Skip to content
Part 2 of 9 in the Series Soyayyar Da Na Yi by Habiba Maina

Haka nayi jugum, na minti goma. Ina ta tunanin yaya zanyi? Ganin wannan saurayin ya matsawa rayuwata, gashi sam bana son abunda zai hadɗa ni da samari.

ina cikin haka, sai mafita ta zo min cikin tunani na cewa babu wani ɗan adam ɗinda ya isa yayi maka abunda Allah bai yi maka ba. saboda haka, nayi shawarar in amince mishi ya kaini gida kamar yadda ya bukata. Amma sai in lauyance mishi.

Akwai wata lambu a unguwar mu mai shigen gida. idan ba shiga kayi ba, to bazaka taɓa sanin lambu ce ba. to a nan zai sauke ni, sai ince nan ne gidan mu.

Shawarar nan ya faranta min matuka naji kamar inyi tsalle da wannan kyakkyawan tunani nawa.

Da murna cikin fara’a na furta masa,

“Na amince ka kai ni.” Cikin wasa na ƙara da “ɗan anaci tunda ka nace muje ka kaini.”

Yayi mamaki matuƙa. yace,

“Gaskiya na kusa na zauce. ganin yarda kika cije amma yanzu cikin bazata kin tashe ni, tabbas ba a fidda rai da samu.”

Nan kuwa sai ya buɗe min kofar mota na shiga sai lallami na yake kamar gimbiya.

haka nayi ta masa kwatantce muna tafiya…! Mun shafe mintuna muna tafiya amma sai kallo na yake kamar zoben zinarinda aka samo, bayan ɓacewa…! shekara da shekaru.

Cikin soyayya mara misaltawa da kuma tausayi sannan kuma, naga mamaki cikin kallon nasa. amma duk da haka, bai burge ni ba.

Nace da shi,

“Don Allah kayi tuƙinnan cikin natsuwa karka jefar da mu.”

sai yayi wata murmushi cikin kyakkyawar fuskarsa mai burge wa nima sai murmushin nayi masa na ce a zuciya ta,

“Ai in’kasan wata baka san wata ba.”

*****

Nan da nan kuwa sai muka iso unguwarmu sai na nuna masa kofar lambun nace masa, ga kofar gidan mu.

sai ya gode wa Allah cikin harshen larabci Allhamdulillah. ya tsaya da motar cikin hanzari ya fita ya buɗe min kofar motar na sauƙa.

*****

“Wanda yasan darajar ɗan Adam baya bari ƙwallar sa ta zubo ƙasa. yana iya ƙoƙarin sa wajen ganin hatta gurgu yayi tafiya.

haka kuwa yana iya ƙoƙarin sa wajen fitowa da mutane daga dajin halaka. amma fa, hakan baya hana idan aka farmaƙe su a hanya, sugudu su barshi. kasan mai yasa?”

Sai yace “a’a.”…

“saboda gudun mutuwa ita kuma mutuwa dole ce kowa sai ya mutu amma da lafiyar ka kuma da saninka bazaka bari a kashe ka ba matuƙar kana da hanyar gudu. amma idan ka tsaya aka kashe ka, to kai ka kashe kanka”.

“Na gode da ƙaramci” Sai na tsaya da faɗin haka. Sai yayi ajiyar zuciya.

“Kina da tarun maganganu masu ruɗani suna sa dogon tunani, kina da fasaha matuƙa. zama da ke kuwa,na ta matuƙar amfani”.

Ya faɗa min haka tare da cewa,

“Hankali na ya kwanta da ganin gidan ku yanzu ki shiga ciki kada hankalin mutanen gida ya tashi. zan koma amma zan sake dawowa, saboda mu gaisa. ina fatan hakan ba zai jawo matsala ba?”

Nace “a’a….! da wuri. babu matsala kuma idan ka zo ka aiko yaro kace a ƙirawo Walida”. na faɗa masa haka duk don mu rabu.”

sai yace,

“Na gode”.

cikin murmushi muka rabu tamkar wasu masoya. take na shiga lambun na laɓe. ina leƙen sa ta ɗan ƙaramin ramin da ke jikin ƙyauren lambun.

*****

Ina kallon sa yana tsaye, sai hawaye ne nagani suke zubo masa. da wuri kuwa, ya share hawayen,nasa ya juya ya shiga motar sa ya tafi.

Nan take na fice a lambun na shige gidan mu da gudu. domin tsakanin gidan mu da lambun, ba nisa. nayi ajiyar zuciya tare da faɗin,

” Allhamdulillah…! Gaskiya na auna arziki, Masha Allah! Da wannan dabara tawa, daga yanzu dai, na rabu da ɗan anacinnan.”

Nayi murna matuƙa, saboda nayi dabarar da duk yarda zaiyi bazai taɓa samu na ba. sai na shiga ciki. shigar da zanyi sai na tarar da mama hankalinta tashe, tana ta danne-dannen, waya. da alama dai ta kira wayata ne a kashe. sai nayi sallama ta amsa. ta ɗago kai,

“Ya…Salam! Mamma…! Ina kika tsaya ne haka? kinsa duk hankali na ya tashi. duk da dai nasan baki fita a gida da wuri ba, amma kin kai lokacin da yakamata ace kina gida. ina kika tsaya?”

Naso na fada mata gaskiyar abunda ya faru. amma sai nace, ta’yaya zan tonawa kaina asiri. tunda duk tunanin mama aljanu ne suka hana ni aure, kuma su ke kore min samari .

haka yasa ta dage min da maganunnukan aljanu. yanzu idan na faɗa mata saurayi ne ya tare ni, ai na tonawa kaina asiri.”

Sai tace,

“Dake nake kinyi shuru kuma wayar kima bata shiga?”

“Ai wayar ce ta mutu babu caji kuma da naje (Islamic chemist)dinma, shamsun baya nan. shine na jira shi. bayan yazo kuma, sai abun hawa yayi min wahala. shiyasa na daɗe.”

mama tayi ajiyar zuciya tace,

“Kinga kuwa, nima bani da lambar shamsun da na ƙira shi.”

“eh cikin tsarguwa nace, nima bani da shi.” Saboda karta fahimci ina da lambar’sa ta ƙarɓa. na bata amsa.

“ganin yamma tayi baki zo ba… na kammala duka aiki. yanzu ki shiga ciki kije ki huta.”

nace, “to nagode mama.”
Sai tayi murmushi na nufi daki na.

“Nace ba…?” Inji -mama. sai na dakata.

“waɗanne maganunnuka ne shamsu ya haɗa miki?”

sai na bata amsa,

“tudamirul jinin ne mama da garin khaltit da kuma man sa. kuma ya faɗa min yarda zanyi amfani da su.”

“Masha Allah toh Ki dage da amfani da su , karkiyi wasa kinji.”

nace, “to mama.”

tace, “shikenan kije.” Sai na wuce ɗaki na.

*****

Ina shiga sai naji kiran sallar magariba.

“Wai…! Ji har na kai magariba? Ai kuwa sai na tuna Shamsu ya ce min magariba na yi inyi hayakin tudamirul jinni.

Bana kin amfani da ita duk da’ma ba abunda ke damu na. amma shi maganin, waraka ne ga wanda ke da ita. kuma kariya ne ga wanda bashi da ita.

sai nace, Bara in yi sallah tu’kunna. ai ban ɓata lokaci ba.
idar da Sallah da nayi, sai naje (backyard) bayan Daki, na. nayi wankan maganin tudamirul jinni. kamar yadda shamsu ya faɗa min.

Ba’a wanka da ita a ban ɗaki kuma akan kwalinta ma haka ne. bayan nayi wankan.sai naje na karɓi garwashi a gurin mama nazo nayi hayakin.

to Allhamdulillah…! mai ya rage min? saura insha garin khaltitt a shayi sannan ina shafe manta a jiki na. kai har idan zan fita ma, nakan shafata a jiki na.

amma sai nace wannan Sai in Zan kwanta bayan na hau gado na.domin in huta sai nayi nisa wajen tunanin haɗuwa na da wannan saurayin.

“Gashi nayi duk wasu dabaru na ganin yanzu na tsira. sai dai, na rabu da saurayinnan bai faɗa min sunan shi ba sannan kuma bai tambayi sunana ba.

nice ma nayi mishi karya a cewar da yayi zai zo min ziyara. Ko dai yana ganin tunda ya san gidan mu babu bukatar yasan sunana.

To ai in Bai san sunana ba babu yarda za’ayi ya same ni toh Banda Abu na Koma mene-ne dai bazai taɓa samu na ba.

to amma mai yasa shi zub,da kwalla. bayan na ɓace mishi da gani,Mai hakan yake nufi?”

Wannan tambayar nai tayi wa kaina.

ina cikin zurfin tunanin’nan. sai naji sallamar da ta zaburar da ni.

domin Muryar raƙiba naji sai nayi ɗan shuru domin in sake sauraro ko dai kunne na ne? ai kuwa sai wani sallamar na sake ji tayi. domin ba’a amsa mata ba.

“Rakiba?”

To mai ya kawo raƙiba gidannan da daddare warhaka? Mai ma zai sa rakiba zuwa gidannan? Bayan itace ta sa baba ya kore Ni a gidan sa.

to, ko dai baban ne ya mutu? kai a’a idan shine ya mutu, ai sai dai a faɗa mana a waya. amma baza ta taɓa zuwa ba.

domin gabar da raƙiba takeyi da Ni ya zurfafa. tamƙar Ni ba yar uwarta bace ta jini.

tayi duk wata manakisa don fadiwata, ta kuma haddasa rigima tsakani na da mahaifi na. har ya kawo ga kora ta a gidan sa.

ta cire duk wata soyayya da ke tsakani na da mahaifi na. wadda yasa har yau, bai san ina raye ba, balle ya ƙirani da yar sa.

dukkan shirin su ita da mahaifiyar ta shine suga baya na. to mai zai sa raƙiba ta sako ƙafar ta a gidannan? idan ba wata manaƙisar suka sake shiryawa ba.

to idan munafircinne suka shirya, wanne-ne yafi wanda sukayi min abaya girma, da suke buƙatar su sake haɗa min?

Babu shakka! raƙiba tazo da shiryayyiya.”

*****

Zuciyata ta ƙasa jurewa sai na tashi da hanzari na fita. sai tsayawar ta nake gani na kallon ɗaki na bayanta kaɗai nake iya gani.

“Bama marhaba da zuwanki kwat-kwata. domin ita salama tana wurin masu salama ne kaɗai. amma ke baki da ita. don haka mai ya kawo ki gidannan?”

Sai ta juya tace da Ni,

“sulhu, sulhu shi ya kawo ni. nazo in roƙi gafararki yar’uwata, Aminiya ta kuma jini na.
Na zamo butulu a rayuwar da nayi a baya. son zuciya ta makantar da ni ganin inda ake so na.

ban fahimci duk wata ƙudiri da cima buri nawa na gaba ba, sai da na rasa ki a kusa da ni….! yau gani nazo neman gafara a gurinki. don Allah….; ki yafe min? nayi danasanin, abunda na aikata.”

Tare da ajiyar zuciya nace,

“ita kalmar so fa ɗaya ce anyi soyayya na haƙiƙa a zamanin da…! amma yanzu, mafi yawan soyayya tana zuwa ne da yaudara. fuska biyu cikin ɗaya. wannan wani sabon salo ne na yaudara domin cimma wani,”

sai mama ta dakatar da Ni,

“Haba mamma yanzu Duk iliminki da tauhidin ki, ki ƙasa jin kalmar Allah a cikin maganganun ta. ta nemi gafara sannan ta ambaci mahaliccin mu. idan sauran kalmar ta yaudara ce, toh Allah da ta furta fa?

Ina so in tunasar da ke cewa, Ubangiji ya fuce wasa duk wanda yayi rantsuwa da Allah akan gaskiya to sai ya ga haskenta.

haka kuma idan kayi rantsuwa da Allah akan ƙarya, wallahi bazaka ga daidai ba. saboda haka duk wata yaudara saboda cimma wani buri, bazai taɓa cin nasara akan ki ba ƴa’ta. ki yafe mata sai Allah ya yafe mana gabaɗaya.”

“Ki yarda da Ni mamma. naje na Sami baba na faɗa mishi abunda ya faru. baba ranshi ya matukar ɓaci ya tunzura matuka har ya yayi yunkurin duka na. da kyar aka karɓe ni a wurin shi. haka yasa shi cikin damuwa da kunci. game da mataki da ya dauka, a kanki.

shine yace, intabbata nazo dake. idan banzo da ke ba, zai kore Ni a gidan sa. tunda nice na jawo komai. don Allah….! mama ki roke ta mu koma gida tare?”

Raƙiba ta roƙi mama.

“Toh kinji mahaifin ki na nemanki. ai wannan abun farin ciki ne matuƙa, ace zargin da mahaifinki yake miki yau Allah ya wanke shi a idanun sa. hasali ma shine ya koma jin kunyar ki.

hakan kuma ya faru ne duk acikin rashin sani. sannan kuma, ita raƙiba Allah ya kawo mata shiriya har ta furta gaskiya. Saboda haka,

Allah yana son Mai naiman gafara. Don haka, ku yafi juna Ni na amince ki koma zuwa ga mahaifin ki mamma.”

inji -mama.

*****

Nan Sai na shige ɗaki cikin zazzafar kuka hawaye ne suke zubo min kamar ruwa. zuciya ta, ta raunana tana ƙuna, na tamkar wuta.

na rasa yarda zanyi to idan na daina kuka zan haɗiyi zuciya.

“shin wannan wani irin ƙaddara ce mara tausayi? idan baba, ya gane bani da laifi, to ina masoyi na yake?

Ina za’a samo shi? ya rabu da Ni da tunanin ina ƙin,sa. a zuciya ta.

sanadiyar maƙirci, ya tafi ya bar ni ba tare da na san yana so na ba. ya rabu da Ni sakamakon ƙiyayya da nakeyi mishi.

Bazan iya ci gaba da rayuwa cikin tunanin ya tafi ina nuna mishi ƙiyayya ba.

ta yaya zan,zama silar ɓacewar wani a wurin iyayensa? ban taɓa tsanar wani ɗan adam ba, sai dai in,ƙi halinsa. Wai ina zanga Abdul?

Wannan sune littafi na na farko a wannan man hajar ta bakandamiya. Kuma na sake ta ne kyauta domin masu son karatun litattafai na Hausa. Idan wannan labarin tayi muku daɗi to ku taimaka kuyi min like, comment Domin sanin yar da labarin yake agurinku.ni kuma sai in inganta rubutu na. Sannan kuma kar ku manta kuyi following Dina Domin ganin sabin labarai idan na ɗaura. Haka kuwa zan fahimci labarun, sunyi muku daɗi ne ta hanyar,rate Mai halamar star. da zarar ka taɓa.

Idan kuwa baka da account da bakandamiya to ka kokar ta ka buɗe domin ta hanyar samun account da bakandamiya ne zai baka hanyar yin kike, comment kayi rating kuma kayi subscribing.

Na gode. Taku Habiba Maina, daga yanzu har zuwa gaba insha Allah.

<< Soyayyar Da Na Yi 1Soyayyar Da Na Yi 3 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.