Kawaye uku da ke tafiya a gefen titi cikin shigar uniform na makarantar islamiyya, riga da wando da hijab ta karshe daga hagu ta taba ta tsakiya sai ta dube ta dan manuninta ta daga ta nuna mata can hannun idanuwanta kuwa suka yi kyakkyawan gani, mahaifinta ne zaune a teburin mai shayi bayan kofin tea da ke gaban shi da sunkumemen bread akwai soyayyar Indomie da aka cakude ta da kwai.
Wadda ta nuna matan ta kwashe da wata irin dariya abin da ya ja hankalin ta karshen daga dama ta ce “Dariyar me kike Raliya? Sai da ta kara dariyar sannan ita ma ta nuna mata, ita da ta gani maimakon dariya daure fuskarta ta yi “Haba Raliya meye haka? “To me na yi? Ke fa Zahra akwai son mayar da kurji ya zama gyambo. Kuma ni sunana Rali ba Raliya ba. Ta kare fadi tana kada ido.
Wadda aka kira Zahra ta kara tamke fuska “Ba dai kyau haka.
Hadiza da fuskarta ta cika da rauni ba ta ce komai ba suka ci gaba da tafiya sai dai suna zuwa kofar gidan su Hadiza da shi ne farko kana shiga layin ta ja tunga tana musu sallama, Zahra ta ce “Amma ba gidanmu kuka ce za ku ba ku kalli maimaicin shirin kwana casa’in daga hadarin da ya sa aka taso mu da wuri ya baje? Ta girgiza kai tana zare hannunta cikin na Zahra “Za ni gida na bar Inna tana ciwon kai.”
Suka wuce ta shiga gidan na su gidan haya ne, irin gidan yawan nan ne dakuna bila adadin don mata goma sha biyar ne cif. Ta tsallake wawukekiyar kwatar da ta raba tsakar gidan ta isa dakin su da ke can karshen gidan, Innarta na tsugune a kofar dakinta tana dirzar kayan jama’a da aka kawo mata wankau. “Sannu Inna har kin ji sauki kike wanki? Ta daga kai tana ma yar ta ta wani busashshen murmushi “Na ji sauki Hadiza.” “To kin sha magani? Ta girgiza kai “Zan sha idan na kammala.” Cike da tausayi ta cusa kai dakin nasu da ba su mallaki komai ba sai shinfidun kwanciyarsu gami da yan tsummokaran sawar su ita da yan’uwanta.
Tana sauke mayafinta ta tsinkayi sallamar babbar yayarsu da ke fita tallar abinci za a iya cewa ma ita ta dauke nauyin cin su da shan su da tallar da take, sai wankau din da mahaifiyarsu take. Ta shigo dakin suka dubi juna da Hadiza ta ce “Kin dawo Yaya SA’a? Ta daga mata kai tana neman wurin zama da daidai sauran kannensu su uku suka fara shigowa mata biyu sai namiji daya, Luba ita ta shigo a karshe ita ce kuma ta biyu ita ke bi ma Sa’a Hadiza kuma na bin ta, ita ta fi su kwayun gani domin wata dattijuwa makociyar su take dauke da dawainiyarta cin ta shan ta har sutura ita kuma tana ma dattijuwar komai na aikace-aikace.
Babbar Cooler da abincin yake Sa’ar ta nuna ma Hadiza ta isa ta bude ganin abincin jingim ta dubi yayar take ta “Yaya Sa’a abincin fa da yawa.” Ta furta “Ku cinye.” Ta fita ta samo yan robobi yaran sai murna suke don tun fitar ta ba abin da suka sanya ma bakin su tun abincin da ta sauke ta dibar musu mahaifiyarsu ta yayyafita musu kowa ya raba jiya da yau. Nan da nan suka rufar ma abincin ta zuba ma uwar ta su ita dai Luba ta ce ta koshi, uwar ta shigo zanenta sharkaf da ruwa ta zauna gefe daya Hadiza ta tura mata nata abincin ta ce “Bai kare ba Sa’a? Tana tambayar tana duban kudin hannun Sa’ar da ba yawa. Ta daga kai don cikin tunani take inda za ta samo cikon kudaden da za ta yi cefanen gobe, wani bakanike da ke ƙulafucin ta kusa da inda take sayar da abincin ta tuna zuciyarta na ƙuna kan abin da za ta aikata amma tana jin ya zame mata dole ta ba ƙannenta da mahaifiyarta abinci. Zumbur ta mike ta fara sauya kayan jikinta ta fesa turare ta goga Hoda ta matsa kusa da Innarsu “Inna bari na je na dawo.” “To Sa’a, amma kar ki kai dare ki kula da mutuncinki don Allah. Ta ce “In sha Allah Inna.” Ta sa kai ta fice Innar na yafutar abincin a hankali Hadiza na kallonta ta gefen ido tana share hawayen tausayin mahaifiyar tasu da ke rugurguza ruhinta ta kare ta kode duk da take siririyar bafulatana amma fata ce kawai ta rufe kasusuwanta. Ba ta fi Loma uku ba suka tsinkayi murya daga kofar daki cikin hargowa tana fadin “Ina Hadizar take? Kafin Hadizar ta yunkura mahaifiyar su har ta isa bakin kofar ta daga yabudadden labulen su mai kama da mayanin tatar Koko da suka sakaya kansu daga ganin da wanda ke waje zai musu. Wata mace gabjejiya ke tsaye tana kada jiki “Me ya faru Maman Ummi? Innar ta tambaya da sanyinta “Hadiza ta bata min Iron kuma wallahi sai an gyara min ba zan yarda ba. Innar ta dubi gefenta inda Hadiza ke tsaye “Garin ya ya Hadiza kika lalata mata dutsen guga? Hadiza ta sunkuyar da kai ita kuma matar ta cigaba da bambami har hankalin ilahirin matan gidan ya dawo kansu, wasu na bada hakuri wasu kuma na fadin babu hauka ce ba ka da shi ba ka hakura? Innarsu dai hakuri take ta bayarwa ita kuma ta tsaya akan sai an biya ta. Karshe dai Innar ta ce “Ki bari a kawo min kudin wankau da na yi ko idan Sa’a ta dawo sai a ba ki ki gyara.”
“Ni ba zan jira har a dawo yawon barbada ba, ko a kawo wasu kudin wankau ba, akai min wurin gyara yanzu.” Luba ta mika hannu ta karbi iron din “Ki yi hakuri za a gyara miki.” Ta koma daki Maman Ummin ta fara barin wurin sannan dafifin matan gidan da yayansu suka fara darewa daya bayan daya. Innar su Luba kamar yadda mutanen gidan ke kiranta ta ja kafafuwanta ta koma daki yaranta suka mara mata baya sai da ta zauna ta fara ma Hadiza fadan aron kayan jama’a aka daga labulai matar kusa da dakinsu ce sai da ta ba Innar su Luba hakuri sai ta mika mata gudar dari biyu “Akai gyaran Innar su Luba.” Ta shiga godiya kamar za ta yi kuka duk gidan ita kadai ke tausaya ma halin da suke ciki.
Tana fita ta ce ban son fitar ku da daddare kasantuwar ku Yaya mata amma ba yadda na iya Luba ke da Hadiza ku je shagon Isuhu mai gyara ku kai mishi, ku yi sauri ku dawo.” A zaure suka ci karo da dan’uwansu da suke uba daya wanda akan shi baban su ya fara samun da namiji ya kuma fifita shi sama da su ya kuma mayar da uwar su tuwon tishe saboda tana haifa mishi Yaya mata don kafin Sa’a ma sai da ta haifi mata biyu duk sai an yaye su sai su rasu. Ganin yadda idanuwansa suka kada suka san da yan rashin mutuncin na shi kusa suka wuce shi suna addu’ar Allah ya sa kar masifar da ya shigo da ita ta shafi mahaifiyar su. Ilai kuwa kofar dakin ya yi burki ya daga labulai ” Ke ina abincina? Ya fadi yana mazurai idonsa akan Innar su Luba da ke zaune cikin tunani kala-kala na kalubalen rayuwa.
Hey ba ki ji na? Ya kuma maimaitawa don ko sanin zuwan shi ba ta yi ba ta daga idanuwanta da duk suka nutse suka koma loko don tsananin wahala sannan ta dauko robar abincinta da ta fara ci ta mika mishi shekeke ya dubi robar “Dan wannan abincin kamar za a ba na goye shi za a ba ni? Ya ja mummunan tsaki ya saki labulan “Ke da Baba. Ya sa kai ya fice yana hada hanya.
Da shigar Hadiza gida Zahra ta dubi Raliya “Kina da matsala Rali, ban son cin fuskar da kike wa Hadiza.” Ta yi fari da fararan idanuwanta da ya zame mata jiki “Mene ne na cin fuska? Dagus din nasu ne mugu wallahi kamar in shake shi, kullum yana gaban masu nama ko teburin mai shayi amma ya bar su cikin wahala. Zahra ta ja ajiyar zuciya Allah ya shirye shi ya ba Maman su Hadiza mafita. Ina tausayin kaina ina tausayawa baiwar Allan nan.
Suna ta maganar har suka kai gidan su Zahra da katanga ce tsakanin su da su Raliya gini ne na bulo akwai dakali guda biyu a kofar gida sai zauruka su ma biyu sannan ka isa filin tsakar gidan mai dauke da Sasa uku na kakarta ne farko sai na yayyen babanta su biyu, dakin kakarta da ke rukon ta tun rasuwar mahaifiyarta tana da shekaru hudu a duniya mahaifinta ba a gidan yake ba a Musawa yake zaune yana aiki da babbar asibitin garin na Musawa duk da yake karamin ma’aikaci ne shi, dangin mahaifiyarta ma duk suna Musawa tana zaune a falonta da babban danta ya kayata mata tamkar na budurwa tana taunar goronta ga radionta a gefe tana saurare ta dube su “Har an taso Islamiyar ?
Suka ba ta labarin tasowar hadari ya sa aka tashe su ta dubi Zahra ki samo muku abinci, akwai fura da Haj Baturiya ta aiko da ita tana cikin fridge.”
Cikin zumudi ta nufi fridge din sanin furar Haj Baturiya yan madaidaitan kofuna ta cika musu ta mika ma Raliya daya ta fara kurbar daya Raliya ta amsa ba a son ranta ba don ita abincin take so sanin ba a kawo ma tsohuwar abincin banza musamman idan daga bangaren Alh Umar ne babban danta da ya fi sauran wadata, mijin Haj Baturiya. Ta kai hurar baki sai ta lumshe ido don dadi da garɗin da ya ratsa ta bayan Madara da kwakwa har da Zuma aka sa a hurar. Nan da nan ta shanye ta dire kofin Zahra da ke sha a hankali ko rabi ba ta sha ba zungurin Zahra ta fara tana nuna mata cooler abincin, murmushi kawai ta saki ta tashi ta zubo mata cikin farin ciki ta karba musamman da ƙamshi ya daki hancinta na lafiyayyar jallop din taliya da ta sha hadin kayan lambu da namomi zuku-zuku, ta fara ci tana sauraron hirar Zahra da kakarta kan jarabawar da za su fara ce ta kammala karatun sakandire sai kuma fada mata da ta yi Haj Baturiya ta aiko idan ta dawo ta je tana neman ta.
Sai da Raliya ta kammala Zahra ta ja ta zuwa gidan Alh Umar da yaran gidan ke ce ma Baba Mai mota, ta cikin gidan kofar shiga na shi gidan take suna tura kofar idonsu ya yi tozali da mqkekiyar haraba da aka malale da enter lock daga gabas kuma rumfar Adana motoci ce sai ainahin ginin gidan wanda upstairs ne yana kallon rumfar adana motocin, can ginin gidan suka nufa Zahra da ke gaba ta tura kofar wata siririyar hanya suka taras da suka mike ta sa da su da wani tafkeken falo da suka samu matasa guda uku zaune dukkan su yaran Alh Umar ne su hudu ne na farkon na China yana karatu, na biyun Abakar ya buga kusa da shi yana duban Zahra ta isa ta zauna wasan ludo suke dukkan su suke jan ta da hira har ta so ta shiririce ganin Raliya na tsaye har lokacin tana kallon su cike da sha’awa don matasan na matukar burge ta, ta ce “Ina Haj? Abba ya nuna mata sama ta mike suka taka zuwa saman zaune suka same ta a shiryayyen falonta ta tare su da murmushi suka gaishe ta ta amsa tana tambayar Zahra saukin jikinta. Mai aikinta ta kira ta kawo musu fruit sai ta shiga ciki kaya na zamani dogayen riguna kala biyu da riga da skirt kala uku har da turare ta ce tsarabar Dubai don yar kasuwa ce, ta karba da matukar murna hajiyar har kamar ta fi ta murnar sanya farin ciki a zuciyar marainiyar yarinyar da Allah ya jarabta da ciwon Amosanin jini wato a turance (Sickle Cell Disease) kwala Kiran sallar magrib ya sa su mikewa suka fito ta get din gidan suka fita Raliya ta shiga gidan su Zahra ta shiga nasu.
A katon tsakar gidan nasu ta tarar da mahaifiyarta ta ce ” Sai yanzu? Labarin tashin da aka yi musu da wuri ta yi mata sai suka wuce gidan su Zahra. Ta wuce dakinta cikin dakuna uku da ke cikin gidan ciki da falo na innarta ne da da suke zaune tare da babanta kafin Allah ya yi mishi rasuwa bara sai dayan da innarta ke ajiye-ajiye kafin ta zama budurwa suka mayar da ita can.
Karamin gadon bono ne tsura a dakin sai shararren sumunti sai shirginta da bai wuce suturunta ba uniform ta fara tubewa sai ta daura zane zuwa kirji, ta fada gadon ta yi rub da ciki tana tunanin yadda za ta samu kudin da za ta biya ma kanta na zana jarabawar WAEC Allah ya sani tana matukar son ta samu ilmi mai zurfi don mijin nuna ma sa’a take so ta aura wanda za ta fantama a rayuwarta, ba za ta zama yar rakiyar mata zuwa duniya ba. Ta dade cikin neman hanyar da za ta bulle da ita ba ta samu inda wadannnan kudaden za su fito ba da za ta biya ma kanta kudin jarabawar. Shamsudden shi ne saurayin da ke masifar sonta innarta da tashi kuma sun zauna kan alkawarin hada su aure kasantuwar su kawaye. Sai dai yanzu shi dalibi ne a Jami’a, yana shekara ta hudu, ba shi da sana’a sai buga-buga duk da mahaifinsa ke dauke mishi dawainiyar karatun nashi a buga-bugar yake hidimar rayuwarsa har ita ma ya fincuno mata duk da ba burge ta abin da yake ba ta yake ba. Hakika tana son Shamsu don saurayi ne santalele dan kwalisa matsalar shi daya rashin masu gidan rana tunanin ta ya fada kan wani Alh da suka hadu a kafar sadar da zumunta ta Facebook yana kuma ta yi mata tayin haduwa tana zullewa yanzu kam ta shirya ma haduwar ta su don ba zai yuwu a yi WAEC ba ta ba. Ta mike a guje ta fita dakin sai dakin Innarta, ba ta bi ta kan Innar ba da ke ce mata tuwo na kitchen ta dauko wayar Innar sai da ta gyara kyauren da aka daure murfin wayar da ya riga ya saki sai ta bar dakin.
Maryam Litee