Skip to content
Part 16 of 68 in the Series Tana Kasa Tana Dabo by Hadiza Gidan Iko

SAMEER

A Ranar wata laraba ya yi nufin zuwa gida cikin ba zata don bai fadawa Farida zai zo ba.

Zuciyar shi ta kasa yarda da Amincewa musamman yanzu da Nisan tazara ya shiga tsakanin su sai week End yake Zuwa gida Yazo juma a ya koma Lahadi da yamma . Don haka cikin son Ganin Wani Abu ya danno motar shi Kirar BMW wacce yake shartowa tun Daga partercout har katsina…

A Ranar ne kuma Farida tana gida wayar ta tayi Kara ta duba sai taga Hajiyar Sameer ce take Kira ta dauka tana Gaishe ta Suka gaisa tana fadin.

“Farida Allah ya yiwa Baba Iro rasuwa in kin Samu iko kizo kiyi musu ta aziyya…

“Inna lillahi wa Inna ilaihir Raju un Haj yaushe ya Rasu?

“Wallahi yau da Asuba yanzu ma zanje ayi janaza Dani.”

“Allahu Akbar Allah ta ala yayi mishi masauki fil jannati Haj Nima Gani Nan tafe gara nazo ayi janazar Dani…

“Ameen Ameen Farida to ko na Jira ki ma sai ku wuce kawai tare?

“Eh Haj ku Jira ni kawai.

Ta mike inda ta soma kiran wayar Sameer don ta fada mishi rasuwar Baba Iro Amma sai ta samu wayar a kashe ta kuma kira amma a kashe sai kawai ta soma Shiri.

Baba iro kanin mahaifin su Sameer ne shine ya karbawa Sameer Auren Farida Kuma shine a madadin Uban su da ya jima da Rasuwa. Ya jima kwance Yana jinya ko watan da ya wuce sai da suka zo ita da Sameer suka duba shi Yana tayiwa Sameer nasiha akan Hak’uri da iyali don ya San dukkan dabin da aka Sha da shi akan yawan zargin da yakewa Farida Ashe wannan ganin shine na karshe tsakanin su. Ashe nasiha ce Mai taken wasiyya don a cikin maganganun shi Yana ta Fadin.

“Dole Namiji yayi Hak’uri da matar sa Sameer in Kuma ya sake ta kubuce mishi to Damar shi ta barshi. Kuma shi zargi da kake Gani shaidan ne ke kulla shi a zukata don ya haddasa husuma . Idan ka Faye zargin Abu to ba zaka tab’a zama lafiya ba ko da baka tabbatar da zargin ka. Mutum Mai Imani baya yarda ya kama jita jita sai zahiri don shi zato zunubi ne ko da Kuwa ya zama gaskiya don haka Sameer kana son matar ka to ka Rik’e ta kayi Hak’uri da ita itama tayi da Kai in ka bari shaidan yafi k’arfin ka ta kubuce Maka to ba fa zaka sake Samun ta ba don Haka ka kiyaye ban Hana kayi Hukunci a gidan ka ba Amma Banda zato don shi Sabani ne Kuma Mai zato ba zai taba zama lafiya ba kullum shaidan da zuciyar shi zasu ishe shi da kunji kunji…

Hawaye ya kawowa Farida ta Soma share su tana fadin.

“Allah Ya yi maka Rahama Baba Iro Allah yasa ka samu masauki a cikin ALJANNAH Mai fadar gaskiya Kuma ya tafi Ashe ganin karshe mukayi Maka…

Ta shirya su Saddam da Hanan suka nufi gidan Haj wacce mota ta kwashe su Zuwa kayalwa gidan baba iro Wanda yake dankam da Dan mutum saboda mutumin kirki ne Kuma mutum na mutane Wanda mutane suka yarda Yana fadar gaskiya ko Babu Dadi . Kuma ya kama kanshi Babu kwadayi ko buri a tare dashi shiyasa ya zauna lafiya.

Tun a hanya yake kiran wayar Farida Amma ya samu wayar a kashe Abinda ya Kara mishi azamar son ya isa gidan don yaga Dalilin da ya sa ta kashe wayar.

Gudu yake tamkar Mai Shirin tafiya sama ta bakwai don gaba Daya hankalin shi da nutsuwar shi tayi can.

Yadda yake gudu da motar zai baka mamaki Domin kuwa duk Gudun BMW sai da ya kure malejin ta shiyasa karfe Hudu na yamma Yana kofar gidan shi inda ya tura kofar get din yaji ta a kulle Abinda ya kuma fusata shi ya tabbatar da in baya Nan Farida fita take.

Ya bude kofar da key din wurin shi ya shiga ya dai tabbatar da Bata Gidan Abinda ke Kara bashi tabbaccin zargin shi na in baya Nan fita take Amma take lullube mi shi.

Kai tsaye ya shige cikin Gidan Yana duba ko Ina na gidan da son ya samu wata Alama da zata Alamta mishi Wani Namiji ya zo Gidan.

Duk ya gama Dube duben shi a sashi sashi na gidan Bai ga komai har ya dire a D’akin baccin farida Wanda Bata iya tsayawa gyaran shi ba inda yaga shimfidar gadon a yamutse tamkar wacce aka Sha buduri akan ta.

Jikin shi har kyarma yake ya Isa gadon Yana shafawa da son ya samu Wani Abu da zai tabbatar mishi da zaton shi . Har ya jawo shimfidar gadon Yana sunsunawa inda yaji Wani kamshi ba na kalar turaren shi ba ba kuma na Farida ba.

Ya fito jiki Yana mishi b’ari Yana Kara danna lambar ta Amma dai wayar a kashe.

Tamkar wanda aka yiwa walkiya ya Kai idon shi Kam kujera tree seater inda ya hango singileti da shotniker da Kuma Riga da Wando na shaddar gizna asha color Mai Daraja.

Idon shi ya yiwa kayan kyar da ido ya taka da sauri ya matsa ga kayan Yana jawo su don yaga ko na nashi ne.

Ya Soma juya su Yana kallo inda Kuma idon shi ya juye tashin hankali da Rudani fall a Ranshi.

Gane ba na shi bane yasa ya Kai hancin shi akan kayan Yana sunsunawa yayin da yaji Wani kalar kamshi da ya jiyo akan Gadon Farida Abinda ya Kuma sabbaba mishi Tashin hankali.

Idanu jajir ya zauna akan kujera Yana Rik’e da kayan kanshi a k’asa Yana Jin zuciyar shi tamkar Zata fito waje.

Ya watsar da kayan ya Mike a haukace Yana nufar kofar fita . Sai Kuma ya dawo ya figi wayar shi ya na Kiran wayar Farida Amma yaji wayar a kashe yayi ta Kira Amma a kashe.

Ya zauna Yana taune Leben shi har Yana fiddawa kan shi jini.

Ya fito da key din mota ya shiga Yana son fita duk da shi da kanshi Bai San inda zaije ba in ya fita don haka Yana shiga motar ya kasa tashin ta bare ya fita.

Ya Kifa kanshi a sitiyar motar Yana Jin wani irin Al Amari Yana zagayawa da shi inda Bai San ko Ina bane. Kayan waye a gidan shi? Singileti da shotniker? Wadan Nan sunfi komai tayar mishi da Hankali. Alama ce da ke nuni da wani Kato ya kwana a gidan shi?

Ya dago kanshi Yana Jin lema tana bin idon shi Abinda ya tabbatar mishi da hawaye ne.

Ya Kuma jawo wayar shi a karo na barkatai ya dannawa Farida Kira Amma har yanzu computer na fada mishi layin baya Samuwa sai dai ya sake Kira Lokaci na gaba.

Abunda kawai yake yawo a zuciyar shi Farida tana can tare da me wadan can kayan wata Kil ma har suna.

Ya dafe kanshi da yake shirin tarwatsewa Yana karewa gidan kallon kafin wata Hikima ta zo mishi ta Kiran Hajiyar su Farida don yaji idan taje Gidan.

Ya samu wayar Haj wacce ta dauka suna gaisawa tana tambayar shi Aiki ya amsa da lafiya Lau alhamdulillah.

“Yaya ne nake Jin ka Sameer muryar ka kamar marar lafiya?.

Yayi Jim don Yana girmama Haj matuka Gaya.

“Kaina ne yake ciwo Haj gashi Farida ta fita unguwa shine nake so naji ko tazo Gida wayar ta Bata Samuwa?

“Subuhanallahi sannu Allahu yashfeeka Wallahi Farida Bata zo ba to Ina Kuma ta lakafe?

“Ta je barka ne Nan kusa da ku Amma na San tana hanya yanzu dama don nace ta taho min da fanadol ne Amma Haj bari na fita na Samo kawai dama fitar ce bana so.

Ya fada da son ya lullabe manufar shi Haj tayi mishi fatan Alheri suka aje wayar.

Yayi ta fitowa Yana lekowa da son yaga zuwan Farida Amma Bai hango ta ba.

Ya yi ta fareti a farfajiyar Gidan Yana Shirin haukace wa don ya gama yarda da Abinda ZUCIYAR sa take kitsa mishi tun farkon farawa.

Yana nan har Duhun magaruba ya Soma kunno Kai Amma baiji kamar Yana son barin wurin ba don ko salla Bai iya tafiya Yi ba don karma ta shammace shi ta dawo baiga kalar Wanda ya kawo ta ba.

Sai da aka yi sallar magaruba su Haj da Farida suka yiwa iyalan baba iro sallama suka taho cike da alhini musamman ga iyalan mamacin Wanda Suka Sha kuka yayin fita da gawar baba iro inda Mafi yawan Ya’yan shi Mata sukayi ta tashin aljanu. Mun dai san yadda Ake a gidan makoki musamman Wanda ba a tab’a Rasa jigo irin wannan ba Dole Mai Imani zai Sha kuka Domin kuwa zaiga Wanda mutuwa tayiwa YANKAN kauna da Matan da ta mayar jawarawa da Kuma Ya’yan da ta mayar marayun karfi da yaji. Amma fa Hakan tana faruwa ne ga Wanda mutuwar ta tab’a yiwa YANKAN ta na Rasa Uwa ko Uba miji ko Mata . Amma Wanda Bai tab’a Rasa Daya Daga Cikin hudun Nan ba to Bai San Yaya Ake Ji ba sai dai ya tausaya ne don zuciyar Imani Amma in kana son Sani sai ta faru da Kai .

Wai aka ce ba a tambayar kaza hanyar Rafi in kana son bayani tambayi agwagwa kasha kashin Labari.

Don haka Haj da Farida sun sha kuka na tausayin iyalan shi Kai hatta da Mazan sun nuna Abinda za a tausaya musu Dole Kuma Mai Imani ya tausaya. Sai dai da yake baba iro yayi kyakkyawar cikawa sai Rad’adin yazo da sauki dama in dai musulmi ya cika da Imani to Arziki yayi kuma Rahama ta tabbata ga Ruhin musulmi da Masu cikawa da kalmar shahada ALLAH ta ala ka cika mu da imanin yayin mutuwa kasa mu mutu a cikin musulunci don Wanda ka Aiko da gaskiya sayyiduna RASULULLAH.

Jiki a Sanyaye suka taho Haj da Farida wacce ta Kara saki da Duniya yanzu Kai yanzu sai Labarin ka Kai Mai Hankali ma baya cika Baki akan Duniya Wallahi.

A motar Hajiyar su Sameer suka tafi don haka da suka dawo ma sai Haj tace a fara Sauke Faridar kafin su wuce Gida. Don haka Isa Direban Haj ya dauki hanyar gidan Sameer don sauke Farida gida.

Yana zaune dafa an duk da sauron Da ya soma yanyeme shi Amma Bai damu ba ga Duhu Babu NEPA Kuma ya kasa tashin gen Babu Abinda ke gifta idanun shi sai singileti da shotniker kawai suke zagaye idanun shi ga shi Kuma har kawo yanzu da Dare yayi Bata waigo gida ba wata Kil can zata kwana ita da shegen da ya hunce mishi gida.

Tuna Hakan yasa ya tayar da gen gidan ya dauki Haske ya game gidan Amma a gidan ne kawai yake da Haske Amma ZUCIYAR shi tafi Bakin ciki Bak’i Babu Abinda yeke sai hadiyar zuciya.

Ya fito motar ya bude bayan motar shi inda bindigar shi take ya fito da ita Yana duba hanjin ta idan tana da d’uri don Wallahi billahi matukar ya kama Wani Namiji a yau din Nan sai ya harbe shi don baiji zai iya runtsawa ba a yau matukar ba dawowar Farida ya Gani ba zai kwana a waje ne yau.

Ya tabbatar da bindigar cike take da harsashin ta ya aje ta a gaban motar Yana Kara taune Leben shi Alamar Bak’in ciki ne fal a zuciyar shi.

Tun daga nesa Farida ta hango Haske a goshin fitilar kofar gidan su Abinda yayi matukar firgita ta shine da ta Soma dubawa taga nefa ce ko Kuwa ? Bata iya Sanin Kwan a kunne ya ke ba ko a kashe ? Abinda dai ta sani kamar layin Babu wuta Kuma ba a gyara ba bare tace ta zama ta game gari.

Gaban ta yayi wata matsiyaciyar sarawa Mai tafe da Ciwon Kai Saboda karasowa da sukayi taji k’arar Gen.

“Inna lillahi wa Inna ilaihir Raju un…
Farida ta fada ba tare da ta San maganar ta fito Saboda kidimewa.

Ta zuge jakar ta tana fito da wayar ta da ta tuna ta kashe ta Lokacin da taga Abinda yake faruwa a gidan makokin Nan.

Haj tana lura da ita da irin tashin hankalin da ya bayyana a fuskar ta don ta gama yarda Sameer ne ya Dawo gidan ya Kuma Kiran wayar ta yaji ta a kashe gashi Kuma Bai San ta tafi gidan makokin ba.

Ta balle murfin motar ta fito tana yiwa Haj sai da safe a Rude… Ta wuce tamkar Zata kife a k’asa saboda tashin hankali da firgici.

Ta tura kofar get din a firgice ta shige inda Sukayi taho mu gama da Sameer Wanda ya taho saboda ganin hasken motar da ya ke hangowa ta Bakin kofar.

Taja baya da sauri tana kallon shi da wani irin Rudani yayin da Saddam da Hanan suke Bayan ta.

Sai kawai taji ya damki wuyan ta da wani irin karfi tamkar ba mace ya Rike ba.

Ya ja ta Zuwa cikin gidan a haukace Yana jin a yau sai ya k’arar da numfashin Farida tunda Bai Yi nasarar kama Wanda ya kawo ta ba Amma zata kawo shi in taji Wuta.

Yayi wurgi da ita a tsakar falon kafin ya kwale belt Yana auna Mata duka tamkar zai aike ta kiyama da duka tamkar mahaukaci ya jefer da belt din ya Kuma shake ta Yana Fadin.

“I hated you Wallahi na tsane ki kin cuce ni Farida Baki da sauran Wani amfani a wuri na Wallahi Na tsane ki ! Na tsane ki ! Na tsane ki ! Na sake ki Wallahi na sake…Ki…da wani irin sauri Farida ta Kai Hannun ta a bakin Sameer Wanda ya kaiwa Bakin ta Wani matsiyacin Duka Yana Fadin na tsane ki.

<< Tana Kasa Tana Dabo 15Tana Kasa Tana Dabo 17 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×