Kasata
01.
Da sunan Rabbi Sarkina, Yau zan waƙe ƙasata
Al-Ƙaliƙu gwanina, kai ka wanzar da ƙasata
Al-Maliku shugabana, kai ke iko da ƙasata
Al-Azizu Ubangijina, kai ne mai biyan buƙata.
02.
Gani zan fara batuna, kan matsalar ƙasata
Kai min lamuni a batuna, ƙarya ka da na furta
Ka shige mini lamarina, ka biyan dukkan buƙata
Albarkacinsa wannan da Ka aiko da bauta.
03.
Yau an wayi gari, babu lafiya a ƙasata
Ko ina in ka duba, rikici ne a ƙasata
Tashin hankula, ya karaɗe dukka ƙasata,
Wayyo ni Ya Allah, Ka yo ɗauki ga ƙasata.
04.
Yau zinace-zince, ake ta yi a ƙasata
Yau luwaɗi ake yi, da Maɗigo a ƙasata,
A yau giya da kayan maye, ko ina a ƙasata
Rayuka ake kisa, kamar fari a ƙasata.
05.
Ga cin hanci rashawa, sun yi yawa a ƙasata
Babu ko lantarkin kirki, in ka duba a ƙasata
Harkar ilimi ta rushe, sai alfarma a ƙasata
Taimake mu ya Karimu, Ka yi ɗauki wa ƙasata.
06.
Kai ba ko hanyar kirki, dudduba a ƙasata
Mun zamo kaza a akurki, amma a ƙasata
Allahu ka yi mana canji, da gyara a ƙasata
In wayi gari da rana, in ga son juna a ƙasata.
07.
Idan na farka daga kwana, in ga zaman lafiya a ƙasata
In na shiga gari, in ga lumana a ƙasata
Idan na kunna TV, in ga nasara a ƙasata,
Idan na kunna rediyo in ji murna a ƙasata.
08.
Ga titi fetal, ko’ina haske a ƙasata
Jama’a kowa na annushuwa a ƙasata
Baƙi na zaryar shigowa cikin ƙasata
Da kuwa zan yi murna da ƙasata.