Skip to content
Part 62 of 73 in the Series So Da Buri by Humaira Bulama

Chan sama ta nufa. Tana tafe tana adduar ‘Allah yasa side d’inta a bud’e yake’. Tana isa ta tura, cikinsa a ta tarar a bud’e dan haka ta shige ta saka key! Tana zuwa ta zauna a kan kujerar parlourn tana haki kamar wadda tayi gudun famfalak’i. Ta dad’e a nan zaune, jin an shiga masallaci ya sanya ta mik’e tana tunanin komawa d’akin dan ta samu ta d’au hijabi ta yi sallah.

Kamar Aslam d’in ya biyota haka ta d’an bud’e k’ofar kad’an ta lek’a!
Ganin babu kowa a dogon corridorn ya sanya ta sauk’e ajiyar zuciya ta fito tana sand’a. Sai da ta kai tsakiyar parlourn taji muryar Ummi a bayanta. “Hudan”. Runtse idanunta tayi a hankali kafin ta bud’e sannan ta juyo, ta shiga k’ok’arin k’ak’alo murmushi…

Kallonta Ummin tayi from head to toe sannan ta nufota, tana zuwa “me ya kawo ki nan?” Kame kame ta fara. chan! Da kyar tace “Daman zuwa nayi In karb’i Qur’ani a wajen Shuraim kuma d’akin nasu ma a kulle ne “

Had’e fuska Ummi tayi kafin tace “Yaushe kika koyi k’arya? Ina d’aki fa Ina karatu naji an hawo, Ina lek’owa naga wucewarki d’akinki tun d’azu! Mai ya faru??” Ta yi maganar tana tsareta da idanuwa.

A hankali ta sunkuyar da kanta ba tai auni ba kawai taji hawaye sun zubo mata.

Sarai daman Ummi ta so ta fahimci wani abun…Murmushi kawai tayi a ranta tana mamakin Aslam! Kafin ta jawo Hudan zuwa jikinta cin son sake fahimtar lamarin tace “Yi shiru, shikenan. Bara in d’auko miki Qur’anin a d’akina sai ki wuce kije ko? Kar Aslam d’in yaga kin dad’e, yau ma na san da wurwuri za su fita. Kiyi sauri kije ki taya shi shiryawa, ko?”

Kuka kawai taji Hudan ta ke ce dashi kamar wadda aka ce za a yankata! Cikin kukan tace. “Ummi dan Allah karki bari in koma, Allah ba zan iya had’a ido da shi ba, baki san meh.”

Kamar kuma wadda aka datse harshenta sai ta tsaya da maganar chak! Tana mai ci gaba da kukanta.

Murmushi Ummin tayi ranta fess. Tace mata “to shikenan jeki ki yi alwala ki yi sallah ki daina kuka haka. Anjima sai muyi magana ko? Muje d’akina. Tayi maganar tana jan hannunta.

Bayan, Ummi ta gabatar da sallar Asubah, ta yi azkar, ta zauna ta hau nazari. Wani sanyi da dad’i take ji a ranta, ta san Huda Arshaad take so amman tabbas kamar yadda su Dad suka ce ‘Ko bayan auren Mammy ba zata barta ta zauna lafiya ba’.

Aslam shine wanda take gani zai bata cikakkaiyar kula da soyayyar da take buk’ata, bayan haka sun yi mugun dacewa sannan ita daman ta d’an fahimci kamar Aslam d’in yana son Huda! In dai kuwa hakanne Allah Ubangiji ya barsu tare ya k’ara musu k’aunar juna ya sanyasu farin cikin da basu yi tun tasowarsu ba.

A zaune taga Huda ta fara gyangyad’i dan haka tace mata “ta tashi ta kwanta a kan gado”. Da sauri kuwa Hudan ta mik’e saboda daman addua take tayi kar Ummi tace mata taje ta had’awa Aslam breakfast. Tana kwanciya bata dad’e ba bacci ya kwasheta Ummi kuma ta mik’e ta fita dan had’a musu breakfast d’in.

Tana cikin bacci taji muryar Abba yana kiran sunanta, a hankali ta bud’e idanuwanta.

Zaune ta ganshi a gefenta yana mata murmushi dan haka itama ta d’anyi murmushin sannnan ta mik’e ta zauna tace “Abba Ina kwana” “Lafiya, Alhamdulillah. Kin tashi lafiya?”

“Alhamdulillah” Tace

Mik’ewa taga yayi tsaye kafin yace “Zamu wuce UK ni da Daddy. Urgent tafiya ya taso, akwai abunda kike buk’ata?”

Murmushi kawai tayi tace “Ba komai. Allah ya kiyaye ya tsare hanya ya dawo daku lafiya”

A hankali ya d’an matso ya shafa kanta yace “Ameen princess, take care. Sai mun dawo ko”.

Yana gama fad’in haka ya juya ya nufi hanyar fita, har ya kama handle d’in sai kuma yaga rashin kyautawar shi dan haka ya juyo ya kalli Ummi dake gefe a tsaye ya ce, “Na tafi. Zan saka miki kud’i ta account ko akwai abun buk’ata. In akwai wani abun you can call me”

Wani kalan murmushin farin ciki ne ya baiyyana a kan fuskarta, tana murmushin tace “Nagode. Sai kun dawo”

Murmushin daya mayar mata ne ya bata kwarin guiwar binsa a baya domin tayi mishi rakiya.

Hudan ma taso ta rakasa amman ganin sun fita da Ummin ya sanya ta bari kawai, dan ta barsu su samu alone time su biyu.

Kallon agogo tayi taga har 10 ya d’an gota. Ta san by now Aslam ya fita dan haka ta sauk’e ajiyar zuciya ta zuro k’afafunta k’asa tana tunani da mamakin guts! Kalar na Ya Aslam, mai yasa yayi mata hakan? Ya san ba sonta yake yi ba mai yasa zai dinga yi mata wasu abubuwan kamar waenda suka yi auren soyayya!? She definitely has to stay very far away from him har sai ta gano inda relationship d’insu ya dosa da ita kanta dan gaba d’aya Aslam ya juya mata lissafi kwana biyun nan kanta duk ya d’aure.

It’s like bama ta san me take so ba! Tabbas ta san tana son Ya Arshaad sannan tana son rabuwa da Ya Aslam. Amman kuma when ever she’s with him she feels complete and safe!

Da farko bata fahimci hakan ba sai a jiya da yayi hugging d’inta ta kasa kwace kanta daga k’arshema bacci ya kwasheta.’ Ajiyar zuciya ta sauk’e, a chan k’asan ranta tace “A complicated marriage is enough! I can’t deal with complicated and confused relationship.”

Tun d’azu idan ta tuna da moments d’insu na tsakanin jiya da yau da safe sai taji tana feeling somehow bata k’aunar wannan feeling d’in at all ba ta son abunda zai na janta garesa shiyasa gara tun kafin ta gama zama confuse tabbas ya kamata ta d’au mataki.

A haka Ummi ta shigo ta sameta. “Tunanin me kike yi?” Ta ji muryar Ummin.

A hankali ta d’ago ta kalleta sai kuma ta maida kanta k’asa ta ce “Ina kwana” Murmushi kawai Ummin ta yi tace. “Lafiya” sannan ta ce “Oya tashi ki shirya mu yi sauri mu tafi ko?”

Ai tun kafin Ummi ta ida rufe bakinta Hudan ta sauk’a ta fita daga d’akin cike da d’oki.

Murmushi kawai Ummin tayi itama ta hau nata shirin. Sai pass 11 sannan suka shirya suka fito. Hudan bata wani yi kwalliya sosai ba, Abaya ce a jikinta nude colour mai kyau sosai, tayi rolling ta d’an saka lipstick, sai zobe da bracelet a hannunta. Ummi kuma lace ne mai kyau da tsada a jikinta peach da farin mayafi da jaka da takalmi.

Suna baya suna d’an tab’a hira driver yana jansu, haka suka kama hanya. A wani babban mall Ummi ta cewa drivern “ya d’an tsaya”.

Sai da suka fita tukunna ta bawa Hudan kud’i, tace “D’azu Aslam ya ce a bata ta yi siyayyan tsaraba ta kai gida”.

“Angode” kawai ta iya cewa daga nan suka shiga suka yi y’ar siyayayr tsarabar suka fito Ummi tana lura da yadda mood d’in Hudan ya chanza tun daga lokacin data ambato sunan ‘Aslam’. So take ta fassara yanayin nata amman ta kasa a haka driver yayi parking a kofar gidan Madu. Fita suka yi, Driver ya taya su kai kayan har bakin k’ofar parlour daga nan suka sallame shi bayan sun yi da shi akan 3:00pm zai dawo ya d’auke su.

A parlourn k’asa suka tarar da Mama tana zaune tana kallo. Sallamar su ce ta sanya ta maida hankalinta bakin k’ofar, kamar a mafarkin haka taji nan take wani farin ciki ya lullub’eta.

Cikin farin ciki Huda ta ajjiye ledojin hannunta a farkon parlourn ta k’arasa da gudu ta fad’a jikinta ta yi hugging d’inta.

Tabbas Mama tayi farin cikin ganin d’iyar tata amman sai ta maze ta zarota daga jikinta ta fara yi mata fad’an ‘mai yasa ta fito? Dududu yaushe ma aka kaita?”

Ummi ce ta k’araso inda suke tace “Ayi hak’uri Mama ni nace sai ta rakoni”. Murmushi Maman tayi dan ita ta ma manta Hudan tare take da bak’uwa hakan yasa ta d’anji kunyar barinta da suka yi a tsaye ita kad’ai. Cikin fara a tace “Bismillah ki zauna. Yi hak’uri wannan ta gudo ta barki bama ta tsaya kun k’araso tare ba”

Murmushi Ummi tayi sanann ta k’arasa ta ajjiye ledar hannunta a gefe tukun ta zauna a kan d’aya daga cikin setin kujerun da Maman tayi mata nuni da.

Tana zama Mama tayi kitchen. Sai da ta cika mata gabanta da kayan kwalama da su lemuka tukunna ta nemi waje ta zauna tana raba d’ayan biyu . ‘Ko dai Babar Auwal ko kuma matar Abba! Amman anya kuwa matar Abba zata yarda tazo kuma tana mata fara’a haka sosai?’

“Ina su Hajiya? Na ji gidan shiru” Muryar Huda ta katse mata tunani.

Sai da ta d’anyi jimm! Tukunna ta ce. “Tana gidan Baaba Talatu, Baba ne aka dawo da shi wai bashi da lafiya sosai”

“Allah ya bashi lafiya”.Shine abunda Huda tace kawai dan jiya ma sai da suka yi maganar ita da Sakina A yanayin take taken Baaba Talatu so take ta fake da rashin lafiyar Baba a maida Mama gidanshi.

“Kafin ku tafi ya kamata ki shiga ki dubo shi”. Hudan taji muryar Mama. “Tam” Kawai tace kafin tace mata, “Sakina fa? Jiya tace min tana nan”

Cikin sigar zolaya Maman tace. “Amarya dai zaki ce! Ta tafi. Gobe suka ce za suje gidan dangin Babanta da shi da Yayansa Babansu yayi tafiya.

Nan da sati biyu kuma in sha Allah za su koma har da su kawunnansa da Mahaifin nasa a saka rana”.

Murmushi suka yi daga Huda har Ummi, a tare suka ce “Allah ya tabbatar mana da alkhairi” Kafin Ummi ta d’an nisa tace “Dota d’an bamu guri, ko?”

A hankali Hudan ta mik’e ta wuce sama ta bar su su kad’ai a zaune.

Gyaran murya Ummi tayi suka d’an sake gaisawa kafin tace “Maryam ni ban ma san ta Ina zan fara ba! Abu biyu ne yake tafe dani wanda duk biyun alfarma ce nazo nema daga gareki amman ina ga gara in fara dana farkon dan shi yafi hanani sukuni a rayuwata.”

Tabbas tun lokacin da taji ta kira ‘Huda’ da ‘dota’ ta fahimci Zainab ce!

A hankali Mama ta gyara zama ta fuskanceta da kyau kafin tace “Ina saurarenki, Allah yasa zan iya taimokonki”

“Za ki iya In sha Allah” Shine abunda Ummi tace kafin ta cigaba da cewa, “Sunana Zainab, na san kin sanni a bad’ini a zahiri kuma yau gani a gabanki. Da farko ina mai neman alfarmarki Maryam dan dan Annabi ki samu ki yi creating space a zuciyarki ki yafe min laifin da nayi miki shekarun baya sannan ki yafe min laifin da nayi ta maimaitawa Ina nanatawa duk akan Abba kar ya dawo gareki! Ba dan ni ba, tare da taimokon su Adama to da tuni tun a karon farko lokacin da kika tura mishi da sak’o na san da kun koma kun ci gaba da zaman ku cikin kwanciyar hankali da k’aunar juna, amma biyewa zuciya da son kai suka kaini ga aikata makircin da wallahi ni kaina idan na tuna kunyar kaina nake ji! Na san I’m asking for a lot, na san da wuya ki yafe min, na san ko da ace kin yafe min to ba lalle ki daina ganina da abun ba.”

A hankali Ummi ta share hawayen da suka zubo mata sannan ta d’an zamo daga kan kujerar ta durk’usa.

Da sauri Mama itama ta sauk’a akan kujerar tace “Dan Allah kar ki yi haka!
Already ni kam na dad’e da yafe miki besides ba ke ce kika saka Abba ya sakeni a wannan ranar ba kawai dai kun had’amu fad’a ne wanda yanzu ya riga da ya wuce, komai ya wuce! Dan haka na yafe miki, Ubangiji ma ake masa lefi a nemi gafara kuma ya yafe mana ballantana ni? Ki manta da komai ki saki ranki In dai dan ta ni ne ina so kisa a ranki kamar komai bai faru ba! Dan Allah. Sannan ki daina d’aura laifin da ba naki ba a kan ki ke kad’ai dan Allah.”

Ummi bata san lokacin da ta fashe da kuka ba! A hankali Mama ta rungumeta. Itama tana nata hawayen da bata san dalilin sa ba A hankali ta share hawayen nata sannan ta cika Ummi ta gyara zaman ta ta hau lallashinta. Da kyar Mama ta iya lallashinta aka samu ta yi shiru. A hankali Ummin ta kamo hannuwanta duka biyu a cikin nata tace “Na gode kwarai! Sai alfarma ta biyu. Ina rok’on ki, ki daure! Na ji kuma na san yadda Abba yake ta faman biko amman kin k’i amincewa!

Na san kina da gaskiya ta wani b’angaren amman kuma duk inda akaje aka dawo Abba ya fiki gaskiya.
Ki yi hak’uri ki daure ki koma gidanki na farko na tabbatar har yanzu kina son Abba kuma a cikin shekaru goma sha taran nan da nayi da shi a matsayin Miji na fahimci zuciyarsa ba tawa bace ba taki ce!
Ba zan tab’a mallakar abunda ba nawa ba kuma indai bakya tare da shi to ba zai samu nutsuwar da ni kaina zan samu koda ace 1/10 d’in kulawar da ya kamata ya bani ba. Ki daure, kar ki cuci kanki ki cuce ku. Ki dawo kusa da y’arki, kusa da masoyinki, ku k’arashe rayuwar ku just like it was soppose to be…Kar ki damu da kowa ke dai kawai ki yi abunda zai sanyaki farin ciki, dan Allah.”

Da sauri Mama tace “A’a zainab gaskiya wann…”

Cikin katseta Ummi tace “Na san alfarma nace Ina nema a wajen ki amman In kikai duba zakiga kamar a cakud’e take da shawara! Shawarar da duk wani masoyinki na gaskiya zai baki. Sanann idan kikai haka za ki sanya mutane da yawa farin ciki.. Kinga na farko ‘Abba’, Ta biyu ‘Huda’. Sannan ta uku ‘Ni’.”

Da mamaki Mama take kallonta. Murmushi Ummi tayi sannan tace “tabbas! Dan ni gani nake yi ma ko Abba ba zai kaini farin ciki ba saboda kinga na farko. Zan ganshi cikin farin ciki Sannan zai daina blaming d’ina akan na rabaku, sannan idan ba gani nayi na gyara abunda na b’ata ba to wallahi har abada har In koma ga mahaliccina ba zan iya samun nutsuwa ba! Ganin ku tare a yanzu, living together happily zan iya ce miki shine abunda nake da kwad’ayin gani a yanzu fiye da komai a rayuwata”

Zuwa yanzu Mama kam tama rasa bakin magana…A hankali Ummin tace “Ki yi tunani mai kyau.
Dan Allah Maryam”. A hankali Mama ta sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya tana kallonta kawai..

Sai a lokacin Shuwa wadda shigo tun d’azu tayi musu sallama.

D’agowa sukai suna kallonta, itanma su take kallo har ta k’araso tsakiyar parlourn inda suke, jikinta duk a sanyaye.

Cikin mutuntawa Ummi ta shiga gaisheta, Itama ta amsa mata cikin karramawa da kulawa kafin ta k’araso ta nemi waje ta zauna tana tambayarta “ya mutan gidan?”

Sun d’an jima kafin Huda ta sauk’o. Shuwa na setin staircase dan haka da ita ta fara tozali!
Salatin da ta rafka sai da ya firgita su Mama dan haka suka juya suna kallon inda sukaga tana kallo
Ita kanta Huda sai da ta tsorata.

Tun kafin ta k’araso ta rufeta da fad’a! “Dan mai yasa za ta fito? Aslam d’in ne ya bata izini saboda shima sakare ne irinta! Ko dai satar hanya tayi ta fito?”

Da kyar ta iya tsayawa ta amsa gaisuwarta daga nan tace “su kama hanya maza maza su koma gida!
Wannan shirmen ba da itaba. Ita tunda uwarta ta kawota duniya bata tab’a ganin amaryar da ta fito bata yi sati biyu ba!”

Da kyar ta yarda suka d’an jira driver bayan sun kirashi, amman da cewa tayi ‘bara ta yiwa Abban Ya Jamilu magana ya maidasu. Ai bai dad’e ta kawo Baba ba akwai mota shima a hannunshi.’

Ba a wani dad’e ba. Drivern nasu ya k’araso:

Ba yadda Hudan ta iya ta fara k’ok’arin tafiya ba dan taso ba haka nan ta yi wa Shuwa sallama ta basu tsarabar da Aslam ya bata kud’i suka tsaya suka siya daga nan ta cewa Mama za suyi waya anjima dan da akwai maganar da itama ta shirya za suyi da Maman.

Har mota Maman ta rakasu, haka nan ta tafi tanata kumbure kumbure..

Sai da Shuwa taga fitarsu tukunna hankalinta ya kwanta, yadda tabi ta d’aga hankalinta zaka ce Huda wani gagarimin laifi tayi…

Mama tana dawowa daga rakasu ta zo ta nemi waje ta zauna a gefenta kan 3 seater tace “Kiyi hak’uri Hajiya nima sai da nayi mata fad’a wallahi. Wai Ummi ta rako ne shiya sanya. Kin san su family d’in nasu boko ta ratsa su da yawa basu wani damu da al’ada ba amman duk da haka na san inda ace a waje d’aya suke da Mommy da ba zata barta ta fito ba.” Ta k’arashe maganar tana d’agowa ta kalli Hajiya Shuwa wadda tunda ta fara magana ta tsareta da idanu.

A hankali taji ta sauk’e ajiyar zuciya kafin tace “Maryam”

“Naam” Maman ta amsa a hankali.

Wata ajiyar zuciyar Hajiyan ta sake sauk’ewa sannnan tace “Naji duk abunda Ummin tace miki yanzu shigowa ta”

Wani yawu Mama ta had’iye kafin tace, “Hajiya na gama deciding tun tuni
Ba zan koma wa Abba ba! Ba kuma zan komawa Baba ba! A barni kawai, itama Ummin
dan tak’i yarda ta saurareni ne da abunda na shirya gaya mata kenan tun da hakan ne ra’ayi na, bana jin kuma zai chanja ko da nan da shekaru nawa ne”

A hankali Shuwa tace “Mai yasa?”

Da tsananin mamaki Mama ta d’ago tana kallonta kafin ta sake yin k’asa da kanta tace
“Hajiya dan girman Allah kar ki biyewa Baaba Talatu wannan karon…har yanzu wasu lokutan ina jin rad’ad’i a k’afata idan abun ya motsa, bayan k’afata har a cikin zuciyata ina jin tsananin rad’ad’in azabar da na sha a hannun Ya Usman. Dan Allah Hajiya kar kice In koma gidansa”. Ta k’arashe maganar
tana me d’ago kanta ta kalli Shuwan da idanuwanta da suka fara zubar da hawaye.

A hankali Shuwa tayi wani sassanyan murmushi sannan ta kamo hannunta duka biyu a cikin nata
ta bata dukkannin attention d’inta tukunna tace “Gidan Abba fa?”

A zabure Mama take kallonta saboda bata tab’a yin tunanin jin wannan maganar daga gareta ba.
Kasa magana tayi bakinta ya hau rawa da alamun akwai abunda take son cewa amman ta kasa.

A hankali Shuwa tace “Maryam, ko ni na kawo taurin zuciya duniya ba zan tab’a bari ki koma gidan Usman ba indai inada rai a doron k’asa”.

Wani kuka ne ya tahowa Mama lokaci d’aya ta sakeshi! Tana sauraron Shuwa tana cigaba da magana. “A baya na yi kuskure, idanuwana sun rufe da takaici da kuma bak’in cikin ganin kina y’ata amman kin kasa yi mini biyayya! Wanda hakan ya kaini ga jefa rayuwarki cikin taskun da na kasa taimokonki kuma na kasa ganin hakan har sai ranar da aka kawo min ke a karye.

Ban san da wannne baki zan baki hak’uri ba Maryam ban san ta yaya sannan ta ina zan fara baki hak’uri ba dan laifukan da nayi miki sunada yawa…Ina jin takaicin yadda na kasa fahimta da ganin laifi da badaidan da na ke ta faman aikatawa da wuri ba. Ki yi hak’uri ki yafewa mahaifiyarki Maryam dan Allah”

Da sauri Mama ta d’ago tasa hannu ta toshewa Shuwa baki tana kuka bilhakk’i da gaskiya.
Cikin kukan ta hau girgiza mata kai alamun ta daina rok’on ta. Da kyar ta iya cewa
“Hajiya dan Allah ki daina rok’ona, ke fa Mahaifiyata ce, tayaya za kiyi ta rok’ona haka.
Laifin in dai kece kikayi min to na riga na saka a raina na yafe miki tun kafin ma ki aikata laifin.”

Kuka itama Shuwa ta fashe da shi, a hankali tasa hannu ta janyo Mama ta rungume ta suna kuka duk su biyun gwanin burgewa gwanin ban tausayi.

Muryar Abba Madu wanda basu san da shigowarsa ba suka ji ya ce “Ni fa? Za a iya yafe min nima?”

D’agowa suka yi duk su biyun suna kallonsa. Murmushi yayi ya k’araso inda suke zaune ya zauna akan kujerar shima. A gefen Mama (ya zamana sun sakata a tsakiya shi da Shuwa)A hankali yasa hannu ya dafa kafad’arta yace “Za a iya yafewa Abba Madu shima?”

Da sauri ta fad’a jikinsa tana kuka at the same time tana d’aga masa kai alamun ‘eh’.

A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya, wani hawaye mai cike da tarin k’aunar y’arsa da dana sani ya samu nasarar zubo masa ta ido d’aya! Hannu yasa ya janyo Shuwa wadda itama take nata kukan ya had’asu guri d’aya da Maryam d’in ya rungume.

Mama, ta manta rabon da taji kwatankwacin wannan farin cikin a rayuwarta a ranta ta shiga aiyyana. ‘Ashe zata ga wannan rana? Ashe zata sake samun wannan opportunity d’in a rayuwarta? Allahu akbar!
Ubangiji mai zamani duniya juyi juyi, mahak’urci mawadaci. Tabbas komai in yayi zafi maganinsa Allah
sannan duk nisa jifa k’asa zai dawo! ’Kuka take yi tana godewa Ubangiji tana sake godiya.

A hankali Madu ya shiga lallashinsu yana cewa “Su yi shiru”. Da kyar ya samu Shuwa tayi shiru saannan ta tayashi lallashin Mama, tukunna itama aka samu tayi shirun.

A hankali tasa hannayenta ta kamo nasu sanann tace “Abba Hajiya
Dan Allah nima kuyi hak’uri akan yadda na gudu na bi Abba, ku yafe min dan…”

Da sauri Abba Madu ya d’aura yatsanshi akan bakinta yace “Ba komai Maryam, komai ya wuce, Allah yayi miki albarka.”

Juyawa tayi ta kalli Shuwa, a hankali tana murmushi. Itama ta d’aga mata kai tace “ya wuce!
Allah yayi miki albarka. Sannan ina neman alfarma nima a wajen ki, kamar yadda Ummi ta fad’a
nima In ba gani nayi kin koma gidan Abba ba to ba zan samu peace of mind ba, Ina so in gyara abunda muka taru ni da dangisa da su Usman muka lalata. In dai kin yafe min da gaske to inaso ki yi hak’uri ki koma gidan Abba, hakan shine abunda zai sanyani farin ciki shine abunda nake so da burin gani a rayuwata”.

Cikin sheshshek’ar sabon kukan da ya tahowa Maman tace “Amman Hajiya..”

Da sauri Hajiya Shuwa tace “Ba zan miki dole ba, ba zan, tilastaki ba amman inaso ki sani
Hakan shine zai sanyani farin ciki hakan shine abunda nake so hakanne zai tabbatar min
na gyara abunda na b’ata ya kuma taimakamin wajen sanyani in yafewa kaina.

Ki daure, ni Shuwa Ina rok’on ki ki koma gidan Abba, na san har yanzu kina k’aunar sa.”

Sunkuyar da kai Mama tayi tana wani gunjin kuka mai d’aci…

A hankali Shuwa ta share hawayenta sannan ta sa hannu ta shafa kumatun Mama kafin ta mik’e ta bar wajen da sauri.

Muryar Madu Maman taji yana cewa “Kiyi hak’uri ki bi shawarar da duk wani masoyinki yake baki
Abba har yanzu yana k’aunarki kema kuma na san kina sonshi. Ki duba kiga ko kwana biyun nan da suka wuce sai da suka zo nan shi da d’an uwansa akan maganarki Maryama a zamanin nan
ba lalle a samu mutumin da zai yiwa wata kwatan kwacin k’aunar da Abba yake yi miki ba.
Kamar yadda Mahaifiyarki tace to haka nima ba zan yi miki dole ba, amman zan baki shawarar
ki bari ki yarda ki amince a maida aurenku da Abba, hakan zai bashi nutsuwa da farin ciki na har abada
dan a yadda na ganshi ranar da suka zo na san ba abunda yake so da buri sama da a maida aurenku, nima kuma hakan nake so Mahaifiyarki itama hakan takeso. Y’arki ma hakan take so, above all, na san kema hakan kikeso achan k’asan ranki kawai dai obstacles ne suke son tsaidake ga isa inda zuciyarki take so.”
A hankali ya shafa kanta yace “Ki yi tunani mai kyau amman ina so decision d’inki ya kasance abunda kike so ne kuma ki tabbatar zai sanyaki farin ciki har k’arshen rayuwarki.” Yana gama fad’in haka ya mik’e ya fice dan lokacin sallah ya gabato….

A hankali Mama take sauk’e ajiyar zuciya, ta dad’e a zaune sai da ta fara jin kiran sallah tukunna ta mik’e ta wuce d’akinta zuciyarta fal sak’e sak’e. Ta san cewa yanzu Abba baya tare da Granpa amman fa duk inda aka je aka dawo uba uba ne, ba a chanjawa tuwo suna kamar yadda take da tabbacin k’iyayyarta a zuciyar Granpa ba zata tab’a chanjuwa ba. Haka nan, har dare Mama jikinta duk yayi sanyi kamar wata mara lafiya
Shuwa da Abba Madu basu sake yi mata maganarba dan basa so suyi ta pressurizing d’inta, haka nan suka yi dinner atare cike da da so da k’aunar juna suna hira gwanin ban sha’awa.

Wani kalar farin ciki kawai Maama take ji wanda ta dad’e bata yi ba, yana ratsa zuciyarta.

A hankali from time to time take d’an fakar idonsu ta juya ta d’auke kwallar farin cikin da ta k’i daina taruwa a idanunta. Da daddare tana shirin kwanciya Huda ta kirata, kamar had’in baki itama maganar Abba ce take so suyi, bayan sun gaisa ta gama y’an kame kamen ta kafin ta rok’eta Allah da Annabi ta dawo gidan Mahaifinta.

Cikin son kawar da zancen Mama ta sako wata hirar ganin da Hudan tayi kamar bata son zancen ne ya sanya bata sake mata maganar ba har sai da suka zo sallama, nan d’in ma d’an shiru Mama kawai tayi, chan kuma tace mata “ta gaida Ummi da Aslam tayi mishi godiya” sannan ta katse kiran.

A hankali Hudan ta gyara kwanciyar ta akan gadonta ta kwanta rigingine tana mai kallon sama.

AFTER TWO WEEKS.

A zaune Ummi ta shigo ta tarar da Hudan ta rafka uban tagumi. Murmushi tayi ta k’araso inda take ta zauna kafin ta dafa ta. A hankali Huda ta d’ago tana kallonta wanda hakan ya sanya Ummin ta fahimci kuka tayi.

Karkatar da kai Ummin tayi kafin tace “Huda ko nice Aslam fa ba kawo kud’i ba ko bikin Sakina za ayi ba zan barki ki je ba, wallahi. Ke kika jawowa kanki dan haka kar ki zauna kina wani kuka, ai baki ma yi kuka ba ki jira sai Abban ku ya dawo gobe, na tabbatar in dai yaji labari wallahi da ni da ke kashinmu ya bushe!
Bar ganin yana lallab’a ki in dai yaji wannan zance to fa ba zaku kwasheta da kyau ke da shi ba. Kuma yana zuwa zan gaya masa tunda ni kin raina ni

Da sauri Huda tace “wallahi Ummi ba rainaki nayi ba.”

Cikin katseta Ummi tace “Raini ne mana Huda! K’iri k’iri fa kika hanani number Mama saboda kin san in na kirata na fad’a mata zata yi miki fada kuma dole ki yi abunda bakya so d’in so bama kya so taji
ballantana har a kai ga tayi miki magana amma ni Ina kallon ki kina kallona a cikin gidannan yau sati biyu kina wasar y’ar b’uya da Mijinki kuma ban isa in hana ki ki hanu ba tunda ban Isa da ke ba”.

Cikin kuka Huda tace “Allah Ummi kin isa”. Mik’ewa tsaye Ummin tayi kafin tace, “Idan har na isa to
ki tattara kayan ki da kika kwaso da hannunki ki maida ki gyara d’akin ki wanke toilet kafin ya dawo.
Wallahi na manta yaushe zan ce na tab’a ganin Aslam yana gyaran d’aki amman jiya dakanshi har mopping naga yanayi kuma ba yadda ban yi da shi akan ya bari a gyara ba amma ya k’i yarda saboda ya san nan d’in turakarku ce bai kamata a shiga ba. Dan maiyasa shi yana mutuntaki amma ke ba zaki kwatanta ba?.
Ki tashi kije ki koma sannan idan ya dawo ki bashi hak’uri tare da alk’awarin ba zaki sake ba… In dai har na isa da ke kenan, kamar yadda kika fad’a.” Tana gama fad’in haka ta juya ta fice daga d’akin.

Sai da Hudan taci kukan ta, ta godewa Allah tukunna ta tashi ta sauk’a k’asan…Ta yarda zata zauna a d’akin amman tabbas zata cire tsoro kunya da kawaici su yi agreement ita da Aslam! Auren su ba na soyayya bane ba Infact k’ok’arin kawo karshenshi ma ya kamata suyi a yanzu so ba zai yiu ya hautsina mata kwakwalwa da zuciya ba bayan ba son juna suke yi ba so gara su san inda suka dosa kowa ya tsaya a iya limit d’insa.

Tana shiga d’akin k’amshin turarensa ya mata sallama, a hankali ta shak’a ta lumshe idanunta! A take wata nutsuwa da kasala suka dirar mata sannan taji zuciyarta tana yin sanyi b’acin ran da take ciki kuma yana d’an raguwa.

Bud’e idanuwanta tayi ta shiga k’arewa d’akin kallo tana ganin fuskarsa a idonta, murmushi ne ya sub’uce mata da ta tuna irin uwar hararar da ya zabga mata sannan yace “Ba zaki je ba!” ya juya ya fice. A hankali tace “Dama maza ma sun iya harara?”

Tana murmushin tana tunani ta shiga gyara d’akin cikin nutsawa kwarewa da iyawa. Tana gamawa ta shige toilet ta wankeshi tsaf tsaf.

A wajen Ummi taje ta karb’o kasko da turaren wuta ta saka a d’akin sannan ta shiga kitchen ta had’a masa spring rolls da tea, duk dan a barta ta fita. Tana gamawa ta fito ta kai dining ta jera a inda taga yana yawan zama.

Tana cikin jerawa Ummi ta sauk’o, dariya tayi kafin tace “Fad’a na ne? Ko kuma biyayyar aure?
Ko dai bribe d’in a barki ki fita gobe??”

Turo baki Hudan tayi sannan ta d’anyi murmushi. A hankali Ummi ta k’araso inda take ta dafa kafad’arta sannan tace “Na gode Huda. Kin nunamin nima na isa da ke”. Ta yi maganar tana murmushi.

Murmushi mai had’e da dariya tayi sannan ta fad’a jikinta tayi hugging nata
tace “Ummina kin isa mana”

A haka su Shuraim suka shigo suka samesu, hakan ba k’aramin burgesu yayi ba kuwa, dan haka Shuraim ya k’araso ya yi joining hug d’in Sudais kuma ya tsaya ya fara bubbuga k’afa shi ala dole sai dai a cika su a yi mishi nashi special. Cika su Ummi tayi yana ganin haka ya k’araso yayi hugging d’inta. Ahankali ta zaroshi daga jikinta ta kama hannun Shuraim ta rik’e da nashi a waje guda sannan ta kamo hannun Huda ta saka mata hannayensu a cikin nata kafin ta fara magana. “Na san ba wani girman su Shuraim kika yi sosai ba amman dan Allah Huda ko bayan raina ki zame musu uwa ki yi musu dukkkannin abunda zan yi, ba su da kamarki a duk fad’in duniyar nan.”

Da sauri Huda ta toshe mata baki da hannunta. Idonta ya cicciko da kwalla, tace “Ummi ki daina dan Allah kar ki d’agamin hankali da yammar nan! Bana son irin wannan maganar in sha Allah babu inda zaki je ki barmu muna tare…”Kukan da ya kufce mata ne ya hanata kasa k’arasa maganar tata. A hankali Shuraim ya yi hugging d’inta sannan ya d’ago idanuwanshi da suka taru da kwalla ya kalli Ummi yace
“Ummi Ki daina irin wannan maganar please, muna tare happy family together forever in sha Allah”
Ya fad’i hakan yana murmushi.

Murmushi Sudais yayi sannan yace “Group hug!” Ya had’asu duka yayi hugging yana dariyar
son ganin ya kawar da sad moment d’in. Suma duk dariyar suka saka suna sharar kwalla.

Sun d’an jima a haka tukunna Shuraim ya jaa kujerar ya zauna yana cewa “Let me eat small, yau haddar pages biyu nayi, tunda muka tashi a English section nake abu d’aya amman dukda haka sai da Mu’allim ya rankwasheni, duk cikina ya zuge.”

Tray d’in Aslam ya shiga k’ok’arin janyowa, nan Ummi ta hanashi ta hanyar buge masa hannu.

Hudan na dariya ta shiga ta d’auko musu nasu wanda ta saka a cooler. Nan kuwa suka hau ci suna santi dan ana bud’e cooler Sudais ma ya dawo yace “ya fasa tafiya saman”

Dariya kawai suka yi musu daga nan Ummi ta d’an jaa ta gefe tace, “One last thing. Taje ta yi wanka ta shirya. Yana zuwa idan ya ga ta yi miishi kwalliya nan da nan zai barta maybe ma ya barta ta kwana, haka ake yiwa maza, tayi sauri maza maza taje ta shirya yana..”

Tun kafin Ummi ta gama magana Huda ta wuce sama d’auko kayanta, kunya
da kuma son aikata abunda Ummin tace ne ya sanya ta kasa tsayawa taji k’arshen maganar.

Kamar yadda ta had’a akwatinta ta hau da shi saman hakanan ta had’oshi harda kayayyakinta waenda ta d’an d’auraye ta shanya, ta kwaso ta sauk’o da su.

Ba iya d’akin ba. Hatta parlourn zuwa yanzu ya d’auki k’amshin turaren wuta.

Tana shiga ta ajjiye akwatin ta fad’a tayi wanka tayi brush ta d’auro alwallar Magrib dan ta gabato, ta fito d’aure da d’an guntun towel, saboda bathrobe d’in da ya had’a ya wanke a washinne machine ya shanya tare da inner wears d’insa har yanzu bata gama bushewa ba.

Wani had’add’en d’inkin doguwar riga A shape ta fitar, kalar atamfar royal blue an yi mata d’inki irin mai stones d’innan…

A hankali ta ware bra da pant sannan ta kinkimi akwatin nata ta nufi wardrobe

Bud’ewa tayi ta sa akwatin nata a chan k’asa sakamokon kayansa da ta gani a jere a side har biyu! A ranta ta ce “Wato har wasu kayanma ya sake kwasowa Ummi tana chan tanata cewa In dawo d’akin bayan shi gashi partyn shi ma yake yi ya samu freedom”. Kamar tana ganinshi haka ta ke kallon kayan tana zabga musu harara. Idanunta ne suka sauk’a akan wata takarda kamar poster haka a ta chan k’asan takardar taga an rubuta ‘2021 tournament mathematics competition, Winner NTIC’

Da k’arfi taji gabanta ya buga! Da sauri tasa hannu ta zaro sticker, tun bata kai ga k’arasa zarowa ba ta fahimci ita d’in ce da gaske! A hankali ta cirota daga k’asan kayan nasa tana kallo tana sake kallon hotonta da sunanta b’aro b’aro a sama ‘Maryam Huda Muhammad’. Ga award d’inta a hannunta da medal d’inta tana murmushi. Kanta ne ya d’aure ta fara k’ok’arin juya takardar dan kamar da tana zarowa taga rubutu a bayan da biro.

“Bincike fa babu kyau” Taji muryarsa a bayanta daff da ita!.

Bata san lokacin da ya shigo ba amman ta d’anji k’amshin turaren da yake tashi ata jikin kayanshi ya k’aru a d’akin.

Kwakwalwar ta already a cunkushe take ga tarin mamaki gashi dama duhu ya d’an farayi bata kunna globe ba tana d’anjin tsoro hakan ya sanya da taji mutum da murya a bayanta ta kwala ihun da ita kanta sai da ta d’an tsorota. Da sauri ya juyo da ita ya sa tafin hannunshi akan bakinta yace “Shiiii.”

Da sauri itama ta sanya dukkanin k’arfinta ta b’intike hannunshi daga bakinta kafin tace
“Ya Aslam banaso Allah ka daina” Ta fad’i hakan tana k’ok’arin kare jikinta a rikice
dan ba k’aramin kunyar towel d’in take yi ba.

Dariya ma shi ta basa yarinyar da ya gama k’arewa kallo ba tare da ta san ya shigo ba itace take wani kakkare jikinta. Wani d’an guntun murmushin gefen baki yayi sannan ya kama towel d’in ta sama yace
“Idan ban daina ba fa? What will you do? Yaji za ki sake yi min ki gudu sama , ko me?”
Ya fad’i hakan yana d’an jan towel d’in kad’an kamar zai fisge.

Cikin tsananin tashin hankali ta sake kurma wani ihun a karo na biyu.

Ido cikin cikin suke kallon juna, so take ta d’auke idanunta a cikin nashi amman ta kasa
sakamokon sak’onnin da yake aika mata daga kwayar idanuwan nasa.

A hankali ya bud’e baki zai yi magana yaji an turo k’ofar d’akin da d’an k’arfi an shigo.

5 MINUTES BEFORE NOW.

Ummi, sauk’owarta kenan daga sama zata d’auki abu a kitchen, sam bata san Aslam ya dawo ba.
Tana shiga kitchen d’in taji kamar an shigo dan haka ta d’au abunda take buk’ata ta fito tana kallon k’ofa. Sakin lemon hannun nata tayi ya fad’i k’asa cike da mamaki da murna tace “Arshaad!!

Sai kuma ta k’arasa da sauri bakin k’ofar inda yake tsaye ta hau dudduba shi tana murmushi fuskarta cike da murna da farin ciki.

<< So Da Buri 61So Da Buri 63 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×