Skip to content
Part 61 of 73 in the Series So Da Buri by Humaira Bulama

Rai a b’ace Ummi ta koma inda Mom take ta rufeta da fad’a.

Ita babu abunda ya fi d’aga mata hankali irin yadda aka jaa Jalila a k’asa despite the fact that she’s pregnant, ai ko ba komai de d’an Auwal ne k’unshe a cikinta!.

Mom bata ce wa Ummi k’ala ba har tayi ta gama ta wuce ciki.

Tana wucewa ta bi bayanta suka bar Hudan a nan tsaye tana mamakin rashin mutunci da rashin tausayin irin na Mom tabbas a wajenta Auwal ya kwaso duk wasu bad habits nasa daga gani kuma ita ta b’ata shi tun farko
dan wannan uwar ba zata tab’a iya yin tarbiyyar da ta kamata a Yaro ba.
Kamar ta bi bayan Jalila haka taji, to kuma kar Jalilan ta ganta tace zata zauna a wajenta taje sabon case ya b’ullo tsakaninta da Mom sannan Mama ta ja mata kunne akan ta fita harkar case d’in Jalila da cikin jikinta da duk wani abun daya shafeta. Shiyasa kawai ta share hawayenta ta wuce ciki tausayi da k’aunar Arshaad suna sake shigar mata zuciya dan maganganun Jalila Mom da Ummi sun sake tabbatar da ciki dai na Auwal ne.

Sai da Ummi ta kusan kaiwa d’akinta tukunna ta lura da Mom na bayanta.
Juyowa tayi tana kallonta kafin tace
“Adama baki da bakin yi min magana yanzu, ba zan saurareki ba dan haka
kawai ki juya ki tafi. In wulak’anci abun yi ne ki je kiyi. Kuma kin san Allah ki guji had’uwar ki da Auwal
saboda duk tsiya dai cikinsa ne a jikinta kika yi mata wannan rashin mutuncin….”

Matsowa Mom tayi tana mai sauk’e ajiyar zuciya tukunna tace “FYI Cikin ya zube. Ta fad’o daga bene ya zube 3 days ago”

Shiruu Ummi tayi tana kallonta
ta jima tana kallon kwayar idanun ta itama Mon d’in haka, chaan ta lumshe idanuwanta ta bud’e ta furzar da iska tana mai girgiza kai duk a lokaci d’aya kafin tace “Adama ki ji tsoron Allah, ki bar ganin cikin shege ne kika zubar
wallahi kina da hukuncin kisa a hannunki”

Murmushi Mom tayi kafin tace
“Gaskiya ya kamata magidanta suzo su d’auki course a wajen Abba! Duk wadda matarsa ta botsare kawai ya mik’ata cell zata dawo daidai”

Cikin b’acin rai Ummi ta juya kawai da niyyar shiga d’akinta, da sauri Mom ta sha gabanta tana cewa “O’o’o’o’!
Tsaya mana, ai akwai abunda ya kawoni wajen ki dear new Ummi, may be na san maganar da zan gaya miki yanzun zata dawo dake hankalinki ki koma Ummin da na sani ba wannan ba..” Dalla dalla! Haka Mom ta zayyano mata duk wani abunda taji jiya Abba da Daddy suna tattaunawa sannan ta k’ara da cewa “Zab’i ya rage naki..
Kina gani dai abunda yake yi miki tun kafin ta dawo d’in, wallahi na tabbatar idan Maryam ta dawo gidan nan wallahi Ummi kin ji na rantse miki sai masu gadi da drebobin gidan nan sun fiki daraja a idanun Abba! Ballantana yanzu ga y’ar ta dan ni ban san ranar barinsu gidan nan ba tunda kika ga sun zaunar da su anan to ba yanzu za su sallamesu su ba! Tunda dai na san Aslam yana da gidaje balle ace wajen zama suka rasa… Kina ji kina gani haka zaku zama y’an kallo ke da y’ay’anki bar ganin kin haifi maza..ki dai duba ki gani yanzu haka yaya Abba yake gwada so tsakanin Hudan da su Shuraim?”

A hankali Ummi ta runtsei danuwanta da suka kad’a suka yi jaaa! Kafin ta bud’e su ta zubasu a kan Mom.

Tausayinta ne ya shigi Mom a take dan haka ta matso kusa da ita ta dafa ta
kafin tace “Ki yi tunani ki yi shawara da zuciyarki. Ina da plan d’in da na shirya wannan karon kwab d’aya kawai za muyi mata. Ummi ke y’ar uwata ce bani da kamarki duk duniyar nan daga Inna sai ke nake gani a matsayin nawa inji dad’i, ba zan tab’a bari a cutar da ke ba! Ki nutsu, zuwa anjima ko gobe ki zo ki sameni ni na san me zamu yi mata.”

A hankali Ummi ta sauk’e ajiyar zuciya sannan tace “Nagode Adama. Bara in shiga in kwanta kaina yana min ciwo”

“Okay sai anjima, bara in wuce.” Mom d’in tace daga nan ta juya direct ta sauk’a ta fice daga gidan ta nufi side d’insu ranta fess!.

Sai yamma chan daff da Magrib Aslam ya dawo. Abba kuwa da Daddy basu dawo ba sai bayan sallar isha. Sarai Ummi ta san inda suka je shiyasa tunda taga Aslam ya dawo shi kad’ai hankalinta yayi mugun tashi! Ta dinga ji kamar zuciyarta zata fashe. Da kyar! Da mugun kyar ta iya danne zuciyarta ta dinga karanto adduoi tana tasbihi
tukunna ta samu ta d’an dawo hankalinta….

EARLIER.
Da kyar Jalila ta iya taimakawa kanta ta mik’e a hankali ta zauna

Wani sabon kuka ne ya kufce mata, tana yi ta shiga tattare kayayyakinta ta na d’urasu a cikin ghana most go d’in da Mom ta had’o da kayanta ta dinga watsowa. Ganin bakkon duk biyun sun cika ya sanya ta ware d’ankwalinta ta d’aure ragowar kayan a ciki bayan ta nemi mayafi ta rufawa jikinta.

Cikin ikon Allah tana cikin rufa mayafinta ta hango mai napep ya taho. Goge hawayenta tayi ta samu ta mik’e tsaye da kyar Ta taka da d’an sauri
ta isa kusan titin ta tsaidashi dan kar ya sub’uce mata.

Har bakin gate d’in gidan ya k’araso ya tayata saka kayanta a napep d’in.
Ko ciniki bata tsaya yi ba tace masa “gandun albasa!”.

A k’ofar gidan Baba ya direta ta shiga sauk’e kayanta tana jin yadda jikinta ke yi mata masifar ciwo, kallon unguwar da layin da gidan take yi. A hankali ta lumshe idanuwanta wasu zafafan hawaye suka shiga tsilalo mata.. Ganin kamar mutane suna ta kallonta ya sanya ta jaa kayanta one by one ta kai soro ta dawo ta sallami me napep d’in tayi cikin gida.

A nan soron ta bar kayan dan bata jin tana da energy d’in d’aukar kaya.

Su Umma suna zaune ita da Anty Zainab. Ya Ja’afar yana gefe kamar kullum su kuma suna tattauna ta yanda za su magance matsalolin da suka sakosu gaba a yanzu Jalila ta shigo. A mugun zabure suka mik’e tsaye duk su biyun suna kallonta dagaje dagaje! Kamar jira take yi a take ta fashe da kukan da take ta k’ok’arin dannewa.

A rikice suka k’arasa suka rufar mata da tambayoyi. Bata b’oye musu komai ba ta zayyano musu abunda ya faru tsakaninta da Mom.

A zuciye Umma ta rarumi mayafinta ta rufa ta fara k’ok’arin fita tana cewa
“Wallahi yau ko ni ko wannan Adamar Sai dai mu tashi da juna ni da ita.”

Da sauri Anty Zainab ta sha gabanta ta tsaya ta rik’eta tace “Sadiya nutsu!!”
Da d’an k’arfi sannan ta d’ora da cewa
“B’ata lokacinki kawai za kiyi, dan na tabbatar ko ganinta ba zaki samu damar yi ba. Kina ji dai ance miki masu gadi har da sojoji ake gadin gidan In ba so kike ta saka ayi miki shegen duka a kulleki ba to ki koma ki zauna mu nemi mafita dan fad’a da hayaniya da ita bata taso ba saboda ba iyawa za muyi ba! Ki bari mubi ta ruwan sanyi sai mu nemo mafita…”
Da kyar ta jaa Umma ta zaunar da ita a bakin gado tanata huci.

A hankali Jalila ta share hawayenta tace “Bara in yi wanka da ruwan zafi tukunna. Jikina duk ciwo yake yi.”

Cike da tausayin ta Anty Zainab tace
“Maza je ki yi, akwai ruwan da na d’aura za muyi d’an wake cike da tukunya, idan kin juye sai ki mayar da wani”

Purse d’in wayarta kawai ta ajjiye ta fice ta nufi hanyar band’akin. Da ikon Allah kawai sai ta tsinci kanta da
shiga tsananin tashin hankali sakamokon kyankyamin bakin rijiyar ta su da k’ofar band’akin da ya shigeta lokaci d’aya!

Tabbas daman ta san ba zata iya rayuwa a gidan nan ba yanzu!

Amman ita a nata tunanin abinci ne da wajen kwana zai fi damunta.

Da kyar! Tsigar jikinta tana tashi ta samu ta d’auki bokitin da ta gani ta wuce cikin kithchen d’in ta juye ruwan.

Hankalinta bai gama tashi ba
sai da ta shiga cikin band’akin!
Yayi mugun yin datti yayi dama dama gashi dama yana fama da nashi yanayin na tsufa da rashin had’uwa, yanzu kuma yazo ya had’a da rashin kula. Har wani gansa kuka yake yi
ga wani ruwa bak’i k’irin a kwance mai uban yawa da wari da alamar makwarar rufewa tayi!

A ranta tace “tabbas Mama bata gidan nan.”

A hankali ta shiga ta ajjiye bokitin ta hau zame kayan jikinta. Ta sak’ale a jikin k’aure.

Kasa wanka da soson wanka nasu tayi dan shi kanshi abun kyankyami ne!
Sabulun kawai ta iya d’auka shima saida ta wanke shi sau uku tukunna ta iya murzawa a jikinta.

Sai da tazo kwara ruwa tukunna taji inama batayi wankan ba! Dan duk zubawa idan tayi sai na k’asan nan mai uban wari wanda ta tarar ya taru ya fallatso mata jiki.

Kamar ta fashe da kuka haka take ji….a hankali ta hau zuba ruwan a hanakali. Ta ci sa a kuwa ya daina fallatso mata d’in amman yadda ruwan kumfan jikinta yaje ya had’e da ruwan dattin nan ba k’aramin kyankyami ya k’ara mata ba!

Ganin ba zata iya jurar gani ba ya sanya ta runtse idanuwanta ta fara laluben kayanta Cikin rashin sa’a ta bi takan d’an guntun sabulun da ya b’antare ya fad’i wanda ta gama wanka da shi yanzun!

Aikuwa santsi ya d’ebeta…
Sai da k’afafuwanta gabad’aya suka bar k’asa tukunna ta dawo ta fad’o gaba d’ayanta a cikin ruwan da take jin kyankyamin kalla!

Wata razananniyar k’ara ta saka!!!
Da gudu Umma da Anty Zainab waenda suka juyo ta suka fito suka nufi band’akin.

A cikin ruwan suka tarar da ita ta runtse idanuwanta da k’arfi ta k’ame waje d’aya tanata kurma uban ihu!
Su kansu sai da suka ji kyankyami da suka d’agata.

Da kyar suka iya kamata suka mik’ar tanata faman ihu mai had’e da kuka sannan tak’i ta bud’e idanunta.

Anty Zainab ce ta d’au botikin ta fice taje ta janyo ruwa a rijiya sannan ta koma ta d’auko silifas d’inta ta dawo band’akin suka shiga shek’a mata ruwa! Sai da suka juye mata ruwan botikin sannan suka rufa mata zani suka fito da ita tana wani irin kukan tashin hankali.

Da kyar aka samu ta bud’e idanuwanta, nan da nan zazzab’i ya rufar mata dan haka ta k’udundune cikin bargon da shi kanshi kyamarshi take yi ta hau rawar sanyi.

NASARAWA GRA.

Tunda ya dawo bai ganta a d’akin ba. Tana d’akin su Shuraim dan ita ba gwanar yin chatting ko danna waya ba ce ba shiyasa in dai su Shuraim d’in suna nan take zuwa wajensu ko suyi ta hira ko kuma su yi game.

Yauma suna lunch ita da Ummi suka shigo, shiyasa suna gamawa suka d’unguma suka yi d’akinsu.

Har ya fito zai je sallar isha bai ganta ba, sai Ummi kad’ai ya gani tana shirya dining dan haka kawai yace
“Ummi ina Huda?” Kamar an fisgi maganar a bakinsa.

Ita kanta Ummi sai a lokacin taga rashin kyautawar ta dan ya kamata ace ta tura ta wajensa, amman ya dawo wajen awa nawa har yanzu bai sanyata a idanunsa ba!

Gabad’aya abubuwa ne suka yi mata yawa shiyasa hankalinta bai je nanba.

Sai da ta d’anyi murmushi sannan tace
“Sorry Aslam. Tana kitchen. Wani abun ne ya shamin kai shiyasa kaga ban turo maka ita ba.”

Murmushi kawai yayi yana kallonta, kamar zai ce mata wani abun sai kuma kawai ya sa kai ya fita.

BAYAN KWANA BIYU.
Kamar kullum yau ma bayan isha suka gabatar da dinner d’insu, cikin nutsuwa da farin ciki. Daga haka aka fara watsewa Dining d’in ya rage daga Abba sai Huda da Ummi. Huda tana mik’ewa shima ya fara k’ok’arin tashi,
da sauri Ummi tace “Am, Abba dan Allah ina son zan je wajen Mama gobe Huda ta rakani”.

Bata yi tunanin zai kula ta ba, ga mamakinta sai taji yace “Yin me?”

A hankali tace “Akwai wata y’ar magana da nake so mu yi. Ni da ita”.

“Wa ta shafa?”

Kame kame ta fara chan tace “Dan Allah Abba. Hak’uri nake so in bata
akan abunda na yi mata”.

Tab’e baki yayi sannan kawai yasa kai ya wuce ba tare da yace komai ba.

Huda na shiga d’aki ta tarar da shi as usual yana aiki. Waje ta samu ta zauna a gefen gadon ta d’auko waya suka hau chatting ita da Sakina.

“Ba ki iya gaisuwa ba”. Taji muryarsa.

Turo baki tayi kafin tace “Ina wuni”
Dan Sakina labari take bata za a kawo kud’in aurenta so bata so ya katseta.

Be ce mata komai ba, ya kyaleta.
Sai da ya kai inda yake son zuwa sannan ya kashe computer yace mata
“Zo”

D’agowa tayi tana kallon shi irin ‘ni?’.

Gira d’aya ya d’aga mata alamun ‘eh’.

A hankali ta mik’e ta ajjiye wayar sannan ta k’arasa inda yake.

Gefensa ta kalla kan kujerar sai kuma ta kalla k’asa kan kafet d’in gaban kujerar ta fara k’ok’arin zama.

Ji tayi kawai ya kamo hannunta ya jaata ya ajjiye ta a gefen sa..

B’ata rai tayi sosai ita kam wallahi zata maka masa warning! Dan me yasa ba zai mata ta zauna a gefenshi ba instead zai wani janyota? Hala bakinsa yana ciwo ne.

Muryarshice ta katseta jin yana cewa
“D’azu Ummi tace za ki rakata wajen Mama”. Da sauri ta d’ago ta kalle shi
sai kuma ta fara murmushi, bata san zancen ba amman kawai sai ta hau d’aga masa kai.

Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin ya juyo ya bata dukkannin attention d’insa sannan yace “Ina jinki”

Cikin rashin fahimta tace mishi “Me?” “Okay, baki san me ya kamata ki yi ba?” Yayi mata tambayar still yana kafeta da idanuwanshi.

Shiruuu tayi ita harga Allah bata san me yake so ta yin ba! A hankali tace
“Me zan yi ni?”

Kallonta yayi na some seconds sannan yace “Tashi ki je, goben kawai kya bata sak’on gaisuwa ta kaiwa Maman
besides saboda Ummi ne ma shiyasa zan barki daman kije dan ai bai kamata ace kinje gida tun yanzu ba.”

Sarai zuwa yanzu ta gano so yake yi ta tambayesa, a ranta tace “Wannan wanne irin mutum ne mai son jan magana? Ba Ummi ta tambayar min ba!”

Ganin da tayi tambayr da yake son tayi shine mafi sauk’inta ya sanya kawai ta kauda kai tace “Ya Aslam zan raka Ummi wajen Mama gobe”

Kafin ta rufe bakinta taji yace “Order kike bani? Ko kuma gaya min kike yi?
Ko kuma tambayata da neman izinina kike yi?” Ya mata tambayar a hankali cikin class da nutsuwarshi.

B’ata rai tayi sosai kamar zata fashe da kuka. A ranta ta aiyyana ‘ga zuwa wajen Mama ga kuma wasu shegun renin hankali da Aslam yake yi mata, wanne zata d’auka?’A ranta tace ‘Ya na iya? Haka zan hak’ura in yi tolerating d’insa.”

Muryarsa taji yana cewa “had’o min coffee. Shikenan tunda ba kya son zuwa”. Yana fad’in haka shima ya juya yana kallon wani wajen kamar yadda tayi mishi.

A hankali yaji tace “Ya Aslam nafa tambayeka. Me zan ce?”

Juyowa yayi yana kallonta itan ma shi take kallo Sai dai suna had’a ido tayi saurin d’auke kai. A hankali ya lumshe idanuwansa kamar mai yin bacci, Sun fi minti biyar kafin yaji tace “Dan Allah Ya Aslam zan raka Ummi wajen Mama gobe”.

Wayarsa kawai taga ya mik’o mata ya ce “ki hau ki yi searching ya ake tambayar Miji fita! Ko kuma ki d’auko wayarki and ask Sakina, na san maybe ita za ta iya sanin me ya kamata ki ce”.

Wani takaici ne yazo mata bata san lokacin da ta fara hawaye ba. Karb’ar wayar kuwa tayi ta hau google ta typer, wasu abubuwa daban aka sako mata.

Shiruu, tayi tana share hawayen da suka k’i tsayamata, a ranta tace
“Wanne irin mutum ne wannan wai shi? Kalla yadda kanshi tsaye yake wani cewa Mijinta!”.

Sun d’an jima a haka chan! Kamar wadda ta tuna wani abun yaji tace
“Dan Allah Ya Aslam Ina neman izinin ka zan raka Ummi wajen Mama”

Wani sassanyan murmushi yayi kafin a hankali ya fara bud’e idanuwanshi yace “That’s more like it…” Muryarshi ce ta sark’e sakamokon ganin fuskarta dagaje dagaje da hawaye.

A hankali ya matso kusa da ita
yace “Mai ya faru?”

Kamar jira take yi kuwa ta saki kukan nata dan ji tayi ya taho mata da mugun k’arfi.

Kuka take yi tun k’arfin ta tak’i ma ta saurareshi, sai faman tambayarta yake yi amman tayi mishi banza! Bata yi auni ba taji ya janyota jikinsa bai yi wata wata ba ya rungume ta gabad’ayanta!

Ba ita kad’ai ba hatta shi sai da ya tsorata da yadda zuciyarshi take bugawa! A lokaci guda kuma wata nutsuwa ta lullub’esa jin shi kawai yake yi a saman gajimare.

A b’angaren Huda itama kusan hakan ne dan d’iff haka kukan nata ya d’auke lokaci guda in banda ajiyar zuciya babu abunda take ta faman sauk’ewa.
Ita dai ba zata ce ga yanayin da take ciki ba saboda lokaci guda firgici mamaki nutsawa da fargaba suka rufar mata.

Da kyar ya iya d’aga hannunsa ya d’aura a kan gadon bayanta ya fara shafawa a hankali, dede setin kunnenta ya ce “Shii, yi hak’uri. Wasa nake miki fa. Naga d’akin kullum boring ne shiyasa nake d’an jan magana da ke amma sorry tunda ba kya so ba zan k’ara ba.”

Zuwa yanzu ita kam ba ma jin sa take yi sosai ba! Mamakin kanta kawai take yi yadda ta kasa turesa daga jikinta Infact ita ji tayi ma bataso ya barta!
Abu d’aya ne bata so shine bugun zuciyarta da yake yi da k’arfi! Amma apart from that bata k’aunar duk wani abunda zai rabata da duk wani part of yanayin da taje ciki a yanzu.

A hankali take shak’ar k’amshin jikinsa da na turarensa tana jin wata nutsuwa da nishad’i suna sauk’ar mata. Bata san lokacin da ta fara lumshe ido tana bud’ewa ba. Wata kasala ce ta rufar mata dan haka ta d’an fara sakin jikinta tana lumshe ido tana sauraron bugun zuciyarshi da yake yi da k’arfi da sauri har ma yafi nata.

A hankali yake jin nauyin jikinta yana k’aruwa a nashi. Sun fi 10 minutes a haka, chaan! Ya ji ta sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya sai kuma ya fara jin sauk’ar numfashinta a kan k’irjinsa a hankali a hankali.

Ajiyar zuciyar shima ya sauk’e
kafin yace “Huda” a hankali.

Shirun da ya ji tayi ne yasa ya fahimci ta yi barci. A hankali kamar wanda rayuwarshi yayi depending akan barcin nata ya janyo trow pillow ya fara k’ok’arin kwanciya da ita a jikinshi. Mik’ewa yayi sosai akan kujerar kwanciyar rigingine.
Kusan dukkan nin sangalalin k’afafuwansa sun kere kujerar gashi kuma akan d’an tudun edge d’in kujerar ya d’aura su, tabbas ya san k’afar zata yi mishi tsami amman
he can’t even think of ruining wannan best moment d’in, ba. A hankali ya kwantar da ita akan hak’ark’arinsa.
Daga shi d’in har ita ba wani k’iba garesu ba shiyasa faffad’ar kujerar ta ishesu ciff ciff. Mayafin kanta yayi dabara ya ware ya lullab’a mata.

Yau ma yana jin sanyin amman yana gudun kar ya motsa ta farka dan haka kawai sai ya hak’ura ya bar bargon…
Bai yi cikakken minti biyar ba wani bacci mai mugun dad’in da ya manta rabon da yayi kwatan kwacin irinsa, ya kwashesa..

Yau ma, kamar yadda ta farka jiya haka ta rigashi tashi. K’amshin turarensa ta shak’a! A hankali ta fara k’ok’arin motsawa amman sai ta jita ta kasa. Addua tayi ta bud’e idanunta sosai tana kallon d’akin.

A chaan ta hango gadon a gefe ba kowa a kai! A d’an zabure ta sake yunk’urin tashi had’e da kallon kusa da ita.

Tsayawa tayi kawai tana kallonshi yana baccinsa peacefull, sannan ya zura hannunsa d’aya ta k’asan ta gefen cikinta, ya kuma d’aura d’ayan a gefen cikinta ta sama ya had’a hannayen nasa guri guda.

Gaban tane taji ya yanke ya fad’i! Sai kuma ta tuna yadda suka yi jiya!
‘Kenan bacci tayi ta kwana a jikinshi?’
Ta aiyyana tambayar a cikin ranta.

Wani takaici da haushin kanta ne suka rufeta a take. Hannunta ta saka ta fara k’ok’arin raba hannayen nasa da suka kanainayeta.

Sai a lokacin ya bud’e idanunsa ya zuba mata. Itan ma shi take kallo dan haka idanuwansu suka sark’e ana juna.

Tun tana k’ok’arin kwance hannuwan nasa a jikinta da sauri har tazo ta fara yi a hankali daga baya ma sai ya zamana hannuwantane kawai akan nasa ko motsasu bata yi.

A hankali take jin fad’uwar gaba da kuma wani sanyi da nutsuwa a yayin da take kallon cikin idanunsa…ta fad’a a yau kuma ta sake tabbatar wa ‘babu wanda ta tab’a gani mai kyawun idanuwa kwatan kwacin na Ya Aslam’
A ranta ta ce “tubarkallah ma sha Allah”. Cikin muryar bacci taji yace
“Good morning wifey!”

A hankali ta lumshe idanuwanta a ranta take tunanin ‘Anya wannan ba aljani bane ba kuwa? Kalla fa yanzun nan ya tashi a barci amman idanuwansa basu yi ja ba sai ma wani kyalli da taga suna yi sannan bakinsa kamar ma sweet ya sha dan in dai
taji da kyau tou k’amshin mint taji.’

D’umin numfashinsa ne taji yana k’ara bak’untar fuskarta!

A hankali take sauk’e ajiyar zuciya tana sake rik’e hannunwansa.

Chan! Kamar wadda ta tuna wani abun, tayi saurin bud’e idanuwanta tarr!! A d’an zabure, daidai shi kuma ya samu nasarar d’aura lips d’insa a kan nata.

A mugun firgice ta sanya dukkannin k’arfinta ta turesa amman ko gezau! Bai yi ba.

Wani rikitaccen kuka ta saka masa!
Dan haka yayi saurin sakinta ya d’an jaa baya yana kallonta.

Tana jin ya saketa, ya bata iska ta bi ta kansa da wani irin sauri ta sauk’a daga kan kujerar! Mayafinta da yake lullub’e a jikinta wanda ya fad’i yanzun kawai ta samu damar d’auka
daga nan ta nufi k’ofa.

Tana jinsa yana kiran sunanta
amman tayi banza da shi ta fice da mugun sauri.

<< So Da Buri 60So Da Buri 62 >>

1 thought on “So Da Buri 61”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×