A hankali Mama ta lumshe idanuwanta wasu hawaye suna zuba. Daidai nan Ummu ta shigo, tana Isa gareta ta sa hannu ta yi hugging d’inta ta ce “congratulations”.
Ajiyar zuciya kawai Mama ta sauk’e daga nan d’akin ya fara cika da jamaa.
Banda hayaniyar mata babu abunda ke tashi.
Suna cikin hira suka ji d’aurin auren Jalila itama, nan take kowa ta hau tofa albarkacin bakinta wasu su ce “Allah shi k’ara” wasu kuma su ce “Ai ta ma yi sa a data auri Abdullahin, Mutum mai kirki da hankali da zuciyar nema wallahi ta. . .