Skip to content
Part 67 of 73 in the Series So Da Buri by Humaira Bulama

Tabbas Mommy taso ace ta gyara Huda kafin ta tare amman jin bayanin gramma yasa kawai ta hak’ura ta k’udurta a ranta zata had’ata da Gwaggo Asabe na kwana biyu. Allah yaso ta taho da wayarta dan haka ta d’auka ta danna kiran Ummu.

Da sallama Ummu ta amsa kafin ta ce “Ina wuni Mommy ya gida”. “Alhamdulillah Ummu ya Yaran” Mommy ta amsa ta.

Sai da taji amsarta tukunna tace “To fa aikin gaggawa ya samemu…..”

Lokacin da ta shigo d’akin Huda na toilet tana wanka.

Gramma bata gaya mata komai ba daman ta fi so sai Mommy ta zo su yi mata bayani tare.

D’aure da d’an guntun towel ta fito gashinta a jik’e gabad’aya wani ya zubo ta gaba wani kuma yayi bayaYana reto yana d’igar ruwa. Sam bata ma lura da su waye a d’akin ba saboda duniyar tunanin da ta lula
Tabbas ko ta halin yaya ne yau dole ta je ta samu Mama! They definitely need to talk. She can’t believe abunda Maman ta gaya mata jiya sannan Sakina ta tabbatar mata wai gidan Baba za ta koma! Mai ya faru?
Ko dai gaba d’ayansu sun samu shigar aljanu ne! Dan in ba haka ba tayaya za ai ga Abbanta amma azo ace wai gidan wani Baba za ta koma! Granpa fa dakanshi ya je ya samesu… Wanne irin abune wannan?
Tun jiya ta kasa gane kanta har kawo yanzun nan…..’

“Dota”. Mommy ta kirata tana d’an kallonta ganin gaba d’aya hankalinta baya a kansu.

Firgigit! Ta yi ta d’ago, suna had’a ido kuma sai ta tuna da towel kad’ai ne fa a jikinta shima kuma guntu
dan haka da sauri ta juya ta koma toilet d’in tana cewa, “Mommy Ina kwana”. Bata jira jin me za ta ce baa ta rufoo k’ofar ta shiga neman bathrub.

Tana shigewa Mommy ta sauk’e ajiyar zuciya kafin a fili tace, “Ko sai yaushe Hudan zata saba da ni kamar Maryam? Sai Allah.” Tana gama fad’in haka ta kalla Gramma tace. “Bara in je In fara shiri kafin su Ummun su zo. Dan na san ba lalle ta iya sake fitowa ba balle ta sake mu yi maganar.

“Ok” Kawai Gramma ta ce mata daga haka Mommy ta juya ta fita. Tana fita dede Hudan tana fitowa itama sanye da bathrub. Ba k’aramin dad’i ta ji ba ganin bata d’akin, dan har ga Allah tayi mugun jin kunya.

Tana shirin nufar gaban madubi Gramma tace. “Zo nan Huda”

A hankali ta k’arasa ta zauna a gefen ta tace “Gani Gramma”

Sai da ta sauk’e ajiyar zuciya tukunna tace “Shawara nake so in baki…Ki daina nunawa Mommy kamar suruka take a wajenki. Instead ki d’auketa kamar Mama ki sake da ita. Tana matuk’ar k’aunarki, ki saki jinkinki ku saba sosai, za ki ji dad’in hakan. Magana ta biyu. Ki shafa mai ki jirani zan kawo miki kayan da zaki saka yanzu! Granpa ya ce akaiki gidan ki za a gyara kina ciki.”

Da sauri ta d’ago ta kalli Gramma.

D’aga mata kai tayi alamar gasgatawa sannan tace “In kuma kinada ja to mu je in raka ki wajensa”. Ta fad’i haka tana d’an b’ata rai saboda ta lura In ba hakan tayi mata ba to fa sai an sha drama da ita
dan gashi idanunta har sun ciko da hawaye.

A hankali ta girgiza kanta alamun ‘a’a’. Sai kuma ta mik’e ta nufi gaban mudubi hawaye na bin fuskarta.

Tana gama shafa man Gramma ta shigo da wasu had’add’un kaya riga da zani da alkyabbarsu sai kyalli suke yi sannan kamar wanda aka yi design d’in edges d’in da gwal! Tana ajjiyewa ta juya ta fita. Bata dad’e ba ta dawo da kasko da wata robar Kaplas, sannan ta sake komawa ta d’auko kujerar tsugunno.

Ita dai Hudan tana zaune kawai tanata binta da kallo dan tunda ta gama shafa man ta dawo kan gadon ta zauna ta yi shiruu tana ta tunani.Gramma na gama shigowa da kayayyakinta ta sa kwaskon garwashin a k’asan kujerar sanann ta bud’e kaplas d’in. Wasu y’an k’ananan robobine masu murfi a ciki! Sai da ta bud’e kusan duka ta d’eba wannan ta d’eba wannan tukunna ta tara akan murfin roba d’aya, ta kalla Hudan tace mata “tashi”. Sai da ta tashi tukunna ta k’arasa ta d’auko k’atoton bargon kan gadonta sannan ta dawo ta wareshi ta ajjiye a gefe kafin ta d’auki had’in da tayi na kan murfin robar ta zuba a cikin kaskon wutar ta saman kujerar tukunna ta umarceta da ta zauna da wuri.

Sai da ta rufa mata k’aton bargon tukunna ta ce ‘ta kwance bathrobe d’in jikinta ta bata’
A hankali ta warware ta mik’a mata sai kuma ta fara k’ok’arin tashi dan wani zafi ne ta fara ji yana ratsa tasaboda hayak’in ya fara turnuk’e koina a cikin bargon.

Sai da Gramma ta yi da gaske tukunna aka samu Huda ta zauna, har da hawayenta kuwa fuskarnan ta yi jajawur.

Tana nan zaune suka ji ana knocking! Sai da Gramma ta kora mata warning d’in karta motsa tukunna taje ta bud’e k’ofar. Murmushi tayi sanann tace “Ashe ma kishiyar tawa raguwa ce nake ta jin tsoro?
Shigo ki ga kuka wiwi a iya tsugunno kawai.”

Tana jin murmushin Ummu ta fahimci itace, ai kuwa ta fara zillo tana lek’awa nan suka had’a ido. Tana shirin tashi Ummu tace “dalla zauna”. Cikin sigar tsokana. Wani sabon farin cikin ta sake ji ya lullub’e ta sakamokon ganin Sakina sun shigo ita da mommy suna yi mata dariya suma.

Cikin mutunta juna aka shiga gaggaisawa daga nan Gramma ta fita tace musu
“Ku k’arasa shiryata dan ni kam ragwanta da shagwab’a take ta yi min”.

Ummu ma da nata ta zo, dan haka bayan ta tashi a na Gramma sai da ta kuma wani zaman
sannan kafin awa biyu suka sakata ta shanye tsumi wajen roba uku! Ita kam gaba d’aya ma fitsari take ta ji sai faman zaryar toilet take yi, da tayi magana kuma Ummu ta rufeta da fad’a! Dan ma Mommy tana d’an kareta. Sakina kam tana gefe kawai a zaune ta yi shiruu sai da murmushi kawai kamar ba Sakina ba.

Aaima na zaune a parlour ita kad’ai tana karatun Alqur’ani, Aslam ya shigo.
Dama itan yake nema kuma yaci sa a ya sameta ita kad’ai dan haka ya k’arasa ya zauna a kusa a ita.

Sai da ta kai aya tukunna ta d’ago tana kallonshi tana murmushi.

Murmushi ya mayar mata kafin yace “Can we talk?”

A hankali ta jinjina kai alamun ‘yes’.

Sai da ya sauk’e ajiyar zuciya tukunna ya ce “Huda zata tare yau”

Shiruu ta d’anyi ta sunkuyar da kanta.

A hankali yana nazartarta yace “You are my only sister Aaima. Relationship d’in dangin Miji da Matar wa yana lalacewa ne idan akai rashin sa’ar samun rashin jituwa tsakanin Sister’s d’inshi da Matar tasa! Ko da ace uwar Miji bata son surukar indai Sister’s d’in suna k’aunarta to su kan iya bata shawara a zauna lafiya kuma itama uwar Mijin in dai taga surukar tana jan y’ay’anta a jiki tou za a zauna lafiya.

Ke ce mace a tsakanin mu duk kan mu har Auwal da da su Shuraim, although Huda is also our sister
amman kasancewarta wife d’ina ya sa dole ta amsa sunan suruka a tsakaninmu. Ni Ke Arshaad Mammy da Mommy. Mommy is morethan good with Huda being my wife amman ban san ke ko Mammy ba! Ke, za ki iya gyara tsakaninta da Mammy sannan za ki iya b’atawa but first Aaiima please. Inaso ki goge haushinta da kike ji na zuwan Mammy cell tunda ba ita ta kaita da kanta ba, ina so ku koma kamar daa, Arshaad yace min kuna shiri sosai da farko ku zauna lafiya please hankalina zai fi kwanciya daga nan kuma sai ki yi aikin gyara tsakaninta da Mammy dan na san za ki iya.”

Tunda ya fara magana Aaima ta yi shiru tana sauroronshi, sai da ya dire aya
tukunna ta d’ago ta kalleshi tace, “Ya Aslam, komai ya wuce. A b’angarena komai ya wuce,
na yi maka alk’awari za mu koma kamar da ni da Hudan in sha Allah after all she’s my only sister sannan sister in-law. Gaskiya Ya Auwal ya fad’a a ranar da zai wuce shi da Mom, kafin ya tafi, ya ce min ‘I really need to relax. In daina biyewa duk abunda zuciyata ta yi karo da shi a karon farko na b’acin rai ko akasin haka! In bud’e idanuna da kyau! There is more to life than holding onto the past’ Agaskiya nima sai yanzu na fahimci ba laifin ta bane” Sai da ta d’anyi murmushi sannan tace “I owe her an apology,
In sha Allah zan bata hak’uri, wannan duk ba wata matsala bace, In sha Allah. Ka kwantar da hankalinka
Hudan and I will be good.” Ta fad’i hakan tana murmushi.

Kamar kuma wadda ta tuna wani abun sai tayi shiruuu ta shiga tunanin, chaan! Ta sauk’e wata k’akk’arfar ajiyar zuciya kafin tace “Matsalar a nan shine. Ya Arshaad! Ba zan b’oye maka ba. Ina jin tsoron wani abu. Not that wai Ina tunanin Ya Arshaad bai hak’ura ba or something like that, amman so makaho ne
kuma inaso ka san cewa har gobe Ya Arshaad yana son Huda, so mai tsanani!! Ban san abun yi ba, ban san abun cewa ba saboda gaskiya ni kaina I’m confused and broken akan lamarin nan. Ina tausaya masa.
Jiya kusan a parlourn nan na kwana ba wanda ya sani saboda Ina so in kammalawa Ummi sauk’ar da nake yi mata a yau shiyasa jiya around 12 na sauk’o na fara karatu dan ina buk’atar chanjin waje…
Da farko magana sama sama na fara ji, sanin da na yi cewa shi kad’ai ne yasa na k’arasa dan inji ko lafiya, sai da na je bakin glass door d’in naji ashe waya yake yi. A hankali na d’an tura na ganshi a tsaye a parlourn yana waya yana safa da marwa gaba d’ayan shi a rikice! Yana gama wayar ya kama hanyar d’akinsa ya shige
ni kuma na zuge na bishi a hankali na tsaya a bakin k’ofar d’akin! Wallahi Ya Aslam kukan da na ji yana yi sai da na tsorata!”

Da sauri Aslam cikin katseta ya ce, “Ki je side d’in Gramma, Ku shirya ki raka Huda
Ta shi ki je yanzu na san sun kusan kammalawa”

Za ta yi magana ya ce “Aaima please, je ki! Ki mata rakiya. Mommy ne kawai achan ata wajena”.

A hankali ganin yadda idanuwanshi suka kad’a suka yi jaaa, ta mik’e ta ajjiye Alqur’anin akan side table ta nufi sama domin chanjawa. Tana shiga ta cire hijabi da y’ar kantin doguwar rigar da suke jikinta ta saka atamfa ta fesa turare ta d’au mayafinta ta fita.

Har ta zo ta wuce bai ma sani ba! Ya rufe fuskarshi da tafukan hannunshi banda “innalillahi wa inna ilaihirrajiun” ba abunda yake maimaitawa cikin tsananin tashin hankali. Ya dad’e kafin ya samu kwakwalwar shi ta gama lissafi, a hankali ya mik’e ya nufi side d’in Arshaad, sai dai yana zuwa ya bincika koina amman babu shi ba alamunshi kamar ma babu abubuwan amfaninshi…Haka ya fito kanshi a hargitse
ya nufi gidanshi dan yana so ya sallami cleaners d’in da suka gyara suka goge su tafi kuma yana so ya duba
waenda suke sauk’a tare da shi ko sun gama nasu suma a samu su wuce kafin su Gramma su k’araso.

Yana shiga ya tarar da su Dad da Daddy tare da masu gadaje ana ta faman jere. Cikin girmamawa ya shiga gaidasu yana mamakin su dan kusan komai an kawo. Daman kuma shima ya siya wasu kayan a nan Kano d’in saboda ba lokaci d’azu! Dan haka nashin ma suna isowa aka hau kafi…..

Hudan na gama shiryawa Gramma tace “su tafi a kaita” Dede nan Aaima ta shigo. Cikin fara a suka gaisa da Sakina bayan ta gama gaisawa da su Ummu daga nan suka fito gaba d’ayansu.

A k’ofar gidan suka samu Junaidu a cikin mota a zaune, gefe guda kuma motar drivern da Mommy tace ya zo ya jira su, dan haka suka shishiga.

Har cikin gidan Junaidu da drivern suka kaisu tukunna suka fito.

Ummu ce rik’e da ita suna zuwa bakin k’ofar shiga tace “ta shiga da k’afar dama da bismillah”
Anan suka tarar da su Dad da masu d’aura kaya. Royal chairs har set biyu ta samu a parlourn k’asa
da dining da tv stand da centers show glass duk komai na royal d’in.

Dad ne ya ce ‘su kaita main bedroom na chan sama an gama shiryawa’ da “to” suka amsa daga nan suka nufi saman. Duk d’akuna biyun an gama kafa gadajen dan haka suka nufi nata d’akin.

D’akin da gani Aslam ne ya sa furnitures d’in saboda favorite color d’inshi ne. Tsayawa fad’an had’uwar d’akin ma b’ata baki ne. A bakin gadon suka ajjiyeta, suka yi mata Nasiha mai ratsa jiki daga nan Gramma da Mommy suka wuce. Ummu ma ta mik’e ta tafi tace “Junaidu anjima zai dawo ya d’auki Sakina.
Saboda kar taji shirun yayi yawa kafin a gama jeran Aslam ya shigo.” Da kyar kuwa Huda ta barta ta tafi itama Ummun har da y’ar kwallarta.

Daga nan d’akin ya rage saura su uku. Ita Aaima da Sakina.

Suna gama fita Aaima ta mik’e ta k’arasa inda Huda take ta yaye mata hular alkyabbar jikinta tana murmushi tace “Amaryar Ya Aslam”

K’asa Hudan ta yi da kanta tana goge hawayenta.

A hankali Aaima ta sa hannu ta shiga goge mata hawayen sanann tace
“Amaren yanzu fa basa kuka, haba mana kar ki bada girlss”
Dariya suka saka gaba d’ayan su har ita Hudan tana d’an share hawaye tana dariya.

A gefenta ta zauna suka sakata a tsakiya kafin tace, “Kwanakin baya mun d’an samu misunderstanding… Uwa daban ce Huda, therefore i hope za ki fahimceni. Sannan ku yi hak’uri daga ke har Sakina”
Sannan ta d’an lek’a Sakinar ta ce “I know i was rude that day da kika kirani a waya, i shouldn’t have talk to yo…..” Cikin katseta Sakina ta ce “Haba Aaima, dan Allah ki manta da komai ya wuce, mun fahimci situation d’inki. You will lways be our big sis sanann kuma friend at the same time”.

D’agowa Hudan ta yi itama ta d’an kalleta sannan ta ce “Ba komai Aaima ya wuce.” Ta yi maganar tana kamo hannunta.

A hankali Aaima ta ce “thank you”. Murmushi suka yi dukkan su kafin Aaima ta ce
“Sakina daman ina son ganinki. Na ma shirya zuwa inje In sameki sai kuma gaki yau Allah ya had’a mu.”
Da mamaki Sakina take kallonta kafin ta gyara zamanta ta bata dukkannin attention d’inta”

Sai da Aaima ta sauk’e ajiyar zuciya kafin ta ce, “A kan Ya Auwal ne”

Da sauri Sakina ta lumshe idanuwanta ta yi k’asa da kanta. Tun ranar da Huda ta ce mata ciwon zuciya gareshi shikenan ta rasa nutsuwarta. Ta tabbata itama yanzu haka maybe ta kamu da nata ciwon zuciyar..

Aaima ba ta tsaya jira ba ta ci gaba da magana “Tun ranar da za su tafi, mun yi magana da shi a kan ki!
Sanann jiya ma sai da muka yi chattinga da Mom! Shi kam yama daina chat zuwa yanzu
tun shekaran jiya da oxygen yake iya numfashi! Bar ganin muna raha a cikin gidan nan wallahi kowa kawai k’ok’artawa yake yi amman dukkanmu hankalinmu a tashe yake. Sakina na san Ya Auwal farin sani!
Ba zan b’oye miki ba har dating d’inshi nayi. Tunda nake a rayuwata ban tab’a ganin Ya Auwal yana soyayya bilhakk‘I da gaskiya ba sai a kan ki! Kinga na farko. Saboda ke ya shiryu, duk wani bad habit da yake yi yanzu ya daina. Sannan ranar da zai tafi duk wani abun da ya tab’a yi a company da sharrin da ya yiwa mutane duk sai da ya fad’awa Granpa! Ya nemi yafiya. Na uku, ki duba kiga mawuyacin halin da yake ciki! Duk fa a kanki ne fa Sakina. Wallahi na manta rabon da inga mutum yana tsananin rashin lafiya akan soyayya sai a lamarin ku!

Dan Allah ki duba halinda yake ciki ki san abun yi tun kafin mu rasa shi. Jiya Mom cemin ta yi
ciwon ya motsa jininsa ya hau, ga ulcer! Sakina ki taimaka. Ni ko number Ashraff d’inne ki ba ni, ni na san me zan gaya mishi.. Please Sakina.” Ta k’arashe maganar cikin karyewar zuciya.

Da gudu Sakina ta tashi ta shige toilet ta rufo k’ofar. Tana shiga ta fashe da wani irin gigiceccen kuka.

Ahankali Huda ta sauk’e ajiyar zuciya kafin ta ce “Me za ki cewa Ashraff d’in in kin samu numbershi?”

Kawai zan rok’esa ne akan ya je ya ga halinda Ya Auwal yake ciki. Zan iya biya mishi kud’in jirgi ma kawai ya je yaga halinda ya ke ciki! Daga nan ya san abun yi. Wallahi Huda zan iya dafa alqurani akan
Ashraff baya yiwa Sakina kwatankwacin son da Ya Auwal yake yi mata.”

Ajiyar zuciya Huda ta sauk’e kafin tace “Kuma itama Ya Auwal d’in take so”

Da sauri Aaima ta juyo tana kallonta sosai.

Jinjina kai Huda tayi kafin tace “Ni dama na dad’e da fahimtar hakan. Tou kuma jiya Ashraff d’in ya sake tabbatar min. Ya min complain akan. Ko kiranta idan yayi bata iya d’auka wani lokacin, sannan In zata kira sunanshi sometimes sai ta ce masa Ya Auwal! Wani lokacin in ta fahimta ta yi saurin gyarawa.
Kwata kwata bata bashi time..Shine ya kirani akan wai In na samu time yana son mu yi magana
face to face sannan kuma wai waye Ya Auwal?!”.

Cikin rashin jin dad’i Aaima ta ce “To ai za su cuci kansu ne daga ita har Ashraff d’in!
Kawai kamata yayi ta fito ta gaya mishi gaskiya shi kuma ya hak’ura.”

A hankali Huda ta sauk’e ajiyar zuciya kafin ta ce “Bara in baki number tasa ku yi magana”

“Okay ba ni”. Aaiman tace tana mik’a mata wayarta.

A hankali Huda ta zaro wayarta wadda ke nan rik’e a hannunta daga cikin alkyabbar jikinta ta bud’e ta juye mata nambobin Ashraff a wayar ta mik’a mata.

Message ta tura mishi, ‘yau an kai Huda gidanta so ba zata samu damar sauraronshi ba
amman ta fad’a mata komai game da issue d’in da yake facing ta b’angaren Sakina! If he’s free ya zo su tattauna’.

A hankali Huda ta mik’e ta k’arasa k’ofar toilet d’in ta fara yi mata knocking..
Ta d’an jima kafin Sakinar ta bud’e k’ofar ta fito a hankali tana tsane ruwan fuskarta da hannunta
alamun ta wanke fuskar ne.

Bata ce mata komai ba ta rab’a ta gefenta ta wuce..

Inda take zaune a kan gadon ta je ta gyara pillow ta koma chan k’arshe ta jingina da jikin gadon ta lumshe idanuwanta bata ma bi ta kan Aaima da take cewa, “Yace gashi nan zuwa har ta bashi adreess” ba.

Kamar minti talatin ya kira number Aaima ya ce “yana bakin estate d’in”.

Aiima bata yi minti ashirinba ta dawo. Tun da ta shigo suka lura da yadda jikinta ya yi sanyi over.

A hankali ta nemi waje ta zauna a gefe ta yi shiruuu, ita kad’ai!

Sai ta d’an yunk’uro za tayi magana sai kuma ta koma ta yi shiru, dan ita ba ma ta san ta ina za ta fara ba.

Su dai su Hudan ido kawai suka dinga binta da shi kafin Huda ta yi k’arfin halin cewa
“Aaima lafiya kuwa?” Dan suma yanayin nata ya saka su a rud’ani.

Har ta yunk’uro za ta yi magana kamar farko sai kuma ta sake yin shiru kafin tace “ina zuwa” Ta fad’i hakan tana d’aukar wayarta.

Gallery ta shiga ta hau bincike har ta nemo hoton da take nema! Kamar za ta mik’a musu
sai kuma ta ce “Bara in baku wani d’an tak’aitaccen labari.

Akwai wata k’awar mu da muke department d’aya level d’aya d’aki d’aya da ita a Nile! Mu hud’u ne a group d’in mu, ni da ita da ragowar friends d’inmu su biyu tun farkon zuwanmu tare muke har yanzu da muka zo k’arshe.” Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin ta ci gaba. “Wadda muka fi shirin da ita ita ce ‘Suhailat’
K’ut da k’ut muke ni da ita sosai. Akwai wani saurayinta da suke tare tun farkon zuwanmu Nile
ta ce min tun a secondary school ta san Abokinsa tare suka yi makaranta secondary ajinsu d’aya!
To irin sun d’an shak’u d’innan kamar besties haka suke.

Wata rana Ina tunawa muna level 1 lokacin ya zo kawo mata ziyara (shi bestyn nata) sai suka zo shi da wani Abokinsa mai suna ‘Sageer’. Tun da Sageer ya kyalla ido ya ga Suhailat tashi d’aya ya ji yana sonta!
Kasa ma hak’ura yayi mu koma a lokacin dayake ni na rakata, a take yake cewa Abokin nasa shifa ya ga mahad’in shi! Bai bar wajen ba sai da number da address d’in gidansu Suhaila na nan Kano.

To ashe itama Suhailan duk kanwar ja ce dan muna komawa d’aki itama ta haukace mun haka nan ta dinga yabon kyawun Sageer d’in da had’uwar shi, sanann ta sanar da ni yanda ya samu kyakkyawan gurbi a cikin zuciyarta.

Kafin wata d’aya, Soyayya da shak’uwa mai zafi ta shiga tsakanin Suhaila da Sageer…

A Dawowar da nayi kafin exams lokacin bikinku da Ya Arshaad, kafin In koma wani mumunnan alamari ya afku ata dalilin rashin wayon Suhaila! Ta biyewa soyayya ta mallakawa Sageer kanta, gaba d’aya bayan ya
d’auketa sun je sun yi court marriage sai kace wasu marasa mafad’i! A cewar sa hakan zai sanya ta yarda da shi ta aminta ita zai rayu da har abada tunda ita a tsarin gidansu. Mace sai tayi phd tukunna take yin aure!
Haka nan Babansu yake da wannan muguwar ak’idar, shi kuma Sageer ya ce ‘in dai ita kad’ai zai so kuma ita kad’ai zai aura zai kula, to ya kamata ta fahimci a yanayin tsarin halittarshi ta d’a Namiji ba zai iya yi mata wanann dogon jiran ba’.

In tak’aice muku labari dai ciki yana yin wata d’aya ya baiyyana kanshi a jikin Suhaila!
Dan tsananin laulayin da take yi ya sanya hatta matan dake gefen d’akin mu sai da suka
soma fahimtar wani abu game da wannan k’addarerren cikin! Dan ta ce babu kalar protection d’in da ba suyi using ba.

Ba yadda muka iya haka muka rufa mata asiri mu uku muka nufi asibiti da ita
dan tace idan Baban ta ya san labarin wallahi na lahira sai ya fita jin dad’i! Yadda kika ga Granpa to haka itama Babanta yake da mugun tsauri! Kuma ita abun nata ma duka biyu za a iya cewa dan Mahaifiyarta itama hakan take da tsauri.

Muna zuwa muka zubewa Likitan kud’i muka gaya mishi flushing muke so a yi mata duk da tanata ce mana ance ‘tana da matsala cikin ba zai fita ba’ Amman still muka zab’i mu gwada sa’ar mu. Bayan y’an gwaje gwaje unfortunately. Likitan ya zaunar da mu yayi mana cikakken bayani akan cikin nan ba zai fita ba!
Saboda tanada matsala kuma in dai ance za a cire d’in tou it’s either ta mutu ko kuma ta samu uterus failure.

Bamu da wani zab’in da ya wuce mu nemi Sageer duk da kuwa ta ce mana ‘tun last zuwanshi da ta ce mishi tana da ciki ya d’auke ta ya kaita asibiti aka gaya mishi abunda aka gaya mana! Kwana d’aya kawai yayi mata a gidan da suke had’uwa daga nan ya k’ara gaba kuma tun daga ranar ko wayarshi ta kira a kashe take jin ta. Although bai nuna mata komai ba dan faram faram ma suka rabu ko amai idan ta yi shi yake kwashewa ya gyara gurin yana ta faman jera mata sannu’.

Wani babban tashin hankali da abun al’ajabin da muka fuskanta shine. Hatta gidansu Sageer da address d’insu da ya bayar a garin Gombe gaba d’aya fake ne! Hatta sunan Babanshi. Alhaji Bashir mai galon da ya fad’a mana gaba d’aya k’arya ne. Har Gombe d’aya a cikinmu ta rok’i saurayinta ya je ya bincika mana
amman babu abu d’aya da yake gaskiya a cikin labarin Sageer! Komai fabricating kawai yayi.

Da muka fahimci haka sai muka koma wajen Bestien ta, to shima dai ta wajen na sa duk sammakal dan ce mana ya yi shima Iyakar wannan information d’in da muka sani akan Sageer shima shi kad’ai ya sani, ya ce
a wajen ball suka had’u suka fara shiri suka d’anyi business tare, ranar kuma suna tare ya ce masa zai je wajen k’awar shi shine yace zai rakashi. Shi bestyn nata ma cewa yayi wai ‘mu yi ta addua gaba d’ayan mu
maybe aljani ko maye muka had’u da Allah ya tak’aita’.” Ajiyar zuciya Aaima ta sauk’e sannan ta ci gaba da cewa. “To yau dai Allah ya had’ani da Sageer!” Bata gama rufe bakinta ba ta mik’a musu hoton data nemo a wayar tata tun d’azu.

Sakina ce ta fara karb’ar wayar tana kallonta kafin ta sauk’e idonta a kan wayar.

A hankali Huda ta ce “Innalillahi wa innailaihirrajiun” Bayan itama ta l’eka ta gani.

Sakina kuwa lumshe idonta kawai ta yi ta bud’e ta kalli Aaima idonta jazir tap kwalla ta ce, “Aaima are you sure??”

“Very sure Sakina! Ki yi ta sliding za ki ga pictures da videos d’insu kala kala irin wannnan shi da Suhaila.

Daga nan ki gaya min Idan wannan bawan Allahn ba Ashraff bane ba.”

<< So Da Buri 67So Da Buri 69 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×