Skip to content
Part 13 of 75 in the Series Tana Kasa Tana Dabo by Hadiza Gidan Iko

.Gaba Daya wasila taji Duniya tana wurwura ta Domin kuwa ko ta ki Allah karya take tace bataji Wani Abu Mai kama da Rashin daidai akan Abinda tayi ba. Musamman Kuma Cewar ISHAQ ya barta da ALLAH. A hukuma ma idan aka barta da ita ta San Akwai matsala bare Kuma sagir Wanda hawayen shi ya tab’a zuciyar ta matuka Gaya Domin kuwa ta hango ace tata Uwar ce tayi Abinda tayi yaya zata ji? Bare shi Namiji Wanda shine ya ke nuna Asalin kishi a aikace.

Yusra da Zainab Ma suka haska a madubin tunanin ta Wanda Suka kasance mata ne Kuma Yara Wanda Suke matukar a kula da su da tarbiyar su Amma ta watsar Anya kuwa hakkin Baiyi Mata yawa ba ga wannan ga wannan ?

Tayi shiru ta kasa motswa Domin kuwa jikin ta ya mutu hakikatan akan maganganu Guda Biyu na ISHAQ da Kuma na sagir Amma Kuma da muguwar zuciyar ta ta Soma Yi Mata hudubar idan ta samu kudi Dole su bita su Kuma Daina ganin laifin ta

Dole ta wuce d’aki tana Duba alert din kudin da Mai Naira yayi Mata Wanda ta Sha mamaki don Bata zaci zai iya Bata kud’in da ta yanko mishi ba sai ga alert ya shigo har ma da Kari akan Abinda ta nema.

Ta kwana cike da Zullumi Amma ko da gari ya waye Bata yarda ta kunna wayar ta ba sai dai ta barta a kashe don Bata bukatar Wani Kira irin na Mai Naira don Haka ta kashe wayar har k’ura ta k’ara lafawa…..

Mai gemu kuwa Ranar da ya dauki nomber wasila a wayar Mai Naira Yana Barin majalisar ya Soma Kiran wayar wasila Amma a lokacin da ya Kira sai yaji wayar a kashe Saboda Mai Naira ya kashe wayar yace Shima tashi zai kashe ta sai jibi don Haka Mai gemu ya wuni Yana Kiran wayar wasila Amma ko da dimuwa Bai samu lambar ba Kuma ya kasa Hak’ura da kiran kullum sai ya Kira wayar sama da sau Hamsin Amma baya Samun ta

Sai a wanaki na shida ne da samun layin Yana Hawa online yaga hoton wasila da yake kan DP din ta Wanda tayi matukar kyau tamkar wata India Domin kuwa dogon gashin kanta ya sauka a kafadar ta ga Jan lallen da ya kwanta Akan farar fatar ta ya Kuma fito da haibar ta sai Kuma kirjin ta Wanda yake cike da kuma surar ta da ta firgita Mai gemu Wanda ya saki wata Kara da Bakin sa Yana zooming din hoton wasila ya fito Sosai ya Kuma ga Abinda Bai Gani Sosai ba …

“Jar ubbann Nan Kai wai haka matar Nan take Mai Naira Yana Wani Abu a wurin Nan gaske shegen ya like ya kasa sararawa Ashe shi kadai ya San Abinda yake amfana Dashi.

Ya Kai Hannu akan Gemun shi Yana shafawa Yana Jin wani Abu Yana yawo dashi a sama . Ya Zubawa kirjin wasila ido Yana kallo Yana hasaso yadda zaiyi a Nan din.

Ya ya sauka daga Kan DP din ya duba last seen din ta don yaga tana hawa online din ? Sai kawai ya Ganta a online din

Da Wani irin sauri ya koma Yana Mata Kiran Vedio call na WhatsApp don Yana son Ganin ta a zahiri.

Wasila da sai a yau ne ta Samu kunna wayar saboda taga Babu dai wata wuta da ta Kuma tashi hasali ma Bata Kuma fita ba ko kofar gidan haka ma Bata kunna wayar ba sai a yau da ta kunna ta hau online

Tana Hawa kuwa ta ga sakkonnin da Mai Naira ya tura mata Wanda ita da kanta ta San da gaske ta kama Dan bawan Allah Nan a Hannu

Tana cikin mayar Mishi Amsar sakon shi sai ga Kiran Whatsapp na Vedio call.

Bata dauka ba har Kiran ya katse taci Gaba da duba sakonnin da suka shigo.

Wani Kiran ya Kuma shigowa da waccan lambar dai Nan ma Bata dauka ba ta bar shi ya katse.

Sai da yayi Mata Kiran takwas duk Bata dauka ba Kuma ya kasa Hak’ura don haka yayi ta auna Mata Kira har dai ta Gaji da nacin Kiran ta dauka inda kyakkyawar fuskar gemu ta bayyana.

Gemu Kam kyakkyawa ne na karshe musamman gemun shi da gashin sajen shi Wanda yayi matukar kawata fuskar shi . Fari ne tas Kuma Mai wata irin haiba da kwarjini. Sau tari kyan sa ne ka sawa Mata basa iya juyawa bukatar shi baya . Sai dai Kuma Dan bariki ne Sosai a harkar Mata Kuma Zaiyi Wahala ya hada ido da mace bata bayar da Kai ga Dukkan bukatar shi ba. Don haka Yana Kira ya samu wasila ta dauka sai kawai fuskokin su Suka hadu da juna suka tsurawa juna ido kafin gemu yayi murmushi Yana Fadin.

“Afuwan Haj na kira ki Vedio call ban nemi izinin Hakan ba kiyi min Afuwa don Allah

Wasila da taji Wani Abu Yana Sauka ajikin ta akan mutumin da tayiwa kallo Daya Taji Wani Abu Yana tsunkulin zuciyar ta Game da shi Wanda da kunya ma ta furta shi Amma ko ta ki ko ta so dai Dole ta amayar.

Ta juyar da kanta daga kallon maitar da yake Mata tana Fadin, “Wata Kil kayi wrong nomber ne.

“A a Babu wrong nomber Haj Wallahi boga nake so na San Kuma kece Mai Yi shiyasa na Kira Ina fatan za ayi mini a Kuma bani account na tura kudin Amma fa ba da yawa nake so ba na k’aramin boket ma ya Isa Wanda Bai wuce two liter ba.

“To Kai Ranka ya Dade Ina ka samu layi na Kuma a Ina ka san Ina boga.

“Eh to koma dai Ina na samu layin ki hakikatan kece Mai boga Kuma Nima din ban ce Wani ya bani layin ba kin San ance Mai so baya Wahala Amma dai a taimaka mini a bani account din don na Yaba matuka Gaya.

“To Babu matsala ga account din kana iya Rubutawa, Ta fada mishi ya Rubuta…

“To Nagode Haj zan iya ajiye lambar ki a waya ta? Tayi murmushi tana Fadin, “Babu matsala kana iya ajewa…

“To Nima ki ajiye tawa idan Babu matsala..

Suka ajiye wayar wasila tana jin bugun zuciyar ta akan wannan mutum Wanda a kallo daya ita kadai ta San Abinda taji a zuciyar ta ba don komai ba kuwa sai gemun shi da sajen shi.

Ta ajiye wayar tana kallon fuskar mutumin Nan a zuciyar ta inda taji k’arar shigowar Sako a wayar ta tana Dubawa sai taga alert ne na kudin da suka Bata tsoro in dai wannan mutumin ne ya turo su Kuma yace Dan kad’an yake so? Ai wannan kudin ko na buhu yace zai samu bare na k’aramin boket Wanda Bai wuce two liter ba.

Ta nemo lambar tashi ta kira tana Fadin, “Kaine ka turo kudi a yanzu?

Ya amsa da, “Eh sun shigo kenan?

“To Amma yawan kudin fa? Kace kadan kake so Kuma ka tura kudin da yawa.

“Sauran ai na ladar Aikin ne Haj a Rik’e Babu damuwa Nagode in an gama zan turo a karba mini.

Ya datse wayar ya barta sake da Baki dama yayi Hakan ne don ya fasa Mata Kai ya Kuma Yi nasarar Hakan

Ta Mike jiki a Sanyaye ta tura yusra ta siyo Mata kayan fulawa ta tashi Aikin Wanda ta cika babban boket ta Kira wayar shi ta fad’a mishi ta gama ya turo a karbar mishi.

Anjima ya Kira ta Yace Wanda zai turo baya kusa Amma gashi Nan Zuwa da kanshi a Ina zaizo

Ta kwatanta mishi Sauki venture a sabon titi tace in yazo Nan ya kira ta

Bai Rufa awa Daya ba ya iso ya Kira ta don haka ta dauki boket din ta fits Zuwa Sauki.

Motar da ta gani farin mutumin da ba zata iya manta kamar sa da ta tsaya mata a Ruhi Ba tayi matukar tsorata Domin kuwa a zahiri yafi yadda ta ganshi kyau da kwarjini.

Ya iso inda take Yana zuba Mata mayun idanun shi Yana Fadin

“Masha Allah Nagode Sosai Haj ga wannan Babu yawa, Ya fada Yana Mika Mata wata ambulan ta karba tana Godiya ta juya zata wuce ya tsayar da ita Yana fadin

“Bari na sauke ki mana Haj ko zakije Wani wuri ne na kaiki? “Nagode Babu inda zanje Allah ya kiyaye.

Ta wuce ya jima tsaye Yana kallon ta har ta bacewa ganin shi inda Kuma yake Jin ta fara zuwa hannu don haka Nan da kwana bakwai sai ya kawo matar Nan

Tun daga wannan Rana Mai gemu yake ta danawa wasila tarko Wanda batayi Wahalar zuwa hannu ba inda ya kashe boss din Baki daya yace zai turo da mota a dauke ta

Ta Kuma Kiran Yar Sokoto ta kawo Mata kayan Mata ta Siya ta biya ta inda ta shiga shirin tafiya amsa Kiran Mai gemu Wanda yayi mata tsaye a Rai Domin kuwa sai a kanshi ne taji zatayiwa ishaq kishiya akan so Domin kuwa lokacin da ta so ishaq Bata iya hada son shi da komai ba Amma a yanzu da ta gama Gane Abinda take so a wurin Namiji Wanda ya hada da son Namiji Mai gargasar gashi a jiki da Kuma gemu da saje. Wanda Babu su a wurin ishaq yanzu in ma Yana da shi babu gyaran da zai fito da su don haka a yanzu Kam Mai gemu ne ya mallaki wadan Nan abubuwan Uwa Uba Kuma Ya’yan banki Wanda Sune Amon sauti a Duniya.

Wannan fitar itace ta farko bayan dawowar ta ga Mai Naira Wanda ya ke ta faman Kiran wayar ta a kashe Domin kuwa ya kasa zama Amma Kuma wayar ta a kashe Don haka ta kusa haukata shi da Duniyar da ya gama bacewa.

Kwanakin da suka biyo baya ga Mai Naira na Rashin samun wayar wasila kwanaki ne masu tsananin gaske don har sauki venture yaje Amma Bai iya Gano inda take ba Dole ya Hak’ura ya koma ga Kiran wayar ta .

Ranar da ya samu wayar tata Kuma sun gama magana da Mai gemu Wanda Kiran Nashi zata amsa don haka Bata iya daukar wayar Mai Naira ba don a yanzu ta Gane shi Mai naira kudi take so a tare Dashi yayin da soyayya Kuma Zatayi Aiki ga Mai gemu don Haka a yau muradin ZUCIYAR ta zata Raya ko da Kuwa Babu kudi taji ta Gani

Kiran da Mai naira yake Mata yayi yawa don haka Kiran Yana katsewa ta so kashe wayar Amma Kuma in ta kashe da me zata je amsa Kiran Mai gemu? Don haka sai Taki daga Kiran Mai Naira ta ci gaba da Shirin ta Wanda take fatan samun zuciyar Mai gemu Wanda taji a bugun numfashi

Wayar ta dauki tsuwwa inda taga bakuwar lamba ta dauka inda Ake sanar Mata da Wanda zai dauke ta ne daga Alh Mai gemu.

Ta fito tsab tana cewa yusra ta kula da gidan zataje ta dawo yanzu. Ta Basu kudi tace su siyi Abinci kafin ta Dawo ta girka musu.

Ta shiga motar wacce Sanyin AC ya game ga kamshin turaren freshener Wanda ya bayar da wani sansanyan kamshi.

Lokacin da ta iso ga motar tana Kiran wayar Wanda ya Kira ta.

Direban ya fito Yana kare da wayar inda ta ganshi ta matsa ga motar ya bude Mata ta shige ya mayar da kofar ya Rufe.

ISHAQ ya karyo kwanar Sauki venture idon shi ya hango mishi wasila da Ake Budewa mota ta Kuma shige Direban yaja suka harba a cikin wata mashahuriyar mota Mai numfashi wacce Babu karya Mai ita ya koshi har ya tayar da Kai.

Wata irin matsiyaciyar sarawar Kai ta sauka akan ishaq Wanda yabi bayan motar da kallo har ta bace mishi….

Ya samu ya daga kafar shi ya na tafiya Amma Bai iya Sanin inda yake jefe kafar shi ba har ya iso gida ba zai iya Cewa ga ta hanyar da ya biyo ba.

Yusra ta amsa sallamar shi ta ga yadda ya shigo ta Mike Yana SHIGA d’aki ta bishi tana fadin

“Abba baka da lafiya ne?

Ya dago Yana kallon ta kafin yace, “Lafiya ta Lau yusra Ina Zainab ne?

“Ta tafi ta siyo Mana wake da shinkafa mama ta bamu kudi tace mu siyo kafin ta Dawo.

“To kuje kuci yusra…

Ya fada Yana kama kanshi da yaji Yana shirin tarwatsewa.

Yusra ta fito ta bashi wuri inda yaji zazzabi da Ciwon Kai Mai tsanani ya sauko mishi. A Nan ya Fadi Saman katifar shi Yana Rawar Sanyi yaja bargo ya Rufu kan kace me? Ya Soma fita hayyacin shi hakoran shi suna gwaruwa Bai San Wanda yake kanshi ba.

Gashi a yau din yadda ya fita haka ya dawo Bai ci komai ba sai Bak’in Ruwa kasancewar Babu Aiki Zaman shagon kawai aka Yi aka dawo Rabon yayi mugun gani bawan Allah.

 

 

 

 

 

 

 

 

Kai wannan wasila Kam tana daukar nauyi da yawa Amma muyi Mata ADDU A Babu Abinda yafi k’arfin Allah Kuma komai daga gareshi ne in yaso sai ya mayar da komai sauki Allah Muna fatan Hakan Aminci Aminci ga musulmi a ko yaushe Kuma ko Wani Amma zukata Kam suna Amsar Rad’adin kaddara😪💄🍀✨☘️🫸🏻💫🫷🏻

<< Tana Kasa Tana Dabo 12Tana Kasa Tana Dabo 14 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×