Tun K’asimu yana b’oyewa har ya zo ya fara nunawa a fili, daga ya je chan ya tsugunna ya zagi Madu sai ya je chan ya tsugunna ya yi masa sharri.
Babu inda zai zauna ya tashi bai zage sa ba, shi kuwa Madu harkar gabansa kawai yake yi sam baya bi ta kan K’asimu dan ya lura ko sallama idan yayi masa ba amsawa yake yi ba.
Tsananin tsanar Madu bata sake tabbata a zuciyar K’asimu ba sai a lokacin da kud’in hayar shi K’asimun na wajen shekaru uku ya taru, anyi anyi ya biya ya k’i biya, gashi gidan na marayu ne suma suna fama da yanayin rayuwa, jin labarin sabon limamin da a ka nad’a ba da jimawa ba mai aiki da addini gashi yayi karatun lauyoyi duk unguwa ana girmamashi ne ya sanya wadannan Marayu suka garzayo wajen Madu akan ya taya su fad’in gaskiya a basu hakkinsu, ai kuwa Madu bai yi k’asa guiwa ba sai da ya tabbata ya karb’a musu hakkinsu har saida ta kai ga tirsasa K’asimu siyar da y’an dabbobim shi ya biya su hakkinsu da kud’in.
Jarumta da tarin ilimin Madu ne ya sanya aka nad’asa ‘mai unguwa’ a lokacin shekarar sa goma da zuwa garin Kano.
Sai kuma a lokacin ne Allah ya bawa Shuwa ikon samun ciki.
Kusan a tare suka haihu ita da matar Bashir da matar K’asimu.
Matar kasimu ita ce ta fara haihuwa,ta haifi y’arta mace aka sakamata Halimatus Sa’adiyyah sai matar Bashir ta haifi y’arta itama mace Zainab,
Shuwa itama ta haifi mace, Maryama.
Duk a tsakanin haihuwar watanni bibbiyu ne.
Murna a wajen Madu kuwa ba a magana, saboda daman shi akwaishi da son Yara, shiyasa su Usman da Jamilu sunfi sakewa ma da shi fiye da Mahaifinsu dan idan ba sani ka yi ba ko fad’a maka akayi ba to ba zaka tab’a cewa Madu da Bashir ba y’an uwa bane ba, saboda tsananin shak’uwa da k’aunar junan dake a tsakaninsu, gashi yanayin jikin su iri d’aya.
Maryama ta taso cikin gata saboda tsananin so da k’aunar da Mahaifin ta yake nuna mata, ga kuma yayyunta guda biyu Usman da Jamilu dan wani lokaci har fad’a ake yi wajen d’aukar Maryam tsakanin Jamilu da Usman duk da kuwa ga Zainab k’anwarsu.
Idan Maryam tace tana son abu nan da nan Mahaifinta zai nemo sam baya bari ta sake tambayar shi a karo na biyo duk da kuwa ba wani k’arfi ne da shi ba, Law ya karanta a lokacin albashinsa ba wani yawa ne da shi ba amman idan kaga Maryama ko y’ar gidan wani hamshak’in mai kud’in sai haka, suturar jkinta kad’ai abun kallo ne.
Tana isa shekara hud’u Madu ya had’ata da Zainab ya saka a makaranta, a wannan lokacin har sai da Talatu ta bawa Shuwa shawarar a nemawa Maryama maganin baki da mayu saboda babu inda zata je ba a tankataba.
Yarinyar chubby da ita gata fara farin ta irin mai yellow d’innan, gashin gira da idonta a ciccike ga gashin kai har gadon baya mai sulbi, idan ka kalle ta dole ka k’ara.
A haka rayuwa ta ci gaba da tafiya har Maryam da Zainab suka kai shekaru goma a duniya, sai a lokacin ne kuma aka saka y’ar gidan K’asimu (Sadiya)a makaranta da kyar!
Don a lokacin duniya ta yi masa zafi, yanayin rayuwa sai a hankali kuma shi ya dage ba zai sakata a makarantar gwamnati ba, a dole ta kud’in da su Maryam da Zainab suke zuwa nan itama zata je, a cewarsa ‘ai tare aka haifesu’.
Bayan shi basussukan da suke kanshi kad’ai ma abun mamaki ne,dan idan aka gaya maka zaka rasa ina yake kai kud’in, abu guda d’aya dai shine ko takalmi ne idan Madu ya sauya yau to tabbata sai ka ga irinshi sak a k’afar K’asimu washegari, duk wai dan ya nunawa duniya ‘ai Madun bai fi sa kud’i ba’ (a cewar shi), sai dai kuma duk inda aka yi sati 1 ko 2 nan zaka nemi takalmin ko suturar ka rasa saboda ya siyar ya cinye kud’in a banza. Yaransa duka uku babu mai zuwa makaranta da kyar ya saka Sadiya.
Layin nasu zuwa yanzu ya cika sosai dan a k’alla gidaje sun kai sha biyar, Bashir ya sayi filin jikin gidanshi ya had’e ya kuma yin wani had’add’en gini, Madu shima gininsa a layin gwanin ban sha’awa daman shi filin sa tafkeke ne ya siya, amman shi K’asimu har yanzu yana wannan gidan haya na marayu wanda k’arfi da yaji yake so ya danne ya mayar da gidan nasa.
Matarshi ta so ta had’u da Talatu da Shuwa amman tunda ta so had’a su fad’a Allah ya taimaka su kai saurin ganewa munafuka ce, sai suka yi saurin ja baya da ita, amma duk da ja bayan da suke yi da ita haka nan sai ta yi ta nanik’e musu.
Inda Allah ya taimake su sai wata dillaliya ta tare, nan ta koma suka jone, aikuwa tun daga wannan lokacin in dai ka ji hayaniya da fad’a a layin to ko daga gidan dillaliya, ko gidan K’asimu dan basa barin takwana, ko kallo ne kayi musu bai musu ba nan za su fara surfa ruwan bala’i, ga rashin sanin ya kamata da munafurci.
Wata rana cikin azumi K’asimu yana zaune a bakin titi, duk magidanta da samarin unguwar suna masallaci ana sauraron tafsirin Modu amman shi ya k’i shiga tsabar bak’in hali, saboda baya shiri da Madu kuma akwai maza guda hud’u a cikin masallacin wadanda yake gaba da su, dan haka ya gwammaci ya zauna shi d’aya har lokacin shan ruwa ya yi yaje ya amshi abun sadaka yayi gida domin dashi suke karya azumi, ko kwayar shinkafa babu a gidanshi.
Suna cikin masallaci suka ji kamar k’arar jiniyar y’an sanda, suna nan zaune suka ji k’arar tana ta matsowa. Kasancewar lokacin addu’a ya yi ya sanya suka rufe su kai addua masu son yin alwala suka mik’e suka yi waje, suna fita kuwa suka ga Yara suna ta gudu sunayin titi,bwani a cikin su ne ya tare wani Yaro ya tambaye shi “mai ya faru” shi ne Yaron yake ce musu, “wai motar sojiji ne mota uku, da na y’an sanda suka zo za su tafi da Baba K’asimu.”
Da sauri wasunsu suka yi bakin titin wasu kuma suka koma cikin masallaci domin sanar da ragowan mutanen.
Wadanda suka yi bakin titin ne suka hango K’asimu ana ta k’ok’arin dan nashi a motar y’an sanda yana tirjewa, yana bada hak’uri amman kafin su k’araso wajen har an tafi da shi.
A bakin Yaran gurin suka ji cewa wai “kud’in wani kurtun soja ya amsa ya sayi mota tun watanni biyar baya, kuma yace zai biya kud’in amman har yanzu bai biya ba.”
Cike da tarin mamaki suka koma masallaci domin lokacin shan ruwa ya yi, suna isa suka bud’a baki da dabino da ruwa akai Sallah kowa yayi gida domin karyawa.
Basu samu lokacin bin bayan K’asimu ba sai da suka idar da asham, Da Madu da Bashir da wasu mak’oftansu guda biyu (Kabiru da Nafi’u) suka tafi a motar Madu.
A cikin motar ne su Kabiru suke hira da Baba Nafi’u wanda yake tambayar “shin wai yaushe K’asimu ya sayi mota ne shi fa bai tab’a ganin motar ba.”
Nafi’u ne ya ce “ai tun watanni shida da suka wuce lokacin da Madu ya sayi mota shima ya tada hankalinshi ya dinga bi yana tambayar bashi kusan kaf layin duk wanda baya gaba da shi sai da ya tambaya bashi aka hana shi.”
Nafi’un ya d’aura da cewa “nima sanadiyyar ya tambaye ni aron kud’i nace masa babni da kud’i ya sanya ya fara gaba da ni har da ce mini ‘wai ni ba makwafcin gaskiya bane ba, Ina yi mishi bak’in ciki.’
To dai na ganshi da mota after one month kuma ina kyautata zaton a wajen wannan kurtun ya karb’a aron kud’i dan bai dad’e da tarewa ba a bayan layi lokacin.”
Kabiru ya ce ”Ikon Allah to ai ni ban tab’a ganin motar ba.”
Dariya Nafi’u ya yi ya ce “Ai motar ba ta kwana ba ina ga damfarar sa masu siyarwan suka yi. A ranar da ya siyota ya kawo ya zo ya yi parking, haka nan ta dunga hayak’i ta cika unguwa saida athma d’in Laraba ya tashi, ni fa da na fara ganin hayak’i wallahi na d’auka gobara ce ta tashi a gidan nasa, lokacin dawowa ta kenan daga kasuwa ko gidana ban shiga ba na ce bara in duba gidan nashi inga, ina lek’awa kuwa na hango shi da Salmanu da Umar sunata bulawa motar k’asa don k’ok’arin kashe hayak’in. Hansai kuma tanata kuka ita da Sadiya suna jijjiga mahaifiyarsu wadda ta sassank’are tana numfashi da kyar. Ban bi ta kansu ba naje da kyar na nemo abun hawa aka kai Laraba asibiti, shi kuma ya tafi kai mota gyara, kusan duk d’an abin hannunshi saida ya k’are a wajen gyaran motar nan. Daga karshe ya maidawa wanda ya saya a wajenshi shi kuma ya ce an kwak’ule motar a wajen gyara bata da wani amfani, inaga a dubu hamsin ya sai da motar da kyar ya amshi kud’in, dan ta tashi a aiki.”
Madu ne ya katse musu hirar su ta hanyar ce musu “Mun iso!!”
Suna shiga kuwa suka ci sa’a inda suka je d’in aka kaishi, bayan sun buk’aci ganinsa ne aka fiddoshi har an fara sauya mishi kamanni. Da farko ya so yayi tirjiya da b’oye b’oye, amma da yaga ba sarki sai Allah sai kawai ya hak’ura ya gaya musu gaskiya “kud’in kurtu ya karb’a ya sayi mota kuma shi yanzu bashi da halin biya.”
Madu da Bashir su suka had’a kud’i su kai belling shi, bayan ya dawo gida Modu da Bashir suka bada rabin kud’in mota, shima K’asimun d’an kud’in hannun shi ya tattaro ya had’a da adashin Laraba aka had’a duk amman duk da haka kud’in bai cika ba. Da kyar da taimakon wasu makwaftan aka had’a ma kurtu kudinshi dan cewa ya yi “wallahi bai san Asara ba!.”
Bayan sun dawo gida ne da washegari, Modu ya samu Bashir ya ce masa “su taimaka su had’awa K’asimu kud’i su bashi ya ja jari ya daina yawon neman bashi, tare aka taso bai kamata su barshi a haka ba.”
Dama shi Bashir da kyar ya yarda, ai kuwa! A cikin azumi suka bashi kud’in lokacin yanata murna yayi ta godiya har da rungume Madu. Bayan Sallah tana yi K’asimu ya rangad’a sabon Aurensa, ya auro baffulatana Yarinya y’ar k’arama shekara d’aya Jamilu ya ba ta. Ai kuwa gidan nan nasa ya sake hargitsewa, gashi shi ba wata tsayayyiyar sana’a garesa ba dan haka kowa zuciyarsa a kusa! Kullum cikin fad’a, daman itama amaryar irin marasa kunyar nan ne, kowa baya ragawa kowa.
Yadda basa ragawa junansu haka nan y’an waje ma ko kallo ka yiwa d’aya daga cikin yaran in bai musu ba duk girman mutun haka za su zuba maka tujara, shi yasa ake yiwa gidan lak’ami da ‘Gidan marasa tarbiyya,’.
Sun kuwa tsani sunan idan suka ji sunan a bakin wani tofa ranar rigima sai inda k’arfinsu ya k’are.
A wannan lokacin ne kuma Shuwa ta sake d’aukar ciki, Maryam da Zainab da Sadiya suna da shekara goma a duniya.
Murna a wajen Maryam da Zainab ba a magana dan har sun fara shirya kalar party d’in da za su yi idan Shuwa ta sauk’a lafiya.
Kullum kuma cikin addua suke Allah yasa k’anwa za a haifa musu don su dinga yi mata kitso suna yi mata kwalliya.
Wani abun mamaki, Zainab k’awar Maryam ce sosai a da amma tunda ta fara zuwa makarantar su sai suka had’ewa Maryam kai, ita Zainab ashe dama tuntuni tana d’an jin haushin Maryam saboda su ya Jamilu sun fi sonta, da taimakon zugar Sadiya kuwa k’iyayyar Maryam ta samu waje a zuciyar Zainab, daman chan ita Sadiya ta tsani Maryam domin kuwa ita ya’yan masu kud’i ta so yin huld’a da su amma sam basa kula ta, Maryam suke so da k’awance duk da ita kuma Maryam d’in ba ta kulasu sosai dan bata da hayaniya.
Duniya ta fara yiwa Maryam zafi a lokacin da k’awarta kwalli d’aya ta juya mata baya. A yanzu ko kai su makaranta Zainab ba ta yarda a yi tare balle a d’aukosu, ta gwammaci ta biyawa Sadiya su tafi a k’afa su dawo a k’afa! Wanda har su je su dawo kuwa basu da aiki sai na zagin Maryam ita amma ta san suna yi ba.
Ana cikin haka ne Shuwa ta haihu, ta samu y’arta mace ranar suna ta ci suna ‘Bilkisu’, bayan suna Maryam ta had’a party duk wani yaro saanta ta gayyata ana i washegari amman Sadiya sai ta hana Zainab zuwa sannan ta sakata ta sato kud’in Babanta da ya ajjiye, abinda bata taba yi ba.
Haka nan suka dinga bin Yara suna raba musu kud’i akan ‘ “kar su je Partyn Maryam’ wai ta saka guba a lemo, su jira su gani babu wanda zai je saboda bak’in jini ne da ita.”
Ai kuwa hakan aka yi ko wanne Yaro ya karb’i kud’i yak’i zuwa party kar ya je a bashi guba.
A ranar Maryam kwana tayi tana kuka, tun daga ranar kuwa bata isa fita ba sai Yara su fara mata wak’ar ‘mai bak’in jini’ Sadiya ta kafa ta tsare duk wanda taga yana shirin fara yin k’awance da Maryam nan da nan za ta saka Zainab ta je ta sato kud’in mahaifinta ta bawa yaran ta ce su zab’a ko kud’i ko k’awance da Maryam.
Bashir tun baya fahimta har ya fara fahimtar ana d’aukar masa kud’i.
A haka shekaru suka yi ta shurawa abun tun yana damun Maryam harta hak’ura ya daina damunta da taimakon Shuwa.
Ranar wata Juma’ah Baba Bashir ya tafi masallaci aka yi rashin sa’a ya manta bai d’auki darduma ba kuma ya makara don Madu yayi tafiya so ba tare za su tafi ba, hakan ya sanya ya dawo, yana shiga d’akinsa kuwa ya kama Zainab dumu-dumu, ai kuwa ta daku a ranar kuma ya titsiye ta sai da ta fad’a mishi komai plan d’insu da Sadiya ba abinda ta b’oye.
Kunya! Kamar k’asa ta tsage Bashir da Talatu su shige haka suka ji. Mutumin da yake biya mata kud’in makaranta bai tab’a nuna gajiyawa ba shine take yiwa y’ar sa haka??
A lokacin suna aji biyu a js amman babu shiri aka siya mata form ta yi junior waec , aka fara shirin tura ta boarding. Madu yana dawowa Bashir ya rok’esa ya ce “yana so zai had’a da Maryam ya kaisu makarantar kwana, anfi karatu dan kwata-kwata Zainab bata karatu”.
Sam Madu bai so haka ba don baya son yayi nesa da Maryam amman kawai sai ya yi kawaici ya amince.
Bashir a tunanin sa Zainab da Maryam za su shirya ne idan an kaisu boarding tare tunda daman chan k’awaye ne, kuma yana kyautata zaton Sadiya ce ta had’asu fad’a. Sai dai kuma ko da aka je boarding d’inma, farin jinin da Maryam take da shi a wajen Malamai da d’alibai sai ya sake jawo mata bak’in jini a wajen Zainab, sannan Yayanta Usman sai ya zo makarantar sau da yawa wajen Maryam amman ita sai dai ya bada sak’o ya ce a bata, kuma sai ya cukowa Maryam leda da kayan kwad’ayi amman ita sai ya bada kad’an yac e a bata.
Abunda ba ta sani ba a ko da yaushe sai Maryam d’in ta k’ara mata a kan wanda Ya Usman d’in ya bayar ya ce bata.
Haka kurum sai ta daina kulata ko ta hau yada magana idan ta ganta, shirin da ake so dai su yi bai yiwu ba domin kuwa alamarin k’ara tab’arb’arewa ma ya yi don kwata-kwata Zainab da Maryam basa shiri, duk mates d’insu sun sani.
Har sai da Zainab ta kai Maryam bango duk kuwa hak’urinta sai da ta tanka mata suka yi wani damben da suka jiwa kansu ciwuka har aka kai ga kiran iyayen su, sai a nan ne Madu ya ji abinda ya faru har Bashir ya kaisu boarding duk dan ya samu daidaita tsakaninsu.
Ganin k’ok’arin Bashir na ganin zaman lafiya ya wanzu ya kuma tabbata a tsakanin Yaran nasu ne ya sanya kawai shima Madu ya barsu suka ci gaba da boarding d’in.
Wanda bayan sun dawo hutun gama ss1 ne Ya Usman ya zo da zungureriyar wasik’ar shi ya bawa Maryam ta inda ya ke bayyyana mata cewa shi fa sonta yake yi tun tana y’ar k’aramar ta.
Ita dai Maryam ba za ta ce bata son Ya Usman ba saboda Yayanta ne kuma ya kula da ita sosai, amman a gaskiya so na soyayya sam bata yi masa kwata kwata. Ko da ta gayawa Umma Talatu da Hajiya Shuwa, kalar murnar da ta gani a kan fuskokinsu ne ya sanya kawai ta amince suka fara soyayyarsu ita da Usman gwanin ban sha’awa.
Zainab kuwa (duk da kaita boarding school d’in da aka yi hakan bai saka sun rabu da Sadiya ba, don indai aka aike Zainab to sai ta biya wajen Sadiya a b’oye).
Ai kuwa tana jin labarin soyayyar Maryam da Usman, Sadiya ce kawai ta fad’o mata a rai, dan ba zata iya irga adadin wasik’un da Sadiya ta bata ta bawa Ya Usman ba, tun tana y’ar shekara sha d’aya take son Ya Usman,
shi kuma Ya Usman idan akwai wadda ya tsana a duniyar nan to Sadiya ce! Idan ka kalli Sadiya sam ba zaka tab’a ce mata mummuna ba, ba doguwa bace ba amman tanada manyan idanuwa da matsakaicin hanci bakinta dai dai misali ga dimples a fuskarta sai dai bak’a ce amman tana da dirin jiki mai kyau sannan tana da gashi wanda ya sauk’o har kan kafad’arta, sai dai sam wadannan qualities na Sadiya basu d’ad’a Usman da k’asa ba hasalima shi ya tsane ta kwata-kwata bata kwanta mishi ba.
A cewar shi Yarinyar bata da kamun kai, ga munafurci irin na Ubanta dan sarai ya san ita ta shiga tsakanin Maryam da Zainab, shiyasa daya ga nacin nata yana neman yi mishi yawa ya had’asu ita da Zainab d’in ya ci ubansu, tun daga ranar ya samu sa’ida.
Sai dai fa duk da hakan da yayi sam soyyarshi a zuciyar Sadiya ba abinda ya ragu sai ma k’aruwa da tayi.
Da wannan tunanin Zainab wadda ta saci hanya ta isa gidansu sadiya, bayan sun gaisa da Baba Laraba ta tambaye ta Ina Sadiya tace mata “tana d’aki”.
Tana shiga ta sameta a kwance tana bacci, jijjigata Zainab ta shiga yi har sai da ta farka sannan ta shiga koro mata halinda ake ciki
A ranar Zainab ta sake gasgata soyayyar Usman a zuciyar Sadiya domin kuwa kuka ta dinga yi harda ihu kamar wata y’ar k’aramar Yarinya da kyar suka lallasheta ita da Baba Laraba bayan ta shigo Zainab ta gaya mata halin da ake ciki.
kafin ta bar gidan kuwa zazzab’i ne mai zafi ya rufe Sadiya dan ko idanunta bata iya bud’ewa.
Satin Sadiya uku tana rashin lafiya, idan ka ganta sai ka tausaya mata, duk ta rame ta fita a haiyyacinta, har shagon d’inkin Usman taje tai sallama da shi daya fito tayi ta masa kuka, ganin da yayi abun nata na gaske ne yasa ya lallasheta ya rakata gida, wannan itace rana 1 daya mata magana mai dad’i shiyasa tana dawowa gida har mamakinta Laraba ta dinga yi saboda yadda ta ware kamar ba ita ba.
Hutun makaranta ya k’are! Su Maryam an fara shirin komawa, wannan karan Baba Bashir ne ya yi musu provision da kyar Madu ya bari kuwa.
Ranar Lahadi Usman da Madu suka maidasu makaranta.