Tun 11 na safe take bulayin neman gidan mai tuwo tuwo har 4 na yamma bata samu ba, kusan kaff Unguwar ta Gandun Albasa har kwargiji da wajejen Gada duk babu inda ba ta duba ba.
Ganin ta kusa shiga GRA d’in Sharad’a ne ya sanya ta koma da baya ta ci gaba ta kutsa kai tana nema.
An nuna mata gidan mai tuwo tuwo har biyu amman ba nan bane ba kuma su ba sa siyar da zob’o.
Idan ka ganta sai ka tausaya mata, duk ta yi wujiga wujiga ga yunwa ga gajiya sannan ga. . .