Skip to content

Ta ki Aure | Babi Na Biyu

4
(1)

<< Previous

Ba shakka shawarar da Sawwama ta bayar shine daidai to amma bayan ta faɗawa mahaifiyarsu sai mama ta nuna sam kada su faɗawa kowa abunda ke faruwa kamar dai yanda ta ƙi da farko, Sawwama tayi ƙoƙarin fahimtar da mama dan a samu a ceto auren ƙanwar ta kuma a kare ta daga faɗawa sharrin shaiɗan, cikin fushi mama tace “wai ke sawwama mai yake damunki ne yarinya ta yi aure ta samu mutumin kirki amma kin dage sai kin haifar da matsala idan haushin auren nata ki ke ji ke mai ya hanaki yin auren? To bari kiji idan kika kuskura ki ka faɗawa kawunku ko baffanku abunda ke faruwa sai na kwashe miki albarka tin da ke bakisan ciwon kanki ba. Kuma in banda ma shegantaka irin na yaran zamani da datake gidan ba tayi haƙuri ba sai yanzu ne bazata iya ba!

“Haba Mama mai yayi zafi ne haka harda maganar kwashe albarka dan Allah kiyi haƙuri kinsan bana san ɓacin ranki, dama gani nayi tana cikin damuwa shiyasa nace ko za’a sa manya cikin maganar dan aji ta bakin jalil ɗin in ma baida lafiya ne sai a samo magani.”

“Rufe mun baki sarkin tsari ke gaki marar kunya, yanzu a ce mutum kamar Jalil ne baida lafiya in ba hassada ba da baƙin ciki kuma in ma da gaske ne baida lafiyan so kike magauta da dangi suyi mana dariya ace muna murna mun aurar da ‘ya ashe gidan mace muka kai ta?”

“Ba haka nake nufi ba mama kuma bazanso kuji kunya ba.”

“To in ko hakane kada na sake jin wannan maganar daga bakinki kuma ko da wasa kada ki sake ki faɗawa mahaifinku dan nasan zai goyi bayanki da zarar kinyi masa daɗin baki zai amince ni ko baki isa ba ina cikin daula da arziki kice zaki fiddani dubi ki ga har gida ya canza mana ya bawa mahaifinku jari yanzu duk bikin da na shiga gurin zamana daban kowa na bani girma ko kishiyata tasan nafi ƙarfinta dan haka ki je ki faɗawa Kawwama tayi haƙuri ta zauna gidan mijinta abunda ta rasa a can ɗin in ta dawo gidan ma ba samu zatayi ba.”

Sawwama ta ce,

“To shikenan Mama amma dan Allah ki sata a addu’a Allah ya kawo ƙarshen matsalan nan,”

Mama tace, “Amin, je ki ki ɗumama mun kazar jiya ki haɗo da lemo.” Sawwama tace, “To mama…”

Jikin Sawwama yayi matuƙar sanyi harma take tinanin ta ina zata fara faɗawa Kawwama abunda Mama tace,

“Dan Allah Yaya ki faɗamun me yake faruwa kinyi magana da Baffan kuwa…?”

“Kiyi haƙuri my sister amma na kasa samo miki mafita dan Mama haryanzu taƙi yarda a faɗawa kowa maganan nan.”

“Na shiga uku yanzu ya zanyi yaya?”

Matsanancin kukan da Kawwama keyi ya ɗagawa Sawwama hankali matuƙa.

“Yi shiru Kawwama kuka ba shine magani ba addu’a zakiyi kinsan kowa da ƙaddarar sa na rayuwa kuma wataƙila shagulgulan bikin ki ma yana daga cikin abunda yasa Allah ya jarabceki dan gaskiya kun taka dokokin Allah sosai kinyi watsi da shawarata kin biyewa ƙawaye dan haka ki yawaita istigfari da salatin annabi sannan kada ki manta da sadaka kuma kamar yadda sunanki ya nuna Kawwama (mai yawan sallar dare) ya kamata ki lizimci sallar dare wallahi ba wata matsala da zaki nufeta da waɗannan ayyuka face ya zamto alkairi kuma in sha Allahu komai zai zama labari. Sannan kuma malam Mukhtar ya ganni cikin damuwa a islamiya sai yake tambayata meya faru sai na faɗa masa shine yake cewa babu laifi idan kika naimi audio na wa’azi musamman wanda ke magana akan hakkokin ma’aurata kika sa lokacin da yake gida dan yaji ko Allah zaisa a dace”

“Hmm, Yaya Sawwama shima hakan nayi amma kinsan me yace mun?”

“A’a sai kin faɗa.”

“Idan zaki canza gara ki caza dan wannan wa’azin naki ba zai taɓa canzani ba hasalima baƙin jini zai ƙara miki a guri na.”

“Subahanallahi to gaskiya dolene musan abun yi amma for now ki ci gaba da addu’a kamar yadda nace, sai dai kuma mai zai hana ki faɗawa alwalinsa abunda ke faruwa tinda ni Mama ta hanani na faɗawa baffan.”

“To yaya in sha Allahu zanyi yanda ki ka ce, ina ma ace banyi auren nan ba da yanzu ina cikin kwanciyar hankali sannan kuma ina gida cikin dangina.”

“Kiyi haƙuri my sister, ya baton soyayyar Amir?

“Kullum ƙaruwa ya keyi a raina gaskiya Yaya badan tsoron Allah ba, ba abunda zai hanani kusantar Amir!”

“Subahanallahi haba my sister kada na sake jin kin faɗi haka sai kace ba musulma ba kin san girman laifin zina da bala’insa kuwa ballantana ace kina da aure, kada na sake jin wannan maganar daga bakinki.”

“Astagfirullaha wa atubu ilaihi, kiyi haƙuri ba zan ƙara faɗa ba.”

Bayan sawwama ta ɗan numfasa sai ta kama hannun Kawwama cikin sanyin murya tace,

“My dear, i know how you feel but we can’t do anything about it. Na san yanda zafin sha’awa yake musamman idan kana kusa da wanda kake so dan haka ba laifin ki bane sannan ita soyayya wani lokacin bata da kan gado ba ruwanta da hali ko yanayin da mutum ke ciki sannan bata la’akari da cancanta ko akasin haka, sai dai a mafi yawan lokuta ita soyayya takanyi tasiri a bisa yanayin alaƙan mutum da irin yanda ya zaɓi rayuwarsa ya kasance ma’na idan kika zama ta kirki sai ki so mutanen kirki haka ma akasinsa sai dai a matsayinmu na musulmai dole ne mu yiwa zuciyar mu linzami dan kada ta kaimu ta baro…”

“… Wato Kawwama babu wani ƙuncin rayuwa da zai sa ki bada kanki ga namijinda bai biya sadakinki an ɗaura muku aure ba domin ko a zamanin jahiliyya ‘ya bata bayyana jikinta kuma bata zina dan haka ko da wasa kada ki bari hannun wani ya kai gareki koda kuwa hakan zai sa ki rasa rayuwarki. Mace ko bata tsare mutuncinta dan kishin kanta ba ai tayi ko dan mahaliccinta wanda Ya yita alhalin jiya bata nan, Ya samar da ita lokacin tana cikin rauni sannan Ya azurta ta da iyaye guda biyu ya yalwata arzikin su dan ɗaukar ɗawainiyar ta. Ya lulluɓeta da gata tsakanin danginta ya bata babbar ni’imar samun addininsa, Ya ɗaukaka darajatta na kasancewa cikin al’umar manzon rahama (S.A.W). Ya damƙa amanar ta ga mahaifinta, wanta, mijinta da kuma yaranta. Babu shakka idan ki kai zina kinci amanar Allah da manzonsa kuma kinci amanar addinin musulunci kazalika iyayenki, mijinki da yaranki nan gaba sannan kin tozarta kanki kuma kin saka alkairi da sharri kuma kin butulcewa ni’imar Allah daya baki dan duk wani saɓon Allah da akeyi a ban ƙasa ana yi ne da abunda Allah ya bamu a matsayin ni’imar da zamuyi amfani da shi wajen bauta masa. Kuma abunda nake so da ke kada ki kuskura ki naimi maganin matsalarki ta hanyar saɓon Allah dan koda ace matsalar ta kau to kinjefa kanki cikin wacce tafi ta baya kuma duk wacce tayi zina dan maslahar sha’awa to tana shiga tsananin nadama da danasani har ƙarshen rayuwata kazalia shima namijin haka, kuma kinsan hukunci rajamu (jefewa) ne ga dukkan wacce ta/ya ke da aure yayi zina ko ace sun taɓa aure.”

“Na sani Yaya Sawwama kawai na faɗa ne saboda stress.”

“Na fahimceki my dear Allah ya fidda ke daga wannan damuwar.” Kawwama tace,

“Amin.”

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×