Skip to content
Part 5 of 9 in the Series Soyayyar Da Na Yi by Habiba Maina

Wani mamaki tayi da yasa ta ƙasa cewa komai sai dai maganar yana susa mata rai. Haka tana gani kuwa Abdul ɗin ya tashi tsaye ya juya ya yi tafiyar sa bayan gargaɗi da ya yi mata.

Da idanu ta bishi, ta ƙura mishi, ta rasa me zata ce har sai da Abdul ɗin ya bace mata da gani. 

ta ɓari daya kuwa, Maliya, Zinat da Na’ima Suna Kallon duk yarda sukayi da Abdul. amma Sai dai basu ji hirar tasu ba. ganin yadda mamma take sabuwa a makarantar yasa Zinat take cewa,

“me kuma Abdul yake yi a wurin mamma? bayan duniya ta shaida baya Soyayya.”

“ke ba mamma ba, Ramlat sunanta.” Maliya ta kaste ta. 

“Eh sunanta Ramlat… amma a gida ana kiranta da mamma.” Zinat ta basu amsa.

“wato kin waye ta ko? to idan ba haka ba a ina kika san inkiyar ta?” na’ima ta tambayi ta.

“mamma ai ƙanwar ƙawata ce raƙiba Wacce suke ‘yan’uba, kuma ai kun santa wacce take (forculty of science and technology ).” Zinat ta fahimtar da su.

“no wonder…, shiyasa Naga Sam! ba kya nuna ƙauna ga Ramlat woto raƙiba na nuna ‘yan ubanci wa Ramlat ko? shine kema kika ɗauka.”

maliya ta faɗi.

“kwarai kuwa, ai duk abunda raƙiba bata so, to Nima Bana so. Kamar yadda duk abunda bana so, ita ma bata so.” Zinat ta mayar Musa da amsa.

“cab! ai kuwa kin kama aiki. indai zaki biye wa raƙiba, banda sheɗanci!, ba abunda zata sa kina yi ki ɗauki alhakin yarinyar nan a banza, kuma ta sa ki cikin da na sani. domin daga ganin yarinyar nan, mutuniyar arziki ce.” inji na’ima.

“kwarai kuwa! maganar Na’im gaskiya ne, gwara dai ki canja.” inji maliya. ta goyi bayan maganar Na’ima. 

Zinat kuwa sai kallon su take bata ce komai ba. domin maganar tasu ma ba shiganta yake ba.

“Ni ina ganin ko, Abdul ya waye ta, shiya sa ya zo mata.” inji maliya.

“babu alama sun wayi juna akwai dai abunda ya kawo shi.” inji zinat. 

“wai ku har kun manta halayyar Abdul ne? da kowace sabuwar ɗaliba idan ta zo sai ya ja mata kunne, don kar ta faɗa soyayya da shi?” Na’ima ta tunasar da su. Halayyar shi wadda sananne ne kowa yasani.

domin duk sun manta wannan hali na Abdul. ta ƙara da cewa,

“Ni ina ga wannan shine ya kawo shi.”

“Eh haka zai iya yuwa don tabbas idan basu wayi juna ba, to Abdul sai ya yi mata gargaɗi.” Na’ima ta karasa maganar, idanunta akan su mamma.

“nifa tunda mamma ta shigo aji, naga yadda kowa yake yaba kyanta ko, naji tsananta ya ƙaru a zuciya ta.” Zinat ta karasa da faɗin haka. da fuskarta a murtuke. 

“a’a! kice dai ta fi raƙiba kyau, wannan shike baki haushi amma ba yadda jama’a ke yaba kyanta ba.” na’ima ta tsare ta da idanu tana faɗin haka. sai wani dariya maliya tayi, Wadda yasa ta ce,

“ni kuma yarinyarnan tayi min, burge Ni take yi wallahi. Ni son ta ma nake da ƙawa.” ta ajiye maganar, na ɗan seconds sannan ta Miƙe tsaye ta ce, 

“bari ma ku gani…” ta yunƙura zata nufi wurin mamma Sai riƙe gyalenta na’ima tayi ta dakatar da ita Da cewa,

“Ke tsaya muje tare. ai kawancen har da Ni.”

 juyawa sukayi ba tare da sun yi mata sallama ba Sai wani hanzari ma suke, kai ka ce ramlat ɗin ma kuɗi ce, Kar ta kare. Sai zinat ce, ta dakatar da su da kalaman ta marasa daɗi.

“lallai sai yau na fahimci ku daƙiƙai ne.” ta cigaba da cewa,

“yaushe zan zubda aji na inje neman wata ya’ mace da ƙawance? ai sai ta raina Ni.” wannan furucin na Zinat ya basu mamaki da yasa maliya ta maida mata amsa, Dai -dai, da maganar ta.

“eh lallai, laifi tudu….” na’ima ce ta karasa mata habaicin nata. da cewa,

“ka hau naka ka hangi na wani ba. ai gwara mu. Kawa zamuje nema, ba saurayi ba.” maliya ta faɗi ta kara da cewa,

“yanzu faɗa min, da mu da ke, wa ya fi zubda aji?” tambayar tayi mata cikin tsare wa. sai na’ima ce ta dakatar da ita da cewa,

” kyale ta muje, kar ta ɓata mana lokaci.”

mamma kuwa na zaune kanta ya kulle.sai maganganu take a zuciyar ta da ya kasa zama, sai da ya fito fili.

“kaji maganar banza? wai Ni yake yi wa gargadi akan so. to Ni me zanyi da shi?” tana cikin tambayar kanta haka ne sai ji tayi an cafke maganar tata da cewa,

“mai yuwa ki zama daban a cikin sauran ‘yan matan da ke ajin mu, da ma sauran ‘yan’matan, da ke makarantar nan baki ɗaya. amma duk budurwar da ta shigo makarantar nan mafi akasari sai taji tana son Abdul.”

Maliya ta zauna tana faɗin haka tare da na’ima ta cigaba da cewa,

“duk da ban san me kike nufi ba, amma maganar ki tayi dai-dai da tunanin mu.” ta dakata da faɗin haka.”

Wani firgita mamma tayi da ba zatar amsar da maliya ta bata. sai suka gabatar da kansu ga mamma. Maliya ce ta Fara gabatar da kannata, da cewa,

“suna na maliya al kasim. Ni course mate ɗin Ki ce.”

“Ni Kuma sunana na’ima Kabir nasir. nima course mate dinki ce.” na’ima ta faɗi ta kuma cigaba da cewa,

“ganin kin gabatar da kanki a aji ɗazu, mu kuma baki san sunan mu ba, shiyasa muka zo mu gabatar miki da kan mu. sannan, muna so ki zama ɗaya daga cikin mu. kamar yadda kika sani ne iyaye sun tura mu makaranta saboda karatu, to shi muke yi, bazaki same mu da matsala ba. sannan idan kina da wata tambaya, zaki iya tambayar mu.”

ajiyar zuciya Mamma tayi wadda ya sa ta ɗan huce, Taji wani sanyi a ran ta da alama dai, kan ta zai warware. ta ce da su,

“na gode da kulawar ku, kuma insha Allah…, zan kasance ɗaya daga cikin ku, muyi karatu mu fitar da iyayen mu kunya.” ta kara da cewa,

“naji daɗin haɗuwa da ku matuƙa! domin haɗuwa da ƙawayen kirki a makaranta, na ɗaya daga cikin addu’a ta.”mamma ta dakata da faɗin haka na ɗan seconds. Sannan ta ce,

“Ina son in tambaye ki maliya, don Allah… waye saurayinnan? kuma ya akayi kika fahimci kaɗan daga cikin maganar da ta haɗa Ni da shi? Saboda maganar sa ce, ta dasa Ni a nan har na kai wannan lokacin. maganar sa ta ɗaure min kai, na ƙasa fahimtar me yake nufi?” cikin neman sani ta faɗi domin karin haske.

“to sunan shi dai Abdul. kuma, Abdul sananne ne a makarantar nan. amma kafin in baki amsa zan so ki faɗa min me ya faɗa miki?” maliya ta tambaye ta.

“gargaɗi yazo ya yi min. wai idan akwai soyayyar shi acikin raina, to in cire. domin shi baya Soyayya, kuma bashi da budurwa, sannan kuma, babu wacce yake so a makarantar nan. wannan ita ce gargaɗi da ya yi min.” Mamma ta bata amsa. dariya maliya tayi sannan ta ce,

“kwarai kuwa. maganar da ya faɗa miki haka ne. Abdul saurayi ne da yan mata suke so a makarantar nan, abdul ya yi karfi wajen rubuta kalaman soyayya da watsa su, wannan shine babban dalilin da ya sa ‘ƴan’matan, ke son sa domin kalaman sa na ratsa zuciyar mai sauraro. duk wacce ta saurari kalaman nasa sai taji tana son sa. ke in taƙai ta miki. Akwai wata amarya da ta so ta kashe auren ta saboda abdul. Da kyar aka sha kan al’amarin wannan shine dalilin da ya jawo babbar matsala a rayuwar Abdul abubuwa da dama sun faru, tun yana final last year sanadiyar haka yasa akayi repeating na shi yayi joining na mu. Haka yasa Abdul ɗin cikin wani hali, daga nan ne makaranta ta dakatar da kowace budurwa da ta dakatar da yakin da take yi akan sa, ta ɗauki kalaman soyayyar Abdul a matsayin kalamai masu sanyaya zuciya, da bada shawara. sannan department dinmu ta ɗauki nauyin rubuceccen bayani da duk wacce ta shigo sabuwa, za’a bata wannan takarda ta gargadi akan Abdul, haka shima Abdul ɗin duk wacce tazo sai ya yi mata gargaɗi da kar ta faɗa soyayyar shi. domin duk wata ya’mace me aji, kalaman sa zasu ɓata mata rai har tayi furucin me zatayi da shi. kamar yadda muka zo muka tarar da ke kina faɗa.

<< Soyayyar Da Na Yi 4Soyayyar Da Na Yi 6 >>

3 thoughts on “Soyayyar Da Na Yi 5”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×