Skip to content
Part 28 of 58 in the Series Tana Kasa Tana Dabo by Hadiza Gidan Iko

Matsalar da Farida ta Kira mishi ita ta Kara Rikita shi ya sake Jin wata damuwa ta musamman tare da fargaba Wanda Suka Saka shi Jin ana wurwura shi ana Shirin makawa da k’asa.

Tun da ta Ambata mishi shigar Mai gemu cikin Al Amarin su yaji tashin hankali marar misali. Ba don komai ba kuwa sai tsabar kishin Farida da yake ji a zuciyar shi na irin son da Mai gemu yakewa Farida Wanda ya tabbatar da ko Farida tana Gidan shi idan Mai gemu yaso cutar shi sai ya nemi Farida. To idan Akwai Wani tashin Hankali da yake ciki wannan ne.

Wannan Al Amarin ne ya haifar mishi da zazzabi Mai zafi har ya Kwana cikin fita hayyaci tafiyar da ba a samu yin ta a Ranar ba saboda Babu lafiya sai washe gari ya lallaba don zuciyar sai fada mishi take ba a bori da Sanyin jiki don haka suka dauko hanya shi da Mustafa Wanda ya yarda zai karbi Auren KISAN WUTAR da Sameer ya sanar dashi ya Kuma fada mishi ladar kudin da zai bashi.

Yaya Dauda ya iso garin katsina Yana Zaune a gaban haj suna gaisawa bayan tambayar shi iyali da Aiki ya amsa da Duka suna lafiya ya Dora da Abinda ya kawo shi.

“Hajiya Abdullahi Yakubu ya same ni da wata Magana ni Kuma nace mishi sai na zo na same ki na fada Miki yadda kika ce haka za ayi.
Mun Hadu da shi a satin da nazo har Yana tambaya ta Farida ni Kuma na fada mishi tana gida Auren ta ya mutu.

Ashe bawan Allah Nan har yanzu Yana layin da ya ke shine yazo ya same ta sukayi magana

“Kwarai kuwa yazo hakikatan ni ma Kuma Bai boye min ba ya Sanar Dani ya dawo nayi musu fatan Alheri to Amma ita Kam bamuyi maganar ba da ita.

“To Alhamdulillah Haj dama Nima Nace sai na zo naji ta Bakin ta duk da yace Farida Bata da Cewa sai Abinda nace Amma ba zanyi Aiki da fadar sa ba sai abinda tace.

“Ba ta da abin cewa dauda sai Wanda ka zartas tunda Kai din a matsayin Uban ta kake ko ni Nan ka yanke Hukunci a Kaina Babu Mai tayar Dashi.

“To Haj Amma aji ta Bakin ta kin San a yanzu ma Shari a ta Bata Damar zabin mijin da take so a matsayin ta na bazawara.

“To tana makaranta dai ka San ta koma makarantar Nan ta tanbihul Islam da zaman kawai gara ko karatun tayi.

Yaya Dauda ya jawo wayar shi ya Kira wayar Farida kara Biyu ta dauka tana Gaishe shi ya Amsa Yana tambayar ta.

“Kunyi magana Abdullahi yakubu? Ya tambaya yana jiran Amsar ta.

“Eh mun yi magana dashi har ya ce yaje wurin ka.

“Ok to shikenan.

Ya katse wayar Yana fadawa Haj yadda suka yi ta ce

“Tunda an yi haka Dauda ka karbi komai na Auren don gaskiya bana son zaryar nan da Sameer yake Mana a gida shi fa shaidan bashi da burki Ina tsoron Wani Abu tunda na kula su Duka an jarrabe su gara kawai ayi gaggawar Auren Shima yaje ya Samu wata ya aura ayi Hak’uri haka da rayuwa.

Tun a nan Yaya Dauda ya Kira wayar Mai gemu Yana fada mishi Abinda Haj tace na Game da Auren.

Mai gemu ya yi murna a Ranar ma sai da aka tsayar da maganar auren su don sai da ya dauko magabatan sa aka tsayar da maganar auren sati mai zuwa.

Yaya Dauda ya koma Kaduna Mai gemu Kuma ya shuga Hidimar auren Farida wacce yake Yi gadan gadan ta hanyar hada Mata lefe da gyaran sashin da zata zauna a gidan nashi Mai sashi uku Daya na Basma sai Biyu Babu kowa don haka ya tashi Aikin gidan gadan gadan.

A Ranar da aka gama tsayar da maganar Aure ce Kuma Sameer da Mustafa suka iso Kaduna gidan Yaya dauda Wanda Basu samu a gidan ba ya taho Nan katsina Dole suka kwana a Kaduna sai zuwa yamma Suka sake komawa Gidan Yaya dauda suka Kuma same shi duk da sun gama tsara komai shiyasa Sameer Bai yarda ya fito ba Amma ya sake jaddada wa Mustafa cewa ya fadawa Yaya dauda cewa shine Wanda yake Neman Auren Farida Kuma sun daidaita har ta Bashi address na Yaya dauda ta Kuma ce yazo ya nemi Auren ta a hannun shi ya Kuma tabbatar wa Yaya dauda ita Farida ce ta turo shi.

Mustafa ya zauna akan hudubar da Sameer ya Dora shi ya Kuma fita a motar ya sallamawa Yaya dauda Wanda ya fito ya same shi har ya sauke shi a falon karbar Bak’i

Bayan sun Gaisa ne Mustafa ya Soma korawa Yaya dauda Dukkan karatun da yayi tarjamar sa Wanda yayi harda Yana biyawa

Yaya Dauda ya zuba mishi ido Yana kallon shi Bai katse shi ba har sai da ya sauka kafin ya Dubi Mustafa Yana Fadin

“Yanzu ita Faridar ce ta turo ka? Ya amsa da hakika.

“To Amma kai Mustafa ai ni ko a labari ban tab’a Jin sunan ka ba bare ace wani ya sanka.

Ni kam ba Katsina nake ba amma akwai kanne na Biyu wa ka sani a cikin su Wanda ya San da zaman ka? Kuma yaushe kuka hadu da ita Faridar da har Zata turo ka wuri na?

Mustafa ya Soma Raba idanu don yaji ana Shirin kure karyar shi . Haka Kuma Bai San kowa na Farida ba ita kanta Faridar sunan ta kawai ya iya sani Amma ba dai fuskar ta ba…

“Gaskiya ne Yaya dauda nayi kuskure Amma bamu jima ba shiyasa ne ban san kowa ba Amma dai Ina ganin su suna shiga gidan Kuma Muna gaisawa dasu.

“To Malam Mustafa kar ma naja ka da Nisa sai dai kayi Hak’uri Amma Farida har kudin sadakin ta an karba Ina ganin kayi latti ne ko Kuma bakaji Abinda ta fada Maka ba wata Kil ba cewa tayi kazo kuyi Aure ba ce Maka tayi ta kusa Aure baka fahimta ba.

“Itace da kanta ta bani wannan Damar har Nan gidan ita ta bani address din ka har da phone number Amma zan same ta sai na fad’a mata Abinda ka fad’a min wata Kil tayi niyar yaudara ta.

“To gara dai ka Gane Hakan Kam malam Mustafa.

Mustafa ya mike yana yiwa Yaya Dauda sallama wanda ya rako shi har inda motar shi take Sameer Yana ciki kasancewar gilashin tinted yasa Yaya dauda Bai iya Ganin waye ba ammma hakikatan yaga inuwar mutum a ciki Amma dai Bai kawo komai a Ranshi ba sukayi sallama Suka wuce

Sameer da yake a zalame da son yaji Yaya Akayi? Ya Dubi Mustafa da yake tuka motar suka dauki hanyar katsina Yana Fadin

“Kayi shiru Mustafa baka ce min komai ba.

“An samu matsala fa Oga.

“Wace irin matsala kuma Musth’afa ? Kar ka ce min ya Hana ka Auren ko ya Gane Abinda muka tsara ne?

“Bai Gane ba Amma dai ya Soma jero min tambayoyin wa na sani a cikin kannen shi Kuma yaushe Muka Hadu da Farida da har za a fara maganar Aure.

“Sai kace Baku jima ba kannen shi Kuma Amadu da Gali zaka ce ai.

“To Ina na San su Oga? Na dai fad’a mishi bamu jima ba Kuma itace ta turo ni.

“Yanzu me yace Maka ne da kake Kiran mini matsala?

“Yace wai har sadakin Farida an karba wai nine banji Abinda ta fad’a min daidai ba.

“Kai ! Ya ishe ka haka Mustafa ka San Abinda kake fada Kuma ? Ya tari Mustafa da wannan tsawar a haukace.

Mustafa ya kusa sakin sitiyarin motar saboda kidima.

“Fatan da kake min kenan Mustafa? Ba dai sadakin Farida ba kaima bakaji Abinda ya fada Maka daidai ba.

Ya fada Yana jawo wayar shi Yana danna lambar Farida Amma inda suke Babu service shiyasa Bai iya Samun ta ba . Sai faman kira yake ana fad’a mishi sai dai ya Kira Lokaci na GABA Amma ya kasa Hak’ura. Babu Abinda zuciyar sa ke fada mishi sai matsala.

Farida ta dana dawowa gida ta iske Yaya dauda Wanda yake ajewa Haj kudin sadakin da Abdullahi ya bayar Wanda kanin mahaifin su baba Yusha U kanin baba iro ya karba ya Kuma tsayar da Ranar daurin Auren

Gaban ta ya sara duk da bata San Abinda ke faruwa ba ta wuce d’aki tana zama tana son ta saurari Abinda Haj da Yaya dauda zasu ce Amma Bata ji komai ba har yayi musu sallama ya wuce.

Tana d’aki taji Haj na kwala mata Kira ta Mike ta fito ta duka a gaban Haj tana kallon kud’in.

“Ga kudin sadakin Nan Abdullahi ya bayar ni ko mantawa yayi da ba budurwa bace ne ya bayar da wadan Nan kudin ? Oho gasu Nan Kuma Sati Mai Zuwa za a Daura Auren ni dama na so ace Bai Kai satin ba don Allah ya sani na gaji da wannan kus kus din da kuke Kuma bana son wata magana ta biyo baya sai ta kinyi Auren ki Shima ya nemi wata can ya Aura Yara Kuma Allah ya raya su.

A Rude Farida take kallon Haj har ta kasa samun Hikimar tambayar Haj.

“Wai Haj sadakin waye?

“Ina ce da Hausa dai nayi Miki maganar Nan ko kuwa sai na juya harshe ne mun koma Wani babin Zaki Gane ? Nace sadakin ki Abdullahi ya kawo an Kuma tsayar da Ranar daurin Auren sati Mai Zuwa Ina ce haka nace ko sai na maimaita Kuma?

A rikice Farida take Duban Haj kafin ta Samu tace.

“Ni fa Haj bance ya kawo sadaki ba Cewa nayi ya bani lokaci Nayi shawara bance na shirya Auren shi a Yanzu ba.

“To Yaya za ayi yanzu? A mayar da kudin ace kin fasa ?.

“Nifa ba Sosai Mutumin Nan yayi min ba Haj duka duka yaushe na gama iddar da za a ce mini Wani Aure?

“To ki dauki kudin ki kaiwa Yusha’u shine wanda ya tsayar da maganar auren sai ki fada mishi Baki Shirya ba ni dai ai Sako aka bani na Kuma isar in yaso ki Kira dauda Wanda har waya naji ya Kira ki Yana tambayar ki kika Amsa mishi Amma da yake kina son Rainawa mutane Hankali ne kike min wannan borin kunyar gara kawai ki fito a Mutum in zaman Kai Zakiyi sai mu sani tunda daga zawarci in an ki Aure sai zaman Kai.

“Don Allah ki fahimce ni Haj nifa ba zan iya Auren Mai Mata ba ko zanyi Aure Haj ba irin Abdullahi nake so ba.

“Ai fa ke magana ta kama ni fa ai duk yadda kike so haka za ayi tashi ki samu Wanda ya yanke Hukunci.

“Bari na Kira Yaya dauda wallahi Ni ai ce mun yayi munyi magana da Abdullahi nace mishi Eh da na San tabbacci yake so ai zan fada mishi gaskiya ne.

Ta Mike tana Kiran wayar Yaya dauda Amma ta kasa samun shi Dole ta Hak’ura Amma Kuma cike take da Tashin hankali ta Yaya Sameer zai tsinci wannan maganar?

Ta koma kan Kiran wayar Sameer Shima kamar hadin Baki wayar tashi a kashe don haka ta wanzu cikin tashin hankali.

Ta juya ga wayar mai gemu Shima tashi wayar a kashe don baya ma kasa Yana can Hado kayan lefen da zai gwangwaje Amarya dasu.

Ta shiga tashin hankali matuka Gaya har ta Rasa Abinda Zatayi don haka ta kwana mafarkin ido biyu.

Da safe ko makaranta bata iya Zuwa ba ta shirya Saddam da Hanan mukhtar ya tafi kaisu ita Kuma ta kasa zuwa don ko taje ba zata iya fahimtar Abinda Ake koyarwa ba.

Tana nan zaune a d’aki abin duniya duk ya ishe ta ko kalaci ta Kasa Yi sai lissafin Dokin Rano har ta fara tunanin ta je ta Samu Baba Yusha’U ta fada mishi ita fa bata ce tana son Abdullahi ba a mayar mishi da kudin shi duk tijarar baba Yusha U dai iyakar shi ya yi tijarar shi karshe dai yace dukan ta Zaiyi to ya jibge ta ya gama Babu Abinda Dukan shi Zaiyi Mata tunda tayi gauri ta rik’a har ta rik’e.

Ta mike da sauri tana Shirin tafiya gidan baba Yusha U tana Shirin fita ne Sameer ya iso Dole maganar zuwa gidan baba Yusha U Tasha Kara

Haj ta ganshi yazo afujajan ya zube Yana gaishe ta Yana Gaishe ta. Ta Amsa tana tambayar shi Aiki

Ya amsa lafiya Lau alhamdulillah ya ajiye Mata tsarebar da ya taho da ita.

Ya shiga dakin Farida yana rungume ta yana fidda kwalla yake Fadin.

“Me yaya Dauda yake fada Farida? Me yake faruwa ne har Yaya dauda yake fadawa Mustafa? Da wa suka karbi sadakin ki Farida? Naji a jiki na matsala na shirin samuna farida tunda kika ce min me Gemu ya shigo cikin Al Amarin Nan.

Itama kwallar take fiddawa tana Rik’e fuskar shi tamkar masu Shirin sumbatar Bakin juna take Fadin.

“Kudin shi ne Suka karba shi da Yaya dauda Sukayi maganar su Babu yawu na tunda kace na sallame shi ma ban Kuma Saka shi idona ba Amma sai Ji nayi wai Yaya dauda ya karbi kudin sadakin.

“Inna lillahi wa Inna ilaihir Raju un Farida Yaya dauda Yana son ganin gawa ta? Me kikayi akan Hakan ? Na tura mishi Mustafa Amma yake fada mishi ya karbi kudin sadakin ki? Kin yarda kenan da Hukuncin da ya yanke? To Rayuwa ta gaba Daya tana Hannun ki Farida idan kika so na Rayu zan Rayu idan Kuma mutuwa kika Zaba min to zan Gode ko Babu komai ke kika Zaba min mutuwa Kuma Zanyi mutuwar shahadar soyayya.

“Ba zan iya karbar auren Abdullahi ba Sameer. Kai kafi kowa Sanin ba zan iya kallon Wani Namiji da sunan Aure ba in ba Kai ba don Haka yanzu ma gidan baba Yusha U zanje nace a mayar mishi da kudin sadakin shi In yaso sai ka tura mishi Mustafa ai Kuna tare da shi ko?

Ya amsa ta hanyar kada kanshi.

Ta Kai Hannu a fuskar shi tana dauke mishi kwallar idon shi da hannun ta.

“Na yi maka alkawarin ni din taka ce kai kadai rayuwa ta tare da taka take Amsa sunan Rayuwa ka San Hakan Kuma Dole ma baba Yusha U ya fahimce ni har aljanun karya Wallahi yau sai na tayar mishi don ya Gane ba zan karbi Wanda Suke nufin bani ba tunda baka son shi Amma da ka barshi cikin Sauki zamuyi komai mu gama Amma tunda Ranka Bai kwanta Dashi ba zan Aure shi ba.

Ya Kara Rungume ta Kam a kirjin shi Yana shakar kamshin da yake fita a jikin ta yaji wata irin nutsuwa da ya manta da ya samu irin ta.

“Na yarda da ke yanzu kije gidan baba Yusha Un in yaso idan kika dawo sai na tura Mustafa ki tabbatar da kin lalata maganar Mai gemu don Wallahi bana son ta Farida matukar akayi Auren Nan da shi ba zai iya kauda idon shi daga kanki ba sai ya taba min ke ni Kuma Abinda zai iya zarar da numfashi na kenan.

Ta zare jikin ta Daga gareshi tana fadin

“Bama zata Kai mu ga haka ba bari naje na dawo zan kira ka idan Na bi baba Yusha U cikin lalama Naga Bai fahimce ni ba zan tashi aljanu ta yadda zai Gane Abin ba karami bane duk fadan sa da tijarar sa na hau aljanu ai Dole a Yi min yadda nake so derling ka Daina damuwa.

Ya Mike Yana fadi “Damuwa Dole ce Amma Naji karfin gwiwa tunda kin bani tabbacci.

Ya fito Yana yiwa Haj bankwana taso tssyar da shi Amma ta kyale shi ya fice.

Farida da ta ga Haj na kallon ta ta Kuma San Karin Bayani take so akan yadda Sukayi idan ta fada mishi maganar auren ta don ta San Dole Sameer yaji Babu Dadi ta Kuma san maganar ce ta kawo shi a Yanzu. Amma Bata ji Farida tace ko uhum ba sai ta kyale ta.

Sai bayan sallar azuhur ne Farida ta Cewa Haj zata je gidan baba Yusha’u, Hajiya ta dube ta tana fadin

“Ba ki ji abinda na ce masa iki ba kenan? To Allah ya baki sa a ai kin san shi ya san ki

Kwalla ta kawo fuskar Farida tana Fadin

“Ni fa Hajiya ban shirya Aure yanzu ba Kuma ko Zanyi ba zan iya Auren Mai Mata ba gaskiya.

“Sai a mayar muku da Auren ke da Sameer na San Hakan kike nufi ko? To Allah ya sa na Gane Akwai hannun mijin ki a cikin Al Amarin Nan don na Fara zargin ku wallahi kus kus din Nan taku akwai munafunci Amma ai karya ke shekara a karya Amma gaskiya na makwafin ta.

Farida taji tsoro da firgici sun kama ta Haj ta Soma farke musu laya? Sai ta karfafi kanta ta fice Zuwa gidan baba Yusha U tana Shirya irin tsoron da zata bashi idan ya kasa fahimtar ta da yaren hausa to zai fahimce da yaren aljanu.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

To Farida bari mu bi ki gidan baba Yusha U muga ko zai fahimce ki da yaren hausa? In Kuma ma da na aljanun ne zamu ga yadda zai fahimta Amma kuwa Bakiyi dabara ba Wallahi ni fa da Zaki yarda ai da nace ki Rabu da Sameer ki tafi ga Mai gemu inda Ake bukatar ki Zaki Fi Daraja Amma kina Nan kina Rashin Daraja har kina Neman zaucewa Amma ai bari ba mu Gani yadda zaku Kare wata Kil kiyi nasara wata Kil kuma ki Fadi 💃😂☘️✨💄🫸🏻🌍🫷🏻💫

<< Tana Kasa Tana Dabo 27Tana Kasa Tana Dabo 29 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×