Ƙwanƙwasa ƙofar da ake yi ne da kwaɗa sallama ya sanya Nabila ɗauko hijabi ta saka. Daga bakin ƙofa take amsa ta buɗe ta ga mai gadi ne.
"Baban Hajja ne ya bayar da saƙo a kai gida Alhaji Ghali. To naje ina ta bugawa babi wanda ya buɗe shi ne na dawo mishi da shi."
Ta karɓa gami da yi mishi godiya ta koma ciki. Kusa da tv ta ajiye farin ambulan ɗin ta ci gaba da harkokin gabanta. Wani abun ya dinga ce mata ya duba wannan ambulan ɗin. Ya yi mata. . .