Gidan mai unguwa suka nufa, a tsakar gida suka sami mutan gidan bayan sun gaisa Uwar gidan ta ce. “Mairamu yau ke ce a gidan namu da daren nan”.
“Wallahi kuwa, mun zo wajan mai unguwa ne”
“To bari a a faɗa ma shi, Hanne faɗa ma shi ya na da baƙi” Hanne amaryar mai unguwa da take zaune daga bakin ƙofarta ta amsa da to tare da tashi ta shiga ɗaki. A na ta hidima Allah ya sanya alkhairi In Sha Allah gobe mu na nan shigowa”.
“Uhm Allah ya kaimu”.
“To amin” tare suka fito da Hanne ya zauna a kan shimfiɗar da yara suke zaune suna wasa, “ma za ku tashi ku tafi ɗakin iyayenku kun dame mutane da hayaniya!” Babban ya ja sauran yaran suka nufi ɗakin uwar gidan.
“Ina wuni ranka ya daɗi?”
“Lafiya lau, aka ce ku na nema na”.
Gyara zamanta ta yi ta na fadi haka ne ranka ya daɗi, dama na kawo maka kukenmu ne a kan auren ‘yata Zainab” ta yi shiru,
“Na’am, ke nake sauraro”.
“Magana ta gaskiya auren nan da za a ɗaura a gobe sam ba ta so daga ni har ita mun yi iya ƙoƙarinmu dan fahimtar da shi mahaifinta da ‘yan’uwa shi da suke so abun amma sam sunƙi fahimta sun dage lallai ko ba ta so sai anyi.
Ni kuma ina jin tsoro kar a lalata rayuwar yarinya ko ma tabi duniya a sanadin wannan auren dole shi ya sa na ce bari na kawo zancen gabanka ko Allah zai sa a dace ya ji maganarka a fasa”.
“SubhanalLah shi kuwa me ya kai shi yin wannan ɗanyin hukuncin, ai an daina irin wannan auren yanzu” ta na gyaɗa kai ta na faɗin “A to ni ma dai abinda na ga ni kenan ina ta ƙoƙarin nuna ma shi amma sam ya ƙi fahimta ya rufe idanun shi na rasa dalilin yin hakan daɗa ko kuɗin mutumin nan yake jansu daga shi har masu ruwa da tsakin a auren oho”.
“Kar ki damu tunda har kika kawo maganar nan a gabana da yardar Allah ba za a yi wannan auren ba. Kai Hamza ka na ina ne!?”
“Na’am ga ni nan zuwa!” Ya amsa kiran daga cikin ɗaki tare da fitowa da sauri, “ga ni Baba”.
“Ka je gidan Malam Umaru gidansu wannan” ya nuna su Mama kafin daga bisani ya ci gaba da faɗin “ka ce ina kiran shi” har ya fara tafiya ya ce.
“Dawo bari na aiki sarkin faɗa” ya faɗa tare da miƙewa tsaye yana gyara babbar rigarshi” gara a aika babba dan ya san ba da wasa a ke ba, ku jira ya zo.” Bayan fitar shi Zainab ta yi ƙasa da murya “anya Baba zai yarda ya janye maganar nan gobe ne fa ɗauren auren?”
“Dolen shi ya yarda ai ba fin ƙarfin hukuma ya yi ba” ajiyar zuciya ta yi ta na faɗin “da na ji daɗi wallahi ji nake kamar zuciyata za ta fashe saboda baƙin ciki”
“Ki kwantar da hankalinki kamar yadda na yi maki alƙawai ba zan taɓa bari a yi wannan auren ba tunda har ba kya so, dan haka ki sanya wa zuciyarki natsuwa kin ji ko?” Gyaɗa kai kawai ta yi dan wata irin fargaba da tsoro take ji.
Zaune suke a gaban mai unguwa ya gama sauraren dukan bayanan da a ka kora ma shi ya kalle gefen da su Zainab suke a zaune fuskarsa a turɓune, ya gyaɗa kai kawai tare da mayar da duban shi ga Mai unguwa “tabbas ranka ya daɗi duk abinda a ka faɗa gaskiya ne, sai dai daga ni har kai mun san cewa musulunci ya ba uba damar zaɓawa ‘yar shi miji matuƙar ya yarda da nagartar shi. Dan haka da wannan na yi duba na kuma zaɓa mata wanda nake ganin ya dace da ita”.
“Eh musulunci ya ba ka wannan damar, amma kuma ai ba a ce ka yi mata auren dole ba. Domin shi aure na mutum biyu ne matuƙar ɗaya ba ya so to babu amfanin a yi domin tamkar ka yi gini ne babu fandishon mai inganci ka ga kuwa ai ba zai yi ƙarko ba, to haka auren da ba a gina shi kan so ba ya ke. Dan haka a hukumance auren nan mun hana a yi shi ka ƙyale yarinya ta kawo zaɓinta idan har kuma ka ce lallai sai an yi wannan auren tabbas za mu sanya hukuma a ciki”.
Jan numfashi ya yi ya furzar da ƙarfi, zuba ma shi idanu ta yi a ranta ta na faɗin ‘ya Allah ka sa kar ya ƙi amincewa idan har bai amince ba shi kenan tawa ta ƙare!’
“Kai muke saurare”
“Na fahimta zan yi magana da Iyayena in Sha Allah”
“Wannan umurni ne ba wai neman shawara ba”
“A gafarceni ranka ya daɗi yarinyar nan fa ‘yata ce sannan babu wata hukuma da ta taɓa zuwa ko da da sau ɗaya ne ta taimaki ni tunda ga cin ta tufatar da ita da kuma shanta, iliminta, uwa uba lafiyarta. To kuma yanzu sai a ce za a nuna mini fin ƙarfi a kan abinda ni nake da iko da shi hakan daidai ne?”
Ya yunƙuro zai yi magana a fusace liman ya yi saurin taran numfashin shi ta hanyar yi ma shi raɗa ta yadda ba kowa ne zai ji ba “Ranka ya daɗi a bi komai a sannu, ya na da gaskiya domin musulunci ya ba shi duk wani ƙarfin iko a kanta. Irin wannan nasiha ce kawai za a masa idan ya ɗauka kan shi idan kuma bai ɗauka ba kan shi an dai fita haƙƙin maƙota”.
Ya gyaɗa kai cike da gamsuwa ya kallesu ya na faɗin “shi kenan Malam Umar mun yarda ‘ya taka ce ikon ka ce amma ina mai baka shawara da kar ka yi wa ‘yarka wannan auren tunda har ta ce ba ta so to ka yi haƙuri ka duba lamarin ko dan goben ‘yarka”.
“Na gode Ranka ya daɗi da har ka fahimcini, zan duba In Sha Allah. Zan iya tafiya?”
“Haba Ranka ya daɗi mun kawo kuken mu ne a gabanka saboda mu na da sa ran za ka share mana hawaye”.
“Ku yi haƙuri ni dai iya abin da zan iya kenan. ku je ku yi haƙuri da duk hukuncin da ya yi wannan ruwan shi” jan hannun Zainab ta yi suka tafi rai a ɓace ta na kuka “Mama kawai ni ki barni na gudu na shiga duniya!” Mari ta kai mata ta na faɗin “kin yi hauka ne? Ni kike faɗawa za ki bi duniya? To maza ji ki tunda kin raina ƙoƙarina ki je tunda so kike baƙin ciki ya kasheni!”
Rungumeta ta yi “ki yi haƙuri na rasa tunanina ne gaba ɗaya na rasa me ya kamata na yi. Na gama fahimtar Baba ba zai taɓa sauya hukuncin shi ba”.
“Ki daina kuka ko da a ce an ɗaura auren ai daga uban naki har shi sarkin nacin ba su isa su sa ki zauna da shi ba. Dan haka mu je gida mu jira hukuncin da zai yi daga nan mu kuma sai mu yi namu” ciki da gamsuwa ta bi bayanta suka tafi, ya zo ta gabansu ya wuce ba tare da ya ce da su komai ba.
“Amma dai an yi mutanen banza yanzu so kike ki nuna bai isa da ‘yarsa ba ko me kike so ki nuna?” Hararata ta yi kamar idanunta za su zazzage ta kai mata ranƙwashi ta na faɗin “za ki daina kallona da waɗan nan idanun naki masu kama da na mujiya sakarya banza, kin biye wa uwarki ku na neman ku kunyata ubanki saboda rashin tunani wallahi ki bi duniya a sannu Zainabu!”
“Ƙyale su Iya ba dai ni suke neman su tozarta ba da son nuna wa duniya ban isa da su ba ai shi kenan ku j… Saurin taran numfashin shi ta yi ta na faɗin “kamar ya Yaya shi kenan kana nufin za ka yarda ne a fasa auren?” Cewar Ƙanwar shi. “Uhm! To ya zan yi tun da har kuka ga sun fara da hakan tabbas ko auren a ka yi ba za su bari a zauna lafiya ba” ya nuna su da ɗan yatsa “Maryam ki je na saki ki saki ɗaya, ke ma ki bi uwarki sai ta nema maki wani uban wanda ya fi ni.”
Wani irin shokin ta ji ta yi saranda ta na kallon shi domin sakin ya zo ma ta a ba zata. “Ni ka saka Malam saki?”
“Haifar shi kika yi ne da ba zai rabu dake ba. Ai ke ɗin ba matar zama ba ce tunda har ba ki zama matar rufin asiri ba ki na neman tozarta shi. Wallahi ka yi mini daidai Allah ya yi maka albarka” Baba Haladu wanda tunda a ka fara maganar bai ce komai ba sai kallonsu da yake, ya yi ajiyar zuciya kafin daga bisani ya fara magana da nuna ɓacin rai “wannan hukuncin ya mini daidai sai dai tabbas aure babu fashi dan ba za ta tozarta mu a idanun duniya ba. Idan har an yi auren ki kashi shi ko ki kashi kanki shi ne za mu tabbar da kina ƙin shi!”
“Wayyo Baba don Allah ka yi haƙuri wallahi na tuba ka yafe mini ka mayar da auren Mama don Allah Baba” tashi ta yi idanunta na zubar da hawaye duk da ƙoƙarin hana su zubowar da take sai dai ta gagara hana su zuba, “ni ka saka saboda ƙoƙarin ƙwatar ‘yancin ‘yarmu tsawon shekaru tun aurenmu da kai ko yaji ban taɓa yi ba sai yau da girmana za ka yi mini sakin wukaƙanci a gaban ‘yata da munafukai ko. Na gode”
Ta juya za ta tafi Zainab ta riƙita ta na kuka “wallahi ba za ki tafi ki barni ba, don Allah kar ki tafi Mama” Muhsin da yake tsaye daga ƙofar shigowa wanda zuwan shi kenan jakar hannun shi ta subaci ƙasa
“Saki, Baba sakin Mama ka yi?” Ya yi tambayar da matuƙar kiɗima, tafiya ta yi da sauri ta rungume shi “Yaya ka ga ni ko Baba da ‘yan’uwa shi sun tsanemu ba sa sonmu burinsu su tarwatsa rayuwarmu” kallon mamaki da zargi yake yi wa mahaifin shi.