Skip to content
Part 70 of 73 in the Series So Da Buri by Humaira Bulama

Abba Madu yana gama waya da Dad, Motar su Baban Sakina tana yin parking.

Sai da Baban Sakina ya raka su har ciki tukunna ya ce, “Bari ya je ya samu d’an uwanshi ya sanar da shi halin da ake ciki.”

Yana fita su kuma suka fara korawa Shuwa bayani.

Har ga Allah Shuwa ta ji dad’in hakan..at least su duka ukun za su zauna a family d’aya.

Basu damu da gyangyad’i da jirin da take yi ba (dan allurai da abun da Ashraff ya shak’a mata masu k’arfi ne sosai)

Haka suka duk’ufa wajen gyarata. Ita kam anayi ma tanata baccin ta.

Sai dare tukunna Huda ta samu ta kira Mama. Gramma Ummu da Abba ta gaidasu.

Suna gama waya da Abba ta fara jiyo motsi dan haka tayi sauri ta runtse idanuwanta kamar mai bacci.

Dama ya bata dinner ta ci ta yi sallah tukunna ya fita bayan ya ce mata “bara ya je ya d’an yi aiki”.

Dan in dai yana gabanta to ya san ba abunda zai iya tab’ukawa.

Yana ganin yadda ta lumshe idanun nata ya fahimci ba bacci take yi ba!

Murmushi kawai ya yi ya k’arasa y’an abubuwan da zai yi ya hayo kan gadon. Tashi d’aya ya lura da yadda jikinta ya hau b’ari dukda kuwa baccin k’aryar da take shararawa amman he cant help it! Ba k’aramin k’ok’ari ma ya yi aka kawo yanzun ba. Addua ya yi ya tofa ya shafa mata shima ya shafa.

Jin an shafa mata addua ya sanya hankalinta yad’an kwanta a tunaninta kyaleta za ayi amman inaa. nan take ta ji sabon labari…

Babu daman kwacewa dan yau ma Aslam d’in da gaskensa ya zo mata kamar jiya.

Babu kalar magiyar da bata yi amman yayi mata kunnen uwar shegu!

Ga rad’ad’i ga azaba ga ciwon kai ga rashin bacci shiyasa kafin asuba zazzab’i ya rufeta, ruf!.

Shi ya kira family Doctor ta zo da sassafe ta yi mata allurai harda k’arin ruwa tukunna ta d’an ji dama dama…

Ba abunda yafi bata tsoro irin yadda ya sake zuwan mata yauma kamar jiya da shekaran jiya.

Ita kam har mamaki da tsoro ya fara bata dan idan yana wani abun kamar wani mai aljanu..yanzun zaka ganshi garau amman yana d’aukar hanya zai birkice sam baya ji baya gani.

Ba shi da aiki sai dai ya bata abinci ya yi ta lallab’ata yana faman lallashinta yana kula da ita, ya yi ta gaya mata kalaman soyayya yana lallashinta.

Idan dare yayi kuma a koma ruwa.

Tun a washegarin ranar aka shirya musu komai na tafiya.

Basu wani sha wahalar yiwa Sakina komai ba saboda Dad ne akan komai.

Auwal, bai san da labarin ba dan ko da aka gayawa Mom da ta ga jikin nasa yad’an nutsu kamar ya sani
sannan nan da kwana biyu Sakinar zata zo sai kawai ta barshi akan sai ta zo d’in ya ganta kawai a surprise
Another thing kuma tana tunanin in dai Auwal ya ji an aura masa Sakina kuma tana Nigeria tou tabbas zai iya tsige oxygen d’in ya dawo gida ko bai gama warkewa ba.

Tun lokacin da aka ce ‘visar su ta fito gobe zata wuce’.

Take kuka! Har yau da safe. Shuwa da su Baaba Talatu da Ummu ne sai kuma matar wan Mijin Ummu sai wata distant cousin d’insa, suka shirya za su kaita MT.

Suna cikin shiri Anty Zainab ta shigo ita da su Khadija waenda zuwansu kenan.

Da mamaki Mama take kallon Anty Zainab d’in wadda duk ta rame ta lalace jikinta yayi mugun sanyi kamar ba itaba ko dan ta jima bata ganta ba dan ko ranar da Kaka ya kirata ta je bata ganta ba
tana d’aki wai tana bacci.

Inda Mama take Anty Zainab ta nufa tana zuwa ta rungume ta sai kuma ta fashe da kuka!.

Duk tsayawa suka yi suna kallonta da mamaki.

A hankali Mama ta zaro ta daga jikinta kafin ta ce. “Haba Zainab kuka kuma?”

Cikin share hawayenta ta ce. “Dole in yi kuka Maryam!

Dole in yi takaici da bak’in cikin abubuwan da na aikata.

Na yi miki laifi na yi kuskure wanda a yanzu nake matuk’ar danasani, sam! Na kasa nutsuwa na kasa yafewa kaina.”

Sai da ta share hawayenta wasu suna sake zubowa tukunna ta d’aura da cewa. “Yanzu haka daga gidan me unguwa naken a je na fad’a masa gaskiyar laifin da na yi miki sharrin da na yi miki, wanda yayi sanadiyyar har aka koroki a makaranta. Na gayawa Kaka shima gaskiya. Ki tayani neman yafiyar Abba dan Allah Maryam kema ki yafe min na yi kuskure. Sadiya ta cuceni! Wallahi duk hud’ubarta ce ta sanya na juyawa aminiyata baya”.

Ta k’arashe maganar tana fashewa da wani sabon kukan.

A hankali Mama ta yi hugging d’inta tana murmushi kafin ta ce “Zainab! Har ga Allah ba zan ce miki zan iya mantawa da abunda kika yi mini ba a lokaci guda ba, dan zan iya cewa ke ce ummulabaisin fad’a na da su Abba.

Amman maganar yafiya kam wannan na yafe miki Allah ya yafe mana gaba d’aya.

Sanna ki yi k’ok’ari ki yafewa Sadiya itama ko ba komai kar abun ya yi mata yawa
saboda ko da bakin y’an layi aka barta ya isheta!

Dan kowa idan ya tashi magana ita, kowa matsalarsa Sadiya. Idan mu bamu yafe mata mun yi mata fatan alkhairi ba wa zai yi?”.

Wani sabon kukan Anty Zainab ta fashe dashi tana mamakin kyakkyawar zuciya irinta Mama.

Da kyar su Shuwa da Ummu har Maman suka samu suka lallasheta ta nemi waje ta zauna tana gunjin kuka.

Basu kai ga fara magana ba. Madu ya shigo ya ce “Su fito da Sakina ga motocin MT sun k’araso”.

Sai a lokacin ta saki kukanta mai sauti…

Haka nan tana kuka tana komai Mommy da Mammy suna shigowa aka d’auketa aka fita da ita.

Tana shiga motar motocin suka d’auki hanyar MT.

A b’angaren Gramma aka ajjiyeta. Hudan, daman ta san da zuwan nasu dan basu ma dad’e da gama waya da Sakinar ba, shiyasa tana jin shigowar motoci ta lek’a ta sama da yake gidantane a farko farko yasa ta hango su.

Ta ma manta da ciwon kafa da na jikin da take yi…Haka nan tana takawa tana d’an d’ingishi ta nufi hanya.

Da kyar ta iya sauk’a daga benen farko kawai sai ta durk’usa a wajen ta saki kuka.

A haka Aslam ya shigo ya sameta.

A rikice ya k’arasa ya hau tambayar ta ‘me ya sauk’o da ita?’.

Ko kallon sa bata yi ba ta mik’e kawai ta fara k’ok’arin wucewa wanda sai a lokacin ne ya gane matsalarta.

Dariya da tausayinta ne suka rufeshi amman ya dake ya b’ata rai ya ciccib’eta.

Duk kalar rigima da yakushin da take yi mishi da kuka bai diretaba sai da ya kaita kan gadon tukunna.

A hankali ya zauna ya kamo hannunta tana shirin mik’ewa ya ce “Ki nutsu.

Kin san dai Sakina ba zata tab’a wucewa ba tare da ta zo ta yi miki sallama ba ko?

Ki kwantar da hankalinki yanzu ma da na ajjiye su na ji suna cewa duk za su shigo miki kafin su wuce”.

Shiru ya yi yana kallonta still kafin ya ce. “Yanzu ke idan aka barki a haka a wannan yanayin naki za ki je gaban su Ummun?”.

Sai a lokacin kanta ya d’an d’au chaji. A hankali ta sunkuyar da kanta kafin ta ce,

“Ya Aslam tou dan Allah ka je ka taho da su, kar su k’i zuwa.”

Sai da ya d’an yi shiruu tukunna ya kamo hannunta ya rik’e ya d’anyi kisssing sannan ya ce
“Okay love, amman ki nutsu kin ji”

D’an d’aga masa kai ta yi alamun ‘okay’.

Ya d’an jima yana kallonta yana murmushi kafin ya sauk’e ajiyar zuciya a hankali ya ce “Alhamdulillah”tukunna ya mik’e ya fice a ranshi yana tunanin ta yadda Hudan take so ya je ya sake fuskantar su Ummu!

Shi fa da kyar ma ya iya tsayawa suka gaisa especially ma Mama lokacin da ta rako Sakina har k’ofa,
wata irriyar kunyarsu yake ji gaba d’ayansu. Shi kam gaskiya idan Mama ta k’araso estate d’inma bai san taya za su kaya ba.

Cikin ikon Allah yana sauk’a parlourn chan k’asa. Khadija da Yayarta suka shigo tare da Gramma da Sakina, dan Sakinar tunda taga su Ummu za su tafi ta sake d’aga hankalinta shine Gramma ta ce ‘bara ta yi bribing d’inta ta kaita wajen y’ar uwarta’.

A parlourn sama Gramma ta ajjiyeta bata k’arasa chan sama ba ta juya ta fice dan tashi d’aya ta fahimci Aslam d’in baya so ta had’u da Hudan.

Ba kunya haka ya kinkimeta bayan ya koma sama wajenta wai zai kaita wajensu.

Da kyar sai da ta saka mishi kuka tukunna ya sauk’e ta ta yi practicing tafiyar da zata yi a gabanshi ta d’an dedeta yanayinta dan duk tayi kalar da duk mai hankalin da ya ganta sai ta tona masa asiri ne, ga kuma ciwon k’afa da na jikin da suka taru suka sauk’ar mata da d’ingishi. Sannan ya kama mata hannu ya d’an karata a jikinsa suka sauk’a tare.

Suna tahowa Khadija ta fara yi mata dariyar tsokana k’asa k’asa.

Sarai Hudan ta fahimceta amman ta basar dan bata shirya biye mata ba.

Ita a ganinta wannan lamarin da take ciki jaje ya kamata ayi mata ba tsokana ba
dan ita komai ya wuce tunaninta.

A kusa da Sakina ya ajjiyeta kafin ya ce “Su zama ready nan da 2 hours su Sakinar za su wuce
In sha Allah” Yana gama fad’in haka ya juya ya fita.

Yana fita Huda ta fad’a jikin Sakina ta yi hugging d’inta.

A hankali ta ji Sakinar ta sa kuka, d’agowa ta yi ta d’an b’ata rai itama idonta yana kawo kwalla ta ce
“Haba mana dan Allah ki daina kar ki saka ni kuka nima”.

Ta fad’i haka ragowar hawayenta yana zubowa.

Murmushi su Khadija ita da yayarta suka yi kafin Yayartata ta ce “to yanzu wa zai lallashi wani?”

A hankali Huda wadda taga d’an rashin kyautawarta ta juya ta yi hugging Khadijar
sannan ta kamo hannun Yayar khadijah daga inda take zaune ta ce “ina wuni”

A hankali tana murmushi dan itama yanzu duk ta sauk’o ta ce “Alhamdulillah, gida yayi kyau Huda Allah ya sanya alkhairi ya baku zaman lafiya”.

A hankali ta juya cikin d’an tsokana da dauriya ta yayewa Sakina fuskarta, dan har yanzu fuskar tata a rufe take cikin mayafin laffayar da aka nad’a mata.

Da kyar ta iya daurewa batayi kuka ba, fuskar nan tayi dagaje dagaje ta yi jajawur
kana gani ka san ta ci uban kuka bana wasa ba, daman tun shekaran jiya da suke waya take jin yanayin muryarta a dashe.

Cikin son sakata nishad’i ta ce “Haba mana Sakina, ki daina kuka, kinga fuskarki kuwa?
Gashi duk kin yi wani laushi kamar ba ke ba.

Ai ba wai zama za ku yi achan d’in ba har abada, yana warkewa fa za ku dawo in sha Allah…Ni kumafaa daa? da zan tafi chan wani gari ba ke kika yi ta bani kwarin guiwa ba?” Ta k’arashe a hankali daga nan ta yi shiru ta kasa ci gaba da magana.

Su Khadija ne suka saka baki, suka taru suka yi ta lallab’ata har sai da ta d’an sake ta bar hawayen ta d’an kwantar da hankalinta tukunna suka d’an shiga hira a hankali. Khadijah ce ta ce “Gaskiya Huda gidan ki ya had’u over!

Kalla kuma kaya koina duk girman gidan. Bara mu lek’a mu kashe kwarkwatar idonmu”.

Ta fad’i haka tana ajjiye mayafinta ta mik’e. Itama yayartata mik’ewa ta yi.

Hudan har ta mik’e ta d’an fara takawa za ta bisu Khadija ta kamo hannunta ta zaunar da ita ta ce “zauna mai tafiyar ta’ta’taaa mun san hanya”.

Duka Huda ta kai mata ta yi saurin gocewa tana dariya suka nufi k’asa ita da yayar tata.

Banda dukan uku uku ba abunda k’irjin Sakina yake yi daman tun d’azu ta d’an tsorata da yanayin tafiyar tata da ta gani.

Maganar da Huda ta fara yi mata ne ya dawo da ita daga duniyar tunani da tsoron data tafi. A hankali ta juyo tana kallonta jin tana cewa “Ya Arshaad ya sake guduwa.

Ba a san inda yake ba! D’azu inaji Ya Aslam suna maganar shi da Dad a waya da na tambayeshi kuma sai ya k’i gaya min komi, kamar ma haushi ya ji.” Ta k’arashe maganar cikin karyewar zuciya.

A hankali Sakina ta sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya kafin ta ce, “Hudan.

I can’t even begin to imagine what Ya Arshaad is goin through! Dauriya ce kawai yake yi dan haka idan ya ga ba zai iya zama ba ya nuna yanaso zai tafi ya kamata ku bashi space ku barshi ya tafin.

Kuma dan Allah ki daina nuna damuwarki over a kan Ya Arshaad a gaban Ya Aslam…Yes! Na san dole abun is somehow amman ki d’an dunga daurewa har Allah ya yaye miki son shi a zuciyarki ki manta da shi ki rungumi Mijin da Allah ya zab’a miki ku zauna lafiya dan na san Ya Aslam yana sonki wallahi tun a mansion d’in chan naso In fahimci wani abun shiru kawai na yi miki.”

Shiruuu, Hudan ta yi kamar tana tunanin wani abu kafin chan ta ce “Yauwa Sakina, kin san
wani abun mamaki?

Ashe Ya Aslam ya sanni tun kafin yazo gidanmu shi da Ya Arshaad…”


Nan ta zaiyyane mata labarin da ya bata da kuma yadda yake nanata mata yana ‘tsananin k’aunarta’
yake kuma gwada mata.

Da zaman da suka yi a chan gidan da komai.

Murmushi kawai Sakina ta yi kafin ta ce “Hudan you are lucky, Very lucky!

Ban yiwa Ya Arshaad adalci ba amman ina so ki rubuta ki ajjiye ni Sakina na ce.

‘Ya Aslam ya fi k’aunarki Akan Ya Arshaad’. Sannan Huda dan Allah ki daina pushing d’insa away ki janyo abunki ku rungumi juna, Allah ya bawa Ya Arshaad shima tashi wadda zai so.

Ki nutsu, ki fahimci karatun soyayyarsu su biyun duk true love suke yi miki that I’m sure of
amman ko waye yaji labarinku ya san Ya Aslam ya fi k’aunarki, although Ya Arshaad shima has sacrificed a lot for you sannan shine ya reneki kika zama mutum therefore na san ba lalle ki iya mantawa da halaccinsa ba wanda ni kaina ba zan tab’a mantawa ba amman Huda soyayyarki da Ya Aslam daban take a cikin labarin soyayya! Ki nutsu kar ki cuci kanki dan kema kina son abunki fahimta ne kawai baki yi ba.”

Hudan na shirin yin magana Aaima ta hawo.

A kan 3 seater da suke zaune ta zauna kafin ta ce “Anty Huda da Anty Sakina, kinga na kasa hak’ura sai da na sake biyoki ko?” Ta fad’i maganar tana kallon Sakina.

Murmushi kawai Sakina ta yi ta kamo hannunta.

“Crying bride” Aaiman ta ce tana d’an lakatar hancinta, sannan ta d’aura da cewa
“Amarefa sun daina kuka yanzu”

A hankali Sakina ta d’an kwanta a jikinta ta ce “Thank you Aaima. A lot!”

Murmushi Aaiman ta yi kafin ta ce “Ba komai Sakina, Allah yasa mu dace.

Ni dai yanzu matsalata shine wannan kukan da kike yi, ki daina pls, ko kun zo tafiya kar ki sake yin wani kuka. Ya Auwal raina ki zai yi! Bar ganin bashi da lafiya. Allah idan ya tusoki gaba ko hmm. Gara ki nuna mishi kema Amaryar zamani ce”

Duk murmushi suka yi kafin Huda ta ce “Aaima Allah duk ranar da za a kaiiki gidanki idan kika yi kuka
ni kad’ai na san me zan yi miki”

Murmushi ta yi ta sauk’e ajiyar zuciya kafin ta ce “Speaking of which..Ina son tambayarku wani abu amman kunyar ku nake ji”.

Ta fad’i hakan tana rufe fuskarta da tafukan hannunta.

Dariya duk sukayi dan yadda ta yi d’in dole ka yi dariya.

Cikin dariyar Hudan ta ce “Mene pls?”

Sai da ta d’an dara itama kafin ta ce “Sakina wanda ya maidaki gida, shekaran jiya wachchar
Brothern ku ne?”

“Woow!!” Sakina ta ce da d’an k’arfi tana d’an zaro idanu waje kafin ta ce “An gama!

Ai harma na hango ranar d’aurin auren ku.

Kin san shima sai da ya ce min he felt something..”

Wani ihu Aaima ta yi a hankali sosai irin na jin dad’in nan kafin ta ce “Shikenan…”

Sai kuma ta sunkuyar da kanta ita ala dole ta ji kunya, k’arshe ma tashi ta yi ta tafi bayan ta yi hugging Sakina ta ce mata “A kula da Ya Auwal plss. Allah ya bar k’auna sai kun dawo”

Tana fita Sakina ta zaro waya zata kira Junaidu, Hudan ta rik’e mata hannu.

Da d’an mamaki ta juya tana kallonta kafin ta ce “mai ya faru?”

A hankali Huda ta ce, “Sakina Aaima bata yi deserving suruka da k’anwar Miji irin Umma da Jalila ba.

Shiruuu Sakina ta yi itama duk sai jikinta ya yi sanyi, a hankali ta ce “Tabbas”

Dede nan su Khadija suka hawo suna haki Yayar Khadijan ce ta ce, “Hudan wannan tour a gidanki ai aiki ne!”

Sai kuma ta ce, “Na ga d’akin da zan zauna idan na zo yi miki wankan jego a chan ma muka shantake.

Gadon laushi Allah yasa dai idan nazo kar in yi ta bacci dan gadon nan duniya ne.”

Dariya Khadija ta yi kafin ta ce “Ai kuwa ki shirya dan alamu sun nuna nan da wata tara cif za ki dawo zaman jegon.

Duk dariya suka yi banda Huda wadda hankalinta ya fara tashi dan ta ga yamma ta fara yi.

Sai da suka huta tukunna suka mik’e suka dudduba saman chan sama kuwa suka ce basu isa su shiga turakar sabbin maaurata ba haka kurum su ganewa kansu.

Haka nan, Khadijah ta tisa Hudan a gaba sai shak’iyanci take yi mata.

Hudan kuwa kamar ta yi kuka dan ita kad’ai ta san halin da take ciki.

Suna a haka Gwaggo Asabe ta shigo, abun dariya suna had’a ido da Sakina kawai sa Sakinar ta saka kuka.

Da kyar aka lallab’ata aka rarrasheta suka yi sallama da Huda tana kuka itama tana kuka. Gwaggo Asabe da su Khadija suka yi mata rakiya har bakin mota su kuma su Khadijan aka saka driver ya maidasu gida daman sun yiwa Huda sallama, ta so ta basu ko d’an inner wears ne na sa rana da ake rabawa, ganin a yanda suka tafi yasa ta yanke shawarar kai musu har gida in shaa Allah.

Aslam, ne ya kai su Sakina har airport, ita da Daddy za su yi tafiyar wanda yaketa janta da hira da barkwanci ba ruwanshi da wani batun surukantaka, sai da ya ga ta d’an sake tukunna ya ji dad’i…

Haka har jirginsu yayi taking off. Duk dauriyar Sakina sai da idonta ya cicciko sanann ta k’ank’ame kujerar da take kai, sai da jirginsu ya dedeta ya lula sararin samaniya tukunna ta samu nutsuwa Daddy yana ta tsokanarta.

Washegari da daddare Granpa ya nemi ganin kowa! A lokacn jikin Huda ya d’an yi sauk’i tafiyar ma ba laifi dan k’afar tata ma da sauk’i dan haka suka tafi tare ita da Aslam.

A chan suka tarar da kowa. Suna zuwa Huda jikin Mommy wadda ta fara mik’o mata hannu taje ta fad’a.
Sai da suka gaisa cikin so da tattali tukunna ta mik’e ta nufi inda Aslam yake a gaban Granpa.

“Hmm” kawai Mammmy ta ce ta yi d’an mitsitsin tsaki sannan ta kauda kai.

Cikin kulawa Granpa ya amsa gaisuwar tata ya na mai tambayarta “ya sabon guri?”

“Alhamdulillah” ta ce ba tare da ta iya d’agowa ba dan gaba d’ayansu kunyarsu take ji.

Sai da kowa ya zauna tukunna Granpa ya kalli. Dad ya ce masa “Ina Muhammad?”

Cikin tsananin tashin hankali da rashin jin dad’i dan su already sun san case d’in tun 3 days ago shi da su.

A hankali Dad d’in ya ce “Ba mu gansa ba since”

Ajiyar zuciya Granpa ya sauk’e, shi kansa bai san ta Ina ma zai fara ba. A hankali ya ce “Yi musu waya su shigo za a nemo shi.”

Mutanen nan da suka zo suka d’auki sample na tomb print d’insu sukayi musu tambayoyi sune suka shigo.

Dukkan su waje suka nema suka zazzauna bayan sun kai wani file gaban Granpa sun ajjiye.

A hankali Granpa ya kalli Dad ya ce “Kirawo Yusuf! Duk da ya san komai ya kamata a yi komai da su har Auwal da Adama”

Computer d’in parlourn ya yi using ya kira Daddy..,, Mom na gefensa a lokacin suna cin abinci, yana
ganin kiran ya ji gabnsa ya yanke ya fad’i! Dan haka ya ture abincin ya d’auka ya ajjiye wayar a gabansu shi da mom.

Bayan y’an gaishe gaishe Granpa ya ce “Ina Auwal?”

Suka ce “su suna hotel su Auwal kuma suna asibiti”.

Kamar zai ce ‘a kirashi shima’ sai kuma kawai ya ce ‘a barsu kawai’.

Daga nan ya yi gyaran murya ya fara magana.

“Last week waennan mutane sunzo sun karb’a tombprint d’in kowa!

Na san ba lalle kun san dalilin d’aukar tombprint d’inba dan haka bara in yi muku bayani.”

A hankali Aslam ya mik’e ya ce “Granpa, please excuse me”. Kana ganin fuskarsa ka san yana cikin tsananin tashin hankali.

Cikin no nonsense face, Granpa ya yi amfani da kakkausar muryar wajen ce masa. “Koma ka zauna!”
Babu alamun wasa a tattare da shi.

A hankali Aslam ya koma ya zauna yana sauk’e ajiyar zuciya a jejjere jijiyoyin kansa duk sun baiyyana…Ya rasa wanne irin taurin kai ne Granpa yake da shi! Shi sam bai yi tunanin wannan maganar za ayi ba da wallahi ba zai zo ba! Shi a tunanin sa sun riga sun gama kashe case shi da su granpa d’in da su Abba
har abada.

Muryar Granpa d’in ce ta katse shi jin ya ci gaba da magana yana cewa “Dalilin da ya sanya aka d’auki tombprint d’inku ba komai bane ba illa…

A lokacin da ake bincike an yi nasarar samun yatsun mutum biyu da palm a jikin tukunyar da Huda ta dafa coffee wanda kamata yayi a samu tombprint d’inta ita kad’ai tunda hatta Ummi ta ce bata tab’a tukunyar ba ma. Ita ta zuba mata da kanta.”

Kwarewa Mammy ta yi da k’arfi wanda duk ya janyo hankalin jama’a kanta.

Da sauri Aaima ta je ta matso ruwa a dispenser ta kai mata suka shiga shafa mata baya ita da Mommy
tana sha tukunna ta d’an dawo dede.

Ajiyar zuciya Granpa ya sauk’e kafin ya ci gaba da cewa “Bincike yana tafiya bayan an yi testing tukunyar an tabbatar da poison mai k’arfi ne a ciki sannan har da shinkafar b’era. Sai kuma still aka samu gidan allura a cikin dustbin d’in kitchen d’in wanda ba komai ne a cikin wannan allura ba face poison d’in da aka yi amfani da shi aka zuba a cikin coffe d’in. Tou a jikin syringe d’inma kuma sai aka sake samun wani sabon tombprint d’in wa..”

Shigowar Arshaad ce ta katse Granpa da kowa na wajen gabad’aya sai kallo ya koma kansa.

Shiruu parlourn ya d’auka na y’an mintuna kafin ya ce, “Assalam alaikom, sorry I’m late”.

Bai jira jin me za su ce ba ya k’arasa gaban officer d’in kawai ya mik’a mishi hannayensa duka biyu.

Kuka Dad ya saka kawai ya mik’e ya fita. A hankali Granpa ya sunkuyar da kanshi k’asa wasu zafafan hawaye suka zubo masa.

Da mamaki Mommy ta mik’e ta k’arasa wajen ta kamo hannun Arshaad cikin zaro ido ta ce
“Arshaad me ye haka ?”

Da kyar ya samu hawaye ya zubo masa a ido d’aya! A hankali yana kallonta ya ce
“Mommy ni ne!

Duk wannan bayanin da Granpa yake yi muku a k’arshe suna na za ku ji a matsayin mai laifi!

Ni na yi poisoning Ummi wanda Aslam naso kashewa tashi d’aya abun ya fad’a kan Ummi
dan haka, dan Allah taron nan ya watse haka, ku daina kwana kwana kowa ya tafi
officer please arrest me”.


Ya k’arashe maganar yana sake juyawa ya mik’awa officern hannuwanshi duka biyu kamar farko.

Mik’ewa kawai officer d’in ya yi ya zaro ankwa.

Ba k’aramin tashin hankali Mommy ta shiga ba bata san lokacin da ta shiga tsakaninshi da officer d’inba cikin fushi ta cewa officer “meyene haka yake faruwa?” Kafin ta juya ga Arshaad ta ce
“Arshaad ba zan bari ka tafi gidan yari ba!”

Ta fad’i haka tana nunashi da yatsanta dede fuskarshi alamun warning tana hawaye sannan ta ci gaba da cewa. “Ko meye ka aikata ba zan bari ka tafi gidan yari ba wallahi! Na san ba halin ka bane ba
pushing d’inka aka yi kayi hak’uri ka dawo Arshaad d’in da muka sani”

Cikin kukan ta k’arasa gaban Granpa ta ce, “Granpa Ummi kanta na san ba zata so haka ba!

Dan Allah in domin ita kake yi to ka yafewa Arshaad ransa ne ya b’aci zuciya ce ta kaishi
ba laifinsa bane ba.”

Gani tayi kawai mutumin yana k’ok’arin sakawa Arshaad wanda ya tsaya kawai yana hawaye ankwar, da sauri ta mik’e ta koma wajen ta fincike ankwar ta yar sannan cikin fad’a ta cewa mutumin
“Wallahi bar ganin aikinka kake yi, na rantse da Allah idan ka saka mishi ankwa sai na tsinka maka mari!”

Runtse ido Arshaad ya yi da k’arfi kafin ya samu ya bud’e ya juyo da Mommy ya ya kama kafad’unta duka biyu ya fara magana cikin d’aci. Idanuwanshi jajawur, “Mommy ba laifi d’aya bane a kaina okay?!

Ko kin kawar da wannan dole zan tafi jail saboda Junaidu ya yi filing complaint a kaina and all evidences are against me so just let it go this is wat i deserve. Dan Allah.”

K’amewa kawai ta yi tana kallonshi.

A hankali Aslam ya k’araso wajen ya dafa shi ya ce, Arshaad!

Ka juya ka fita a parlourn nan zan san abun yi please. Dan Allah ka tafi kawai!

Meye ma ya kawo ka nan in the first place?!” Ya fad’i hakan cikin d’an d’aga murya.

A hankali Huda wadda ta k’araso wajen yanzu itama tare da Aaima ta ce, “Ya Arshaad me ya had’aka da Ya Junaidu?”

Lumshe idanuwansa ya yi a hankali ya juyo yana kallonta ya ce “Kin tuna sharrin da aka yi masa akan case d’in Chief Justice!? Sannan aka so a sake d’auke shi bayan an sakeshi? Those that ring a bell??”

A firgice wani kalan kuka yana taho mata ta ce “Ya Arshaad dan Allah kar ka ce min kaiine!
Dan Allah Ya Arshaad”

Sai da ya matsa dede setin fuskarta tukunna yana kallon cikin idonta ya ce, “It was all me!”

Wani irin kuka ta fashe da shi ta durk’ushe a wajen cikin kukan ta ce, “How?? Why???”

Ranshi a tsananin b’ace ya ce Why? Tambayata ma kike yi ‘why’!? Bara ki ji dalili ‘It was all because of you’ And bari ki ji abunda ya faru…Naga take taken Junaidu, At that very day kuma kema naga kamar kina k’aunar sa, nuna miki ne ban yi ba amman hankalina a matuk’ar tashe na bar wajen ki. Na biya ta wajen friend d’ina Jamil! Sai na samu suna tattaunawa akan wata magana…Yanayi na yasa ya tambayeni dan haka ban b’oye mishi komai ba na fad’a mishi damuwa ta.

Ya san ki ya san yadda nake sonki shiyasa ya ce ‘in bashi number da information d’in Junaidun kawai’.

Abun ya zo mana da sauk’i saboda already best friend d’in Junaidun Yaron Abokin nawa ne Jamil.

A time d’in ban san me za su yi ba kawai ni dai nace ‘a san yadda za a yi min da Junaidu’
Sai da aka kashe mutumin tukunna na fahimci me sukayi.”

Cikin d’aci ya ce, “Kinsan wani abu?” Be jira jin me zata ce ba ya ce “Ban damu ba!

Kwata kwata ban damu da kisan kan da aka yi ba saboda. Idanuwana sun rufe
I was just selfish and bad! And happy tunda Junaidu ya b’ace kenan babu abunda zai sake shiga tsakaninmu ko ya yi yunk’urin raba mu. Ban damu da yadda ya sha wahala a Prision ba, bayan an sake shi na sa a d’auko mini shi.” Yana kallonta ya sake cewa, “Kinsan wani abu?” Nan ma be jira amsa ba ya d’aura da cewa. “Ko da aka ce motar su ta kama da wuta. Hudan ban ji haushi ba ban ji babu dad’i ba, ban kuma fad’awa kowa na san wani abu ba! Na take komai, na rufe idona duk dan inga na mallakeki! I was bad!
Ban yi deserving freedom ba so pls dan Allah ku bari kawai su tafi da ni.”

Cikin fushi Aslam ya ce, “Ba za a bari ba!

Da kasa aka kama Junaidun ai kuma still kai kasa aka dinga bashi shelter da abinci mai kyau.

Kaga hakan yana nuni da still akwai good in you Arshaad you felt guilty which is good.”

A hankali ya juyo ya kalleshi kafin ya ce, “For your information nine na janyo aka rufe maka company d’in takalman ka! Is there any good in me left?”

Ya fad’i hakan yana kafeshi da dogayen idanuwanshi.

A hankali ya ji Aslam d’in ya ce “I know Arshaad, na san komai!

Tun kafin In tafi a time d’in da aka kirani na fahimci kai ne, So dan Allah maganar nan ya wuce
please”.

Cikin katse shi ya ce, “Na so In kashe ka! Ka bar duniya gaba d’aya, In auri matarka! Is there any good in me? Still kana da hope a kaina.”

“Ina za ki je?”

D’in da Granpa ya ce ne yasa gaba d’ayansu suka juya suna kallon k’ofar da Mammy ta nufa sad’af sad’af zata fice.

A hankali Mom wadda tun d’azu take magana ba a jinta tace, “I have something to say”
Da d’an k’arfi.

Duk juyawa aka yi aka zubawa screen d’in ido, suna kallonta. Idonta sharkaf da hawaye ta ce “Arshaad baka so kashe Aslam ba! Ka dai yi yunk’urin yin hakan, amman kuma baka aikata ba saboda baka so ba.

A ranar birthday d’in su Shuraim! Bayan Dad ya gama yi mana fad’a akan Sakina da abubuwan da muke yi..I was furious!

Sannan burin da na d’aura akan Auwal ya mallaki MT duk sai naga yana shirin tab’arb’arewa tunda na lura shi soyayya ce a gabanshi a yanzu!

Hankalina bai sake tashi ba sai da Mammy ta sanar min da cewar ta ga copies d’in takardun MT da Granpa ya mallakawa Aslam a d’akin ka a ranar. Lokacin da ta shiga, kai kuma ka fita ka barta a d’akin, wanda bamu san ma an mallakawa Aslam d’inba kuma bamu san ya aka yi kai ka sani ba.

A take take ce min. ‘Komai ya zo mana k’arshe ni da ita! Amman ta samo mana solution
dan daman tun da taji labarin kyautar gidan da Granpa ya yiwa Aslam ta gama cire hope akan MT a Yaranmu muddin Aslam yana raye!. Dan haka yanzu it’s either I’m with her ko kuma I’m doomed’.

Sai da muka keb’e mu biyu tukun ta yi min bayanin abunda za a yi shine…
‘Ga shinkafar b’era nan daman ita da shirin ta ta zo gara kawai a yita ta k’are!’.

Duk da a lokacin i was furious amman ban yi amanna da shirin nata ba, sai da ta yi mini
cikakken bayani kuma na lura komai ya kusan zuwa mana k’arshe tukunna na yarda but still sai na ce mata ‘Gara mu zuba iyaka wadda zata la’antashi ko ta sakashi doguwar jinya dan ni gaskiya ba zan iya kashe Aslam ba’.

D’ari bisa d’ari ta nuna min ta yarda, ban tashi sanin Mammy yaudarata ta yi ba sai da na ga gawar Ummi a kan cinyata”. Ta fad’i hakan tana fashewa da kuka.

Da sauri Mammy ta k’araso wajen ta ce “bana son munafurci! Munafuka ai da ke aka yi….”
Wata mahaukaciyar tsawa Dad ya daka mata ya ce “wallahi idan kika sake yin magana sai na kasheki da hannuna kafin a tafi da ke gidan yari!”

In a serious tone Granpa shima ya ce mata,“Ki nutsu! Ko In saka a fasa miki kai da bindiga”.

Sannan ya juya ya cewa Mom “Continue”.

Cikin kuka Mom ta ci gaba da magana. “Muna tunanin ta yadda za mu shiga d’akin su Aslam mu zuba a lemon cikin fridge d’in da yake a d’akin nasu ko mu zuba a ruwa ya sha, sai Allah ya kawo sauk’i
muka ji ya cewa Huda “ta had’a mishi coffe”.

Hudan na shigewa kitchen aka fara watsewa, muma muka fita. Mammy ta cewa Dad ‘zata tafi tare da k’awarta ta ajjiyeta a bakin gate yanzu’. A gaban sa ta shiga motar kawar tata, motarsu shi da Aisha tana fita ta fito ta yiwa k’awartata sallama muka zagaya baya ta ce min ‘in tsaya a nan baya in tabbatar babu wanda ya ganta. In yi keeping mata watch daga nan ita kuma zata shiga ta aiki Huda ko kuma dai ta d’an ja hankalinta ta watsa gudun kar idan zance ya fito Huda ta ce ita ce ta aiketa’.

Har zata juya na rik’o hannunta na ce mata ‘ta zuba d’an mitsitsi kawai dan Allah’.

A gabana ta nuna min d’an k’aramin da zata zuba wanda na tabbar ko b’era ba lallae ya iya kashewa ba!
Na so ta bani ragowar amman sai ta ce ‘ko dai ban yarda da ita bane ba?’ Shiyasa kawai na yi trusting d’inta na barta ta wuce.

Kafin Mammy ta zagaya ina zuwa bakin k’ofar kitchen d’in ta baya sai na ga. Hudan ta fita! Ina shirin kiran Mammy a waya naga an shigo.Wallahi Arshaad fuskarka da jikin ka a rufe suke ko’ina amman tashi d’aya na gane ka.

A tunanina bakin ku d’aya kaida Mammmy sai da na ga ka zaro allurar da bata cikin tsarin mu tukunna gabana ya fara fad’uwa.

Ba k’aramin sanyi na ji ba da naga har ka bud’e allurar zaka zuba kuma sai naga ka yi tsaki ka rufe ka mayar ka ajjiye alamun ka fasa”.

A take gabad’aya kowa a falon aka ce “Alhamdulillah”

Cikin kuka ta ce “Garin lek’en ka da nake ta yi yasa har ka gannni, ka fito ba tare da ka d’auke allurar ba.

A cikin filawowi na b’uya kana wucewa na zagaya, ta k’ofar parlour, zan shiga kitchen d’in tun a bakin main door na parlourn na hango Huda tana shirin shiga kithchen d’in amman ban hango Mammy a kitchen d’inba wadda na tabbatar ita ce ta had’a da allurar da ba lalle ta gama sanin ta mecece ba ma da shinkafar b’erar ta matse gabad’aya a cikin coffee d’in wanda sanadiyyar hakan ne na rasa y’ar uwa ta d’aya tilo
a duniya.

Da sauri na fita na zagaya baya. Ina zuwa bayan kitchen d’in na ga Mammy a wajen tanata gumi, ta ce min ‘ta zuba amma fa saura kad’an Huda ta kamata’. Jin kamar tahowar mutum ta bayan mu ne
ya sanya kawai muka yi sauri muka bi ta gaba muka bar wajen. Na saka driver ya mik’a Mammy estate
ni kuma na koma part d’ina.” Cikin kuka ta ce “Arshaad ba kai za a kama ba, Mu za a kama…baka da laifin komai”.

Da sauri Mammy ta ce “Ke dai za a kama munafuka!!

K’arya take yi min, duk abunda ta fad’a k’arya ne wallahi.”

A hankali Arshaad ya lumshe idanuwanshi wasu zafafan hawaye suna zubo masa.

Mom bata damu ba ta ce “Another things…

Although ban san waye ya turo Mommy daga bene ba but Mammy nake zargi dan na ji tana waya rannan kamar da malaminta ne tana cewa ‘a sake toshe mata baki a goge mata tunani kar ta tona mata asiri kafin ta san abun yi next da ita’ da kuma na tambayeta sai ta k’i gaya min komai dan haka bani da tabbas
amman tabbas na san wanenen musabbabin ciwon nata tun farko. Mammmy ce ta yi mata asiri!

Har wajen bokan da yayi aikin idan kuna so zan kaiku. Shiyasa tun a cell Mommy tana warkewa mu bama ma saniba. Ita kuma Mammy ta fara mugayen mafarkai. Inaga sauk’ar da akeyi a gidan nan kullum ne ya sanya abun bai koma kanta ba ta samu mafarkan suka barta.”

A hankali Aslam ya ce “Ita ta turo ta daga bene” Kafin ya kalli Mommy ya ce, “Mommy ranar da naje zan ce miki Ina son tafiya Uk ana i jibi auren su Arshaad. Pretending kawai na yi dan ban san ta Ina zan fara ba
sannan naji kin ce peace da kwanciyar hankali kawai kike buk’ata a yanzu. Amman tabbas na ji conversation d’inku ke da Dad.”

Mom ce ta sake cewa “Sannan mammy.”

Da sauri Mommy ta k’arasa gaban screen d’in ta had’e hannuwanta biyu ta ce, “Dan Allah dan Annabi Adama ki yi shiru”. Sai kuma ta fashe da wani sabon kuka.

A hankali Granpa ya ce “kowa ya zauna”

Ba ayi minti uku ba duk suka zazzauna har Arshaad da Granpa ya sake ce mishi. “Muhammad zauna kaima”

Da kyar Granpa ya samu ya ci gaba da magana. “da za mu yi amfani da tombprint mu hukunta mai laifi.

Second hannun da ya fito a jikin tukunya apart from na Huda hannun Rukayya ne!

Sannan ya sake fitowa a jikin syrinji tare da na Arshaad. wanda na tabbatar kafin ya saka safar da Adama ta fad’a ne ya yi mistake ya rik’e dan bai fito a jikin tukunya ko murfin ta ba.

Ya fahimci hakan ina ga tun a ranar da aka d’auka samples d’in shiyasa ya yanke shawarar ya gudu!

Ban kuma san me ya dawo da shi ba dan haka yanzu inaso ka fad’i gaskiya da gaskiya tun da an san komai
kuma muma mun fahimci komai.

Kaga waennan manyan y’an sanda da ss ne kar ka cuci kanka ka yi bayanin da zasu d’auki rahoto dan na yi alk’awari sai na hukunta duk wani mai hannu a kisan Ummi!.

Shin maganar da Adama ta fad’a gaskiya ce?”

A hankali Arshaad ya girgiza kanshi kafin ya ce “Ba haka bane ba! Ni ne na zuba!

Ni na yi hacking wayar Sakina na kira Huda waje tana fita ni kuma na je na zuba!

Dama ina da wannan plan d’in a raina tun dawowata saboda na fahimci Aslam yana son auren shima.

Granpa na rok’eka da girman Allah ka barsu su tafi da ni.”

Tsabar takaici Aslam bai san lokacin da ya shak’o sa ba ya ce, “Meyene ribar ka Idan an tafi da kai?
Me za ka ji a jail!? Arshaad ka san inane jail kuwa?”

Sai yanzu Gramma wadda tunda aka fara case d’in ta sunkuyar da kanta tana salati ta samu ta fashe da kuka. A hankali ta d’ago kanta ta taso ta iso inda suke ta kama Arshaad ta mik’ar da shi tana kuka ta ce “Aslam ka manta waye Arshaad ne?

Tun kuna Yara. Idan ya yiwa mutum laifi b’uya fa yake yi ko da ace mutumin ya yafe masa sai yayi kusan wata yana wasan y’ar b’uya da shi. Ka san Arshaad yana da kunya yana da kawaici kuma yana k’aunarka!

Na tabbatar laifin da ya aikata ne ya saka shi yake jin ba lalle a yafe mishi ba sanann shi kanshi ba zai iya fuskantar kowa ba shiyasa ya gwammaci zaman jail a kan zama da mu sannan kuma ka tuna Arshaad
yana iya sacrificing komai saboda Mahaifiyarsa unlike her! I’m pretty sure ita yake ta k’ok’arin rufawaa asiri
wanda hakan ya had’u da guilt shiyasa yake k’ok’arin tura kanshi jail!

Haka ne ko ba haka ba! Arshaad?” Gramma ta k’arashe maganar tana sake fashewa da wani sabon kukan.

Gaba d’aya kuka suka saka. Aiima Huda Dad Sudais Shuraim Mammy Daddy Mommy hatta Granpa da Abba wanda yake chan a zaune ya kasa motsi kowa kawai hawaye yake yi.

Hannuwan Gramma ya rik’e gamm! A cikin nasa ya ce, “Gramma dole Ina da laifi one way or the other..
Ga Junaidu sannan ga successful company d’in da na tarwatsa na lalatawa Aslam. Na biyewa son zuciya Gramma! Na biyewa, So da buri, ki kyaleni dan Allah ki rabu da ni. I need time alone away from all of you!
Besides Ina jin tsoron kaina a duk lokacin da na ga Huda da Aslam na kan ji tsananin kishi!

Ba zan iya ba! This is torture! Ni kad’ai na san abunda nake going through”. Ya k’arashe maganar yana fashewa da kuka.

Wanann karon hatta Abba kuka ya saka.

Da sauri Huda ta mik’e ta fita da sauri. Aaima kuma ta bi bayanta.

Bata tashi sanin Aaiima na bayan nata ba sai da suka shiga cikin parlourn gidanta.

Jin mutum a bayanta yasa ta juyo suna had’a ido kawai sai suka fashe da kuka a tare gaba d’ayansu.

Da kyar Huda ta iya d’akko wayarta ta kira Junaidu yana d’auka ta ce “Dan girman Allah ya zo tana son ganinshi a kan case d’in Ya Arshaad! Ya dubi girman Allah ya taimaketa idan wannan ce alfarma d’aya tak da zai yi mata a duniya ya zo ya yi withdrawing complaints d’inshi dan ya rasulillahi.”

“Za mu yi arresting Rukayya Yusuf za mu tafi da ita! Za a sake bincikar ta sannan a kotu za ta ji hukuncinta” Daya a cikin y’an sandan ya fad’a.

Anfi 20 minutes ana fama da Mammy dan hauka tayi musu tuburan da kyar sai da aka nuna mata bindiga tukunna ta tsaya aka datsa mata ankwa.

Kukan da Arshaad yake yi sai da ya saka kowa kuka. A hankali ya durk’ushe a wajen.

Mommy ma ta so hanawa amman Dad ya rik’eta haka aka fita da Mammmy tanata kuka tana tonawa kanta asiri dan sai faman jerowa Dad Granpa da Mommy Allah ya isa take yi a cewarta su ne suka tunzurata ta yi komai sannan in da Granpa bai bawa Aslam gida sannan ya bashi Mt a b’oye a munafurceba to da bata yi abunda ta yi ranar birthday d’in su Shuraim ba.

Ana fita da Mammy bayan d’akin ya d’auki shiru na kusan 7 minutes.

Babban y’an sandan ya yi gyaran murya ya sake cewa, “Unfortunately za mu tafi da Arshaad shima.

Bashi da laifi a case d’in Ummi amman yana a case d’in Junaidu! Kuma Junaidu a sama shima ya kai k’arar shi dan direct case d’in daman hannuna ya fad’o.

Sannan Aslam ma idan yanaso zai iya filing complaint ya yi shara’a da shi akan tarwatsa mishi company da ya yi.”

Cikin tsananin b’acin rai Asalm ya k’arasa inda mutumin yake tsaye ya ce, “Who the hell do you think you are? Ni zaka gayawa abunda zan yi da brother d’ina!?

Idan na sake ji kace zan yi shari’a da shi I ‘ll make sure ka yi regretting kasancewarka d’an sanda!
Off you go. Just leave! Za mu k’arasa issue d’in mu mun gode.”

A hankali cikin d’an b’acin rai mutumin ya ce, “Mr Aslam watch you words!


Kuma let me assure you. Idan ba Junaidu ne yazo nan ya ce ya yi withdrawing complaints d’inshi a Arshaad ba to dole za mu tafi da shi! And idan ka yi interfering to, za mu had’a da kai”

A hankali Arshaad ya mik’e ya k’arasa ya dafa kafad’un Aslam ya ce, “Let it go, It’s fine i’m fine.”

Yana shirin yin magana Junaidu ya shigo shi da Aaima. Tabbas! Ya so ya hukunta Arshaad, yaso ya hukuntashi akan irin abunda ya yi masa amma ta dalilin Hudan sannan tsakanin shi da Aaima tabbas ya san watak’il wani abun ya k’ullu dan tunda ya ganta ya rasa sukuni sam! Waennan dalilai biyu suka sanya kawai ya k’arasa inda mutumin yake tsaye ya ce “Na yi withdrawing complaint d’ina! Arshaad can go free.
Allah ya sa mu fi k’arfin zuciyoyinmu.”

Wata nannauyar ajiyar zuciya Aslam ya sauk’e, kafin ya juya inda Junaidun ya ke ya yi hugging d’inshi sannan ya d’ago yad’an yi tapping shoulder d’inshi ya ce. “Thank you Junaidu, thank you so much.”

Murmushi kawai ya yi Arshaad yana shirin yi mishi magana ya juya ya fita.

Da sauri Aaima ta bi bayansa dan yi mishi godiya.

Bata samu ta cimmasa ba sai a compound d’in Granpa dan sauri yake yi sosai. Da d’an k’arfi ta ce
“Hey”

Ajiyar zuciya ya sauk’e ya lumshe manyan idanuwanshi tukunna ya juyo.

Gaba d’aya jikinta a sanyaye yake a haka ma bata ga sanda aka tafi da Mammy ba.

Tana zuwa ta ce “Thank you. Mun gode kwarai!


Allah Ubangiji ya taimakeka kaima a lokacin da kake buk’atar taimakon gaggawa”

A hankali ya d’an sunkuyar da kanshi, har ya d’ago zai yi magana sai kuma ya lura da yanayinta.

Ganin da yayi bai kamata su yi wannan maganar yanzu ba yasa ya ce,.

“Ba komai. Amman akwai alfarmar da nake nema a wajenki! Naga yanzu, you are not in a good shape idan ba damuwa zan iya zuwa nan da 1 week da laasar, around 5 haka! I need to talk to you.”

A hankali ta ce “Allah ya kaimu”

Daga nan suka yi sallama ta sake yi mishi godiya ta koma ciki. Tana tafe tana matsar hawaye.

Abakin kofar shiga taga mutumin ya fito da ragowar mutane biyu

Haka kawai jikinta ya bata an tafi da Mammy dan daman bata ganta ba d’azu da ta dawo parlourn.

Anan wajen kawai ta durk’ushe ta sa kuka.

Aslam yana ganin mutumin ya fita ya sauk’e ajiyar zuciya ya kalli Gramma ya ce,

“Gramma Ina takardun dana baki d’azu da safe?”

A hankali Gramma tana matsar hawaye ta juya ta nufi hanyar d’akinta.

Bata yi 4 minutes ba ta fito rik’e da wasu takardu masu yawa file file wajen uku.

Bai bari ta k’araso ba ya k’arasa ya karb’a sannan ya zaunar da ita a kan kujera ya ce “thank you”

A hankali ya k’arasa ya d’an rissina ya mik’awa Granpa ya ce ‘ya duba, yana zuwa
bara ya d’anyi magana da Arshaad.’

A hankali ya k’arasa inda Arshaad yake ya ce “Arshaad you are my brother and best friend.

Bani da d’an uwa kuma Aboki kamar ka amman ka yi hak’uri ba laifina bane. Allah ne ya d’aura mana son mace d’aya!

Ba zan iya b’oye maka ba, I loved Huda tun kafin ka kaini wajen ta mu gaisa i knew her tun ina Uk….”

Nan ya bashi brief labarin da ya gayawa Huda. A hankali ya ce “Da na dawo naga yadda kake k’aunarta
shiyasa kawai na yi deciding. In bar maka ita! Which almost kill me shiyasa yanzu nake mai baka hak’uri.

Da ace inada iko da zuciyata to da na hak’ura na bar maka ita amman ba zan iya ba!

I’m sorry to say this to your face wallahi ban san irin k’aunar da nake yi mata ba
ban san ma kalar wannan son nake yi mata ba sai da na mallaketa a matsayin matata!

Dan Allah ka yi hak’uri ka fahimceni.”

Hugging d’inshi kawai Arshaad ya yi yana hawaye.

Dakyar suka cika juna. Arshaad d’in ya ce “You have sacrificed a lot for me ka gaya min dalilin da zai sa ba zan hak’ura In cire matarka a raina ba? Kar ka damu you have tried Aslam for my happines, kanaji kana gani ka danne farin cikin ka saboda ni in yi farin ciki.

You are the best brother and the best friend in the world. Komai ya wuce.

Ina so ka saka a ranka kamar ban tab’a had’uwa da Huda ba.

Amma dan Allah please inaso zan bar k’asar nan! For some years.


Ina son in yi healing daga Mammy da kuma everythin..

Don’t stop me please…”

Murmushi Aslam ya yi kafin ya ce “ba zan barka ka tafi haka ba”.

Ya fad’i haka yana mai juyawa ya isa inda Granpa ya ke yad’an rusuna tukunna ya karb’a takardun da Granpa ya gama dubawa ya fara magana.

“Granpa ya mallaka min Mt duk da na san kowa ya sani a nan a yanzu, wanda maganar ta fito ne ta wajen Mammy da ta ga copies d’in takardun a d’akin Arshaad, shi kuma na san a mota ta ya ga takardun ranar da ya d’auka ya fita ya ce tasa ta lalace.

A ranar da ya bani gida a UK a ranar ya bani had’e da MT.

Ba yadda ban yi da shi ba
amman ya ce ‘yana so yayi komai ya gama ya gaji da cases kuma daman shi ni ya shirya bawa.’


Na yi godiya tabbas na kuma yi farin ciki amma a ranar na fara working akan nima nawa decision d’in.

Arshaad, mun yi magana da kai a kan kana so ka bar k’asar nan shiyasa na baka na Uk! Hope you are happy.”

Da sauri kowa ya zuba mishi ido.

Murmushi ya yi ya d’aga musu kai alamun tabbatarwa. Sanann ya ci gaba da magana. “Auwal kuma na bashi na Abuja, ni kuma na d’auki na Kano”

A hankali ya juya inda Granpa yake ya ce. “Granpa ba wa ban ji dad’i akan kyautar da ka yi mini ba No I really appreciate it but this has been my wish since.

It was your wish ka mallaka min MT ni kuma wish d’ina shine mu rabashi a tsakaninmu brothers uku. I hope ban b’ata maka rai ba sannan kayi farin ciki da decision d’ina.

Ban yi tempering da wish d’inka na passing MT from generation to generation ba. Instead na sake fad’ad’a wish d’in naka ne Na tabbatar duk mu uku zamu zage kwazo wajen kular maka da MT in sha Allah, kowa zai kula da nashibsannan za mu yi passing d’in shi each to our capable child just like you wanted sannan zamu rubuta mu ajjiye y’ay’an mu suma su bawa capable jikan mu each suma kuma jikokin namu su bawa capable a ƴaƴansu. A haka dai har illa masha Allah.

I hope ban sab’a maka ba.” Ya k’arashe maganar yana sunkuyar da kanshi
ganin yadda Granpa ya kafeshi da idanuwa.

A hankali Granpa ya mik’e ya sauk’o daga kan kujerar tashi ya dogara sandarshi ya k’arasa inda Aslam yake tsaye ya shafa fuskarshi a hankali
yana jin tsantsar k’aunar jikan nashi tana sake shiga cikin zuciyarshi, a hankali ya ce “I wonder why
mutane suke jin haushi. Idan nace kaine favorite jikana.”

Yana gama fad’in haka ya ce “Allah ya yi muku albarka. I’m very happy with your decision, thank you.”

Daga nan yasa kai ya wuce side d’inshi yana dogara y’ar sandarshi Gramma itama ta mik’e ta mara mishi baya.

A hankali Dad ya k’arasa ya yi hugging Aslam sai kuma ya jawo Arshaad shima ya had’asu duk su biyun ya rungume.

Murmushi Abba yayi shi da su Shuraim waenda suka koma kusa dashi tun d’azu da za a tafi da Mammy suka mak’ale masa.

Haka shima Daddy yana d’an murmushi idanunshi tap kwallah ya ce
“Ina ma a ce ina da super powern da zan yi using in ganni a tsakiyanku”

Dariya duk suka yi har Mommy.

A hankali ya ke kallonsu kafin ya ce
“Sai mun dawo in shaa Allah. May this smile never fade away a fuskokinmu”

Duk had’a baki suka yi wajen cewa “Ameen” Daga nan su Daddy suka yanke kiran.

<< So Da Buri 70So Da Buri 72 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×