Skip to content
Part 8 of 9 in the Series Soyayyar Da Na Yi by Habiba Maina

Cikin kallon kuda suke ko ina yayi tsit! kamar a dokan daji, sai kukan tsuntsaye ne ke tashi ta ko ina. zinat ce da ke gefe a zuwan da ta yi ta tarar da su cikin hargitsin, bata ce komai ba sai da ta bari ta gani, kuma Taji duk abunda ke faruwa. irin cin mutuncin da Abdul ya yi wa mamma yasa ta ji daɗi, ya matuƙar birge ta. da murmushi ta yunƙura cikin jama’a ta isa wurin Abdul tana mai cewa,

‘Abdul ba girmanka bane sa in sa da ire-iren yan’ matannan. kuma ba ajinka bane gargaɗi ga wa’yanda basu kai ba domin Ni a guri na wasu yan matan be dace kana musu gargaɗi ba, saboda basu kai…’ Abdul bai bari ta karasa ba ya dakatar da ita da cewa,

‘Wadda ta dace da wanda bata dace ba, ba sune damuwa ta ba. wannan gargaɗi ne akan matsalar da kuskuren barinsa zai jawo hargitsewar rayuwa ta cikin minti guda. Saboda haka, ya zama dole in dakatar da shi ko ta ina ne ma.’

ya dakata da faɗin haka yana kallon zinat har cikin idanunta sannan ya ci gaba da cewa,

‘You have no right to tell me what to do or to do, cause this is non of your business. wannan ba abunda ya shafe ki bane zinat…, don haka karki ƙara sa min bakin a Cikin al’amura na.’

tsabar tsoro da gudun bacin ransa yasa ta amsa da gaggawa,
‘ I’m sorry! in Allah ya yarda bazan sake ba.’ ta faɗi kanta a sunkuye cikin kunya.

‘Better!’ Abdul ya faɗi

‘Ni shiyasa ko, ban cika shiga sharo ba shanu ba, kuma sam! bana kai kaina inda ba a san daraja ta ba wallahi…!’

maliya ce ta wurga wa zinat habaici da yasa wasu daga cikinsu ɗaliban sukayi dariya, wasu kuma suna dariyar suna rufe baki kar ya fito fili. babu ko batan second zinat ta fice a tsakanin su ta bar wurin cikin gaggawa ita ma mamma ta tattara takardun ta ta sa a jaka ta fice a Tsakiyar su, sai gate ɗin fita ta nufa.

‘Ramlat…!’

‘Ramlat….!’

Maliya ce da na’ima suke kwalla mata kira a yayinda suka biyo ta da gudu domin su hana ta tafiya amma sun ƙasa iso ta har ta samu mashin ta Hau, sun iso ke nan mai mashin ɗin kuma ya tashi, sai briki suka ci.

‘kash!’ Na’ima ta faɗi.

‘amma zinat ko…! wannan karon sai na seta mata rashin hankalinta, domin ba dan ta sa baki ba, da Ramlat bata fice a makarantar nan ba.’ Kugunsu duk suka riƙe suna masu bin hanyar da mamma ta ficed da idanu.

‘Ai ba laifin ta bane.’ maliya ta faɗi ta ci gaba da cewa,

‘laifin Abdul ne, domin shine ya tsaurara cakunan Ramlat…, gaskiya abun nashi yanzu yayi yawa, haba! kullum! sai yayi mata gargaɗi, tunda yake yi wa yan’mata, gargaɗi a makarantar nan bai taɓa matsawa budurwa, kaman yadda ya matsawa Ramlat ba. gargaɗin nashi ya wuce ka’ida wallahi! domin kuwa sau ɗaya aka ce yayi, bayan wanda su makarantar ke bayarwa.’

‘Wallahi! kuwa.’ inji na’ima ta ci gaba da cewa,

‘Ni kuma Ko…, har na fara tunanin wani abu game da shi.’

‘ me kike tunani?’ in ji maliya.

‘duk yadda zaki ji maganar tawa dai, Ni haka nake gani…, Abdul ya fara son Ramlat! domin kamar yadda kika ce ne, babu wacce Abdul ya yi wa gargaɗi da matsi, sai ita. to in dai gargaɗi sau ɗaya ya kayatar kamar yadda aka yi wa saura, to sauran gargaɗi da yake yi wa ramlat na mene ne? ɗaya ne a cikin biyu, faɗa ko soyayya! Abdul kuma da maza ma yan’uwansa beyi faɗa ba, balle mace. to idan babu faɗa, yanzu kuma amsa ɗaya ce ta rage, soyayya.’

Maliya ta bita ta da kallo cikin mamaki da fahimtar ta. sakin zuciya tayi sannan ta ce,

‘ maganar ki ta shige Ni, amma ina kokonto a kan haka, domin zamu iya tunanin hakan amma ke kanki kin san Abdul shu’umi ne karshe dai zaki tarar kwata-kwata babu soyayyar ta a tattare da shi.’

‘to indai haka ya kasance, wannan karon Abdul bazai ji da daɗi ba. domin Ramlat ɗin ma da kanta ba son shi take ba.’ na’ima ta faɗi ta kuma ci gaba da cewa,

‘gaskiya ko…, ran Ramlat ya ɓaci, idan har ta kaisu ga ganin Principal, abun bazai yi kyau ba.’

‘Haka ne Allah dai ya takaita.’ maliya ta faɗi.

‘Amin…’ inji na’ima.

‘mu koma ko…; daga nan suka koma cikin makaranta.

*****

Mai mashin ya kawo ta har kofar gida, ta bashi kuɗin sa yayi tafiyar sa. ƙwanƙwasa kofa tayi mai gadi ne ya buɗe mata, ta shiga. kokarin magana yake yi mata domin sun saba wasa da dariya yakan yi mata labari masu daɗi amma yau mamma kauda kai tayi ta shige ba tare da ta tanka mishi ba, da babanta tayi ciɓis! tsabar hanzari bata ma ganshi ba, sai shi ne ya hango ta yana shirin shiga Mota zai je wurin aiki. ganinta ya bashi mamaki domin bata daɗe da fita ba me ya kawo ta gida? ko dai tayi mantuwa ne? tunanin da yake yi a ransa kenan ta iso shi a gigice har zata wuce shi don bata Ganshi ba sai ya dakatar da ita da cewa,

‘mama na…’ firgita tayi domin batayi zaton mutum a kusa da ita ba sai hirar da take yi a zuciyar ta,

‘ai ko samarin duniya sun kare bazan taɓa sonka ba Abdul…!’

‘mama na…’ mahaifin nata ya sake cewa,

‘ya na ganki a firgi ce!’ dakatawa tayi, ta kuma ƙarasa kusa da shi tana me cewa,

‘yauwa baba…, naji daɗin samun ka a gida, don Allah…, baba ka cire Ni a makarantar nan. daga yanzu bazan iya ci gaba da zuwa Makarantar nan ba wallahi…..’

tana faɗin haka ta fashe da kuka sai hawaye ne suka yanko mata wanda yayi daidai da fitowar mahaifiyar ta. da jakan baban nata a hannu dama a duk lokacin da zashi aiki ita ke riƙe masa jaka su fito tare, sai ya shiga Mota ta ke miƙa masa sannan suyi sallama ya tafi. Jin Magar mamma yasa shi zabura cikin fushi ya ce,

‘mama na me akayi miki? wa ye, ya sa min ke kuka har kike ji zaki bar makarantar? babu shakka, ko wanene shi sai ya ɗan-ɗana kuɗar sa. faɗa min waye…?’

Ya daka tsawa, ranshi ya baci matuƙa da ganin hawayen ta, domin soyayyar da yake yi wa mamma ya wuce misali, ji yake kamar ranshi aka taɓa, ya kasance idan mamma Taji haushin wani abu, sai ranshi ya ɓace, ya sa shi kamar ya yi kuka, yakan manta cewa shi babba ne, a kullum mahaifiyar mamma na cewa tun mamma na karama baya son ya ji ko motsi na damuwar ta, domin ta kanga shauƙi na soyayya me ƙarfi a tattare da shi, musamman ta ɓangaren mamma mai sunan mahaifiyar sa.

‘babu wanda ya taɓa Ni baba, ba ayi min komai ba, Ni dai kawai ka canza min University, idan ba haka ba wallahi bazan iya karatu a makarantar ba. wannan hawaye da suke sauka a idanu na kuma, na zubar da sune a gaban ka domin ka fahimci gaskiyar abinda nake fada maka, ta haka ne kawai zaka fahimci cewa bana son makarantar.’ ta faɗi.

ajiyar zuciya ya yi ya ce da ita,
‘ki share hawayen ki mama na, hakan yana ɗaga min hankali…, tunda bakya so to, Ni zan cire ki. amma bana so kina zubar da hawayenki a banza dama ina so inji dalili ne to tunda wannan ne dalili to ki ɗauka ma kin fita.’

baban ya faɗi ya ci gaba da cewa,

‘idan na dawo daga office zamu zauna mu tattauna akan haka kin ji?’ ta ce,
‘eh! na gode…’

‘bani Jakata.’ ya ce, da mahaifiyar mamma. ta miƙa mishi jakar ya ce,

‘ina fatan kinji abinda ke faruwa…? mama na, tazo da complain akan bata son makarantar a canza mata, kina gani harda kuka. so i have to do something about it saboda haka ku shiga ciki kiyi comforting ɗinta idan na dawo zamuyi meeting.’ ta ce,

‘to Allah ya tsare…’ ya ce,

‘Amin.’ mamma ta ce,

‘a, dawo lafiya.’ ya ce,

‘Amin.’ ya shiga motar shi ya fita suna tsaye suna ganin fitar sa, juyowa mahaifiyar tayi tana yi mata wani irin kallo na rashin yarda domin ita sam! Bata gamsu da maganar mamma na cewa haka kawai take so a canza mata makaranta ba, domin ta san halin ‘yar ta, tana da zurfin ciki ba komai take bayyana shi ba, sai ya zama dole saboda haka ita kwata-kwata tunanin ta be kai ga ace wasu ne a makarantar ta sami matsala da su ba sai dai in rakiba ce, tayi mata wani abu, ita ma hankali ta ya tashi saboda wannan karon bazata yarda rakiba tayi amfani da shiru da take yi akan komai ta ce zata matsawa mamma ba. zuciyarta ta kulle amma haka ta ɓoye domin Taji ainihin abinda ya faru ta ce da ita,

‘ke! ki fito ki faɗawa mutane gaskiya…, definately Akwai abunda ya faru kike kuka amma ba haka kawai ba, me ya sa kike kuka? Kuma me yasa kike so a canza makarantar?’

Kallon mahaifiyar tata, tayi sannan ta kau da kai cikin tsarguwa ta wuce ciki tana cewa,

‘babu abunda ya faru kawai bana son makarantar ne.’ ta bar wurin saboda kar mahaifiyar ta fahimci gaskiyar abinda ke faruwa, yadda zuciyar ta ya ɓaci bata ji zata iya jure sauraro daga tambayoyi da za’a yi mata game da abinda ya faru, tabbas zata iya fashewa da kuka, kuma hakan zai iya jawo babbar matsala har a gano, kuma ita bata so kowa ya sani.’

‘To shikenan, idan tayi tsami zamu ji warin ta.’ mahaifiyar ta faɗi a yayinda itama ta biyo bayan ta suka shige cikin gida.

*****

Komawar su maliya cikin makaranta kuwa har ‘ila yau malami bai shigo musu aji ba don haka suka koma gefe suka zauna, a nan ne maliya tayi tunanin ta nemi Abdul tayi mishi magana akan abinda ke faruwa tsakanin shi da mamma don haka ta nemi shawarar na’ima,

‘kin san me?’ maliya ta faɗi.

‘sai kin faɗa.’ inji na’ima.

‘ina ganin yakamata mu sami Abdul muyi mishi magana akan matsalar nan da ke faruwa tsakanin su, Kinga bai dace muyi shiru mu zuba musu ido ba, mai yuwa idan mukayi mishi magana ya fahimce mu. Kinga sai abun yazo da sauki.’ maliya ta faɗi.

‘haka ne, wannan Shawara ne mai kyau, Nima nayi wannan tunanin. na riga ki a zuci ke kuma kin riga Ni a baki. to tunda haka ne me muke jira muje mana mu same shi…’ maliya ta miƙe suka nufi cikin, ɗaliban nasu maza sukayi ta duba shi basu same shi ba na’ima ta ce,

‘to ina ya shiga ne haka? karfa ya bi Ramlat har gida?’

‘ke!! don Allah…, mahaukaci ne shi zai bita har gida? yana wani wurin dai.’ inji maliya suna cikin haka waigawa da zatayi sai ta hango shamsu close friend din Abdul,

‘Yauwa! Ga Shamsu can shi kaɗai ne zai iya sanin inda Abdul yake muje mu same shi…’ suka nufi hanya da hanzari ita na’ima sai huci take don ta gaji sallama sukayi wa shamsu ya amsa

‘A’a! maliya, na’ima, kune?’

‘Eh mune;

‘Ya hakurin abunda ya faru ɗazu?’ shamsu ya faɗi cikin jaje ya ci gaba da cewa,

‘don Allah! kuyi hakuri Abdul bai yi daidai ba, Ni kaina raina ya ɓaci wallahi! Amma don Allah kuyi hakuri…’

‘Gaskiya babu daɗi, amma yanzu ma shi muke nema domin mu sami zama mu tattauna akan babban tashin hankalinnan da ke shirin afkuwa a makarantar nan, ko Allah zai sa a sami masalaha.’ Maliya ta faɗi.

‘Kunyi tunani me kyau! Ni kaina zan so inyi joining ɗinku a matsayi na na close friend ɗin shi. sai dai bayan ficewar ramlat da ku, shima ya fice ko ina yaje ban sani ba, na kuma neme shi domin nuna masa abinda ya yi ba daidai ba ne, Ban same shi ba. hatta wayar shima bata shiga.’ inji shamsu.

‘Mu ma haka, mun zaga ko ina duk inda muka san yana zama munje baya nan, shiyasa ma muka ce Bara muzo wurinka don kai kaɗai ne zaka iya sanin inda yake.’

Ta dakata da faɗin haka duk sukayi jugum! na ɗan mintuna da damuwa a fuskar su.

‘to ina ya shiga ne haka?’ inji maliya cikin matsuwa amma babu wanda ya tanka mata don dukkan su ma basu san inda yake ba, daganan dai maliya ta ce,

‘Na’ima…, Kinga mu je mechanical workshop mu zauna, gaskiya na gaji….!’

‘Nima haka…’ inji na’ima ta ƙara da cewa, ‘shamsu sai an jima…’

‘Yauwa…, na’ima ku huta gajiya….’

‘aha…!’ suka amsa a nan ne suka je suka sami wuri suka zauna a tsakanin motocin gyara da ke premises na workshop ɗin wasu mota ne da suka sa workshop hole din a Tsakiya sannan, da mazauni a ta jikin motar ɗayar motar ma kofarta a ɓalle ɗalibai sukan shiga ciki su zauna domin babbar mota ce saboda, haka suka zauna ta gefen ɗayar motar. inda aka ajiye mazauni ba ‘a cikin, motar Ba. a nan ne Na’ima ta kawo shawara da cewa,

‘um…! maliya me zai hana mu kira ramlat a waya mu bata hakuri me yuwa ta hakura ta dawo, ko ya kika gani?’

‘Anya kuwa…, bana ganin zata hakura har, sai Abdul ɗin ya bata hakuri da kanshi.’

‘A’a kar ki ce haka komai na iya faruwa cikin sauki! sai ki ga ta hakura. don ramlat me sauƙin kai ce.’

‘Kuma me taurin kai ba, domin irin su idan ransu ya ɓaci suna da wuyar lallami…, suna da taurin kai! amma dai ki gwada….’ maliya ta faɗi.

‘Yauwa…, haka nake son inji kince, ai Sai an gwada akan san na kwarai.’

******

Lokaci ɗaya nadama ta shige wa Abdul bisa abinda ya haɗa shi da ramlat…, ɗazu yadda ya tunzuzra ta da yanayin da ta fice a makarantar ya tsorata shi. sannan maganar da ta faɗa mishi ya dame shi. sintiri yake ta yi a yayinda ya ke jin maganar tata a kunnen sa yana ta maimaita maganar ta a zuciyar sa.

‘Ki bari in isar da sakon zuciya ta zuwa gare shi saboda yau Nima gargaɗi na na karshe a gare shi kenan.

Abdul ina so ka sani kamar yadda kake tunkaho baka soyayya to haka Nima bana yi ba taɓa yi ba kuma ban san yadda ake fara ta ba,

Kuma kamar yadda kake ji babu wacce kake so kuma babu wacce zaka so a makarantar nan,

To Nima haka, babu wanda nake so kuma babu wanda zan so a makarantar nan. haka kuma ina so ka sani idan Ni zan so wani ɗa na miji a makarantar nan to bazan so ka ba.

Saboda haka ka cire duk wani tunani na cewa Ramlat tana sonka domin indai Ramlat ce, to ko a mafarki haka bazai taɓa faruwa ba.

Saboda karatu ya kawo Ni makaranta ba soyayya ba.

Munyi karo ɗazu Ni da kai cikin rashin sani mun bigi juna, kayi hakuri.’

Wayannan maganganunne suke ta kai kawo a zuciyar Abdul ya kasa zaune ya kasa tsaye cikin matsanancin damuwa,

‘Anyi yan’mata da dama a makarantar nan, tunda na shigo makarantar nan, ban taɓa haɗuwa da ya’mace irin ramlat ba, babu shakka! duk abinda ke fitowa a bakinta daga cikin zuciyar ta ke fita.
Kuma da ganin ta mai kunya ce, tana da wuyan sabo da mutane.

Ya Allah! wannan gargaɗi da nayi mata zai iya zama barazana a gare ta, tace bazata sake dawowa makarantar nan ba.
To me zai faru idan ta faɗi, abinda ya faru a gida?

Yakamata in hanzarta neman Na’ima da maliya, domin su haɗa Ni da ita a waya in bata hakuri.

Hakika nayi da nasanin abinda na aikata domin ramlat ba irin sauran yan’matannan bane da na sani.’

Cikin wannan tunanin yake bayan yanke shawara da ya yi a karshe. juyawa yayi cikin hanzari don gudun ɓata lokaci. daga cikin mechanical workshop ɗin shima ya fice sai dai daga cikin hule ɗin ya fito wadda Dukansu basu san suna wuri ɗaya ba har suka gaji wajen neman juna Na’ima da maliya ya hango zaune yayinda na’ima ta kira mamma bai shiga ba har ta ke cewa maliya,

‘Kinga wai, is not reachable.’

‘Sake kira network problem ne.’ maliya ta faɗi.

Cikin kira na biyu ne sukayi Sa’a ya shiga mamma ta ɗauka Abdul kuwa ya iso dab da su.

‘Hello! ramlat….’ na’ima ta faɗi jin kiran sunan ramlat da Na’ima tayi ne a waya yasa Abdul ya dagakata, sannan su kuma basu Ganshi ba.

‘Hello! maliya…’ mamma ta faɗi

‘Ba maliya bace, Na’ima ce ga maliyannan a gefe tana jinki.’

‘Nace kin isa gida ne?’ kai tsaye maliya ta tambaye ta.

‘Ai tun ɗazu na isa gida.’

‘Don Allah! ramlat kiyi hakuri da abinda Abdul yayi miki ɗazu wallahi! ba yin kansa bane, dole ce ta sa kuma makaranta ma ta bashi daman ya yi hakan. amma wannan gargaɗi da yayi miki yau shine na karshe insha Allah!’

‘na’ima ta ta faɗi tana mai nuna damuwanta akan abinda ya faru.

‘Makaranta ce ta bashi dama ya dinga ci wa yan’mata zarafi a makaranta?’ amma sun ƙasa bata amsa ta ci gaba da cewa,

‘ya yi daidai ga wacce ta furta masa tana son shi, amma Ni wallahi bai isa yayi min gargaɗi akan Soyayya ba, kuma ina ganin wannan gargaɗin nashi shine na karshe.’ ajiyar zuciya Abdul ya yi hankalin shi ya ɗan kwanta da jin hakurinda suke bawa ramlat a kan shi sun zame mishi kamar wakilai.

‘Me kike nufi da gargaɗi na karshe? kin faɗi maganarnan ɗazu yanzu ma gashi kin maimaita, me kike nufi da haka?’ maliya ta tambaye ta a tsorace.

‘Eh ina nufin yau shine zuwa na makaranta, ta karshe, saboda na faɗawa baba na, bana son makarantar kuma ya ce za’a canza mini saboda haka Abdul bazai sake ganina ba balle ya yi min gargaɗi akan wani abu wai shi, Soyayya.’

Na’ima da maliya duk idanun su sai da suka ciko da hawaye jin maganar mamma ya sare musu zuciya matuƙa domin suna son zama da ita duk suka zaro idanu don haka sun kasa cewa komai.

Wani jiri ne ya ɗebi abdul hakan yasa ya kasa jin kansa waje ɗaya, ji yake duniya juyawa take da shi kamar a sararin samaniya cikin minti guda ya faɗi dap! da Na’ima wanda babu shakka! suma ya yi. Na’ima da maliya sukayi tashiwar doki a zabure kamar zasu tashi sama tsantsa faɗiwar gaba domin basuyi tsammanin da mutum a bayan su ba, sai faduwar sa suka gani. cikin wannan tashin hankalin kuma sun ma manta basu kashe wayar ba mamma tana jin duk abinda ke faruwa.

‘Hello…!
Hello…!’

Take ta faɗi amma basu ji ba balle su amsa mata,

wani ihu ta ji sukayi da ganin Abdul ɗin a yashe, ‘innalillahi wa innailairraju’un.

Abdul……!!!’

<< Soyayyar Da Na Yi 7Soyayyar Da Na Yi 9 >>

3 thoughts on “Soyayyar Da Na Yi 8”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×