Skip to content
Part 23 of 58 in the Series Tana Kasa Tana Dabo by Hadiza Gidan Iko

Yusra Zaune a Bakin kofa ta na fifita garwashi a kurfoti inda wasila take d’aki Rik’e da waya tana Magana da Shama wacce take fadawa wasila yaushe zata shigo Abuja don Mutumin ta fa Dan majalisar Nan ya matsa da son Ganin ta.

“Gaskiya Shama ba yanzu ba don a yanzu Akwai sanwar da na Dora Amma dai kome kenan Zaki jini don Allah ya sani na gaji da zaman katsina Abuja kawai nake son komowa na fantama yadda nake so.

“Kema ai kin kasa yin Wani motsi ni Ina Jin dai wannan karfan mijin Naki kikewa mayata bana Jin Zaki iya Rabuwa dashi don Alamun ki sun Nuna Hakan.

“Ai wannan ce sanwar da nake fada Miki na Sanya kome kenan Zaki jini Shama sai munyi magana.

Wasila ta fito inda yusra ke ta fifita garwashi a kurfoti ta dube ta tana fadin.

“Wai mama ke kika siyi kajin Nan? Na gansu da yawa.

“Ni na siye su Wani Abu ne? So nake yau muyi shagali a gidan nan.

“Ranar Nan ma da Bakya Nan Abba ya siyo Mana kaji har Hudu Amma yace mu dauki Daya ni da Zainab sauran kuwa ya kaiwa Goggo da Inna suwaiba yace ban iya dafawa ba kar na lalata sai da na dafa ya Gani yace Ashe na iya.

Wasila taja tsaki ta koma d’aki tana Fadin, “Wannan dai idan yaci ta Ajalin sa ya ciwo don a yau dai ba zai Kuma kwana a Duniya ba sai na huta karbar takardar saki takaba ce da nayi ta na gama na balle nayi tafiya ta Babu Wanda yaji bare ya Gani.

Yusra ta dafe kirji Lau lafiya sun Sha citta da tafarnuwa ga attarugu yaji

Ta fadawa wasila ta gama..

“Yauwa Yar Albarka kar bi kud’in Nan ki siyo min lemun dansa Mai sanyi za a Baki.

Tayi Hikimar tura yarinyar waje don ta aiwatar da mugun kudurin da yake Ranta.

Yusra ta fita wasila ta SHIGA D’aki ta dauko gawa Dubu ta fito tana dukawa tana kasafin Naman ta zuba Wanda take Shirin bawa ISHAQ ta kece takardar gubar ta Soma Zubawa tana murmushin mugunta.

Sagir ya turo kofar gidan idon shi ya sauka akan Abinda mahaifiyar sa take Yi. Gaban shi yayi masifar Sarawa yaja baya da sauri Yana dafe Kai Yana Ambato sunan ALLAH.

Ya jima a soron Yana laluben Abinda mamar tasu take nufi da Zuba gawa Dubu a cikin Naman da ya Gani Wanda ya tabbatar mishi da ba Alheri take nufin ailatawa ba.

Ya jima a soron Yana laluben abinyi Amma sai ya ga wautar shi ta tsayawa kar ta aiwatar da mugun kudurin ta Yana tsaye Yana kama tasha don haka sai ya tura kofar ya shiga Yana sallama.

Wasila ta dago kanta taga shine sai ta mayar da kanta ga Naman gabanta da take dannawa a Baki.

Ya duka Yana gaishe ta Amma Bata ko tada Kai ta Dube shi ba Wai gaba take da shi . Wai karfin Hali SATA LAHIRA ita da take da abinda Zaiyi gaba da ita baiyi Baiyi ba sai ita Mai nad’e tabarmar kunyar ta da hauka.

Ya wuce d’aki yusra ta Dawo da lemun dansa ta bawa wasila ta Mika Mata Naman ta ta zauna tana Fadin

“Yau Zee Zee bacci take mama an Rage Mata ?

“Gashi Nan a tukunya na Rage Mata wancan Kuma na baban ku ne in ya dawo ki dauka ki kai mishi.

“Yaya fa mama Ina Nashi?

“Ke kin ishe ni da tambaya Uban waye ya bani kudin ne da za ayi mini IKO da Rayuwa

Sagir Yana d’aki Yana Jin duk abinda yake faruwa tsakanin yusra da maman su yayi mamaki matuka Gaya da Jin wai in Abban su ya dawo a bashi Naman Nan Wanda ya tabbatar da Wanda yaga tana Zubawa GAWA Dubu ne . Me take nufi? Ta kashe Abban ko Kuwa? No wonder idan tace ta Hana sagir Naman ta ta bawa ISHAQ tunda su Duka ya San haushin su take ji Amma tana iya kashe Mijin ta don haushin da take ji. A take ya Gane manufar tata ya Kuma Jin HAWAYE na bin idon shi Bai taba Ganin Uwa irin ta shi ba wacce Babu Abinda ta Saka a Gaba sai DUNIYA

Yana zaune a D’akin ko makaranta ya kasa tafiya har yaji shigowar Abban nasu Wanda ya shigo yusra tana mishi Sannu da Zuwa. Ya amsa Bai dubi wasila da taji Wani matsiyacin lugude a zuciyar ta ba don tayi zaton Zaiyi Mata magana Amma Bai ko Kalli inda take ba ya wuce zuwa D’akin shi

Sagir ya fito waje inda ISHAQ din ma ya fito sagir Yana mishi Sannu da Zuwa

Wasila ta Mike ta shige daki tana Kiran yusra wacce ta shiga tana cewa ta dauki Naman Abban su ta Kai Mishi.

Yana Zaune Yana yanka shadda wacce zai Dinka yusra ta ajiye tana fadin, “Abba ga nama yau ma ni na dafa shi Kuma Yayi Dadi Sai ka Ragewa Yaya don mama Bata bashi ba.

ISHAQ ya Dubi yusra Yana Fadin, “Ina muka samu Nama kuma Yusra?

Ta yi Maza ta ce

“Mama tazo dashi ni kuma na dafa.

“To an gode amma bawa Yayan tunda ba a bashi ba ni na koshi ma ko da an bashi ba zanci ba Yusra.

Yusra ta Soma Fadin, “Wallahi Abba yayi Dadi don Allah ka danci kaji ko kadan ne.

Sagir da ya Zubawa Naman ido Yana kallon Yana hawaye Amma duk Babu Wanda ya lura da shi tsakanin ishaq da yusra.

“Yusra na koshi Amma bawa sagir in zaici in Kuma ba zaici ba sai ku ci ke da Zainab.

Yusra ta Dubu sagir ta ga Yana hawaye tace
“Yaya ga Naman…

Yayi saurin share Hawayen shi Yana Fadin, “Na gode yusra tashi Maza ki kaiwa Goggo naman nan,

Wasila da take d’aki tana Jin duk dabin da suke Jin sagir yace a kaiwa Goggo naman sai gata ta fito a rikice tana fadin

“Kafi ni sanin Abinda ya dace ne ko kuwa da zakayi min wannan abun?

Sagir ya Mike Yana Fadin, “Kiyi Hak’uri mama amma wannan Naman Abba ba zaici shi ba bare ni Amma Goggo ita ya dace taci shi Kuma zataci shi.

Bata Jira komai ba ta gaura mishi Mari a fusace tana fadin, “Kai ka fa kiyaye ni Wallahi.

Sagir da ya girgije marin da tayi mishi ya suri kwanon Naman a guje ya nufi kofar fita inda ya fito da kwadon d’akin shi ya fita Rike da kwanon Naman ya kuma ja kofar ya Saka mata kwado ya murza.

Wasila da ta Figo mayafi ta Rufa wa sagir baya tana zuwa Yana murza kwadon taji ya Rufe kofar ta Soma jijjiga kofar Amma Yana tsaye Yana kallon ta tana fadin.

“Wallahi tallahi idan ka kaiwa Goggo naman Nan zan tsine Maka Albarka.

“Sai dai ki tsine min mama amma wallahi sai na kaiwa Goggo naman nan kuma ba zan taso ba sai ta cinye shi tas ai na fada miki mama koma meye kika fara baki fara shi da nasara ba don Haka naga Abinda kikayi kuma dama k’etar gwaiwa Mai ita take kashewa idan har Kinga ban Kai Naman Nan ga Goggo ba to Wallahi kin fadawa Abba Abinda kika Saka a ciki . A wurin ki ne Goggo take wata Amma ni Bakiyi tunanin a wuri na Uba na Wani ne ba? Rayuwar Goggo kike so ni Baki hango min abin Kunyar da Zaki jaza min ba? To sai Goggo taci Naman Nan Wallahi Kuma duk Abinda ya biyo baya zan Fadi Abinda allah ya nuna min kinayi Wanda na juyar da shi gareki Wallahi mama na tsane ki in Ina Kaunar ganin ki Allah ya tsine min Wallahi gara mutuwa ta sau dubu Ina da kyakkyawan zato akan ta Amma akan ki Babu wannan zaton Alherin tunda Banga kina nufi na da Alheri ba.

Jikin wasila yayi sak Jin abinda Dan nata yake fada. Babu Abinda yafi tsaya mata a Rai da zuciya irin kalmar tsanar da ya Ambata.

ISHAQ Yana Zaune Yana Jin duk abinda yake faruwa amma bai ko motsa ba.

Ganin Wasila ta juyo zuwa d’aki tana fidda kwalla yasa ya Mike ya leka ta kafar makulli ya hango sagir durkushe Yana kuka…

“Sagir !
Ya Kira sunan shi ya juyo ido jajir Yana Amsawa…

“Bude kofar Nan “. Ya bashi umurnin Hakan Babu Kuma wata gardama ya bude inda ishaq ya wuto Yana cewa ya shigo, Ya shigo ya ajiye kwanon ya zauna Yana share fuska.

“Me yasa baka Jin magana sagir? Ba ni na fada maka kar ka sake fadawa mahaifiyar ka magana ko Ka Saba umurnin ta ba? Kana kuwa Neman Albarka da Zaki Rik’a mayarwa Uwar ka magana? Kome kaga tayi bance kar kayi Mata nasiha ba Amma ba cikin hargagi da nuna kaima ka Isa ba. Idan ka sake ka fusata ta Wallahi Babu yadda za ayi kaga daidai. Ina son daga wannan Ranar ya zamo mun Rufe irin wannan maganar da Kai da wasila zata fada ka mayar Mata.

Kuka ya kwacewa sagir ya Soma Fadin, “Kayi hak’uri Abba Amma ba Abinda kake zato nayi ba. Sau da yawa mama tana yin abubuwa Wanda take zaton a Duhu tayi sai Allah ya nuna min. Abba ba zan iya fada Maka komai ba Amma Ina Rokon Ubangiji ya nuna maka kowacece Mama na San zaka fahimce ni ba zan iya tona Mata Asiri ba saboda ko Babu komai sunan ta mahaifiya ta . Amma ka sani wannan Naman sai na kaiwa Goggo shi Allah sai taci shi Abinda Duk ya biyo baya sai ka yanke min Hukunci da shi.

Ya Mike Yana surar kwanon Naman zai fice ISHAQ ya tsayar dashi, “Kar ka kaiwa Goggo naman Nan tunda na fahimci akwai wani Abu. Ka Kali Goggo a matsayin Uwa ta idan ka cutar da ita sagir ba zan iya yafe maka ba fad’a min kawai Abinda ka fahimta.

“Ka yi hak’uri Abba Amma sai na kirawo Goggo kafin na fada maka Abinda na Gani.

Ya Mike ya fice ISHAQ yanajin Baiyi mamakin komai ba akan Wanda ya Gani a yau wasila da Zuwa hotel to wane mamaki ya wuce wannan ?

Sagir ya dawo tare da Goggo wacce take a Rude takalmin ta ma wari da wari ta Sako.

“ISHAQ me yake faruwa ne ? Allah ya Sa ba maganar Wasila zakuyi min ba.

Wasila ta fito tana Gaishe da Goggo wacce Bata Amsa ba tabi ta da wani matsiyacin kallo Mai cike da tsana da Bak’in ciki.

ISHAQ ya Bawa Goggo wurin zama Yana Gaishe ta Yana Fadin, “To ni dai Goggo ban jima da Dawowa daga Aiki ba sai ga Nama yusra ta bani na tambaye ta tace Mamar su tazo dashi.

Ni Kam banji Ina son Naman ba shine yusra tace Mamar su Bata ajiyewa sagir ba shine nace ya dauka yaci ni na koshi . Shi Kuma yace ke zai kaiwa Amma wasila ta fito tana Sababi har tana ikirarin zata tsine mishi.

“Ai da ka barta ta tsine mishi tunda tsinewa Ake ai sagir Baiyi Abinda za a tsine mishi ba itama da tayi Wanda zan tsine Mata ai na barta da ALLAH da fitar Rana da faduwar ta na barta da Duniya.

Sagir ya dauko guntuwar takardar maganin Bera Dan china Wanda Ake cewa gawa Dubu ya kawo gaban Goggo Yana fadin.

“Goggo kinga Abinda Nazo na samu tana Zubawa a cikin wannan Naman tana fadin a bawa Abba .. Goggo me mama take so a cikin Duniya? In Bata son zama da shi ya sauwake mata ba sai ta kashe Mana shi ba in ita Bata son shi mufa? Goggo har lamarin ya Kai da kisa a ciki ?

Goggo ta dafe kanta tana zurarar hawaye ta kasa cewa komai. Sagir kuka yake ISHAQ Kuma mamaki Yana Neman kashe shi Jin inda wasila tazo da Neman Rayuwar shi.?

Aka yi tsit tamkar masu makoki aka Rasa Wanda zai tabuka yayin da wasila take Jin ta a tsiraice. Me yasa maganar yaron Nan sagir take tabbata komai Zatayi sai Allah ya nunawa Wanda take lullube wa?

Goggo ta fyace majina da gefen zanin ta tana fadin

“Ai ni sagir ma ban gode maka ba da baka kaiwa Uwar ta Naman Nan ba in takamar mutum Sharri ai akan Mai shi yake k’arewa. Ni Kam ISHAQ anzo gab’ar da zance Maka ka Nemi zama lafiya ta hanyar sauwakewa wasila Auren ka don ni da kaina na ganta inda Dole ka barta ko da Kuwa itace autar mata a Duniya tunda har ta Soma neman Rayuwar ka don Allah ka barta bari Kuma na har Abada tunda Duniya ta Zaba gata ga Duniyar Nan Wanda Bai zo ba ma tana Jiran shi.

“Goggo tuni ba tun yau ba Wallahi Babu Aure tsakanin mu ba barta ne ban furta ba saboda kunyar ki da kunyar yaran Nan Amma a yau din za a kare komai.

Ya shiga d’aki ya fito da takardar ya bawa Goggo wacce ta chilla wa Wasila a fuska.

“In Sha Allah Muna Nan zamu ga matar da Ubangiji zai Maka misaya ta Alheri ita Kuma zaka ga yadda karshen ta zai Kare ko Babu komai ta wulakanta Aure da Haihuwa da idona naga yarinyar Nan a inda bana fatan aga Ya’yan musulmi.

Goggo ta Mike tana Fadin, “ISHAQ Allah ta ala ya maye Maka gurbin Bak’in cikin ka da FARIN CIKI har karshen Rayuwa. In dai Allah ya haramta zalunci to azzalumai kuwa zasu ga karshen su tun a Duniya. Kai Kuma sagir Allah ya baka Hak’uri Uwar ka ta Zubar da kimar ta gareka Amma kar ka biye Mata ka barta da ALLAH kamar yadda Nima na barta da ALLAH Duniya da ta Zaba gata ga Duniyar Nan.

Goggo ta fice tana Kara fyace majina da gefen zanin ta tana kuka.

Wasila ta Mike tana Fadin, “Haka Mazan kwarai suke da kayi Hakan tun tuni ai da ka huta ni Kam gobarar titi a jos Wallahi.

Wannan shine karshen Auren wasila da ISHAQ inda a Ranar ma wasila Bata kwana a katsina ba Kai tsaye ta wuce Abuja bayan ta Nemo mota ta kwashe mata kayan ta tas ta aike da su gidan Goggo Amma fa ita ko da wai Bata je gidan ba sai kayan da ta aike ta biya Mai motar da yayi jigilar Kai Mata kayan ita Kuma ta yanki tikitin jirgi ta wuce Abuja tana Jin ita da katsina Kuma sai baba ya Gani.

Yusra Kam da Zainab sunyi kuka Ganin sun dawo makaranta Amma d’akin Uwar su Babu komai duk da ba akan idon su Al Amarin ya faru ba Amma ganin D’akin mamar su Babu komai nata ya tayar da hankalin su suna ta kuka ishaq Yana Rarrashin su da dadin bakin ta tafi unguwa zata dawo.

Ya sama musu katifa don su Rik’a kwanciya ya Kuma sama musu abubuwan da zasu bukata don haka suka Hak’ura suna Rayuwa cike da alhini kafin suka Saba da kad’aici dama kallafa ce ta yaro da in yaga Abinda bai yarda dashi ba Amma yaushe Uwar tasu take zama gida? Sune suka fi zaman gidan su sai in sagir ko ISHAQ ya dawo . Sagir Kam sai a yanzu yake Kara tausayin Yan Uwan Nashi yusra da Zainab Wanda da ya Dawo Aiki Yana Gida. Lokacin makaranta su tafi makaranta in Kuma sun dawo su Bude gida su Zauna haka Ake ta Rayuwar yusra Kam tuni ta Goge da girki tun da kuruciyar ta . Tun tana kwamacala har ta iya Komai take Kuma yin komai Babu fargaba.

<< Tana Kasa Tana Dabo 22Tana Kasa Tana Dabo 24 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×