Skip to content
Part 7 of 73 in the Series So Da Buri by Humaira Bulama

Tun 11 na safe take bulayin neman gidan mai tuwo tuwo har 4 na yamma bata samu ba, kusan kaff Unguwar ta Gandun Albasa har kwargiji da wajejen Gada duk babu inda ba ta duba ba.

Ganin ta kusa shiga GRA d’in Sharad’a ne ya sanya ta koma da baya ta ci gaba ta kutsa kai tana nema.

An nuna mata gidan mai tuwo tuwo har biyu amman ba nan bane ba kuma su ba sa siyar da zob’o.

Idan ka ganta sai ka tausaya mata, duk ta yi wujiga wujiga ga yunwa ga gajiya sannan ga k’ishirwa. Tana cikin tafiya ta ga ta fara hango kwandila a tsallaken titin side d’in da take, sanin da ta yi cewa gidan mai tuwo tuwo ba a kwandila yake ba ne ya sanya ta yanke shawarar komawa gida kawai! Ko da kuwa Ya Ja’afar zai kashe ta da duka ne.

Har za ta juya sai ta hango tuk’a tuk’a, k’ishin da take ji yasa ta yanke shawarar ta tsallaka ta sha ruwan inya so sai ta tsallako ta koma ta tafi gida.
Da kyar ta samu ta tsallaka, ta rok’i wani almajiri ya buga mata, ta samu ta sha.

Ta gama sha kenan! D’agowar da zata yi sukayi ido biyu da wani mahaukacin kare, da alama shima k’ishin ruwan yake ji dan ya k’urawa ragowan ruwan da bai gama tsiyaya ta kan famfom tuk’a tuk’an ba ido.

Yunk’urawa ya yi ya tunkarota cikin sauri, ai kuwa babu shiri ta nannad’e zanin jikinta ta kwasa a guje, a tunanin ta ita ya biyo. Shikuwa Karen ganin ta hau gudu kamar jira yake yi kawai sai shima ya bita a guje.

Tsere suke zubawa ita da Karen nan tana ihu tana neman Agaji, musamman ma da ta tuno da wata magana da Sakina ta tab’a gaya mata in dai kare ya kama saman dunduniyar k’afar mutum ta baya to cirewa yake yi gaba d’aya. Kai da tafiya har abada.” Ai kuwa nan ta karaa ƙarfin gudun nata.

Wasu su yi mata dariya wasu su ji tausayinta wasu kuma ta basu mamaki. Gata nan dai doguwa kyakkyawa y’ar budurwa da ita amman ta zage tana tik’ar gudun ceton rai a wajen Kare.

Ganin da tayi k’afafuwanta sun fara zafi sosai, gashi ta gaji!! Ya sa kawai ta yi kalmar shahada ta tsaya chak! sannan ta juyo ta durk’usa, daidai karen ya iso dab da ita, ta rufe idanunta da mugun gudu da k’arfi ta hau had’ashi da Allah tana cewa “dan Allah dan Annabi ka yi hak’uri, kar ka cijeni, na gaji ka yi hak’uri…”

Ta kusan mintina 2 a haka, Jin shiru yasa ta bud’e idanunta a hankali k’irjinta na dukan uku uku.

Cikin ikon Allah kuwa babu Kare babu alamar shi. Hamdala ta yi ta mik’e da niyyar tafiya gida, sai ta ganta a tsakiyar kwandila. Layin shiru ba kowa sai maka-makan Gidaje, mota d’aya ta hango a k’ofar wani had’add’en gida da alamar mamallakin motar yana jira ne mai gadi ya bud’e masa ya shige.

Bayan wannan motar babu komai kuma babu kowa a layin. Dubawa ta yi sosai ta ga ba ma ta san a ina take ba, sai a lokacin ta fashe da wani irin kuka ta zauna dab’ass!! A wajen ta cusa fuskarta cikin cinyoyinta.

Bai dad’e da shigowa cikin Unguwar ba, akwai wasu takardu da Abba ya sanya shi zuwa ya d’auka dan yana son yin amfani da su kuma har an tarkato an kawo sabon Gida.

Yana shirin danna horn kenan ya ji kamar ihu!! Kasancewar bai rufe gaba d’aya glass d’in motar tasa ba.
Yana kallon direction d’in da ya jiyo ihun nata kuwa ya hango ta ita da Karenta. Da farko abun dariya ya bashi, sai kuma ta fara bashi tausayi…da har zai je wajenta sai kuma ya fasa ya dannawa sabon mai gadin da aka saka a Gidan horn ya bud’e masa ya shige.

Bai b’ata lokaci ba ya shiga, inda takardun suke ya je ya d’auko ya fito ya shiga motarsa ya sake yin horn aka bud’e mishi gate d’in ya nufi waje.
Kamar ance ya juya, yana juyawa ya ganta this time around ta cusa fuskarta tsakiyan cinyoyinta kuma babu Karen a wajen.

Kawai tsintar kansa yayi da son zuwa wajen ta, da farko kamar ba zai je ba sai kuma yayi tunanin inda Aaima ce a wajen ai da ba zai so a barta ita kad’ai haka ba.

D’an rivers ya yi sannan ya karkata hancin motar ya nufi inda take.

Yana isowa ya d’an tsaya, ya kasa fitowa kawai yana kallonta, dan ji yake yi kamar ya juya.

Ya d’an jima a haka sai kuma yayi tsaki ya bud’e motar ya fito ya zo ta gabanta ya tsaya.

“Hey!!”

Ya ji shiru, sake maimaitawa yayi tukunna a hankali jin kamar mutum a tsaye a kanta yasa ta d’ago fuskarta wadda ta jik’e da hawaye tana kallonsa.

Da k’arfi ya ji zuciyarsa ta wani irin bugawa sakamokon had’a idanun da suka yi, ita kuma ganin sa da tayi ya sanya da saurinta ta mik’e tana karkad’e zaninta d’ayan hannun kuma tana goge hawayen da ya k’i tsayawa da bayan hannun.

Tsayawa yayi yana k’are mata kallo a ransa yace “Who’s she?? How can someone be this beautiful??”

“Ina yini” d’in da tace masa ne ya dawo da shi daga duniyar lissafi da k’are mata kallon da ya tafi.

Da kyar ya iya tattaro kalmar “Alhamdulillah” Dan zuciyarsa bugawa take yi ba kad’an ba.

“Dan Allah ka san hanyar gidanmu?”

Ya sake jin muryarta. This time around sai da ya lumshe idanunsa ya bude tukunna ya iya ce mata “A’a, why are you crying?”.

Ta fahimci tambayar da yayi mata, duk da cewa a iya primary ta tsaya. Amman kuma sai ta tsinci kanta da kasa bashi amsa, ta ga yawan maganarsa turanci ne, kar taje ta bashi amsa da Hausa ya kasa ganewa kuma
tana tsoron yin turanci dan ba wani iyawa ta yi ba, kar taje yayi mata dariya kamar yadda su Ya Jalila suke mata a duk lokacin da ta yi turanci.

Ganin ta yi shiru yasa ya fara tunanin ko bata jin turancin ne domin kuwa yanayin duk’unk’unennen hijabinta da kod’add’en zanin jikinta kad’ai sun isa su fad’awa mutum ita d’in ba wata shahararriyar y’ar Boko ba ce ba. Dan haka ya yanke shawarar maimaita mata tambayar da Hausa.

“Me ya saka ki kuka??”

Da mamaki a fuskarta, ta ke kallon sa jin Hausar tasa tarr!! A ranta ta ce “To ko dai koya yayi??” Dan tabbas ita dai ta san wannan ba bahaushe bane ba, ko dai balarabe ko kuma d’an India, saboda yanayin cikar gashin kansa, gashi a kwance sai kyalli yake yi, shigen na larabawa, gashi fari sosai, duk da cewa itama bakinta pink ne amman ta san nashi ya fi nata zama pink sosai, ga hancinshi mai kyau d’an dogo, sannan idanunsa irin manyan nan kuma a kwance dogaye, kuma wani ikon Allah yanayin shape na gashin girarsu iri d’aya, ba irin cika d’innan ne da girar ba, amman shape d’inta na medium arch ya fito sosai.

Shi kam Arshaad zuwa yanzu ya fara tunanin ko dai kurma ce Yarinyar nan?! To amman kuma ai d’azu har gaida shi ta yi. A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya ya sake ce mata.

“Umm?”

Yana mai tsare ta da idanuwa dan yaga kamar ba ta ji na farkon ba.

K’asa ta yi da kanta ta fara wasa da y’an yatsun hannunta kafin tace
“Ya Ja’afar ne ya ce in siyo mishi zob’o, na manta gidan, tun ina Yarinya aka hanani zuwa, kuma yanzu na b’ata.”

Ta yi maganar tana share siririn hawayen da ya zubo mata da bayan hannunta.

Shi kam he don’t know Y amman yanayin maganarta burgesa yake yi, komai nata a nutse take yinsa, ya dad’e bai ga mace mai magana cikin nutsuwa da kamewa ba kamar ita.

A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya ganin ta d’ago kai ta kalleshi a karo na biyu bayan gama yi masa maganar, sai kuma ta sake yin k’asa da kanta ta cigaba da goge hawayen.

Wani white handkerchief ya zaro daga cikin aljihunsa ya mik’a mata. Da farko k’in karb’a ta yi sai da yace “Ungo ki goge fuskar ki, ya b’aci da yawa da hawaye, Yara za su yi miki dariya.”

Tukunna a hankali ta sanya hannu ta karb’a ta fara goge fuskarta tana lumshe idanu saboda wani fitinannan k’amshi da yake shigar mata hanci.

Sai da ta goge hawayen tass sannan ya ce “Zo, mu je ga mota sai in kai ki Gida.”

A hankali ta girgiza masa kai sannan tace “Ban san ka ba, ba zan shiga motar ka ba.”

Wani d’an cute smile ya yi, kafin yace “To in tarar miki napep za ki shiga??”

Da sauri ta d’aga mishi kai alamar ‘eh’.

Smiling ya yi har sai da hak’oransa suka d’an baiyyana, sannan ya ce “To shi a ina kika sanshi? Me napep d’in!”

Rau rau ta yi da idanunta, har za ta yi magana sai kuma tayi shiru tana wasa da yatsun hannunta, dan bata da amsar da za ta bashi.

Ganin hakan yasa yayi locking motanshi daga inda yake da key d’in, sannan ya fara tafiya ya ce “mu je In saka ki a napep d’in.”

Da saurinta ta bi bayanshi a hanyar yake tambayar ta sunan ta, tace masa “Huda.”

Basu wani dad’e suna tafiyar ba, tun kafin su fita a kwandila suka samu napep, ta fad’a mishi inda zai kaita ta shiga.

D’an sunkuyowa ya yi yana kallonta a cikin napep d’in, ji yake kamar kar su rabu amma da ya tuna ya ji sunan layin Gidan nasu yanzun har ma da d’an guntun kwatancenta da ta yiwa mai napep d’in duk ya haddace. Sai kawai yace mata “ki gaida gida da su Mama.”

Daga haka ya zaro 1k a aljihunshi ya bawa mai napep d’in, kafin ya yi waving nata yana smiling suka yi gaba suka bar shi a wajen.

Har ya isa inda motarshi take ya shiga ya ja yai gaba, yana smiling.

Ita kuwa Huda mamakin kyau da had’uwa da gayun shi take ta yi, duk da ta san su Ya Junaidu ma kyawawa ne sosai amman wannan kam ya fi su, gashi da kirki.

A haka suka shigo layin su, ta nuna k’ofar gidansu aka ajjiyeta. K’irgo y’an chanji mai napep d’in ya yi (950), har ta d’an yi gaba ya kirata ta dawo ya mik’a mata.

Sai a lokacin ta ji gabanta ya fad’i domin kuwa ta san tabbas ba za ta b’oyewa Mama abunda ya faru ba, gashi kuma har da sakota a napep har k’ofar gida, ta ina za ta fara bayani, waye shi?? ya aka yi ma ta sake da shi haka bayan jan kunnen da Mama ta sha yi mata a kan maza!? Mai ya sa duk wannan tunanin ba su zo mata ba d’azu??.

Muryar mai napep d’in ce ta katse mata tunanin da take yi “Ungo mana, ko bakya so?” D’aga mishi kai ta yi a hankali tace “Ka rik’e na bar maka.” Daga haka ta juya ta nufi gida da sauri.

Tana d’ago kanta gabanta ya fad’i da k’arfi sakamokon had’a ido da suka yi da Baba ya hard’e hannayenshi a k’irji ya jingina da jikin bangon gidan da tafin kafarshi kwaya d’aya da bayanshi, yana kallonta yana kallon mai napep d’in. Da sauri ya d’ago daga jinginar da ya yi ya zira silifas d’insa guda d’ayan wanda ya cire ya jingina da k’afar, ya tunkari mai napep d’in da yake shirin buga mashin d’insa ko gaisuwarta bai amsa mata ba.

A hankali ta tura k’auren ta shiga, tun daga soro ta fara jiyo maganar Jalila da Umma, Umma tanata masifa Jalila na zugata, tana ida shiga tsakar gidan kuwa ta hango Mama a zaune a bakin k’ofar d’akinsu tana kuka, Ya Junaidu ya durk’usa a ta gefenta da alama hak’uri yake bata, Umma sai ce masa take yi “shanyayye!! ya tashi a wajen kafin ranshi ya b’aci!!” Jalila kuma tana cewa “ai dama ya fi son Mama a kan Umman tasu.

Sallamarta ce ta sanya duk suka juyo suka zuba mata idanu. Ganin Mamanta na kuka yasa da sauri ta yi inda take ta durk’usa a gabanta ta saka hannu ta hau share mata hawaye.

D’an kama hannunta Mama ta yi sannan ta goge hawayen da d’ayan hannunta kafin ta ce “Daga ina kike? ya aka yi kika dad’e? Jalila tace Ina fita kema kika fita.” Mama ta jero mata tambayoyin tana kafeta da idanu.

Za a wani tsaya ana yi mana kukan munafurci kamar ba ki san Ina ta tafi ba!! Kawai ke dai kice baki san waye saurayin ba amman sarai kin san me ta je ta yi.” Cewar Umma sannan ta d’aura da cewa “Yo Allah na tuba daman Yaran yanzu ka haifo su ta hanya mai kyau ma ya aka k’are, ballantana ta hanyar da ba ta dace ba!!”.

Da k’arfi Mama ta runtse idanunta wasu zafafan hawaye suka shiga tsiyayo mata. Umma bata damu ba ta ci gaba da cewa, “sannan sai ki dinga goya mata baya tana abubuwan da ta ga dama idan anyi magana ki ce sharri aka yi mata saboda bakin ku d’aya ko?? Kina samu tana kawo miki taro da sisi.”

Hudan ce ta mik’e ta k’arasa kusa da Umma tace “Umma dan Allah ki yi shiru kinga fa maganar ki yadda take saka Mama kuka.”

D’an zaro idanu Umma ta yi kafin tace “Eh lalle Yarinyar nan kin rik’a!!!! Ko da yake ba zan ga laifin ki ba, yanzu ai gani kike yi daidai kike da ni tunda duk abinda na sani kema kin sanshi, zafin ciwon nak’uda kawai ya rage.”

Da sauri Mama itama ta mik’e ta k’arasa daff da Umma ta ce “Dan Allah dan annabi Sadiya ya isa haka! Za kisa Yarinya ta san abunda shekarunta ma basu kai ba, tun d’azu kinata aibantata da bakinki kuma yanzu kin zo kina irin wannan maganar a gaban Yara saboda Allah.”

Mamaki ne ya cika Umma saboda ta dad’e ba ta ga b’acin ran Mama kamar haka ba, cikin matsowa kusa da sosai itama tace “Lalle Maryam!! na jinjina miki. Son y’arki ya rufe miki ido har kina gaya mini magana dan na fad’i gaskiya??”.

Mama bata bari ta k’arasa ba tace “Wallahi ba gaskiya kika fad’a ba!” Sannan ta juya ta kamo hannun Huda wadda take ta kuka ganin ana fad’a a kanta, ta kawo ta gaban Umma tace “Zan iya dafa Al Qur’ani akan sharri kuke yi mata, Allah ne shaida ta na san kalar tarbiyyar da na yi mata.

Idan kuma kina da shedar da zaki tabbatar da abinda kike cewa gaskiya ne to Bismillah Ina sauraron ki.”

Hudan garin k’ok’arin goge hawaye bata saniba handkarcheif d’in da Arshaad ya bata ya fad’o k’asa!
Karaf! kuwa a kan idon Jalila, da sauri ta k’araso inda ta ga handkarcheif d’in ya fad’i,har tana gurd’ewa.
Duk sai suka zubawa inda ta nufa ido, cikin sauri ta durk’usa ta d’auka,sai a lokacin Hudan ta lura aikuwa ta fara rarraba ido gabanta na mugun fad’uwa kana ganin ta ka ga mara gaskiya.

K’arasowa Jalilan ta yi kusa da Mama, dai dai fuskarta ta d’ago handkerchief d’in ta yi mata fifita da shi a dai dai setin fuskarta kafin tace “kowa dai ya ga lokacinda ya fad’o daga hannun Huda ko?
Tambayata a nan itace ‘shin a ina kamila nitsatstsiya Huda ta samu handkerchief mai kyau haka da k’amshin turare wanda na tabbata na maza ne?’.”

Ya Junaidu wanda kishi ya turnuk’e sa a take ne, yace “Kawo in gani!”

Mik’a masa ta yi ya k’arasa warewa…Farine tas! Hanky d’in, kana gani ka ga had’add’en personalize handkerchief, ta chan k’asa an rubuta ‘AY’ da wani had’add’en glitter gold, ga uban k’amshin da yake ta zubawa na had’add’en designer perfume.

Da kyar ya samu ya d’an yi controlling temper d’inshi tukunna ya kalli Huda yace “na waye???“
Ya yi mata tambayar yana tsareta da manyan idanuwanshi da suka fara chanja kala.

Shiru Huda tayi ta fara goge hawayenta da suke zuba a yanzun babu k’akk’autawa.

Mama ma da gabanta yake ta fad’uwa tana kiran sunan Allah da k’ok’arin kawar da mugun tunani akan y’artata tace “Huda tambayar ki fa akeyi, kin yi shiru ki bamu amsa!”

Baba wanda ya shigo yanzu ne yace “Ku barta ai ba zata tab’a cewa komai ba! Gani nan, ni ne zan baku amsa!.”                   

<< So Da Buri 6So Da Buri 8 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×