Skip to content
Part 5 of 5 in the Series Ta Ki Aure by Fatima Abubakar Saje (Ummu Adam)

Rayuwa kenan, bayan wata huɗu da mutuwan auren Ƙawwama sai ita kuma Sawwama ta samu mijin aure wato Malam Mukhtar, anyi biki normal babu hayaniya babu almabazzaranci.

Cikin farin ciki amarya ta tare gidanta!

Malam Mukhtar mutumin kirki ne kuma mahaifiyar shi ma haka, ya taɓa aure amma matar ta rasu ta bar ‘yarta mai suna Zainab mai kimanin shekara uku. Maman Mukhtar shi kaɗai ta haifa hakan yasa take matuƙar ƙaunarsa kuma take son Sawwama kamar ‘yar cikinta.

Kamar a mafarki Ƙawwama tayi aure kuma har auren ya zo ƙarshe. Haƙiƙa damuwar da ta shiga yafi na kafin aurenta da Jalil domin yanzu ko ina ta shiga sai taji ana itace wacce ta auri matsafin nan, wasu ma su ce ai mijinta neman mata yakeyi, wasu suce ai itama cutar ce da ita yanzu kam wa zai aure ta bayan ga can tsohon mijin nata yanata jinyar ajali komai sai ammasa ga dukiya amma ta kasa sayan lafiya.

*****
Ƙawwama ta kaiwa yayarta ziyara ina ta sameta a parlour zaune tare da mijinta suna hira suna wasa da dariya. Bayan shigar Ƙawwama sai suka gaisa da Malam Mukhtar sannan ya tashi ya tafi masallaci dan yayi tilawa kuma ya basu guri su sake.

Gidan Sawwama bai wuce ɗaya cikin uku ba idan an kwatanta da girman gidan Ƙawwama amma sam baza’a haɗasu ba wajen samun farin cikin zuciya da nitsuwa da kuma kwanciyar hankali.

Bayan sun shiga ɗaki suna tattaunawa sai Ƙawwama take cewa,

“Zaman gidan sam babu daɗi yaya gashi kema kinyi aure.” Sawwama ta ce

“Allah sarki my dear kada ki damu, kuma ina fatan ki samu miji mai hankali da addini ki aura kema ki tafi gidanki, dan koni lokacin da ba kya gida naji irin haka amma dake ina zuwa islamiya da makarantar koyon ɗinki hakan ya taimkamun sosai wajen ɗebe kewa.”

“Hm, yaya kenan, wa zai aure ni bayan kowa gani yake ina da HIV kawai nima islamiyan zan shiga nayita hadda.”

Sawwama ta ce, “Haba Ƙawwama ai Allah ya san lafiyar ki ƙalau kuma muma munsani dan haka ki yawaita addu’a kawai.”

“To yaya, gaskiya kina jin daɗin ki, watanni biyar kawai da aurenki amma kinyi fari kinyi ƙiba kinata sheƙi ga wani murmushi da kikeyi mai cike da annuri,..”

“Kawwama sarkin iya zance, gaskiyar ki dan a iya wata biyar da nayi a gidan Noorul Qalbie ji nake kamar banyi zaman kaɗaici ba duk wata damuwa da baƙin ciki da ƙunci da jurewa zolayar mutane da tsangwamar dangi da wulaƙancin ƙawaye kamar ba a yi ba duk na manta.

Sannan kuma ganin murmushin fuskar masoyi kaɗai ta isa gusar da dukkan damuwar zuciya, na jima ina ƙaunar Malam Mukhtar saboda addinin sa da kuma kyawawan ɗabi’un sa, ga shi da kyau. Ƙawwama bana gajiya da kallonsa sannan idan yana magana bana gajiya ƙosawa da jin kalaman sa. Shauƙin soyayyar sa ta kanyiwa zuciyata tasiri ko da ace baya kusa da ni gashi mutum ne mai ƙoƙarin yiwa matune umarni da alkairin da kuma hani da sharri, ina matukar kaunarsa.”

Ƙawwama ta ce “Masha Allah gaskiya yaya kina cikin Aljannar duniya!”

“Hmm ai sai ma kinganmu muna buɗa baki in mun kai azumi, watarana in nace bazan yi ba sai ya ce, “ke da sunanki Sawwama (mai yawan azumi) ai ke ya kamata kina sani yin azumin ma, ko in muna sallar dare ko tilawar Alqur’ani sai na jini a sabuwar duniya. Yanzu fa innaje halqa ba karatunda yake bani wahala dan ko wani littafi da ake karantawa a can yana koyamun a gida har nima nakan koyama wasu. Gashi ya iya rarrashi yadda kika san ‘yar shekara sha takwas haka yake tarairayata a gidan nan gaskiya Alhamdulillah ina cikin ni’imar duniya abunda ya rage mun shine na duƙufa wajen neman Aljanna!”

Ƙawwama ta ce, “Allah sarki na miki murna yaya Sawwama. Haƙika ba auren wuri ne aure ba, auren wanda ya dace shine aure.  Suna tsaka da magana sai taji saƙon waya ya shigo mata, tana dubawa taga Amir ne yana sanar da ita rasuwar yayan shi kuma tsohon mijinta wato Jalil!”

Nan take Sawwama ta sanar da mijinta a waya yazo da sauri ya kaisu gida suka ɗau Mama da Malam suka wuce gurin jana’iza.
Hajiya tana cikin alhinin rashin babban ɗanta, sannan kuma rasuwarsa ya dawo mata da rasuwar mahaifinsa sabo kamar yanzu akai.

Tabbas Jalil ya yi nadama kuma ya tuba sannan kafin ya fara jinya ya yanke alaƙa tsakaninsa da bokaye sannan ya yi ta ƙoƙarin yin aikin alkairi dan ya gyara kuskurensa.

Abunda ya rage shine a masa addu’a da fatan Allah ya karɓi tubansa. 

*****
Bayan wata shida da ‘yan kwanaki Amir da Hajiya da Alhaji Adamu suka kawo ziyara ta musamman gidansu Ƙawwama, sun kai kaman minti biyar suna tattaunawa akan rayuwa sannan daga bisani suka faɗi dalilin zuwansu, wanda ba komai bane face neman suren Ƙawwama ga dansu Amir!
Allahu akbar, Allah maji roƙon bawansa kuma duk wanda ya dogara ga Allah to haƙiƙa Allah ya ishe shi.

Tabbas Alƙawarin Allah gaskiya ne dukkan tsanani yana tare da sauki.

Alhamdulillah nan shine ƙarshen wannan littafin mai suna “Taƙi aure”
amma ba auren taƙi ba tana jiran wanda ya dace ne.

Allah yasa mu amfana kuma mu dace baki ɗaya dani da ku da dukkan ɗaukacin al’umar musulmi.

Da wannan nake so naja hankalin ‘yan uwana mata da su kwantar da hankalisu su yiwa Allah biyayya wajen bin dokokinsa da kuma suturce jikinsu ta hanyar yin shigar da ta dace da koyarwar addinin musulunci.

Bayyana kwalliyar ki da tsiraicinki zai nesantaki daga mutanen kirki domin duk mutumin kirki mai hankali bazai so ya sai abincinda ƙuda da ƙura suke yawo akai ba.

Sannan kuma kisani a duniya kowa da ƙaddarar sa, ba kowane Allah ya kaddara masa aure a cikin rayuwar sa ba. Abunda yake waji a kanki shine ki bautawa Allah kuma ki nemi yardar sa. Allah ya azurta ta mata da mazajen kirki, suma mazan haka.

Amin thumma amin.

*****

All my stories are free to read. If you willingly want to help, then here is my account details: 0091869462; Fatima Abubakar Saje; Access Bank.

<< Ta Ki Aure 4

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.