Ganin Hassan da ta yi a kwance a kan gado ya saka ɓacin rai ƙara lulluɓeta. Wato shi bacci ma yake bayan wannan masifar da ya kwaso musu. Wani tsaki ta buga tana saurin ƙarasawa inda yake kwancen. Hannunta ta saka ta ɗaka mishi duka a cinyarsa. Allah yasa zafin hannunta ya karya mishi ƙashinsa yanda zai buƙaci ɗori ta ga ta yi mata kishiya.
Hassan da tun shigowarta ya ji ta dan shi kam bai yi bacci mai daɗi ba kasancewar bata kusa da shi. Juye juye ya dinga yi karshe ma ya tashi ya dinga. . .