Skip to content
Part 5 of 73 in the Series So Da Buri by Humaira Bulama

Jan hannunta Mom ta yi sannan suka yi sama, suna shiga d’akinta ta ce
“Adama ba fa inda zan je sannan suma babu inda za su je.”

“Na sani”.

Shine abinda Mom ta ce sannan ta fara dube-dube kamar tana neman wani abu.

Drowern gaban mudubi ta kai hannunta ta bud’e, aikuwa ta ci karo da abinda take nema, da sauri ta d’auko littafin da ta gani da biro sannan ta ce “oya d’auko mini takardar gidanki wanda ya baki in kalli signature da wani note haka da ya taɓa rubutawa.”

D’an tsayawa Ummi ta yi tana kallon ta da alamar tsoro a fuskarta.

Ganin haka ya sa Mom ta kawo gabanta ta tsaya sannan tace “I’m just trying to help, ba mu da ishesshen lokaci, ki daina dogon nazari. Besides har yanzu ukune akan ki so don’t worry about one ballantana ma bashi da masaniya, so babu shi a lissafi.

Kowa ya sani a estate d’in nan ke ce weakness d’in granpa, ki duba ki ga abubuwan da yake yi just to make sure u stay happy, I can assure u ba zai bari Abba ya tafi ko ina ba idan ya ga wannan.” ta yi maganr tana nuna mata takardar da ta yaga daga jikin book d’in.

Shiru Ummi ta yi kafin ta ce “Adama I love my husband, ba na so in shiga tsakaninshi da mahaifinsa.”

Wannan karon tsaki Mom ta yi sannan ta ce “Zainab kin fara ba ni haushi wallahi zan yi tafiyata, shiga tsakani kuma na nawa? Waye ummulaba’isin fad’an nasu? Sai da abu ya zo gangara za ki fara tunanin tsame hannunki?”

“To bari kiji! ta inda aka bi aka hau ta nan ake sauk’a, sannan na san Dr Abba farin sani If things get out of control zan yi paying nashi ya maka masa case na memory loss, a ce ya yi for a day ne, a time din kuma ya yi ta misbehaving, sai mu ce a lokacin ne yayi shi kansha kenan bai san yayi ba. Dan mutumin da ya kwana ya wuni bai san inda kansa yake ba ai zai yi morethan this, kuma babu wanda ya isa ya musa.”

Da sauri Ummi ta ce “ok ok” sannan ta nufi wardrobe d’inta ta d’auko key a k’asan tulin kayanta sannan ta saka key d’in a jikin wani d’an k’aramin locker wanda yake nan ata k’asan kayan nata ta murza mukullin ya bud’u. Wani suitcase ta d’auko ta yo kan gadon da shi, a tare suka hau bincikawa har sai da suka d’auko wani file da wata envelope.

File d’in takardun gida ne, envelope d’in kuwa da suka bud’e ta wani had’add’en rubutu ne ya baiyana a cikin da alama wasik’a ce .

Zama Mom ta yi a kan gadon sannan ta saka wannan wasik’ar a gaba ta yi shiruu, ta kai kusan 2 minutes tana k’are mata kallo kafin ta ajjiye ta a gabanta tukunna ta hau rubutu akan wannan blank papern data ya go, exactly handwriting d’in irin na wannan wasik’ar take yi.

Ta d’auki y’an mintuna tana rubutawa kafin ta d’auki dayan file din ta bud’o daidai wajen signature ta kalla da kyau sannan ta ajiye ta yi irinta a k’asan takardaar da ta gama rubutu a kai. Tashi tayi daga kan gadon sannan ta juyo ta kalli Ummi tace mata,

“Done!!”

Mik’a hannu Ummin ta yi ta karb’a ta karanta sannan ta sauk’e ajiyar zuciya kafin ta ce “yanzu ta ina zan wuce??
kin san fa yana falo.”

“D’auko mayafinki,” inji Mom.
Cikin wardrobe d’inta ta bud’e wajen mayafai, sannan ta jawo abinda hannunta ya kai, kai.

Warewa ta yi tana shirin saka hijabin Mom ta ce a’a ba ni nan zan saka a cikin nawa mayafin in fita in yaso sai ki sauko daga baya ki yi kamar kin shiga kitchen, ni kuma zan jiraki a k’aramin compound ta baya, sai ki fito mu wuce.”

Har ta juya za ta fita, sai kuma ta dawo ta k’ara rad’a mata wata magana sannan ta fice.

Yadda Mom d’in ta tsara hakan kuwa aka yi.

Bayan sun fita daga gate d’in gidan suka nufi na Granpa.

Suna zuwa Daniel ya gaida su suka shige suka isa k’ofar main parlor.
Suna shiga kamar kullum suka ga ba kowa, shiruu sai karar A.C.


Ganin hakane ya sa suka nufi kitchen a tunanin su ko za su ga Grandmata yi musu iso amman nan d’in ma ba su sameta ba, sai masu aiki.

Ganin suna b’atawa kansu lokacine yasa Mom ta d’auko wayarta, ta kira Gramma, bugu biyu ana ukun ta d’auka.

“Assalamu Alaiki, Adama.”

Aka fad’a daga d’ayan b’angaren.
Cikin girmamawa mom ta ce “Ameen wa alaiki assalam, ina wuni gramma”

“Alhamdulillah.”

Shi ne abinda gramma ta ce.

Cikin ladabi Mom ta ce “daman yanzu Zainab ta zo ta sameni akan wata magana, shine muke son ganin Granpa, ban sani ba ko yana nan?.”

“Yana nan.” Ta ce, daga haka ta katse kiran.

Kusan mintuna talatin suka yi a kitchen d’in, har sun fara gajiya suka ji k’arar bud’e k’ofa.

Da sauri suka fito a kitchen din daidai k’ofar da take kallon kitchen d’in aka bud’e sosai, wata farar tsohuwa ta fito, ba ta da tsayi sosai amman tana da k’iba, idanunta sanye cikin medicated eye glasses, tana sanye cikin wata royal blue d’in atamfar super xclusive
ta yi d’aurinta irin na tsoffi. A hankali take tafiya tana tunkaro k’ofar kitchen d’in tana yin mitsi-misti da idanu alamun so take ta fahimci su d’inne a wajen domin kuwa dudda glass d’in ba kasafai take iya hango abu idan yayi nesa sosai ba.


LGane hakan da suka yi ne ya sanya suka yi saurin k’arasawa inda take sannan suka d’an rissina suna sake gaida ita. Cikin kulawa ta amsa sannan tace “ina fata dai abu mai muhimmanci ke tafe da ku ba shirme ba, dan kar ku je ku yi ta shiririta, kun san ba yawan son surutu yake ba, yanzu hakan ma da kyar ya yarda zai ganku..”

Takardar hannunta kawai Ummi ta mik’a mata.

Kallonta Gramma ta yi sannan ta sa hannun ta karb’a takardar ta fara dubawa, gyara glases d’in idanunta ta yi da kyau cikin zaro ido kafin ta d’ago ta kalle su sannan ta ce,

“Shi Yakubun ya baki wannan! yaushe!!”

K’asa Ummi ta yi da kanta sannan a hankali ta ce, “shekaran jiya”.

Cikin fad’a Gramma ta ce “kuma to me kika tsaya yi tun shekaran jiya baki zo nan ba?

Ai cewa ya yi ki tafi wajen iyayenki, ko kina da iyayen da suka fi mu ne?”.
Da sauri Ummi ta girgiza kai tana share hawaye.

Cikin tausayawa, Gramma ta kamo hannunta ta rungumeta tana bubbuga bayanta, sai da ta yi shiru sannan tace su je wajen Granpa d’in.

Ta cikin parlourn da Gramma ta fito suka shiga, suka bi ta wani had’add’en staircase suka isa wani tafkeken parlour sannan suka sake bin bene kafin su iso wani had’add’en parlour.

A tsaye suka hangosa gaban wani k’atoton glass wanda gabad’aya bangon wajen glass d’in ne ya cinye ya
juya baya yana kallon glass d’in wanda ta cikin k’atoton glass d’in kana iya hango har compound d’in estate d’in.

Waje Gramma ta nuna musu sannan ta k’arasa gabansa ta mik’a mishi takardar, kafin ahankali ta ce “ga abinda yake tafe da su”.

Ya kusan 2 minutes tukunna ya ce

“Read it loud”

Cikin nutsuwa grmma ta fara karantowa.

“Ni Yakubu Umar Farouk Mai Turare, na saki matata Zainab Umar Farouk Mai Turare, saki d’aya. Dalilin kuwa Ina gudun shiga hakkin aure domin na kasa bata kulawar da ta kamata da waje a zuciyata, ta koma gidan iyayenta ta ci gaba da zama, nima zan tafi nawa gidan, idan ta samu miji ta yi aure.”

Shiru kake ji d’ip! Kamar ba halitta a parlourn. Da farko tari Ummi ta fara a hankali, chan kuma sai ta farayi da k’arfi har da kamar kakarin amai kafin a hankali ta sulale daga zaunen da take akan kafet ta kwanta a wajen.

“Ya subahanallah jini!!!”

Shine abinda suka ji Mom ta fad’a, da sauri Gramma ta yo kansu, itama tana zuwa ganin alamun jini-jini a cikin bakinta yasa a rud’e ta ce,

“Adama mai ya faru?innalillahi wa inna ilaihirrajiun, maza d’auko ruwa ga firij chan ki zo ki yayyafa mata.”

Ruwa aka d’auko aka fara yayyafa mata amman a banza sai ma jinin da yake ta biyo yawu yana dalala a k’asa, Da sauri gramma ta ce maza kira wani a cikin samarin nan ya zo a taimaka a kaita asibiti, da sauri mom ta mik’e sai kuma ta tsaya ta ce “Gramma duk ba sa nan na manta, amma d’azu naga Dr ya zo duba Abba, in kira shi??”

Da sauri gramma ta ce “Eh kira wo shi, Allah ya kawo sauk’i ma ai.”

Nan ta fita Gramma kuma ta cigaba da jijjiga Zainab tana tofa mata addu‘o’i.
Cikin mintunan da basu gaza ashirin ba Mom ta dawo Dr na biye da ita,suna zuwa aka gyara wa Ummi kwanciya anan kan kafet din Dr ya shiga duba ta da kayan aikin da ya shigo da su.

D’agowa ya yi ya kalli Mom sannan yace”tun yaushe ta fara?”

“Bata tab’a suma irin wannan ba gaskiya, sai dai tarin jini kuma ba ya zuwa sosai kamar na yau.”

“Tun yaushe ta fara?”

Doctor ya sake jeho mata tambayar ba tare da ya kalleta ba dan ya duk’ufa ya tarkata hankalinshi duk a kan Ummi burinsa kawai ya ga ta farfad’o.

Kwanaki ta yi a gaba na har sau biyu, na yi mata magana ta ce “wai ta je asibiti an ce ba komai. Yau kuma sau uku kenan har da wannan,shima da naga ta yi ta sake yi na tamabayeta tace mini ba komai fa.”

“Uhhm”

Shine abunda Dr ya ce yana zuk’o wani ruwan allura sannan ya saita jijiyan hannun Zainab d’in ya juye mata shi a ciki ya ci gaba da bata taimakon da ya kamata.

Bayan wasu y’an mintuna. A hankali take bud’e idanuwanta wadanda suka yi jazir, da sauri Gramma ta k’araso gabanta ta fara ƙoƙarin mik’ar da ita tana ta faman jera mata sannu, Allah sarki Gramma duk ta rud’e.

“Doctor mai ka fahimta yana damunta???” Granpa ya yi mishi tambayar yana dogara sandarshi yana mai k’arasowa wajen.

Mik’ewa tsaye ya yi sannan ya zare farin glasses d’in idonsa ya d’an mutsitsika idon ya maida glass d’in kafin ya ce,

“Heart d’inta ke da matsala, and da alamar ya yi serious gaskiya tunda har ga jini, ban san dalilin da ya sanya ta b’oye ba ta gayawa kowa ba, but this is very serious, idan ba damuwa yanzu zan tafi da ita mu yi ECO, saboda mu san matakin d’auka ,dan ba a d’aukar issue na heart irin wannan likely.”

“A wanne asibiti za a sameka?”
Granpa ya sake mishi tamabayar.

Card d’insa ya mik’awa Granpa mai d’auke da suna da address na diagnostic center d’inshi sannan yace “nan waje nane it’s a private place.
I’m a consultant a AkTH, idan hankalinku ya fi kwanciya da chan sai ayi mata a chan d’in, dai nasu zai d’auki time kafin a gama.

“Za a sameka a chan (nakan)nan da 1 hour, get every thing ready”

“Ok sir,” Shine abinda Doctor ya ce sannan ya juya ya fita.

“Let me show him the door” Mom tace sannan ta bi bayan shi.

A hankali ya k’arasa takowa inda suke kafin ya kalli Gramma ya ce mata

“Leave us”

A hankali Gramma ta mik’e ta juya ta fita.

K’arasowa yayi ya zauna a kan kujerar da take zaune a gefenta kadan a kan kafet sannan ya ce, “since when kika yi realizing baki da lafiya??”

“2 years ago” ta ce.

“Wa kika fad’awa?”

“Ba kowa.”

“Mai ya yi causing abun?”

Shiruu ta yi wannan karon.

Zan b’ata miki rai Ummi, kin san ba na son kame-kame da kyaliya.

Hawaye ta share kafin ta ce “Abba ne” cikin sheshshek’ar kuka. Tari ta fara yi sai da ya dan tsagaita sannan ta ci gaba da magana,

“Ba ya bani time d’inshi, kullum cikin zancen Maryam yake, i tried very well inga na daidaita relationship d’inmu amman na kasa, yak’i ya bani had’in kai at the end ma gashi ya zo ya rabu da ni gaba d’aya. Ina ji yana waya da Abokinsa wai ya san idan ya had’amu ni da Maryam ranar lahira da shanyayyen b’arin jiki zai tashi tunda yanzu ya samu chance d’in da zai iya maida ita, kuma wai yana jin tausayina, gara ya sauwak’e mini inyi aure nima in samu wanda zai iya ba ni kulawa tun kafin lokaci ya k’ure. Granpa it’s like har yanzu suna tare a yanayin maganarsa.”

Tana kaiwa nan ta fara tari irin na marasa lafiya, abun tausayi.

A hankali ta ji Granpa ya dafa ta sannan ya ce “ki huta, ya isa haka.”

Waya ya d’auka ya fara lalube sannan da kyar ya nemo numbershi, yabyi mamaki da ya samu number dan ya jima basa waya, ko abu zai fad’a mishi sai dai ya gayawa Dad ya fad’a mishi, ko Abban ya kirashi domin ya gaidashi baya amsawa.

Sometimes kuma ya yi rejecting
shiyasa tun yana kira har ya zo ya daina shima.

Abba yana zaune Sudais yana ta zuba masa surutu ya ji k’arar wayarshi, zaro ta yayi daga aljihun gaban rigarshi ya kalla screen d’in, k’ara kalla yayi ya d’an bud’e idonshi, ganin da gaske ne yasa yayi saurin d’auka had’e da toshe wa Sudais baki “Assa…”

Kafin ya k’arasa sallamar ya ji ance
“Ina falona, ka sameni yanzu” Kit!! Ya ji an kashe wayar.

Mik’ewa ya yi a take sai dai da kyar k’afafuwansa suka iya d’aukar sa saboda sanyi da rawar da suke yi dama kuma ga yanayin rashin lafiyar da yake ciki.

Ajiyar zuciya ya sauk’e, ya tattaro dukkanin kuzarinsa sannan ya fara tafiya a hankali domin amsa kiran mahaifin nashi.

Gaban Ummi ne ya fara dukan uku uku gashi Mom bata kusa, duk da suna da mafitar abinda za su fad’a amman hakan bai hanata jin tsoro ba, da kyar ta samu ta saisaita kanta gudun kar Granpa ya fahimci wani abu, duk da ta san shi ba mutum ba ne mai zurfafa bincike iyakar abinda akai akan idanunsa da shi yake aiki sannan bashi da time d’in bibiyar abinda bai shafe shi sosai ba above all ya yarda da Ummi yana ji da ita sosai ba ya son abinda zai b’ata mata rai ita kad’ai ce in abu ya shafeta yake sawa ya sauk’o daga dokin zuciya, tana cikin wannan tunanin suka ji sallamar Abba.

Granpa ne ya amsa sannan ya ce ƙaraso ciki.”

Shigowa ya yi, sannan ya k’araso inda ya ga Ummi a zaune ya nemi guri ya shima ya zauna a d’an gefenta kad’an.

“Barka da yamma”

Shi ne abinda Abba yace da Granpa, kan shi na kallon k’asa.

Juyowa granpa ya yi ya kalle shi sannan ya ce “ai ban yi tunanin har yanzu ina da darajar da zaka gaidani ba.”

Bai jira jin abinda zai ce masa ba ya d’aura “bara in baka wani gajeran labari, duk da na san ka sani amman bara in sake maimaita maka.”

Mik’ewa ya yi yana dogara sandarsa ya koma wajen da su Ummin suka shigo suka same shi d’azu ya tsaya yana kallon waje, a hankali ya fara magana.

“Asalina d’an k’asar Chad ne, mahaifin mahaifiyarmu ma haka, sai dai mahaifiyarta ce ta fito daga yankin Niger, Agadaz.

Mu biyu iyayen mu suka haifa a duniyar nan, da ni da d’an uwana, gudun hijira ya sanya muka baro k’asarmu ta haihuwa, domin a lokacin har kakanninmu sai da aka kashe da kyar muka tsira, kasancewar Fulani bamu da yawa a yankin ya sanya aka yi galaba akanmu.

A lokacin ina da shekaru tara a duniya d’an uwana kuma yana da 11, tun a hanya na lura mahaifin mu bashi da lafiya, da na tambaye shi sai yace mini gajiyar tafiya ne.

Yanayin gudun hijira ba abu bane mai sauk’i don ko ruwan da mutum zai sha ma aikine.

Mahaifin mu ya zab’a mu bi ta Agadaz domin mu duba ko zamu had’u da dangin mahaifiyar mamana ko zasu taimaka mana akan mu tafi garin da bamu san kowa ba. Mahaifiyarmu ta so yin tirjiya akan gara mu bi ragowar mutanen rugarmu wadanda suka yi saura, saboda ta san a wannan lokacin danginta kowa yayi nashi wurin sannan y’an uwanta idan ma za ta samu yanzu mutun d’aya ce, wadda take aure a chan, don mahaifiyar tata su uku aka haifa a gidansu kuma itace auta, babbar yayyarsu a ghana take aure.

K’in yarda da zancenta da mahaifinmu ya yi ne ya sanya muka nufi Agadaz
Amma sai muka yi rashin sa’a muna zuwa aka tabbatar mana ciwon k’afa ya kamata an kaita Yemen neman magani.


LDa kyar wani makwafcinsu ya bamu gurin kwana da abinci mu kai wanka da safe muka nufi Marad’i, don Yemen akwai nisa sannan babu ko sisi a wajenmu, da yake mahaifinmu ya tab’a zuwa daura ya sanya shi cewa mu zo Daura ko Marad’i in yaso idan ya d’an samu aiki yayi ya tara kud’i daga baya sai mu tafi Yemen d’in mu dubo ta.

Kasancewar hanyar Sahara ce ko ina,ya sanya muka wahala babu ruwa babu abinci kowannenmu idan ka kalla a wahale yake, shiyasa da zaran mahaifinmu ya nemo d’an abinci ko abun sha sai ya ba mu mu ci ya ce mana shi ya ci a hanya saboda yana gudun kar wani abun ya same mu dan a ganinsa laifinshi ne saboda babu yadda mahaifiyar mu ba ta yi da shi ba akan mu bi tawagar y’an hijira mu gudu tare amman ya k’i.

A lokacin naga amfanin ilimi domin da muka k’arasa Marad’i babu wanda yake jin yarenmu, sannan muma bama jin nasu, sannan bama jin turanci ballantana mu yi communicating da su.

Haka nan muka kwana a y’ar kasuwarsu da kyar mai k’osai ta bamu sadaka muka ci, da safe muka samu wanda zaije Daura ya tausaya mana muka bishi a motar katakon shi (kiya kiya).

Ga wahala ga yunwa ga kuma yin tafiya mai nisa a kiya kiya a wannan lokacin ba dadi .

Tun kafin mu k’arasa mahaifinmu ya fara jijjiga idanunsa suka k’akk’afe, muna isa garin aka taimaka mana muka yi asibiti da shi, ba a jimaba Allah ya karb’i ransa ta sanadin rashin abinci likitoci suka tabbatar mana da cewa ya shiga hypoglycemia ne, sannan bai samu taimakon gaggawa akan lokaci ba.

A lokacin bamu san kowa ba, ganin haka yasa Likitan ya nemo mutane aka sallaci mahaifin mu aka kaishi gidanshi na gaskiya, bayan ya tabbatar da mu Musulmai ne.

Bayan an dawo daga mak’abarta lokacin tafiyar sa gida yayi still ya ga bamu da niyyar tashi, dan haka ya zo ya sami Mamanmu yace mata idan ba damuwa mu bishi gidanshi, kafin a san ya za a yi.

Muna isa gidan kuwa matar sa tace ba za ta rik’e mutum uku ba sai dai a kaimu gidan marayu da ni da d’an uwana In yaso ita mamanmu ta dinga mata wanke wanke da shara.

A lokacin rigima ce ta b’arke tsakanin Likitan nan da matarshi, domin ita ta ce ‘ba za ta rik’e tsintacciyar mage ba ai ya ma yi sa’a da ta yarda za ta d’auki Maman namu aiki’.

Shi kuma ya dage akan sai mun zauna ai daman ba yau ta saba yi mishi irin haka ba!

Taya yana miji amman ita ace ita za ta dinga zartar da hukunci.

Rigima suka hau yi sosai, har ta kai ya fara ik’irarin rabuwa da ita.

Ganin hakan ya sanya Maman mu ta ce, ta yarda a kaimu gidan marayun In yaso idan ta yi aikin ko na wata hud’u ne ta d’an tara kud’i sai ta fara sana ‘a taje ta d’auko mu ta kama haya.’

Hakan kuwa aka yi muna kuka muna komai aka kaimu gidan marayu.

Maman mu mace ce da baka iya gane tak’memen abun da yake cikin zuciyar ta amman zan iya cewa a wannan lokacin na ga tsananin tashin hankali da k’unci a fuskarta domin kuwa itama harda kukanta.

Every weekend take zuwa ta dubo mu
A lokacin ne kuma yayana duk da k’arancin shekarun shi ya dage wajen koyan sana‘a, dan zan iya cewa duk wata sana ar da ake koyarwa a gidan marayun nan babu wadda bai iya ba, ba ya isheshen bacci kullum cikin aiki, idan nace mishi ya huta yakan ce mini ‘ba dan kan shi yake yi ba, saboda ni da mama yake so ya yi sana’a ya tara kud’i ni da shi mu koma makaranta sannan ya siya mana gida.’ A kullum maganarshi kenan.

Tun muna Yara mun kasance masu tsananin k’aunar juna, soyayyar da yayana yake yi mini ba kad’an bace ba, ba ya son ya ga rai na a b’ace duk da kuwa ni d’in na kasance miskili ne amman in dai ina tare da shi sai ya san yadda yasa na ware sosai saboda baya bari na ma har sai ya ga ina dariya.

Kamar yadda mahaifinmu ya dinga sacrifice yana bamu abincin da ya samu (lokacin gudun hijira) haka shima ya dinga yi mini a gidan marayu, gashi ya hanani aikin komai, shi yake had’awa nawa da nashi ya yi, zan iya cewa ni kam ban san wahalar gidan marayu ba kwata kwata.

Mun shafe wata uku a gidan Marayu muna neman shiga na hud’u.

Ranar wata lahadi muka tashi mu kai wanka da sassafe muna jiran mahaifiyarmu, kasancewar ranar zuwanta kenan amman har yamma bata iso ba, sai da daddare wannan Likita ya zo ya tura aka kira mu. Muna fitowa da ya had’a idanu da mu kawai sai naga ya fashe da kuka, da sauri muka k’araso gabanshi muka hau tambayarshi amman sai bai amsa mana ba kawai ya cewa shugaban wajen ya yi checking namu out zai tafi da mu.

Sai da muka je gidan nasa muka gane dalilin kukanshi, ciwon zuciya mahaifiyarmu take fama da shi tun watanni uku da suka shud’e tanata nuk’u-nuk’u babu wanda ta fad’awa yau kuma da safe ta yanke jiki ta fad’i jininta yai high sosai, babu irin taimakon da basu bata ba amman rai yayi halinshi.

A ranar kam mun sha kuka iya kuka hatta wannan matar Likita sai da ta tausaya mana.

A ranar sadakar uku ne kuma ta tada balli tace ‘sai dai mijin ta ya nemi wani wajen ko ya kama mana haya mu koma dan ba zai barta da yara maza a gida ba bayan ita mata ne nata kuma k’anana, ai mu maza ne ko aikin k’arfi ne za mu iya mu samu mu rik’e kanmu.’

Hakan kuwa aka yi sai dai kud’in da mahaifiyarmu ta tara bai isa kama haya ba balle a had’a da Sana’a.

Shawara Likita suka yi da yayana aka kama haya shima sai da ya cika mana.
Gefen gidan wata tsohuwa da y’ar jikarta aka kama mana haya, sannan Likitan ya bata amanar mu.

Kasancewar Yayana ya iya sana a kala kala ya sanya yake fita sana a, Allah kuwa ya sanya mishi albarka domin duk abinda yayi ko ya tab’a sai ka ga budi da karb’uwa ta ko ina dukvda kuwa k’arancin shekarunshi, hakan ya sanya masu shago suka rik’esa kowa yanaso ya yi aiki da shi.

A cikin shekaru biyar yaya ya bud’e shagon d’inkinsa, da wajen had’a hula da takalma, da turarurruka, sannan ya koma makaranta nima yasaka ni a makaranta, kuma cikin ikon Allah har gidan wannan y’ar tsohuwa shi yake ciyarwa, domin ta zame mana kamar uwa jikarta kuma y’ar uwa likita kuma ya kan zo duk wata ya duba mu, haka nan muka zama kamar family.

A lokacin da shekaru na suka ja, naje na samu yayana da batun ina so inyi aure don a lokacin ina matuk’ar k’aunar mahaifiyarku, kuma babanta har ya fara shirin maganar zai bata wani d’an uwanta za ai musu aure, to a wannan lokacin shima d’an uwana ashe yana da tashi budurwa harya gama hada kudin lefe da na siyan gida da komai amman ganin yadda hankali na ya tashi yasanya ya bani kudin lefen muka je ya siya mini gida da duk wani abun da za a buk’ata, sannan ya ba ni wajen had’a turarenshi a matsayin kyauta yace in kula da Iyalina da shi.

Both mahaifiyar ku da budurwar da yayana yake nema, y’ay’an masu kud’i ne neman auren su ba abu ne mai sauk’i ba hakan ya sanya da yayana ya nemi da a k’ara mishi lokaci ya sake shiryawa, mahaifin ta ya k’i amincewa bare ma da ya ji k’aninsa zai
yi aure sai ya yi tunanin raina musu hankali yake son yi.

Haka nan yana ji yana gani aka aurar da ita kuma ya b’oye mini don ya san ba zan bari ba shi kuma ya fi son ya fi son farin cikina akan nashi.

Shi ya wuce mini gaba ya tabbatar na auri Maijiddah, likita ya yi mini wakili.

Bayan nan muka ci gaba da karatu da business gadan-gadan, Yaya iyakacin shi masters amman ni har PHD sai da ya tabbatar nayi, ya rik’e gabad’aya companies d’in harda na turare na daya babni wanda a lokacin ya bunk’asa , yace zai iya inje inyi karatun nawa.

Yaya bai yi aure ba, sai bayan shekaru goma mutane sunata gulmace gulmace amman ya toshe kunnuwanshi, saboda shi tunda aka aurar da wacce yake so aure ya fice mishi akai. Sai da na saka baki ni da Likita tukun ya yarda ya yi auren a lokacin har kai an Haifa.

Matar Likita wadda ta dinga korarmu a gidanta itace ta kawo d’aya a cikin y’ay’anta ta ce ‘ta bashi ya aura’.

Don a lokacin Yaya ya yi kud’i na ban mamaki, sai kuma aka yi dace ya yarda don yana ganin ta ta kwanta mishi, sannan kuma ko da ace baya so ya ci ace ya karb’i y’ar Likita a matsayin mata ko dan halaccin ubanta.

Tunda na yi aure nake burin in haifi y’a mace, sannan ina son in saka mata sunan Mahaifiyarmu, amman Allah bai bani ba, da kai da Yusuf da Yahaya Allah ya ba ni.

Bayan auren Yaya kuwa da shekara d’aya aka haifi Zainab(Ummi)
Da ni da Yaya ban san wa ya fi wani sonta ba gashi sunan mahaifiyarmu gareta.

A lokacin ne kuma Yaya suka yi wani accident wanda akai mishi aiki aka tabbatar mana magudanar kwayayan haihuwanshi sun sami matsala, ba zai sake haihuwa ba! Mun girgiza sosai amman kasancewar mu masu tawakkali ne sai muka mik’awa Ubangiji lamuranmu muka rungumi k’addara.

Abu d’aya muka sa a gaba shine faranta ran Ummi, Yaya ya tab’a gaya mini yana neman kud’ine saboda faranta raina da na mahaifiyarmu amman hakan bata faru ba a b’angaren mahaifiyarmu domin mun rasa ta tun kafin ta ji dad’in da muka so bata, shiyasa yayi alk’awarin d’aura dukkan wani gata na duniyar nan akan tilon y’ar sa tunda takwarar ta ce, ya kance idan ya ga Ummi tana dariya gani yake yi kamar mahaifiyarmu ya sanya farinciki, domin kusan halinsu d’aya dan itama Ummi tun tana da shekaru biyu da y’an watanni muka fahimci tana da nuk’u nuk’u da b’oye abu a rai.

Shiyasa ya zama har y’ar rige rige muke ni da Yaya wajen cika mata burinta, muddin ta furta.

Shekararta biyar a duniya Yaya da Likita suka tafi Abuja, a hanyar su ta dawowa suka yi wani mummunan hatsari!! Likita tun a lokacin ya cika sai da aka kawoshi emergency yana ta cewa yana son ganina, a lokacin ina office aka sanar mini ana san ganina a asibiti tun a lokacin gabana ya fara fad’uwa, ina zuwa kuwa a reception aka ce mini ai y’an uwanane suka yi hatsari d’ayan ya rasu d’ayan kuma yana wanchan d’akin aka min nuni da d’akin da Yayana yake ciki.

A gigice na shiga inda yake,ina ganinshi cikin jini nai kanshi da gudu na rik’esa ina kuka. Dukda halin da yake ciki bai hanashi lallashi ba, sai da ya ga na yi shiru tukunnan ya kamo hannuna duka biyu yana d’an tari da nishi da kyar., Kalmarshi ta k’arshe itace, dan Allah dan Annabi ka kula mini da Zainab ka bata duk wani farin cikin da kake da iko ga amanarta nan na bar maka ,sannan ya yi kalmar shahada daga nan na ji jikinshi ya sake idanunsa suna kallon sama.

A lokacin na yi kuka mai yawa dan na rasa rabin jiki na sannan ba ni da kowa ba ni da wani ba ni da elder mai kula da ni. Maraicin sai ya dawo mini sabo fil.”

Hawaye granpa ya share ya gyara tsayuwar shi ya ce “ko mutuwar iyayena ban ji ta ba kamar yadda na ji ta Yaya, na yi alk’awarin faranta mishi ko bayan ranshi ko da kuwa ace hakan zai sanya in karya tawa k’aidar. Ga matarka nan, ko ka san tana d’auke da ciwon zuciya???”

Ya yi maganar tare da juyowa yana kallon Abba wanda ya juya a razane yana kallon Ummi da kamar mamaki a fuskar shi.

Juyawa Granpa ya yi ya ci gaba da cewa, “U won Yakubu, ka yi amfani da weakness d’ina and ka ci nasara a kaina! This time around, zan iya yafe maka laifin da ka yi mini tunda na ga alamar so kake ka dawo da baya yanzu. Komai ya wuce!! Sannan ka rushe maganar tashinka daga estate d’innan babu ita. Abu d’aya zuwa biyu zan baka umarni shine “Ka maida matarka yanzun nan, sannan ka kaita asibiti ga katin nan, Dr yana chan yana jiranku, and kamar yadda na fad’a maka a baya, babu kai ba Maryam, amma in dai har ka shiryawa tsinuwa ta to bismillah ka je ka bibiyi rayuwarta.

                 

<< So Da Buri 4So Da Buri 6 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×