, in dai mutum yana neman sauk’i! Waraka!
Taimako! To kuwa ya nema a wajen Ubangijin Talikai wanda bashi da kishiya.
Da kyar ranar ta barsu suka tafi, ita Huda mamakin ma yanda matar take mata take yi, kamar ta santa tun daa chan amman da ta tuna yanda Mommyn ta bata labarin shak’uwarsu ita da Mama sai tayi tunanin ko saboda Maman ne yasa take yi mata haka. Sannan itama a lokaci d’aya taji girma da k’aunar matar ya shige ta.
A b’angaren Mommy kuwa, kawai tsintar kanta tayi da tsananin k’aunar Huda, dan koda bata kasance y’a ga Maryam ba tabbas Ubangiji ya d’aura mata k’aunar Yarinyar a ranta. Ba abunda yafi sosa mata rai irin da taji cewa ‘an sa ranar ta da Arshaad!’ Saboda ita har ga Allah tun da ta d’aura idonta akan Yarinyar ta fara kwad’ayin ganinta da Aslam d’inta a matsayin maaurata! Amman kuma da ta duba taga abunda yayi Aslam shi yayi Arshaad sai ta hak’ura ta barwa Allah komai sannan ta bisu da fatan alkhairi.