Skip to content
Part 2 of 18 in the Series Soyayya Da Rayuwa by Oum Suhaiba

Ganin Hassan da ta yi a kwance a kan gado ya saka ɓacin rai ƙara lulluɓeta. Wato shi bacci ma yake bayan wannan masifar da ya kwaso musu. Wani tsaki ta buga tana saurin ƙarasawa inda yake kwancen. Hannunta ta saka ta ɗaka mishi duka a cinyarsa. Allah yasa zafin hannunta ya karya mishi ƙashinsa yanda zai buƙaci ɗori ta ga ta yi mata kishiya.

Hassan da tun shigowarta ya ji ta dan shi kam bai yi bacci mai daɗi ba kasancewar bata kusa da shi. Juye juye ya dinga yi karshe ma ya tashi ya dinga jero salloli. Shi yasa baya son yin tafiya kwata kwata in dai ba da ita ba. Hajiya Mama ta yi faɗan ta gaji kan cewar baya son tafiya yana ma kanshi baƙin cikin ci gaba. Da ta san dalilinsa kila da son da take ma Safina ya koma tsana, fiye da wanda take yi ma Nabila.

Zumbur ya tashi zaune dan bai yi tunanin abunda zata yi mishi ba kenan. Hannu ya kai yana sosa wajen tare da bin ta da kallo. Kwata – kwata bai ji haushinta ba dan ya san a karon banza ba zata kai mishi wannan mugun dukan ba.

Waje ta samu ta zauna tana mai wani irin kallo da za’a fassara da na takaici.

“Tashi zaka yi mu yi magana wallahi.”

“Maganar me?”

“Maganar me? Ina jiya cewa ka yi zaka yi aure? Zaka yi min kishiya. To ban yarda ba. Ban ga wani dalili da zai sa ka yi min wata kishiya ba. Meye bana maka a gidan nan? Da me…”

“Babu”

Ya yi saurin katseta ya janyo hannunta…..
“Wannan maganar zamu yi ta anjima amma gaskiya bacci nake ji. Jiya fa ban yi bacci ba. Kin san bana iya bacci idan ban ji ni a jikinki ba”

Kici – kicin kwacewa take yi dan ita ba wasa ne ya kawota ba. Ba zata bari ya yaudareta ba haka kurum tana ji tana gani.

“Ashe ka kusa daina bacci. Ka san da haka kake zuwa wajen wata har zaka aureta sai…”

Cizon da ya kai mata a kunnena ya saka ta yin shiru ta saki kara

“Ke fa kin faye magana. Kawai ki bari mu yi bacci. Idan muka tashi zan miki duk wani bayani.”

Tana kokarin magana dan ita bata ga abunda zai sakata wani bacci ba bayan tarin matsalolin da take hangowa a gabanta ba. Ta ƙarfi da yaji ya sakata kwanciya duk da tuburewar da take yi. Ya saka hannunsa daya da kafa daya ya danneta yana cewa.

“Kin san idan ba bacci na yi ba abunda kike nema ba zaki samu ba. Hour biyu zaki ara min kawai.”

Yanayin yanda yake mata magana ya sakata yin shiru. Ta san duk abunda zata yi ba zai bata amsa ba sai dai ranta ya fi haka ɓaci. Ta yi ƙwafa ta saki jikinta, ai dai zai tashi kuma dole ya mata bayani.

Kwankwasa kofa ne ya tashe su daga baccin da suke yi. Babu tantama sun san yaran ne suka tashi suka zo neman su. Safina ta matsa daga kusa da Hassan da ya riga ya matsa mata. Bata bari yaran sun shigo ba ta ja su suka yi falo.

Iman ta ce mata Suwaiba ta dafa musu indomie sun ci harda Ihsan. Ta so ta yi musu wanka ta shirya su amma ranta baya mata dadi. Dan haka ta saka Suwaibar ta musu, kaya kawai ta fito musu da shi ita taje ta watsa ruwa.

Yau bata ɓata lokaci wajen yin kwaliyya ba dan zuciyarta na gaya mata hakan bashi da amfani. Doguwar riga mara nauyi ta saka ta koma ɗakin Hassan. Ya yi wanka shi ma ya saka farar shaddarsa sai kamshin turare yake yi.

“Ina zaka je Hassan?”

Abunda ya fara zuwar mata zuciya shi ne zai tafi wajen wacca yace zai aura ne. Ta manta cewar shi ma’abocin kwaliyya ne a ko da yaushe.

“Abinci zaki bani, yunwa nake ji.”

“Gaskiya na gaji da wannan kwane – kwanen da kake min. Bacci ne ka ce sai ka yi ka tashi. Ka tashi kuma kana neman abinci.”

Bai ce mata komai ba ya raɓa ta ya fita. Bin shi a baya ta yi ranta yana ƙara ɓaci. Yau sai dai a yi abunda za’a yi amma ba zai fita ya bar gidannan ba tare da ya amsa mata tarin tambayoyin da ke zuciyarta ba. Ganin ya doshi teburin cin abinci ya sakata sararawa. Ta san nufinsa ta bashi abinci. Wata durowa ce saitin teburin cin abinci wanda ya zo da madubi ta buɗe ta ɗauko kofin tangaran sannan ta laluba cokali ta ajiye mai a gabanshi. Ta koma teburin ta dauko kwalabe guda biyu wanda ɗaya madara aka ajiye a ciki, ɗayan kuma sikari.

Ganin abunda take sai ya tsaya yana binta da kallo. Ganin ta nufi dispenser ta taro ruwan zafi sai ya yi tunanin shayi zata bashi kafin ta dora mai abunda zai ci. Ga mamakinsa, sai ya ga ta dauko golden morn ta ajiye mishi.

“Haba Safin Hassan. Dan Allah ki bani abinci. Wannan wani irin horo zaki min?”

Muryarsa kamar mai shirin kuka yake magana. Ta sani sarai baya son abubuwan nan. Ko cornflakes ba sha yake ba. Balle golden morn da yake mai kamar an barbada gari cikin madara.

“Ni fa Hassan gaskiya bani da lokacin ɓatawa. Kawai ka sha nima shi zan sha. Idan ba haka ba kuma Suwaiba ta dafa maka indomie kai ma.”

Harara ya watsa mata saboda sarai ta san baya cin abincin masu aiki. Kofin ya jawo ya haɗa ya dinga turawa yana ji kamar zai yi amai. Yana gamawa ya je ya dauko chewing gum kar ya yi aman bayan ya samu nasarar abin da ya sha din ya kwanta.

Ɗaki suka koma suka zauna suna fuskantar juna.

“Wacece?”

Safina ta tambayeshi babu alamun wasa a fuskarta.

“Baki san ta ba. Sunanta Afrah. A nan Court Road su ke da zama.”

Jin sunan yarinyar, da unguwar da take sai ta ji duk wasu tarin tambayoyi da take da su sun ɓace mata. Zuciyarta ta kama lugude bisa allon kirjinta. Wani sanyi ne yake ratsa ilahirin jikinta tana ji kamar zazzabi zai rufeta. Ganin bata kara yi masa wata tambayar ba ya saka shi mikewa tare da ce mata,

“Zan fita gaida Alhaji. Sai na dawo.”

Abu ɗaya zuciyarta ke gaya mata. Ƙarya yake yi! Court road zai tafi wajen Afrah! Nan ta ji hawayen baƙin ciki sun wanke mata fuska.

*****

Tana bude idanunta misalin ƙarfe karfe huɗu da rabi na asubahi, abun da ya faru daren jiya ya faɗo mata. Sai ta shiga tunanin shin gaske ne ko kuma mafarki ta yi? A wannan tunanin da take yi ne ta kunna ƴar ƙaramar fitilar gefen gado wanda haskenta ba mai wadata bace amma yana taimakawa wajen ɗauke duhun ɗakin.

Kwanciya ta gyara ma Hajja sannan ta tashi ta shiga bayan gida. Hussaini ya so a barta ta dinga kwana a ɗakinta ita kaɗai amma zuciyarta ta kasa aminta. Ranar da ta ƙoƙarta barinta a ɗaki ta kwana ita kaɗai, juyi ta dinga yi a kan gadon bacci ya gagara ɗaukarta. Dole ta je ta dauko ƴar ta wacca ke ta baccinta ta rungume a kirjinta.

Nafila ta fito ta yi,  tana mai addu’ar Allah ya sa mafarki ne ta yi. Bata san dalilin da ya saka take fatan hakan mafaraki bane. Ta san ba soyayya suke bugswa ita da Hussaini ba balle ta yi tunanin zai zauna da ita ɗaya. Ba zata ce tunanin bai taɓa gitta mata a kai ba. Ta kan ɓata lokaci tana wannan tunanin. Lokacin kafin ta samu cikin Hajja.

Bayan ta idar da sallar asuba ta tashi ta hau shirin girkin ranar kamar yanda ta saba. Bata da mai aiki saboda wasu dalilai na Hussain da bata sani ba saboda bai so ta sani ɗin ba. Da farko bai dameta ba amma bayan ta haifi Hajja ta zo mishi da zancen, amsa daya ya bata.

“Ban yarda ba”

Ta so ta tambaye shi dalili amma babu fuska. Sau da yawa ta kan zauna ta yi kuka idan Hajja ta so rigima sannan aikin gidan ya kacame mata. Bata iya raino ba. Bata saba da yara ba, ita kaɗai iyayenta suka haifa sannan Daddy baya barinta yawon gidan ƴan uwa. Tana dai zuwa ta wuni. Amma bata taba zuwa ko’ina ta kwana ba duk yawan ƴan uwansu da ke birnin Kano. Sukan je biki wani garin ko suna ko gaisuwar mutuwa amma iyakacinsu Kwana ɗaya ita da Mummy.

“Kun dai taho ko?”

Daddy zai dinga waya yana tambaya washegarin ranar da sukai tafiyar. Idan suka ce basu taho ba kuwa ya dinga doka waya a kan su yi da jiki su taho. Idan sun taho din kuwa, bayan mintuna ashirin- ashirin wayar Mumny zata dinga tsuwwa. Idan bata yi ba kuma, to tabbas sun shiga inda babu service ne na waya Daddyn ya kasa samunsu.

Allah kaɗai ya san iya lokacin da yake ɗauka a tasha yana jiransu dan duk tafiyar da zasu yi, sai dai su tarar da shi a tasha ya faka mota yana jiransu.

“Muntari na Sadiya.”

Kakarta da ake kira da Maman Tudun, kasancewarta gidanta a Tudun Maliki yake, haka take tsokanar ɗan nata tana dariya. Ta kuma ƙara musu da addu’o’in zaman lafiya da kwanciyar hankali haɗi da ƙarin soyayya.

Da yawan mutane kuma sukan ce Mummy ta basu sirrin. Sirrin yanda ta kame Daddy. Ko ta basu laƙani. Ko ta haɗa su da malaminta.

Abu mai sauƙi ta yi niyyar ɗorawa yau dan haka ta hau firar dankali. A nan ta yi tunanin me zasu ci da rana da kuma dare. Tana gamawa ta duba abubuwan da take da buƙata idan akwai su ko babu su. Sai a lokacin ne ta ji dawowar Hussaini daga masallaci. Kamar yanda ya saba, bai leƙo inda take ba ya wuce ɗaki yai kwanciyarsa. Sai ta saki ajiyar zuciya. Tabbas! Mafarki ta ke. Nan da nan ta ji ta sami ƙarin ƙarfin jiki har ta karasa girkin safe ta saka a flask ta ajiye. Nama ta ɗora na abincin rana ta wuce ɗaki dan yin wanka.

Ta fito daga wankan ne wayarta ta yi tsuwa. Ko bata duba ba, ta san Mummy ce ko Daddy. Ƙara na musamman ta saka musu a wayarta. Ta ɗauko mai ta zauna sannan ta amsa wayar.

“Mummy ina Kwana?”

“Lafiya kalau Alhamdulillah. Kin tashi lafiya? Ya ƙawalli?”

“Alhamdulillah Mummy. Ƙawallinki bacci take yi. Ina Daddy?”

“Yanzunnan ya fita kofar gida ana sallama da shi. Yaushe zaki shigo din? Ina son leƙawa asibiti dubiya kar ki zo bana nan.”

Take wani ciwon kai ya dirar ma Nabila. A cikin mafarkinta ta tuna ta kira Mummy ta ce zata zo. Kenan gaske ne Hussaini auren zai yi ba mafarki ba? To ko dai wasa yake mata? Amma me yasa zai mata irin wasan nan. Muryar Mummy ce ta katse mata tunanin da take shirin faɗawa.

“Ko ya hana ki zuwa ne? Idan ya hana ki, ki yi hakuri ki zauna. Kar ki ce sai kin taho dole – dole yau. Sai ki lallaba shi wataran ya bar ki kin ji?”

“Bai hana ba Mummy. Ina shirya Hajja zamu taho In shaa Allah.”

Suka yi sallama Nabila ta bi gado ta kwanta. Sunan Allah kawai take kira. Jikinta har rawa yake ta miƙe ta fita daga dakin ta fada na Hussaini. Yana zaune kan gado yana danna laptop.Ta san lissafi yake yi. Kai tsaye ta tambayeshi abunda ya kawota.

“Jiya ka gaya min zaka ƙara aure?”

Kai ya ɗaga mata tare da ce mata.

“Eh”

“Da gaske kake yi ko wasa ne?”

“Da gaske ne Nabila. Saboda…”

Kaɗa kan da tayi ta fice ne ya saka shi yin shiru. Shi kanshi bai san abunda zai ce mata ba da ta tsaya ɗin. Aikin ma sai ya ji bazai iya ƙarasawa ba dan haka ya shiga ya watsa ma kanshi ruwan ɗumi. Text ɗin da ya shigo wayarsa ya saka shi daukar wayar ya duba. Murmushi ya saki tare da girgiza kan shi. Bai bada amsa ba wanda hakan ɗabi’arsa ce amma ya ji daɗin saƙon.

Bai san tsawon lokacin da aka ɗiba ba daga fitar Nabila da ƙwanƙwasa ƙofar Hajja. Sunanshi da take kira ya saka shi tashi ya buɗe. Tana tsaye a korido sanye da doguwar rigarta ta atamfa.

“Mimi ta ce ka zo.”

Sai da ya yi ɗan jim. Bai taɓa jin Nabila ta aika a kira shi ba. Ko dai bata da lafiya ne? Cikin sauri ya wuce Hajja yana leƙa ɗakin Nabila, amma bata nan. Ganin Hajja ta zarce palo ya saka shi bin ta. Nabilar ya gani a tsaye tana lalube cikin jakarta. Tana ɗagowa ta gan shi ta ce,

“Zan je gida.”

Bai sani ba ko yanda ta yi maganar a dake ne ko kuma jin yanda bata neman umarninsa ko kuma shiryawar da ta yi ba tana shirin fita bane amma sai ya ɗaga mata kai. A cikin shekaru bakwai, yau kawai ya ga wasu abubuwa a tattare da ita wanda bai taɓa gani ba.

Ta shigo dakinsa dazu ba tare da sallama. Duk halin da Nabila take ciki, bata taɓa ƙin yin sallama ba. Bata gaishe shi ba yau, shi ma bata taɓa ƙin yin sa ba. Sannan a yau ne bata nemi izininsa ba zata yi abu. Izinin ma a kan fita.

“Da Hajja zaki?”

Bai san daga inda tambayar ta fito ba, kawai ya san ya ga ta rike hannun Hajja sun nufi ƙofa. Bai yi aune ba ya ga ta saki hannun Hajja ta ci gaba da tafiya.

“A’a ki tafi da ita.”

Ya yi saurin faɗa. Ya ga ta ɗan juya ta kama hannun Hajja sai ya ce,

“Ku jira mana sai na kai ku”
Juyowa ta yi ta kalle shi. Kallon da ya san cewa da zata bude bakinta, maganar da zata fito ba zata yi mishi daɗi ba. Ya san ma’anar kallon, kallon da yake nufin bata buƙata. Kallon da yake nufin ta saba tafiya babu shi. Kallon da yake nufin kar ka fara abunda ba zaka iya ba.

Yana kallo ta buɗe ƙofa ta fice riƙe da Hannun Hajja. Yana ji kamar ya dace shi ya kai su. Duk da bai san yanda take ji ba, amma yana tunanin zuciyarta a cunkushe take. Amma yana jin tsoron kallon da ta yi mishi ɗazu. Take ya ji tsigar jikinshi ya tashi ba tare da wani dalili ba.

*****
Ina godiya gare ku da kuka ara min kokacinku domin karanta wannan labarin nawa. Na gode.

Ku taimaka min ta hanyar sharing, liking da comment. Ina tsananin buƙatar hakan. Na gode, na gode.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Soyayya Da Rayuwa 1Soyayya Da Rayuwa 3 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.