Skip to content
Part 7 of 18 in the Series Soyayya Da Rayuwa by Oum Suhaiba

Ƙwanƙwasa ƙofar da ake yi ne da kwaɗa sallama ya sanya Nabila ɗauko hijabi ta saka. Daga bakin ƙofa take amsa ta buɗe ta ga mai gadi ne.

“Baban Hajja ne ya bayar da saƙo a kai gida Alhaji Ghali. To naje ina ta bugawa babi wanda ya buɗe shi ne na dawo mishi da shi.”

Ta karɓa gami da yi mishi godiya ta koma ciki. Kusa da tv ta ajiye farin ambulan ɗin ta ci gaba da harkokin gabanta. Wani abun ya dinga ce mata ya duba wannan ambulan ɗin. Ya yi mata kama da ambulan ɗin da ake saka katin ɗaurin aure. Ko na ɗaurin auren su Hussaini ne?

Ta san wannan watan da ake ciki za’a yi auren. Bata son tunanin auren kwata kwata. Abunda ma zai kusantata da ganin shirin da ake yi bata so. Shi yasa rabonta da gidan tun ranar da Alhaji ya saka a kirawo ta.

Har Hussaini ya fita sai ta gan shi ya dawo. Wai Alhaji ne yake nemansu. Bata yi tunanin komai ba, sai dai ta san cewar kila zai yi magana kan rashin shigowarta ne. Ta ga gidan ne an yi mishi sabon penti sannan ana ta hidindimu a ɓangaren Hajiya Mama sai kace bikin fari ake yi. Abunda ya saka ta daina shiga ma shi ne wani murmushi da Hajiya Mama ke sakar mata idan sun haɗu a maimakon rai da ta saba haɗewa.

A falon Alhaji suka samu Alhaji da Hajiya Mama, ga akwatuna nan a tsakiyar falon har seti biyu ƴan yayi. Ta gaishesu kamar yanda suka saba har Alhaji na tsokanarta.

“Nabila wani akwati ne ya fi miki kyau a waɗannan? Ki zaɓa”

“Ta zaɓa?”

Ta ji muryar Hajiya Mama a mamakance. Ita dai bata ɗago ba sai murmushin da take yi.

“Je ki kira min Ummanku ta zo ta taya ki zaɓe ta fi sanin ka kaya”

Babu musu ta miƙe ta fita dan kiran Umman. Ta gaya mata yanda suka yi da Alhaji.

“Zagewa zaki yi ki zaɓa. Wani kalan akwati ne yai miki?”

“Milk ɗin”

Sarai Aunty ta san kayan dan amaryar Hussaini aka yi shi tunda ɗazu Hajiya Mama ta kawo kayan take faɗa har Alhaji ya tambayi kayan Nabila na faɗar kishiya ta ce tana nan ana shiri.

Alhaji ya ba Umma umarnin taya Nabila zaɓar kayan yana jadadda a raba shi gida biyu. Babu wani tantama, mugun ɓacin rai ne a shimfiɗe a fuskar Hajiya Mama ta miƙe fuu ta fice.

Kamar waɗanda suk shiga shago haka suka zauna Umma na taya ta zaɓen kaya. Ita ma tana taɓa kasuwanci tunda tana taimakawa wajen zaɓen kayan da su Alhajin ke kawowa. Hussaini kuwa yana nan kamar an dasa shi saboda fitar Nabila sai da ya zage shi tas kamar zogale.

Duk da Hajiya Mama ta gaya ma Alhaji fiye da rabin kayan ciki kuɗinta ta saka ta saya yace shi wannan duk bai dame shi ba. Adalci kawai yake so a yi.

Suka gama zaɓen kayan sakawa aka cika ma Nabila akwatin da ta zaɓa Alhaji ya ce ya kai musu ɗakin Umma a ajiye a can. Nufinshi idan an kai lefen amaren, sai a kai ma uwayen gida nasu.

Ta ɗauki ambulan ɗin ta ɗan jujjuya a hannu kafin ta buɗe, gabanta na dukan uku uku.

                      Alhaji Mai Saƙa

                              Da Na

                Dr Sulaiman Muhammad

                          Tare da na

                 Alhaji Salihu Haruna

                 Na farin cikin gayyatar
                      ________________

          Zuwa Ɗaurin Auren Ƴaƴansu


         Abubakar Mai Saƙa (Hassan)
       
                                Da

                       Afra Sulaiman


             Umar Mai Saƙa (Hussain)

                               Da

                Lawisa Salihu Haruna

Wanda za’a ɗaura shi….

Sunan Lawisa Salihu Haruna ne ya dinga yi mata ƙararrawa a cikin kai ya hana ta karanta sauran abunda aka buga a kan katin. Lawisa Salisu Haruna suna ne da ta sani. Amma wacca ta sani da wannan sunan…. Kai inaaaaa ba zai yiwu ba a ce ma hakn zai faru ba.

A dai dai wannan lokacin Hussaini ya fito daga ɗaki. Ganin ambulan a hsnnunta ya saka shi tsayawa yana son tantance idan abunda ke hannunta yake tunani.

“Lawisa. Wacce Lawisar?”

Kasa buɗe baki ya yi ya bata amsa. Bai san abunda zai mace a yanzu ba. Ba haka ya shirya ta sani ba. A tsarinsa sai ranar da aka ɗaura auren zai zo ya zaunar da ita, ya yi sharar fage da kalmomin ƙaddara da rabo. Zai gaya mata daɗaɗan kalamai ya kuma bata haƙuri sannan ya gaya mata wacca ya aura. Ba haka ba.

Ba sai ya buɗe baki ya gaya mata ba. Shirun da ya yi ma ya isheta amsar tambayarta. Ji ta yi iskar falon ya yi mata kaɗan dan haka ta juya ta fita.

“Nabila”

Hussaini ya kirata yana bin bayanta amma ta wuce gate. Kiran da yake mata ya saka babu abunda take gani sai shi da Lawisa a cikin idanunta. Do take ya ƙyaleta ko zata daina hango Lawisa cikin idanunta.

Ganin ta fita daga gidan ya leƙa ya ga ta nufi hanyar titi ya yi saurin komawa ya fito da mota, ko gate ɗin bai rufe ba sai maigadinsu Alhaji ya yi ma sigina kan ya rufe masa.

“Nabila shigo na kai ki inda zaki je”

Abunda ya fada kenan yana yin slow a kusa da ita. Ya san ba zata wuce gidansu ba. Bata kula shi ba ta ci gaba da tafiya da saurinta. Magana yake yi mata yana magiya kan ta shiga motar amma ta yi biris da shi. A haka suka karasa kan babban titi.

Ganin ba ƙyaleta zai yi ba ya sakata tsallaka babban titin Zaria Road tunda ta san dolensa sai ya je ya nemi waje ya juyo. Ai kuwa hakan aka yi. Ya yi saurin saka motarsa kan titin yana kallonta ta gilashi.

Wani wawan birki ya ja dalilin ganin wni ɗan acaɓa ya kusan kwasheta. Ya ga ta ci gaba da tafiya bata kula shi ba. Shi kan shi vai saurari mai motar da yake sirfa mishi zagi ba. Wuta ya ba motarsa saboda ya san sai ya tafi can wajen fly over zai samu juyowa.

Ko da ya ƙarso, sai yaga babu ita babu alamunta. Gidansu ya wuce kai tsaye dan ya san tan wuce. Amma sai ya samu ƙaton kwaɗo a bakin gate ɗin. Nan take zufa ya fara keto mishi. Hannu ya saka a gaban aljihunsa don ɗauko waya, sai a lokacin ya lura ashe singlet ce a jikinsa. Bai ga ta komawa gida ba har sai Nabila ta iso.

*****
“Eh an kawo min, yanda zan yi amfani da shi zaki gaya min.”

Safina kenan tana waya da Hajiya Bilki bayan an kawo mata wani saƙo. Rubutu ne a ƴar ƙaramar jarka wanda zata sha. Na kariya ne da kuma kwarjini. Ta riga da ta bayar da kudin sadaka sai kuma na sauka.

“Ba’a zama haka.”

Cewar Hajiya Bilki a wata waya da suka yi.

“Sauka zaki bayar a dinga miki kafin a yi auren nan. Idan Allah ya taimaka zaki iya ji an fasa.”

Ba dan karatun jarabawa da take yi ba, da ita zata zauna ta yi saukan da kan ta. Lambar bankinta Hajiya Bilki ta aiko ita kuma ta samu ta tura dubu huɗu ta maida hankalinta kan karatu.

Sauka uku akai mata kafin ta zana jarabawar JAMB ɗin. Da ƙyar ta yi bacci a daren ranar saboda zulumi. Yara gidansu ta kaisu kwana biyu kafin nan dan bata son abunda zai saka Hajiya Mama ta dinga doko mata kira.

“Yanzu ke Safina duk faman da nai da ke dan ki koma makaranta kika ki, sai dan wacca za’a auro miki zaki koma?”

Dariya mahaifiyarta ta yi tana ƙara jinjina ma ‘shirme’ irin na Safina. Addu’ar sa’a kawai ta yi tana girgiza kai. Ita dai bata ga wani dalili da wata zata sakata abunda bata so bata kuma yi niyya ba. Bata manta ba kafin gama sakandiren Safina, bata da aiki sai waƙe waƙen da ke nuna son aurenta a lokacin. Bata manta wata waƙa da ta yi mijinta yace gwanda a haɗa a yi auren da na Nabila.

Na yi primary na ƙare
Na yi Secondary na ƙare
Baba ya ce min my daughter
Ni ma na ce mishi my daddy
Aure kike so ko karatu
Baba one Baba two Baba wise
Baba wayo kake ka samu Doctor
Baba ko baka so ka samu jika

Suna ɗaki suka jiyota tana waƙar, ita ta san da gayya take waƙe waƙen nata. Kunya duk ta lulluɓeta ta kasa kallon mijin nata. Shi kuwa ya yi dariya ya ce tunda ta nuna tana so ai matan.

“Ni fa Umma secondary din ma dan ba yanda na iya nake yinshi. Amma bana son karatun. Idan na ce ma zan iya jami’ar ba ci zan yi ba.”

Abunda ta gaya mata kenan da ta ce mata ta bari ko shekara ta farko ne ta gama. Sai kawai ta jinjina kai ta ƙyaleta.

Suna sallar asuba ta yi wanka ta haɗa musu abunda zasu ci ta ce Hassan ya haƙura da bacci ya kaita center ɗinta. Nan kwakwaci ne center ɗin wanda tun kafin ranar ya je ya nemi wajen dan kar sai ranar a zo ana diri diri. Haka ya kaita ya ajiye ya koma gida.

Da samako ya fito kuwa murna kamar ta yi yaya. Ta ƙanƙame Hassan wanda shi ma murnar yake taya ta. Mahaifiyarta ta kira take gaya ma, ta taya ta murna ita ma sannan ta kira mijin mahaifiyarta.

“Tunda kin nutsu, lokaci zaki samu mu je ki samu Malam ya baki duk wani taimako da zai baki.”

Da fari ta ji tsoro saboda ita harkar malamai bata wani son ta. Ganin Hajiya Bilki ta dage sai ta saka rana suka tafi can Ƴar Gaya inda Malamin yake. Ganin ya bata addu’o’i wanda yawancinsu duk sunayen Allah ne sai ta ji hankalinta ya kwanta da shi. Da ma da ta lura Malamin shirka ne, da har Hajiya Bilkin ta rabu da ita har abada.

Wata ranar talata ce, ta je gida gaida mijin Mahaifiyarta bai ji daɗi. Kafin ta tafi ta biya ta saya mai ruwa katan uku a cikin kuɗin da Hassan ya bata. Ta je tana jadadda mishi kan ya haƙura da ruwan leda tunda typhoid ce take damunshi. Ta ɓoye mishi inda ta san ƙannenta ba zasu gani ba balle a mai wasa da shi tunda shi ruwan roba farin jini ne da shi.

A hanyarta ta komawa, kamar wasa ta gano wata mota kamar ta Hassan, leƙawar da zata yi kuwa sai ta ga ashe shi ɗin. Amma akwai wata a motar. Kallo ɗaya ta gane figalaliyyar yarinyar da yake shirin aura ne. Wato dan zai ɗauki wata shi ne zai ce mata ba zai samu zuwa ya ɗaukota daga gida ba.

“Bi min wancan motar”

Ta gaya ma mai adaidaita sahu zuciyarta na saƙa mata abubuwan da ya kamata ta yi. Baƙin ciki na ƙara lulluɓeta da take ganin yanda suke hira suna dariya. Zuciyarta kamar ta fito ta baki dan baƙin ciki.

A wani babban shago suka tsaya suka shiga. A nan waje suka tsaya tana jiran su fitowarsu. Mintuna kusan arba’in suka shuɗe mai adaidaita ya fara nuna gajen haƙuri

“Dalla Malam ba kyauta nace zaka jira ni ba kuɗi zan baka balle kai min rashin kunya.”

Da yake ɗan zafin kai ne sai yace ta bashi kuɗinsa kawai shi ya gaji baya aikin jira. Rai a ɓace ta ɗauko kuɗi yan dubu guda uku ta miƙa mishi.

“Ni ba matsiyaciya bace dan ka ji. Da mutuncina a kan wannan banzar adaidaitar taka zaka ɓata min rai.”

Bai kai ga bata amsa ba ta ga fitowar Hassan hannaye cike da leda ita kuma ƴar afiruwar wata ƙaramar leda ce a hannunta sai wata munafukar jaka. Nan idanun Safina suka rufe ta sakar ma mai adaidaita kuɗin ta yi motar Hassan.

Bata yi aune ba, Afra sai ji tayi kunatunta na mata zugi. Kafin ta farfaɗo ta ji wani duka a kafaɗarta.

“Shegiya karuwar banza bai min mazajen mutane.”

Abunda ta ji matar na faɗa, ta gane matar Hassan ce.

“Ke Safina meye haka?”

Hassan ɗin ya tambaya hankalinsa ya kai ƙololuwar tashi ganin Safina na kai ma Afra duka a kai. Da sauri ya janye Safina da ke ta masifa tana zagin Afra.

Tsawar da ya daka mata ne ya sakata dakatawa. Hassan bai taɓa ɗaga mata murya ba, kullum cikin lallashi duk laifin da zata yi kuwa.

“Wuce ki tafi gida”

Tana shirin magana ne Afra ta girgiza kai tana murmushi.

“A’a Boo ku tafi gida, I’ll find my way. Zamu yi waya”
Cikin ɓacin rai ya shige motar yana tayarwa. Ganin zai tafi ya barta Safina ta buɗe ta shiga. Ko gama rufe ƙofar batai ba ya fizgi motar kamar mai shirin tashi sama.

“Fita!”

Ya ce da ita suna isowa ƙofar gida. Duk wani koke koke da take yi a moyar banza ya yi mata dan ji yake kamar ya rufe ta da duka.

“Yanzu tsakani da…”

“Nace ki fitar min daga mota. Safina ran ki zai yi mummunan ɓaci idan baki fita ba this instant”

Ta saka hannu ta ɓalle murfin ƙofa

“Toh ina zaka?”

“Wajen wacca kika zubar ma da kan ki mutunci a gabanta. Ban san baki da hankali ba sai yau.”

“Ni kake ce ma mahaukaciya Hassan?”

“An faɗa ɗin. Dalla fita”

A tsakar gida ta kira Hajiya Bilki ta jira isowarta. Daga nan gidan Malam suka wuce aka duba mata lamarin.

*****
Kada ku manta, like, share and comment

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Soyayya Da Rayuwa 6Soyayya Da Rayuwa 8 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.