Skip to content
Part 3 of 9 in the Series Soyayyar Da Na Yi by Habiba Maina

Ina cikin hawaye Raƙiba ta bini ɗaki tana cewa,

“Yar uwa ta.”

Na dakatar da ita da hannu.

“Kin warware kwata amma rabi da kwatan shine misalin nauyin shimfiɗaɗɗen ƙasa da muke takawa. kin zaiyyanawa Abdul ƙiyayya a sako da sunan ni na rubuta.

Abdul yana matukar so na wadda sanadiyar ƙiyayya da nake mishi ne ya ƙaurar da shi zuwa gari mai nisa. garinda babu wanda yasan a ina, yake.

Alhali ni ban San yana so na ba. wasiƙar da ya turo min ta ƙarshe kika boye, ina so in tabbatar miki da cewa, ya shigo hannu na bayan zuwa na gida.

abdul ya zaiyyana zafafan kalamai a gare ni, game da soyayyar da yake min. wadda aikaceccen aikinsa ne game da soyayya ta.

tabbas ranar wanka ba a ɓoye cibi idan kika yi sanadiyar mutuwar Abdul ta wannan hanyar, ki Sani, nima zan mutu.kuma bazan yafe miki ba kamar yadda Abdul ya tafi da tunanin cewa karshen soyayyar mu bata ɗaya daga cikin alfaharin masoya. Haka Abdul ya zai’yana a cikin sakonsa.

“Wani irin so ne yake sa masoya suji kamar su tashi a doron ƙasa su koma sararin samaniya, su zamo taurari?

shin tsananin so ne yake sa masoya a ruɗani? ko-ko tsan-tsan ƙiyayya ne yake haifar da hakan?

Mai ne-ne tasirin zurfin ciki game da masoyan da suke mutuwar son junan su,amma sun ƙasa furtawa juna?

shin akwai riba a so maso wani, ko ƙoshin wahala ne kamar yadda ake faɗa?

wani irin raɗaɗi masoyi ke ji a lokacinda zai yi ban kwana da masoyiyyar sa, ban kwana ta har abada?

babu ingantacciyar rayuwa ga masoyin da ya rasa masoyiyar sa.

Farin ciki yakan nisanta da shi na wani lokaci, yakan shiga ƙunci mai tsanani ya dasa masa bishiyar takaici a zuciya.

ingantacciyar rayuwa yana samuwa ne ga masoyin da yayi dace da masoyiya na gasjiya.

masoyi na gaskiya shine yake jajircewa akan masoyiyar sa ko wuya ko daɗi.

shi ke sadaukar da farin ciki ga masoyiyar sa , ko zai dauwama cikin baƙin ciki.

shine Wanda so baya ƙaurace wa zuciyar sa, domin yayi dace a so.

shine ke ji kamar ya ɗauki masoyiyar sa su koma sararin samaniya, su zamo taurari.

******

Allah sarki so a sanadinki na faɗa so maso wani na apka matsananciyar soyayya da zukata ke azaptuwa.

ta sanadinki na killace so a zuciya,ta zamo kamar wuta tana min ƙuna.

mutunci da mafarin halaƙa ta da ni da ke, kin ban farin cikinda ya faranta zuciya ta.

shine maƙasudin samuwar kishi a kanki.
Haka ne yasa ko maganar wani ɗa namiji ba na so naji ya fito daga bakin ki, da zarar kinyi, nakan ji kamar ruhi na zai fita.

Nakan yi asarar hawayenda ban san iya adadin sa ba, a wannan lokacin nakan ji na tsani kaina, gami da dana sanin saninki a rayuwa.

Nayi iya kokari na domin na kaucewa rayuwar ki, sabida barazanar da kike wa zuciya ta. Kishi a kanki ne, yake auna zuciya ta, yake kokarin fasa ta.

Ina matukar daraja ki a cikin rayuwa ta, buri na, a ko da yaushe ki zamo cikin farin ciki da anna’shuwa.

Muryar ki ce tafi ko wacce murya daɗi a kunnuwa na. Ji nake kyau, kamar a fuskar ki ne kaɗai ta yaɗa san-sani.

Mun saba da ni da ke, sabo na haƙiƙa. Tunani na a kullum babu abunda zai kawo rabuwa ta da ni da ke, koma bayan mutuwa.

Domin, munyi wa juna alkawarin, baza mu rabu da juna ba har abada. Duk wannan alkawarin, sai gashi rana ɗaya kince, bakya buƙata na a cikin rayuwar ki.

Kina buƙatar in nisance Ki, nisanta na har abada. Ashe duk ƙarfin so, yakan iya zama guba ya gurɓata zuciya?

Ina roƙon ki da ki yafe min. idan har laifin da nayi miki ne ya sanya ki haka.

Zan kauracewa rayuwar ki, kamar yarda nayi miki alƙawari tun farkon haɗuwar mu, daga ranar da kikayi fushi da Ni, ya taɓa zuciyar ki, daga ranar zan kauracewa rayuwar ki.

*****

Na yanke hukuncin hakanne, domin kada halaccin da kikayi min ya zamo butulci. Zanyi nesa da ke kamar yarda kika umurce ni. Duk da ke halitta ce da ke rayuwa a cikin zuciya ta.

Sai dai ina taƙaicinda ƙarshen labarin mu, baya sahun cikin labaran,da duniyar masoya ke alfahari da shi. Ban kwana na har abada!
Naki Abdul Nams.”

Na ƙarasa karanta saƙon cikin kuka tare da hawaye mai zafi a fuska ta. Amma Raƙiba bata ce komai ba.

“Kinyi mamaki ko? Kinyi mamakin, yarda saƙon ya shigo hannu na ko?”

Ganin yarda Raƙiba ta tsorata, idanun ta sunyi tsilli-tsilli.

Na ƙara da,

“ina zanga Abdul?”

“Ban san inda Abdul yake ba, a halin yanzu. Amma nayi miki alƙawari, idan muka koma gida, zanyi iya ƙoƙari na, in gano inda yake.”

Wannan kalmar nata suka sa nace,

“alƙawari fa? Kinyi alƙawari kika ce?”

Tace da ni,

“eh Mamma nayi alƙawari.”

Cikin bazata sai Muryar mama muka ji tace,

“waye Abdul?”

“Duk muka juya cikin tsoro da firgita. Domin mun bar ta a falo. Babu zaton zata biyo mu ɗaki;

Sai ta ƙara da cewa,

“nace waye Abdul?”.

Mu hadu a babi na hudu domin jin yarda da labarin zai kasance.

Wannan sune littafi na, na farko a wannan manhajar ta bakandamiya. Kuma na sake ta ne kyauta domin masu son karatun litattafai na Hausa. Idan wannan labarin tayi muku daɗi to ku taimaka kuyi min like, comment Domin sanin yar da labarin yake agurinku.ni kuma sai in inganta rubutu na. Sannan kuma kar ku manta kuyi following Dina Domin ganin sabin labarai idan na ɗaura. Haka kuwa zan fahimci labarun, sunyi muku daɗi ne ta hanyar,rate Mai halamar star. da zarar ka taɓa.*

Idan kuwa baka da account da bakandamiya to kayi kokari ka buɗe domin ta hanyar mallakar account da bakandamiya ne zai baka hanyar yin like, comment kayi rating kuma kayi subscribing.

Nagode. Taku Habiba Maina. daga yanzu har zuwa gaba insha Allah.

<< Soyayyar Da Na Yi 2Soyayyar Da Na Yi 4 >>

1 thought on “Soyayyar Da Na Yi 3”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×