Skip to content

Ta Ki Aure | Babi Na Hudu

4
(2)

<< Previous

Da ƙyar Jalil ya buɗe baki cikin tsananin kunya yace Hajiya nima abunda ya faru ba’a so na bane, kuma nima abun yana damuna amma ba yadda zanyi ne!

Hajiya ta ce, “Karka rai na mun hankali kaji ko. Domin idan ka bari rai na ya ɓaci zaka iya rasa albarka ka gaba ɗaya!”

Alhaji adamu ƙanin mahaifin Jalil ya ce, “Hajiya abi a sannu dolensa yayi bayani dan duk nan ba abokin wasan sa. Kai Jalil za kai bayani ko kuwa? Dan ni kaina idan kai wasa zan cire babban rigar tawa na maka dukan tsiya kuma na haɗaka da ‘yan sanda daga nan mu wuce koto alƙali ya karɓa mata hakkinta ta.”

Da jin haka sai Jalil ya tsorata ya ce, “Dama wani malami na ne yace mun in dai ina so na samu takarar kujeran gwamna da zan tashi nan gaba kuma na samu riba mai yawa a kasuwanci na to sai nayi aure cikin sati uku kuma in nayi auren kada na kusanci matar har sai bayan shekara huɗu, amma zan iya kasancewa da wata macen daban in dai ba aurenta na yi ba. Ni kuma na amince da sharaɗin, shiyasa bantaɓa kusantar ta ba daga bisani ma sai na ƙaurace mata na koma ɗayan gidana dake unguwar tamu sai lokaci bayan lokaci nake zuwa mata. Allah ya gani tayi ta ƙoƙarin fahimtar dani akan hakkinta amm na rufe idanu na toshe kunne na ƙi ji, kuma ni kaina nasan na zalunceta nasha jinta tana kuka wanda hakan yasa na koma gun malamin nawa amma sai yace mun in har na yadda na karya doka to zata iya mutuwa dan aikin ya yi nisa.”

“Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un,” Yanzu ashe Jalil duk abunda nake faɗamaka game da tsoron Allah baya shiga zuciyar ka?”

Zazzafar hawaye ne suka fara zuba daga idanunta, ta ce, “Ka cuce ni kuma ka cuci kanka! Wai ace ɗana ne yake zuwa gurin boka kuma har kake kiransa malam kai jahilin ina ne?”

Alhaji adamu ya ce,”Ni harma na rasa mai zance wai ace mutum kamarka da iliminka da arzikinka da wayonka da dabararka ace wani baƙauye wanda ko brush baya yi ƙazami kuma maƙarya ci ya mai da kai tamkar raƙumi da akala sai yanda ya yi da kai?”

Kuma in banda wauta irin naka mai makon kayita istikhara ka naimi zaɓin Allah shi ne ka tafi wajen mushiriki kuma ka yadda da shi kabar Alqur’ani da sunna!
Wallahi ka bani mamaki kuma ka bani kunya ji be ka, ka wani sha hula kamar mutumin arziki!”

Hajiya ta ce, “Ka ga illan rashin neman ilimin addini ko? Kullum nai maka magana sai ka ce in sha Allah zaka fara, dama ta yaya mutum zai zama na ƙwarai ya inganta imaninsa ba tare da neman ilimi ba? Allah wadaran na ka ya lallace!”

Amir ya ce, “Gaskiya yaya ka bani kunya ban taɓa zaton haka daga gare ka ba.
Allah ya baka arziki sannan ya baka matar arziki maimakon kayi masa godiya sai ka tafi wajen yi masa shirka. Na sha ganin anty cikin damuwa amma in na tambayeta sai ta ce ba komai harma na fara tayata hira ina koya mata karatun computer amma dan gudun kada shaƙuwar ta yi yawa da kuma gujewa sharrin shaiɗan sai na daina zuwa gidan sosai  kuma zan iya rantsewa da kamun kan anty Kawwama kullum cikin hijabi amma kai kana can kana wulaƙanta ta!”

Mama ta ce, “To shikkenan dai yanzu ba amfanin tone-tone tinda wa’adin aikin shekara huɗu ne ai abun yazo gaf dan haka ni ina ganin gwara a sasanta su koma gida kunga shikkenan matsala tazo ƙarshe.”

Cikin fusata Malam ya ce, “Ashe baki da hankali ban sani ba? To ina miki rantsuwa ko Ƙawwama tana sansa baza ta koma gidansa ba sai dai bayan raina! kuma kema in ki kai wasa sai naki auren yazo ƙarshe!”

Hajiya ta ce, “Abun bai kai ga haka ba, kuma ni kaina ban goyi bayan ta zauna da Jalil ba.”

Jalil ya ce “Hajiya a yi haƙuri nima ba zance ta koma gidana ba, dan nayi gwaji kuma likitoci sun tabbatar min ina ɗauke da wannan cuta mai karya garkuwar jiki! Haƙiƙa na yi nadama kuma ina naiman afuwa a gurinku baki ɗaya!”

Bayan ya durƙusa gabanta yana kuka ya ce, “Ƙawwama na sake ki saki ɗaya. Allah ya ba ki miji na gari ba iri na ba.

Kawwama ta ce, “Babu shakka ka cutar da ni ka aure ni ka wulaƙanta ni sannan daga bisani ka sake ni! Ka mai dani ƙaramar bazawara! Amma kamar yadda nake fata Allah ya sa naci wannan jarrabawar, kai kuma Allah ya shiryeka yasa ka gane gaskiya.”

Jalil ya ce, “Ki ƙara haƙuri nasan na cutar da ke amma gashi Allah ya saka miki, dan Allah ki yafe mun ko zan samu sauki!”

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×