Skip to content
Part 10 of 11 in the Series Su Ne Sila by Aisha Abdullahi Yabo

Kwance ta ke a kan gado ta na karanta wani littafin A’isha Abdullahi Yabo mai suna Kuskuren waye? Hansu’u ta yi sallama da ga bakin ƙofa “shi go”.

Ajiye wayar ta yi ta na kallon ƙofa, “ki na da baƙi a falo”.

“Je ki na ji” ta faɗa tare da komawa ta kwanta ta na tsaki. Zaune ta same su saɓanin yadda ta barsu a tsaye “ta ce ta na zuwa”

“To ba damuwa” Hafsat ta faɗa ta na gyara zamanta. “Hansa’u!”

“Na’am Aunty!” Ta amsa tare da juya wa da sauri ta koma ɗakin ta na zuwa Zainab ta ce. “Na san halin ki ban ce ki ba su ruwa ba”.

“Amma Anty yayar mai gidan ce da kuma matarsa sai ‘yarsa”.

“Shi ne me na gayyace su ne” ta yi maganar ta na harararta  shiru ta yi “maza ki yi tafiyar ki wajan aikin da ya ke gaban ki”

“To” ta faɗa jiki a sanyaye tare da barin ɗakin ta na da kyakyawan mu’amala sai dai ta rasa wace irin ƙiyayya ce take yi wa mai gidan da duk wani abu da ya shafe shi. Ta yi maganar a ranta ciki da mamaki. Kusan minti goma shiru babu alamar za ta fito Ilham ta yi tsaki “Momy me yarinyar nan ta taka ne da za ta wani shanya mu kamar wasu kayan wanki”

 “Ni ma dai na fara ƙosawa kawai dai so na ke na ga wacce wannan yarinyar me take da shi ne da har Dadyn ku ya nace wa auren ta duk da cin mutuncin da a ka ce ta na yi masa”.

“Ni kam ba da ni ba  wannan zaman, ni ba na son raini wallahi shi da ya auro ta shi ya ji kuma ya ga zai iya, ke Ilham tashi mu tafi” miƙewa tsaye Ilham ta yi ta na gyara zaman mayafinta Hafsat ta tashi ta na faɗin “Aunty Laila ku zo don Allah mu shi ga ciki mu duba ta” kasancewar ita ma ɗin ta na so  ta gan ta yasa ba ta mu sa ba su ka nufi ɗakin Zainab. Su na shi ga ta na fitowa banɗaki kallo ɗaya ta yi masu ta kawar da kanta ta zauna gefen gado  kallon juna su ka yi su na taɓe fuska wayarta ta ɗauka kunna waƙar M. Sharif ta yi ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya ta na bin waƙar ta na rawa.

“Ikon Allah! Kai namiji da ɗaukar wa kai wahala ya na zaman zaman sa ya je ya ɗauko wa kansa wannan mai kama da figaggar kazar ta na gasa masa aya a hannu, ni ban ga abin so a wannan yarinyar ba da har zai na ce ma ta duk tijarar da ta ke masa, wannan ai kara da kiyashi ya ɗauko wa kansa”.

“Hahaha Allah Lamiɗo in ji fulɓi wannan ‘yar ƙuwailar ce wai har ya ga abin so to ni wannan da me ta fi ni ne ma” so ta ke ta yi mayar masu da magana sai dai ta na danni zuciyarta da ta tuna shiru ya fi ban haushi ga karnuka masu haushi. Ilham kuma tsoron kar ta yi magana ta kai ga Dady yasa ta ja baki ta tsoki sai dai ji ta ke kamar ta yi mata shigen duka. Har su ka yi su ka gama ko kallonsu ba ta yi ba bare har ta tanka masu, su ka tafi Yaya Laila sai masifa ta ke. Su na fita ta fito falo ta na faɗin “sakarkaru kawai Allah yasa ku yi zuciya kusa ya sake ni.”

Gidan Aunty Laila ya nufa kasancewar Hajiyar su ta zo ganin likita kamar yadda ta saba duk ƙarshen wata ta na zuwa ganin likita a kan ciwon suga da ta ke fama da shi.  Su na zaune falo bayan sun gaisa ya ke tambayarta yanayin jikin na ta.  “Da sauƙi sosai kwana biyu ne dai da maganin ya ƙare ciwon ya din ga damuna”.

“Haba Hajiya dan me za a dinga barin magani na ƙarewa  ba na ce da ya kusa ƙarewa ba a dinga kirana na sayo ko na kawo da kaina ko na aika a kai” mika ƙafafunta ta yi da su ke ɗan yi mata ciwo sannan da ga bisani ta ce. “Kai ni maganin ne na fara gajiya da shan sa wallahi, kullum shan magani kamar wata ‘yar ƙwaya”.

“To ya za a yi ai sai haƙuri tun da lalura ce Allah ya riga da ya ɗora wa bawansa sai haƙuri da fatan canye jarabawar da mutum ya samu kansa a ciki”.

“Hakan ne Allah yasa mu dace ya inganta mana lafiyar”.

“To Amin dan Ya RasululLah (S.A.W) kin dai ƙi yarda ki zauna wajan Hafsat”.

“A’a barni na zauna a nan ɗin dai ya fi, gara mutum ya riƙi girman sa kasan yaran nan na yanzu ba daidai a ke yi wa juna ba ga mu iyayen na ku har matan na ku. Ko ita Lailar da mijin ba ya a raye ne ai da ba na zo gidan Siriki na zauna ba” murmushi ya yi kafin ya ce. “Shi kenan ai dole na yi haƙuri tun da Aunty  Laila ta ƙwace mini ke. Amma dai ai za ki je ki ga amarya ko, kafin nan dai In Sha Allah gobe zan kawo ta ta gaishe ki”.

“Wa! Kar ma ka fara cewa za ka kawo mini wannan nakasasshiyar amaryar ta ka a gidan nan, kuma Hajiya ma ba zan bari ta je ba” Aunty Laila ta yi maganar idanunta fis a kansa. “Me kuma ya faru da ga maganar zan kawo ta sai faɗa, shi kenan ba za ta zo gidan na ki ba,  amma ai Hajiya ina da haƙƙi a kanta na ta zo gidana ko?”.

“Ka ga Umaru bar maganar tafiyar nan ni kaina ko ba ta ce ba ba za ni ba, yau sun je gidan ka ta wulaƙanta ‘yar’uwar ka da matar ka, dan haka barni na kama tsofana” ajiyar zuciya ya yi ransa ya yi matuƙar ɓaci “ku yi haƙuri”.

“Idan ba mu yi haƙuri ba za mu dake ta ne, ai ko me ta mana kai ka janyo ka na zaman ka lafiya da matar ka ka je ka ɗauko wa kan ka kara da kiyashi, mu dai ba za ka sake ganin mu a sabgar amaryar ka ba, kai da ka ji ka ga za ka iya sai ka yi ta fama dama ko wa ya sai rariya ya san za tai zuba”.

“Umaru tun farkon maganar neman auren nan sai da na ce ka haƙura tun da ba ta so kar a zo a yi matsaloli su biyu baya, amma ka na ce yanzu ga irinta nan kai da ka ajiye ta ba ta daraja ka ba bare kuma wasu dangin ka karan kaɗa miya”.

“Ku yi haƙuri Hajiya ƙurciya ce ke damun Zainab ina da tabbacin za ta daina da yardar Allah”.

“Ai shi kenan Allah ya taimaka kai da ka ɗauko wa kan ka sai ka yi ta fama” shiru ya yi ya kuma rasa me zai ce. Sallama ya yi masu tare da fita da Jafar ƙaramin ɗan Yaya Laila ya bashi sayayyar da ya yi masu.  Gida ya je ya samu har sun kwanta “yau kuma baccin wuri za a yi”.

“Sanyi a ke sosai yau wallahi” ta yi maganar ta na yin hamma. “To a yi bacci lafiya sai da safe” tashi ta yi ta zauna ta na faɗin “yau mun je mun ga amarya”

“Madallah hankali sai ya kwanta an ga abin da a ke so a gani ko” ya faɗa ya na miƙewa tsaye “humm! Hakan ma za ka faɗa, wai yari… Ɗa ga mata hannu “na ji komai haƙuri kawai zan iya ba ku. Ba na son jin wata maganar” yasa kai ya fita, taɓi baki ta yi tare da komawa ta kwanta “hum iska na wahalar da mai kayan kara.”

Bayan ya yi pakeng maigadi ya zo ya na yi masa sannu da zuwa, “sannu da zuwa Alhaji” hannu ya miƙa masa su ka yi musabaha “yawwa Malam Mudi fatan ku na lafiya”, “Lafiya lau”. “Madallah hakan a ke so, babu wata matsala dai ko?”

“A’a ba komai lafiya lau” fito da ledojin da ya shi go da su ya yi ya ba maigadi ɗaya ya karɓa ya na godiya tare da barin wajan ya na she wa Alhaji albarka.  Kamar yadda ya zata ɗin hakan ya samu ba kowa a falon ya ajiye ledar a kan sentr tebur ya je ƙofar ɗakin Zainab ga mamakin sa ya na tura ƙofar ya samu a buɗe shi ga ya yi ya ga wayam ba kowa zama ya yi gefen gado ya na kiran sunanta “Zainab, Zainab! Zainab!!” Shiru tashi ya yi ya ɗan tura ƙofar banɗaki ba kowa gabansa ne ya bada dum! Fitowa ya yi ya dudduba ko ina bai ganta ba zama ya yi falo a kan kujera ya riƙi kansa ‘kar dai yarinyar nan guduwa ta yi?’ ya yi tambayar a zuciyarsa “Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un!” Kamar wanda a ka tsikara da allura ya miƙe tsaye ya nufi harabar gidan har zai tafi wajan mai gadi ya ji waƙa can bayan gidan hakan yasa ya nufi baya ya na zuwa ya tarar ta na wankin tufafinta ta na bin waƙar Kawo ɗan sarki. Ajiyar zuciya ya yi kafin da ga bisani ya ƙara sa wajan ta ya tsaya da ga bayanta ta na shanya zanen da ta ɗauraye.

“Wanki cikin dare?” Ta juyo a tsorace ganin sa a tsaye yasa ta saukar da ajiyar zuciya ta ɗaure fuska tamau ta juyawa ta ci gaba da shanyar. “Me yasa  ba za ki faɗa mini ki na buƙatar wanki ba a kai wajan masu wanki”.

Shiru ta masa takwankwahi hannun rigar sa ya yi ya dauƙa ya na ɗauraye na cikin roba komai ba ta ce da shi ba har su ka gama shanya  ya zubar da ruwan tare da haɗa robibin waje ɗaya ya na faɗin “da ga yanzu idan ki ka tara wanki ki mini magana a kawai masu wanki” wayarta ta ɗauka ta yi wuce warta. Bin bayanta ya yi ya na mai saukar da ajiyar zuciya ƙofar ɗaki ya sameta ta na shirin shiga ɗaki

“Zainab me yasa ki ka karya alƙawarin da ki ka yi mini”.

“Alƙawari? Wani alƙawarin na yi ma ka?” Ta masa tambayar ta na juyowa ta masa ƙuru da idanu. “Me ki ka yi wa baƙin da suka zo?”

“Me su ka ce da kai na masu?” Jan numfashi ya yi ya furzar “shi kenan ji ki ki kwanta fatan dai kin ci abinci?” Ta juya ta na buɗe ƙofa ta ce. “Ai ko ba ka ce ba dama kwanciyar zan yi, na ci ko banci ba damuwar ka ko ta wa”  murmushi ya yi ta shige tare da rufo ƙofar juyawa ya yi zuwa sashin sa a ransa ya na faɗin ‘lamarin Zainab ya fara karyar mini da zuciya anya za ta sauya kamar yadda na ke tsammani kuwa.?’

Hakan kawai yau ta ji ta na sha’awar yin lalle “bari na je na kira Hansa’u idan ta san in da a ke sayar da lalle ta sayo mini har yanka” ta yi maganar ta na miƙewa tsaye ta jiyo muryarsa ya na ƙwala mata kira tsaki ta yi a ranta ta na faɗin ‘ana ce sarkin mararssa zuciya number ɗaya a rashin zuciya an shi go’

“Zainab! Zainab kina ina ne”? Fitowa ta yi daga uwar ɗakin tana yatsina fuska ta ce. “Ga ni miye kake wani yi min kiran mafarauta”? Murmushi yayi  ya na faɗin “Allah ya ba ki haƙuri mai tagwayen suna, yanzu dai taimaka kizo mu je ɗakina kiga wani abun” kawar da kanta tayi gefe tana shan ƙamshi “ko miye nuna mini a nan ɗin”.

“Haba ki dai zo ki gani Please” ya yi maganar cikin magiya, “ba fa inda zani” ya kai hannunsa ya janyo mata hannu ta fizge da ƙarfi tana faɗin “wallahi na faɗama ka daina gigin taɓa mini jikina”! Ajiyar zuciya ya yi kafin daga bisani ya ce. “Miye dan na taɓa jikin ki ba nawa bane, sadaki fa na biya”.

“Shikenan ka sake taɓani ɗin ka gani!” riƙe kansa yayi cike da damuwa “wai ke miye matsalarki ne Zainab, ke a wajanki abu baya wucewa ne?  Auren mu kusan wata biyar har da ‘yan kai amma kin kasa saduda komai ya wuce” Ya matsa dab da ita zai janyota jikinsa ta yi saurin gaucewa “wallahi idan ka yi gigin sake taɓani zan kashe ka!!”

“Innalillahi wa inna Ilaihi raji’un Zainab kisa ƙanen nawa ne za ki kashe!” Dukansu kallon ƙofar shigowa falon suka yi Hajiya Laila ce take a tsaye bakin ƙofa hannu a gaba tana kallonsu da matuƙar tsoro, cikin tsiwa ta ce. “Eh ɗin idan kuma kina musu ki sa shi gwada hakan” ta murguɗa baki ta juya ta shige ɗaki,  “ai ba tafiya za ki yi ba dawowa za ki yi ki sake faɗan abinda ki ka faɗa marar mutunci marar kunyar banza!” Za ta bi bayanta yayi saurin shan gabanta ya karyar da kai ya na “Aunty Laila Dan Allah ki ƙyaleta ɓacin rai ne kawai da yarinta ya ke damunta”.

“Dalla can ai tun farko ba yanda bamu yi da kai ba a kan kar ka auri yarinyar nan amma baƙin nacinka ya sa ka je ka auro mana ita, yanzu  ga shi nan tana gasa ma aya a hannu, harda ikirarin kisa to wallahi dole mu shigo da hukuma ciki domin a yi wa lamarin tufka”.

“Oh Aunty Laila kema dai kin san faɗa kawai take yi babu yanda za a yi ta aikata”.

“Tunda ta furta tabbas abinda ya ke  zuciyarta ne ta fito da shi fili munafuka fito!” Ta ɗaga ƙafa ya sake shan gabanta yana mata magiya a kan tabar maganar  ya rakata bakin ƙofa ya na faɗin “don Allah kar ki faɗa wa Hajiya maganar nan”.

“Ai kuwa kamar a kunnenta a ka yi, dan ba zan ji ni kaɗai ba dole na samu abokin sheda idan har wani abun ya same ka wallahi ba yarda za mu yi ba”.

“Don Allah don Allah kar ki faɗa mata wannan zancen ke ma kuma ki fitar da maganar a ranki duk abin da ki ka ji faɗa kawai ta ke ba wai har ranta ba ne” shiru ta masa ta juya za ta tafi “dan Isar Annabi (S. A.W) kar ki ɗaga maganar nan”.

“(S.A.W) uhm! Shi kenan na ji ba zan faɗa mata ba”

“Na gode.” Duk abinda suke faɗa tana jikin ƙofa tana sauraronsu tana jin fitar ta tayiwa ƙofarta key ta je ta kwanta zuciyarta na mata suya, ba ƙaramin haushin Alhaji Umar take ji ba mutum sai shigen naci zuciya kuwa kamar kare ya canye, mtsw!” Tsayawa ya yi da ga bakin ƙofar ya na fadin “dama albishir ɗin da zan ma ki jam ne na kawo ma ki a kan maganar karatun ki. Ga shi nan na ajiye ma ki a kan kujera idan kin fito ki cika” kira ya shi go wayarsa ya ɗaga  “hello Alhaji Bashir don Allah ka yi haƙuri wallahi wani uzurin ne yasa sam na manta da za ka zo, ka jirani yanzu ina dawowa office ɗin In Sha Allah.”

Ta na jin fitarsa ta fito cikin murna ta ɗauka kiran Raliya ta yi a waya ringing ɗaya zuwa biyu ta ɗaga “Amarya a gidan Alhaji Umar”. “Mtsw! Ke fa banza ce wallahi ni har kin ɓata mini rai wallahi, sai anjma”
“Yi haƙuri kar ki kashe don Allah na daina”.

“Mtsw! Dama albishir na kira na ma ki kin ga Form a hannuna zan ciki makaranta zan koma”.

“Kai gaskiya na yi ma ki murna wallahi, ni ma dai zuwa zan yi na matsa wa Baba har ya amince na koma”
“Eh wallahi ki matsa masa kin ga idan kin samu gurbin karatu a ABU kawai sai ki dawo mu zauna tare”
“Lallai ba ki da kai gwaɗaigwadai da ni na zo gidan matar aure na zauna shi kuma mijin na ki fa” tsinki kiran ta yi ta na yin tsaki ita Raliya ba a taɓa yin magana da ita ba tare da ta ɓata wa mutum rai ba. Ta yi maganar a zuciyarta ta na duba form ɗin.

Ci gaban labari…

“AlhamdulilLah ta farfaɗo mun mata allurar bacci dan ta samu ta huta” Dr. Mansur ya yi maganar cikin farin ciki, Dsp Mashkur ya ce. “Yanzu ke nan za ku iya ba mu ita zuwa gobe?”

“A’a gaskiya ya kamata a barta ta huta ƙwarin jikinta ya dawo sannan a ba ta sallama, bayan hakan ma a kwai wani abun da na ke zargi ta na ɗauki da shi amma dai za a yi auni auni dan tabbatar wa” cewar Dar Hafiz  da fitowar sa kenan da ga ɗakin da a ka kwantar da ita. “shi kenan za mu bar ‘yan sanda uku da za su kula da ita”

“Ba damuwa” Dr Hafiz ya yi maganar tare da shi gewa ta gefensa ya wuce zuwa office ɗin sa. “DSP da za ku barta ni zan kula da ita, sannan ya kamata a ce an kira iyayenta sun zauna da ita”

“Ba zai yu ba Dr Mansur matsala ce  fa na kisan kai dole ‘yansanda za su tsaya kanta gudun kar ta yi yunƙurun guduwa ko sake aikata wani abu kwatankwacin wanda ta yi. Maganar iyayenta ma duka ba zai yu ba” ajiyar zuciya Dr Mansur ya yi ya shiga ɗakin ya na barin wajan Dsp ya ce da ‘yansanda da su ke tare da shi “ku sanya idanu sosai a kanta da kuma masu shige da fice a cikin ɗakin kun ji dai abin da na faɗa ma ku ko?”

“Sir In Sha Allah za mu kula” ɗayan ya faɗa ya na sara masa.

Idanu ya zuba mata tausayin ta ya ke ji matuƙar ya na ji a ransa da da yadda zai yi tabbas da ya kuɓutar da ita da ga wannan hukuncin wayarsa ta yi ƙara ya duba tare da ɗaga wa. “ki yi haƙuri yanzu zan dawo In Sha Allah” ya tsinki kiran ya juya ya fita ya ƙara jajjada wa nus su kula da ita sosai.

Zaune ta ke a kan tabarma ta yi tagumi sai kuka ta ke duk ta rame shigowa ɗakin ya yi ya zauna gefenta idanunsa a kanta ya ce. “Kukan nan ba zai ma ki maganin damuwar ki ba, kamar yadda ba zai taɓa sauya ƙaddarar mu ba. Addu’a ita kaɗai ce mafitar mu a ɗan wannan taƙin da mu ke ciki Maryam”
“Malam ko me ya faru da Zainab ku ne SILA da tun farko kun duba maganar ta kun fasa auren nan da duk ba mu kai in da mu ke a yanzu ba” gyaɗa kansa ya yi ya na faɗin  “na amince ɗin mu ne SILA amma ki daina cire kan ki a cikin mu domin ke ɗin uwa ce da idan kin so tabbas za ki sa ta so abu ko taƙi abu, da a ce kin nuna mata illar da rashin biyayya ta ke haifar wa  da ba ta tsinci kanta a wannan mummunan ƙarshe ba. Sai ki goye bayanta a kan ta kwaye wa umurni na baya, kin ga ko me ye dai idan ta yi taliyun taliyun ke ɗin ce dai SILA”.

Tashi ta yi tsaye ta na faɗin “hakan ka ke faɗa a koyaushe ka kasa yarda da kai da dangin ka ku ne Silar faruwar komai. Wallahi Allah sai ya sa ka mata kun cutar da mu saboda son zuciya irin na ku!” Ta shi ge ɗaki ta na kuka mai cin rai. Ɗakin sa ya shi ga zuciyarsa babu daɗi ya rasa da me zai kira al’amarin shin silar kafiyarsa ce ko silar ta ta kafiyar ne ya janyo faruwar abin da ya faru.?

<< Su Ne Sila 9Su Ne Sila 11 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×