Kwance ta ke a kan gado ta na karanta wani littafin A'isha Abdullahi Yabo mai suna Kuskuren waye? Hansu'u ta yi sallama da ga bakin ƙofa "shi go".
Ajiye wayar ta yi ta na kallon ƙofa, "ki na da baƙi a falo".
"Je ki na ji" ta faɗa tare da komawa ta kwanta ta na tsaki. Zaune ta same su saɓanin yadda ta barsu a tsaye "ta ce ta na zuwa"
"To ba damuwa" Hafsat ta faɗa ta na gyara zamanta. "Hansa'u!"
"Na'am Aunty!" Ta amsa tare da juya wa da sauri. . .