Duk juyowa suka yi suna kallonshi da mamaki a kan fuskokinsu. K’arasowa yayi ya kalli Mama ya ce “Na ce miki yarinyar nan yawonta ta tafi irin wanda kika yi amma kin k’aryata ni ko? To mai adaidaita sahun da ya kawota shi na bi na tsare na tambaya ya kuma tabbatar mini da cewa ‘ita da wani saurayi dogo fari tass suka tsaida shi a wajen kwandila, bayan ta shiga har yana ce mata ta gaida su Mama har ya bada dubu d’aya a kawota, da mai napep d’in ya bata chanji tabce ta bar. . .