Skip to content
Part 8 of 11 in the Series Su Ne Sila by Aisha Abdullahi Yabo

Babban Yayan Mahaifin Zainab ya shigo yana waya, ya tsaya daga bayan Muhusin bayan ya gama ya kalle Muhusin da har yanzu yake yi wa mahaifinsa kallon zargi, “kai meye ka zo ka tsaya a hanya kamar wani dogari?” Muhusin ya janye daga kan hanya ransa a matuƙar ɓaci. “Ku kuma lafiya na ga duk kunyi cirko-cirko?” Ɗaya daga cikin ‘yan’uwa ta masa bayanin abinda ya faru, cikin mamaki ya kalle Baba “wannan wani irin shirme ne da shashanci Umar?” Baba ya sunkuyar da kansa ƙasa yana huce har yanzu wani irin zafi yake ji a ransa dan ji yake duk da sakin da yayi bai huci daga baƙin cikin tozarcin da sukai masa ba.

Bayan ya samu waje ya zauna ya umurce Muhusin da su Zainab su zauna, Mama ta kafe a kan ba za ta zauna ba “ni fa ba zaman da zan yi dama aure ne ya zaunar da ni yanzu kuma babu banga kuma me zan zauna nayi ba”

“Maryam in har ina da darajar da zance ki yi abu ki yi to na roƙe ki da ki zauna mu yi magana” tana huce ta zauna daga gefe, Zainab na jikinta har yanzu kukan take sai dai marar sauti.

“Dukanku kunyi kuskure ke Maryam babu dalilin da zai sa ki kafe a kan Umaru ba zai aurar da ‘yarsa ga wanda ya so ba, domin ya fi ki iko da ita, sannan wanda ya fitar a matsayin zaɓinsa ba mutum ne mai mugun hali ba, da a ce zaɓin da yayi mata ba mutumin kirki ba ne tabbas da kina da ikon da za ki yi tsayin dakan ganin ba a yi auren ba.

Amma yanzu ba ki da wata hujja da zai sa ki ce lallai ba za a yi auren nan ba, wanda ko musulunci ya ba shi damar zaɓa wa budurwar ‘yarsa miji”

“Amma kuma ai musulunci bai ce a yi wa yarinya dole ba ko?” Mama ta karɓi zancen nasa tana huce, “tunda har a ka bai wa uba damar ya zaɓa mata miji ai ba a wani bambanta tana so ko bata so ba. Kawai dai idan a ka bi maslahar rayuwa da kuma wani ɓangare na shari’a za a iya cewa auren dole ba shi da fa’id a addinan ce da kuma al’adance gudun kar sanadin hakan yasa yarinya ta faɗa cikin halaka na fushin Ubangiji da kuma rayuwa”

“Ai dai maganata ta fito kenan, yarinya ta ce bata so saboda me da shi da iyayensa za su tilasta ta auren nasa, saboda kwaɗayen abin hannunsa su je su jefa rayuwar yarinya a masifa”

“Ahir ɗinki Maryam karki nemi ki ci mutuncin mu daga ni har Yaya Haladu mun fi ƙarfin ki kiramu da ma su son abin duniya. Ko me muke yi ba saboda goben ‘yarki tayi kyau muka yi ba”
“Ki yi haƙuri Gwaggo Hari don Allah kiyi shiru ki daina maganar”.


“Bar ni da ita Mansur raina mutane tayi ai, sannan har da shi da ya bata fuska shi yasa har ta samu damar yi mana rashin mutunci”

“Ni Allah ya gani ban yi wannan haɗin dan kawo fitina a tsakaninmu ba, nayi duba da nagartarsa ne, sannan sai da na tabbatar da ba ta da tsayayye sannan na kawo zancensa. Idan har bata son shi to ta kawo wanda take so a yi da shi, amma dai aure babu fashi a gobe da yardar Ubangiji” Baba Haladu ya yi maganar ransa a matuƙar ɓace.

“Ni babu wanda nake so, kuma ai ban ce na tashi aure ba bare a tilastani yinsa a sanda ban s… Marin da Yaya Muhusin ya yi mata ne yasa ta saurin haɗiye sauran zancen ba tare da ta shirya wa hakan ba, ta dafi kunci tana kuka “shashar banza marar kunya, a she ko me ya faru ke ce kika yi silar faruwarsa. So kike ki tozarta mahafinmu a idanun duniya kenan ko me?

“Ya isa haka Muhusin, ke Zainab kina da wanda kike so?”

Tana kuka ta ce. “A’a, ni ba na kula kuwa”

“Tunda hakan ne kinga sai dai kiyi haƙuri da zaben da a kai maki, da a ce tun farko na san da wannan badaƙalar da ba a kai ga hakan ba sai a warwareta, to ni ba wanda ya faɗa mini ba kya so, dan haka sai kuyi haƙuri tunda ba zaiyu an tara jama’a gobe ɗauren aure ba a ce an fasa, mun zama ƙananun mutane kenan”.

Ihun kuka tasa tana birgima “wallahi ni bana sonsa in har a kayi auren nan sai na kashe shi na kashi kaina wallahi Allah!” Muhusin ya zaro bel ɗin wandonsa ya yi kanta Mama ta riƙi tana masa masifa

“Karka kuskura ka dakar mini yarinya, wannan shi ake kira a dukeka kuma a hanaka kuka. Kai ko takaici ba ka ji irin tozarcin da a ka yi mini da masifar da suka jefa ƙanwarka ba ka yi wato goyon bayansu ma kake!” Tsayawa ya yi yana huce yana hararar Zainab.

Murmushin takaici Baba Mansur yayi “Muhusin koma ka zauna. Umaru ka mayar da aurenka yanzun nan kuma”
“Kayi haƙuri Yaya am… Ya tari numfashinsa “bana son jin komai ka mayar da aurenka na ce, wannan tunanin na banza ne, shekarar da shekaru kuna zaune lafiya ba a taɓa jin kanku ba sai yanzu da girma ya zo maku za ku ce ku rabu saboda auren ‘yarku wacce kuka fara rayuwa tun kan kusan za ku haifeta. Shirmen banza kenan!”

“In dai a kan auren nan ne ni wallahi na bar shi har abada bana buƙatar auren!” Mama tayi maganar tana huce. Ransa a ɓace ya ce. “Na janye sakin da nayi maki na mayar da auren” daga nan ya miƙe ya bar gidan, da kyar Baba Hamisu ya Sha kan Mama ta yarda ta zauna.

Zainab yadda taga rana hakan taga dare, kwana tayi kuka da tunanin irin matakin da za ta ɗauka matuƙar a ka ɗaura wannan auren. Tana ji a ranta me yasa tun farko bata yi tunanin guduwa Kano wajan Yayan Mahaifinta ba tunda ga shi da bakinsa ya faɗa da ya san da maganar ba zai bari a yi auren ba.

*****

Washe gari da ƙarfe goma na safe a ka ɗaura aure, wanda ya samu halartar dubban jama’a. Farin ciki a wajan ango baya misiltuwa bakinsa har baka. Yayinda a marya take ta ihu da burgima Mama tayi lallashi har ta rasa abin cewa ta zuba mata idanu, ita ma lokaci-lokaci tana share hawayen da yake kan fuskarta.

Shigowar Yaya Muhusin ne da taga da gaske dukan nata zai yi sannan ta ja baki tayi shiru ta dawo kukan zuci da ajiyar zuciya. Raliya da take gefe itama ta ci kuka sosai saboda tausayin halin da Zainab take ciki, cikin muryar kuka ta ce.

“Zainab ki tashi kiyi wanka don Allah, kinga mutane suna ta shigowa kuma kusan wasu tsegumi ne yake kawo su, don Allah ki shirya kiyi haƙuri ki mayar da komai ba komai ba tunda har an riga da an ɗaura”

“Ba zan yi ba, idan kuma za ki sani dole ne sai na ga ni!!” Shiru tayi da taga abun na ta ba na ƙarewa ba ne tashi tayi ta bar gidan dan bata ga amfanin zaman nata ba tunda kafiya tayi wa Zainab yawa.

Ana yin azahar a ka zo ɗaukar amarya. Gwaggo Hari ta shigo ɗakin tare da Ƙanwar Baba, “Hassana ki shiryata Babanta Hamisu na waje yana jiranta ya ce shi ne zai kaita tunda abun ya zo da hakan ba wanda zai ji gudun kar wata fitinar ta biyu bayan tafiyar”

“To Gwaggo ana kai amarya ba tare da danginta ba, kamar ba ‘yar dangi ba?”
“A to baƙin halinta ne ya janyo mata ai, ba sai ta je ita kaɗai ba kamar ƙoƙon masaki a lahira ba. Idan kin zauna lafiya da mijinki kiji daɗi idan kuma kika yi masa rashin mutunci ke ce za ki wahala kuma kishiya ce da ke ta samu abun dariya”

Zainab ta shige jikin Mama ta yi masu banza. Cikin lallashi Inna Hassana ta ce. “Yi haƙuri ‘yata tashi ki shirya kin ji. Idan har kika yi biyayya watarana za ki ji dadi za kuma kiyi farin ciki” tsaki Zainab ta ja wanda har yasa Inna Hassana fito da idanu waje cikin mamaki “ni kike yi wa tsaki Zainab?”
“Fin hakan ma ai sai tayi maki tunda ta sha a nono” cewar Gwaggo Hari.

“Kun ga dai na zuba maku idanu tun jiyan nan baku sake jin bakina ba ko, to don Allah ko me za ku yi karku sake saka sunana a ciki don Allah. Mama tayi maganar tare da janye Zainab daga jikinta ta fita daga ɗakin, Zainab za ta bi bayanta Inna Hassana ta ce. “Bari na sa a kira mini Muhusin yanzu ya lallasa mana jikinki tunda mu kin raina mu!”

Fizgar kayan hannun Inna Hassana tayi ta jefar a kan gado tana cire na jikinta, “hakan za ki sa ba za kiyi wanka ba?” “Eh!”

“Allah ya baki sa’a” cewar Inna.

Ruƙayya ta je gidansu Raliya ta samu tana uwar ɗaki kwance zazzaɓi ya rufe ta. Zama tayi gefenta “wai ba dai kema taya Zainab damuwar kike ba” tashi tayi ta zauna cikin damuwa “Zainab na ba ni tausayi gaba ɗaya ta sauya sai ina ji ina ma ina da iko da ba za a ɗaura auren nan ba”

“Uhm! Ni kuma wallahi haushi take bani domin kafiyarta tayi yawa, amma ba laifinta ba ne har da mamanta da take ɗaure mata gindi”

“Allah dai ya kyauta kawai. Allah kuma ya sassauta zuciyarta ta zauna lafiya da mijinta”

“Uhm! To amin dai, na zo nayi maki sallama ne yau za mu tafi gida” “A’a ba sai an kai amarya ba?’

“A’a Baban Kano ya ce kowa ya tafi gida shi ne zai kaita da kansa”

“Allah sarki Zainab, to Allah ya tsare hanya. Sai mun yi waya”

“Amin. Saduwar alkhairi.”

*****
Da ƙyar aka cireta jikin Mama a ka kaita mota tana ihun kuka, an je kaita wajan Baba aka samu baya nan ya fita, wanda kuma hakan ya gujewa dan har yanzu yana jin ɓacin rai a kan abinda sukai masa. Cikin mota Baba Hamisu sai lallashinta yake. “Ki yi haƙuri shi aure muƙaddari ne daga Ubangiji, Allah ya riga da ya nufa shi ne mijinki babu wanda ya isa ya sauya ƙaddarar hakan.

Abu ɗaya nake so dake kiyi haƙuri ku zauna lafiya da mijinki kiyi masa biyayya, ni kuma nayi maki alƙawari idan har kika kwantar da hankalinki komai kike so zan maki shi a duniyar nan matuƙar bai fi ƙarfina ba kinji ko?”

Shiru kawai ta yi masa Allah kaɗai yasan abinda take saƙawa a zuciyarta.

*****

Tun bayan da suka isa ya sadata da ɗakinta, da aka ƙawata da kaya na alfarma masu kyau da tsada a cikin tambatsetsin gidanta da yake Kinkinau Kaduna, wanda komai angon ne ya saya mata ya hana iyayenta sayen ko da cukale. Tana zaune uwar ɗaki gefen gado sai ajiyar zuciya take irin na wanda ya ci kuka har ya godiwa Allah ɗin nan.

Baba Hamisu tare da Alhaji Umar suna zaune falo “to Alhaji Umar ga amanar Zainab nan na danƙa maka don Allah ka kula da ita, ka kuma yi haƙuri da halin da duk za ta nuna maka, har yanzu a kwai ƙurciya a tare da ita, idan kayi haƙuri watarana komai zai zama labari da yardar Allah”
“In Sha Allah Baba za ku sameni mutum mai riƙi amana da kuma haƙuri fiye da yadda kuke tunani, fatana dai ku cigaba da yi mana addu’a”

“In Sha Allah. Allah ya baku zaman lafiya da zuri’a ɗayyaba, Allah kuma yayi maku albarka”

“Amin. Mun gode Allah ya ƙara lafiya da girma.”

Bayan tafiyar Baba ya shiga ɗakinsa jim kaɗan ya fito yana riki da leda ya nufi ɗakin da yake mallakin Zainab. Har yanzu tana nan inda Baba ya Barta. “Amarsu ta ango ba kya laifi ko da kin taɓa ɗan masu gida. Yayi mayafin da yake kanta tayi ta ja dogon tsaki da tofa masa yawo a riga, kallon rigar yayi kafin daga bisani ya ɗago ya kalleta da murmushi a fuskarsa “fatan kina lafiya?”

“Mtsw! Aikin banza, ita dai zuciya an bawa kare ya canye!!” Ya ajiye ledar da take hannunsa dab da ƙafafunta tayi saurin janye ƙafafun ta ɗora a kan gado tare da koma wa tsakiyar gado ta zauna tana harararsa. “Ko na kawo maki a kan gadon ne? Abinci ne da abin sha na san baki ci komai ba saboda hidima” rufe kannuwanta tayi da hannayenta tare da rufe idanunta tana ihu “ni ka dameni ko ka fita ko ni na fita na bar maka gidan gaba ɗaya!!”

“Allah ya baki haƙuri, zan tafi amma don Allah ki taimaka ki ci abincin kafin ki kwanta kin ji ko?” Yayi maganar cikin sanyin murya tare da barin ɗakin jiki a sanyaye kamar wanda ƙwai ya fashewa a ciki. Yana fita ta je tasa wa ƙofar key ta dawo ta kwanta tana ci gaba da zubar da hawaye. Dare ya raba bacci ya ƙaurace wa idanunta yunwa ta ƙwanƙwasa mata ƙofa yayin da hanjin dake cikinta suke ta ƙoge suna neman abincinsu. Da yake yunwa ba a yi mata Lahaula babu shiri ta sauko daga kan gado ta janyo ledar da ya ajiye mata ta buɗe, kaji ne guda biyu, sai Holandia da furar Rufauda. Taci naman da Holandia sai da ta ji tayi nat sannan ta ture ledar gefe tayi tsaki tare da yin tagumi tana zancen zuci.

‘Oh ni Zainab yanzu da na kama naci naman nan idan kuma magani ya sanya a ciki fa?’ Ta sake yin tsaki a karo na ba adadi, ta miƙe tana kakaren amai ta nufi wani ɗaki da take tunanin banɗaki ne, ai kuwa shi ɗinne, taita ƙoƙarin amayar da abinda ta ci hakan ya faskara, ta jingina jikin ƙofar banɗakin tana mayar da numfashi, “koma da magani ne wallahi na fi ƙarfinsa ba zai taɓa kamani ba” tayi maganar ciki da jin gamsuwa da hakan.

*****
Washegari sallah asuba kawai ta idar ta koma ta kwanta wani nannauyan bacci ya sake yin awon gaba da ita, saboda rashin isasshen baccin da bata samu tayi a daren jiya ba. Wurarin ƙarfe goma ya sake zuwa ya ƙwanƙwasa ƙofar shiru babu ko alamar motsi a cikin ɗakin, hankalinsa ya tashi Allah dai yasa ba wani abun ya samu ‘yar mutane ba, wannan ne karo na uku da yake zuwa yana ƙwanƙwasa mata amma shiru, sake ƙwanƙwasa ƙofar yayi jim kaɗan ta zo ta buɗe idanunta ciki da bacci ta manna masa harara tana jan tsaki ta ce.

“Mene ne ka zo ka wani takura mini ka hanani bacci?”

“Kibyi haƙuri, ina so ne na fita ga shi kuma banga tashinki ba shi yasa. Fatan kin tashi lafiya?”

“Da ban tashi lafiya ba za ka ganni ne!?”

“Ki je kiyi wanka idan kin idar abin karin kumallonki na a kan dani. Ki kularmini da kanki kinji” ya yi maganar fuskarsa da murmushi ta sake jan tsaki tare da koma wa ciki ta rufo ƙofar da ƙarfe tare da sa key ta rufe. Gyaɗa kansa kawai yayi yana murmushi ya bar wajan.

Kusan sati biyu kenan da kawota tun washegarin kawota bai sake sanyata a idanunsa ba, bata fitowa har sai idan ta ji tashin motarsa alamar ya fita kenan, sannan za ta fito, tana da ‘yar aiki Hansa’u, yarinya ce da ba za ta wuce shekara 15 ba daga ƙauye a ka kawota, ita take gyara gidan ta yi masu girki, sai Musa wanda yake gyaran harabar gidan da kuma gadinar gidan, sai Baba Mai Gadi. Zainab iya taci ta kwanta bata aikin fari bare na baƙi.

Idan ta ji motarsa ta shige ta rufe ƙofa. Duk sanda ya shigo gidan a wajan Hansa’u yake jin yadda ta wuni. Tun bayan da a ka cika sati ɗaya ya koma ɗaya gidan uwar gidansa. Ya raba masu kwana idan ran girkin Zainab ne zai zo ya kwana a gidan idan gari ya waye ya fita wajan aiki, ranar girkin uwar gida idan ya zo ya koma can.

Bai taɓa yarda ya bada ƙofar da za a fahimci irin zaman da suke ba.

*****
Tana zaune falo suna fira da Hansa’u wacce ta zama abokiyar firarta, tana bata labarin abinda wani ƴaƴanta yayi.

“Ai Aunty har yanzu ban ga matsoraci kamar Yaya Sani ba, akwai fa ranar da yana tafiya zai je gona kawai yaga yara suna gudu sun fito ta wajan rafi ba kawai shima sai ya arci na kare ba yabi bayansu da gudu, ana Sani lafiya lafiya ina ko ji bai yi ba bare har ya tsaya sai ga ni yayi sun tsaya, ɗayan yana haki yana faɗin yee! Na riga ka, dama na faɗama na fika gudu ka gani ni nayi na ɗaya”

“To fa ya yayi da ya ga hakan?” Zainab tayi tambayar tana dariya, “ya kuwa yayi bayan dukan su da yayi da ƙyar aka ƙwace su a hannunsa” ta gyara zamanta tana ci gaba da bata labari “ranar kuma da dare ya shiga banɗaki a ka jiyo ihunsa duk mutanen gida aka fito ana tambayarsa lafiya, har maƙota sai da suka shigo gidanmu ga shi irin gida ne babba na family.

Ihu yake yana faɗin ataimaka masa maciji zai kashe shi. Baffa ne yayi ƙarfin halin shiga banɗakin yana haska banɗakin da fitilar hannu. Kin san me a ka gani?”

Ta gyaɗa kai “a’a ke nake saurare dai”
“Hum! Ba komai ba ne baƙar leda ce cikin ruwa ta huro iska shi ne fa yana gani ya tsandara ihu ya daka tsalle tare da riƙi wani kataku da yake sama haɗi da kwanon da a ka yi wa banɗakin rumfa. Baffa yayi tsaki ya ce to sauko ka mayar da wandon jikinka leda ce sakarai kawai kana abu kamar ba namiji ba wannan ai ko mace ba za tayi abinda kake yi ba, ya dinga yi masa faɗa”

“Kai Innalillahi Hansa’u wannan Yayan naki a kwai abin dariya SubhanalLah leda baƙa ce maciji!?” Tana magana tana dariya. Fira ta ɗauke masu hankali sam basu ji shigowarsa ba, cikin sanɗa ya ƙarasa shigowa ya zauna a ɗaya kujerar da take wajan ƙofa ya ciro wayarsa yana yi mata video, yana murmushi ji yake kamar su tabbata a hakan yana ganin wannan farin cikin a fuskarta.
Hansa’u ce ta ankara da shi za tayi magana yasa hannu akan laɓɓansa yana girgiza mata kai alamar kar tayi magana, tayi shiru tare da sunkuyar da kanta ƙasa.

Hakan kawai ta ji a jikinta kallonta ake hakan yasa ta tsagaita da dariyar tare da waiwayo wa tana yin tozale da shi ta haɗiye ɗan sauran fara’ar dake a kan fuskarta kamar wacce bata taɓa yin dariya ba ta kawar da kanta gefe.

“Ina wuni Alhaji?”

“Lafiya lau Hansa’u fatan kuna lafiya?” Yayi mata tambayar yana mai ajiye wayar gefensa, “lafiya lau” tana bashi amsa ta tafi. Tasuwa yayi ya dawo kujerar da take a zaune ya zauna dab da ita har jikinsu na gogan juna.

Ta yunƙura ta tashi ya janyota jikinsa ya rungume ya saukar da wata nannauyan ajiyar zuciya, ji tayi kamar an zuba mata roshin wuta a jikinta. Ƙoƙarin ƙwatar jikinta take daga gareshi hakan ya faskara ya kai bakinsa saitin kunnenta zai yi magana nan ta samu sa’ar kai bakinta a ƙirjinsa ta kafa masa haƙora bai san sanda yayi wata ‘yar ƙara ba saboda azabar da ya ji ta shige shi

<< Su Ne Sila 7Su Ne Sila 9 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×