Wane Ne?
01.
Bismillah Sarki mai iko, Ilahu ne,
Da sunanKa sarki mai sama, Rabbu ne,
Gatanmu Kai ɗai ne Allah, babu wani,
Kai ke da ikon komai, Al-Musawwiru kai ne gwani.
02.
Wanene ne zana fara da shi, in ba Allahu ba?
Wanene ne ake fara komai da sunan shi, in ba Allahu ba?
Wenene Sahibul ƙalbi, in ba Annabi ba?
Wanene Sahibul sabri, in ba Allahu ba?
03.
Wanene ke saukar da ruwa, in ba Allahu ba?
Wanene ke ciyar da mu, in ba Allahu ba?
Wanene ke yi mana suturata, in ba Allahu ba?
Wanene ke raya, da kashewa ba Allahu ba?
04.
To in hakane ku jama’a, ko baku jini ba?
Wanene za mu kama da gaskiya, ba Allahu ba?
Wanene za mu yi wa biyayya, in ba Allahu ba?
Wanene za mu roƙa, in ba Allahu ba?
05.
To wanene matsalar mu ne, ku faɗa mu ji,
Wanene ke gajiyar da mu, ku faɗi kowa ya ji,
A ina ake samun matsala, ku fito mu ji,
Sauran bayanin namu ne, kuma za mu ji.
06.
A cikin ita wannan rayuwar, ku tsaya ku ji,
Wanda duk ya kama Allah, da Annabi,
Ya wuce fagen bauta ace wai, yau ya gaji,
Kuma ko me Annabi ya ce, Lallai kuwa to za ya bi.
07.
Idan muka kama Allah, zai yi mana agaji,
Da zarar mun bar Allah, za mu faɗa garari,
Mu yi ta wahala, da shan azaba muna gunji,
Ga makoma babu tabbas, cikin kabari.
08.
Mu saki kowa mu kama Allah, kun ji ‘yan uwa,
Mu zam neman sani, Ilimin Allah da na rayuwa,
Mu bi Manzonmu, Mijin Khadija ba mu faɗuwa,
Malam duk mun sani, sai dai kawai mantuwa.
09.
Allahu Shi ɗai za mu riƙe, bai guje mu ba,
Manzon mu shi zamu riƙe, mu samu ci gaba,
Addinin mu ɗai za mu riƙe, mu samu martaba,
Komai na nan cikin duniya, bai kai shi ba.
10.
Allahu sarki mai iko, Ka shirye mu dai,
Ka zamo gata gare mu, ka sa mu cikin yardarKa,
Ka sa Annabi ya cece mu, a gabanKa,
Mu cika da imani, bisa addininKa.