Skip to content
Part 32 of 58 in the Series Tana Kasa Tana Dabo by Hadiza Gidan Iko

Yayi murmushi Yana Fadin

“Basma Baki Sanni bane Amma nayi Miki uzuri.

Ya zura Hannun shi a cikin aljihun shi ya dauko makullan ya nufi kofar fita ya zura ya bude . Basma ta manta ne Yana da key din Duka kofofin gidan a makullan shagon sa da na motar sa? Ya fice Yana Jan kofar ya datse tamkar yadda ta barta.

Basma Kam son ta cusa mishi haushi da takaici Yasa ta Rufe mishi kofar kuma Bata ji ko dar ba ta Haye gadon ta ta kwanta tana Jan bargo tana murmushin mugunta don ta San yau dai Babu wannan kwanan da take cike da Rudani akan yadda za ayi shi sai dai wani jokon ba na yanzu ba .

Farida na gama sallar magaruba ta SHIGA bandaki da niyar wanka ta Kuma shiga kofar da ta Gani a matsayin toilet ta SHIGA tana k’arewa toilet din kallo hakika Abdullahi ya zarce Sameer da tazara Mai yawa. Ba a ma hadawa …

Ta hada Ruwan wankan da Ruwan zafi Saboda lullumin sanyi da akeyi ta Kuma Yi amfani da kumfar sabulu Mai kamshi Wada taji Dadin wankan ta fito tana zama a gaban dressing mirro tana kallon kanta ita da kanta Taji Lallai ta sauya ba Kuma sauyin komai ba sai Ruwan Aure da ta wanka a jikin da Kuma Albarkar da akayi ta sakawa Auren .

Zuciyar ta ta buga Da taji Sameer ya dawo Mata a Rai musamman Asibitin da Haj tace Yana Can kwance Babu lafiya.

Sameer Yana da matsayi Mai girma a zuciyar ta Amma Kuma matsalar shi gareta tana Neman dusashe matsayin sa don har ga Allah ba ta so Wani Namiji kamar shi ba Amma ta Gaji da zargin shi a kanta duk da ta so tayi amfani da Damar Auren Abdullahi ta cimma burin komawa gareshi amma Kuma matsalar da zata Kuma haddasa musu husuma Yana Nan tare da Abar sa wato zargi Dole zata bar shi ta Rik’e Abdullahi taga Nashi kamun ludayin.

Tana zaune Gaban mirro tana shafe jikin ta ya shigo Yana hango ta daure da tawul gashin ta ya sauko a bayan ta sai kyalli yake Alamar ya Sha mayuka ga kuma fatar ta Mai daukar hankali wankan tarwada da yake mutuwa a so kasancewar sa fari tas Amma farar fata bata burge shi yafi son wankan tarwada don haka Yana ajiye ledodin da suke hannun sa ya nufi Bakin madubin.

“Da GIRMAN kujerar ki Amarya ba Kya laifi ko kin kashe dan masu Gida har anyi min wankan ne?

Ya fada Yana Dora Hannun sa akan kafadar ta Yana kallon ta ta cikin madubin.

Tayi murmushi Wanda yaji shi har cikin Ranshi ya zagaye ta Yana zama dab da ita Bakin shi da aswaki Mai kamshi irin na Saudi ya a jiye aswakin ya na Zuba Mata idanun shi Yana kalle ta Abinda ya sa ta Jin kunya Ganin Yana Mata wannan kallon na mayata.

“Masha Allah Farida Nagode Allah da ya nufe ni da Auren ki Mai hak’uri wata Ran zai dafa dutsi yau ga ni da ki a d’aki daya Farida a matsayin matata ni kuwa wace irin Godiya zanyiwa Ubangiji?

“In ka yiwa ANNABI MUHD S A W salati ma itama Godiya ce.

Ya kama hannun ta da yake dauke da Jan lalle Yana runtsewa a hannun shi Yana Fadin

“S A W wannan ma gaskiya ne bari Nayi wankan na fito kafin ki gama Shiryawa ko?

Ya fada Yana mikewa ta Mike itama ta jawo Kayan da zata Saka wata doguwar Riga ce maroon wacce akayiwa gaban ta Aiki da wasu stone masu kyau Kuma Kala kala aka matse gaban ta sai hannun ta Mai ban Sha awa sai Kuma hular Rigar wacce akayiwa designs Mai kyau.

Ta fesa turare kala kala har ta Rasa kalar kamshi da take kafin ta Saka kananun Yan kunne da k’aramar sarka.

Tana cikin shirya table din ne ya fito daure da tawul Yana Goge Ruwan jikin shi Yana Fadin.

“Wai har da Wahalar min da kanki kikayi farida? Ga fa abin tabawa Nan na taho da shi fiddo Mana su yau fa nake Ango don duk wata mace a wuri na ba mace bace Farida sai ke.

Tayi murmushi tana kama Hannun shi zuwa D’akin Nashi tana fiddo mishi jallabiya milk color Mai budadden gaba da gajeren hannun ya karba ya Saka yayin da gashin da yake kwance a kirjin shi ya fito ga Kuma gargasar da ke lullube a jikin shi don Allah yayi mishi mutum ne Mai gashi Al Amarin da ya Soma tafiya da ita akan sa kenan Bak’in gashin da ya lillube kirjin sa da sassan jikin shi akan farar fatar sa ita da kanta ta Gane ko bashi da kyawun fuska Yana da kyawun jiki bare ma ya tserewa Sameer din ta a kyau in dai gaskiya zata fada Abdullahi ya zarcewa Sameer Abinda kawai Sameer yafi shi shine fadin kirji da tsayi Amma bayan wannan Babu Abinda zai nuna Mishi.

Ta dauki turare tana fesa mishi Yana murmushi Yana kallon ta har ta gama kafin ya dauki kum din sa Yana gyara gashin gemun sa da na saje suka futo Yana fadin tayi alwala suyi salla kafin su Zauna…

Sai da sukayi salla Raka a Hudu suka sallame yayi ADDU A Mai tsayi suka shafa ya Dube ta Yana murmushi….

“Farida Allah ta ala ya sakawa Auren mu Albarka a yau MAFARKI na ya tabbata Farida Allah ya yarda na zama mijin Farida.

Tayi murmushi tana Fadin, “Allah kenan Abdullahi ya tsara Aure a tsakanin mu Ina fatan Aminci a tsakanin mu da Kai tare da matar ka.

Yayi maza ya amsa da Ameen Ameen Farida ta na Dade Ina mafarkin kwanciya a kirjin ki Farida Allah ya halicce ni ne da kaunar ki.

Ya fada Yana Kai fuskar shi akan kirjin nata kafin ya daidai ta fuskar su Yana Kai Bakin shi a nata Yana kiss din ta.

Tun a wurin kissing din Nan ya fahimtar da ita Maza ma suna suka Tara a nuna soyayya da kulawa. Bata kasance bakuwa a kissing ba Amma ya ganar da ita nashi ba irin Wanda aka sabar Mata bane don ita da kanta ta Gane bambancin.

Tana Rike da fuskar shi hannun ta cikin tattausan gashin gemun shi Yana jin yadda yake mata kissing Mai nuna tsantsar kulawa da tafiya da Hankali.

Jikin ta yayi Wani irin Sanyi Yana Rungume da ita Yana Rad’a Mata Kalaman da suka mantar da ita wacece ita.

Ya dauki kofin da ya zuba Madara Mai sanyi ya nufi Bakin Farida ta karba ta Sha kad’an kafin ya Soma Bude kayan da Yazo dasu Amma Bata iya cin komai ba Bayan fruit Amma Naman shi kadai yaci Shima Bai ci Da yawa ba.

Duk yadda yaso taci abubuwan Bata iya ci ba bayan inabi da tuffa sai kuwa kankana da ta Sha.

Ta kawar da komai ta dawo ta same shi Yana Mata fira jifa jifa ya na Kuma nuna Mata irin matsayin da take da shi a gareshi . Kalamai masu Kima da Dadin sauraro har suka siye ZUCIYAR ta duk da ta so fakewa da Bak’on wata Amma Kuma yadda yake Mata yasa taji Lallai me Gemun ya Soma fasa zuciyar ta Yana shiga.

Bata saki ba sai suka kure turaka ya shimfide ta cike da wata irin soyayya da kulawa wacce ta fasa Mata zuciya.

A wannan Dare Abdullahi ya siye ZUCIYAR Farida kakaf din ta Domin kuwa ta Gane da gaske yake son ta itama ya dasa Mata soyayyar da Bata tab’a zaton Hakan take ba don a Nan ne ta Gane Ruwan Zuman da Ake fad’a a soyayya. Shi ma kam ya tabbatar da Farida itace Duniyar shi musamman da ya samu fiye da Abinda Duniyar Mafarkin sa Tasha nuna mishi.

Yana Rungume da ita Yana faman kalaman ce ta da dukkan kalmar kauna da soyayya wacce yake jin ya gama mallakar mace a Duniya Kai hatta Matan bariki ya barsu bari na har Abada kuwa. 

Basma ta fito da Asuba da son taga Abdullahi sai ta Tara’s da kofa a Rufe Amma Kuma Babu kowa sai a nan ta tuna da Yana da key din kofofin a tare Dashi ya fice kenan? Tayi turus tana Jin gaban ta Yana tsananta faduwa tana can ta shanya Baki tana BACCI Ashe Yana can Yana…

Taji Wani matsiyacin lugude a zuciyar ta Amma a haka ta koma ta shiga toilet ta daura alwala Tayi salla Amma ita da kanta ba ta iya kiyaye surar da ta karanta a cikin sallar ba.

Ta fito ta Soma Kai da kawo tsakanin kofar sashin ta da shashin farida inda take hango kofar a kulle har zuwa karfe Sha Biyun Rana Amma ba a Bude kofar ba inda ta matsa tana tambayar sabo Mai gadi ko Mai gidan ya fita ne? Yace babu Wanda ya fita ga motar shi can a ajiye.

Ta koma ta ci gaba da lekowa da son Ganin an Bude kofar Amma har la asar ba a Bude ba Abinda ya tabbatar Mata da ba zai fito ba ma bare ta samu Abinda take son Samu.

Ta koma ta dauki waya tana Kiran shi tayi mishi sama da missed call biyar kafin ya dauka Yana Fadin

“Basma Kuna lafiya?

“Wai har yanzu fa baka leko ba ni Kuma bani da lafiya Abdullahi don Allah kazo.

“Kije Asibiti Basma Amma ni Kam ba zan fito ba Gobe ma Albarka ke Babu Mamaki ma Nan da kwana bakwai ba Zaki saka ni ido ba Basma in ciwo kike na yarje Miki kije Asibiti in Kuma kudi ne babu zan tura Miki Amma ni ai kin San ban karanci Aiki likita ba.

Yana gama fadar Hakan ya datse wayar shi ya bar Basma tana kwaso maganganu Amma ya barta da hayaniyar ta inda take Jin tamkar tayi hauka don Abinda teke Gudun dai ya faru.

Tayi ta auna mishi kira Yana kallon Kiran ya kyale ta don ya San makirci ne lafiyar ta Lau.

Yana kallo tayi ta jera mishi kira har ya gaji ya kashe wayar Gaba Daya.

Haka Basma ta kafa zarya tsakanin kofar ta da ta Farida Amma dai sammakal har dare Dole ta Hak’ura ta koma Amma har gari ya waye Bata ga keyar shi ba wayar shi ma Bata Kuma Samu ba.

Kwanaki UKU cif Bata Saka shi a ido ba inda duk tashin hankalin Duniya ya Kai to Basma ta shige shi har ta Rame saboda tashin hankali.

Sai dare ta ga shigowar shi cikin yadin filters coffee brown Wanda ya fito da shi tas taga ya sauya matuka Gaya yayi jajir da shi ga Wani annuri Yana fiddawa.

Ya zauna Yana Duban ta hular sa a gaban goshi yake Fadin, “Yaya jikin Basma? Ta Sha mur tana Hararen shi Bata tanka mishi ba.

“Amma ni sai naga wata Uwar k’iba ma kika narka Banga Alamar ciwo a tare da ke ba sai dai idanun ki cike suke da masifa naga wannan Kam.

“Ai ni Kam na tsinewa mijin waccan Farida sau fin Dubu d’ari biyar Da ya sake ta har ka dauko min ita.

“To gara dai ki zagi mijin nata ni Kuma Kinga Albarka ma na Saka mishi da ya Sako min ita . Amma kar kiyi kuskuren zargin Farida.

“Allah ya tsine mata Albarka.

“Kinyi na marmari kar kiyi na tilas don Wallahi zan Baki mamaki Basma.

“Allah Ya tsine.

Ba ta K’arasa ba ya Kifa Mata Mari dama Yana cike da takaicin Abinda tayi mishi na Rufe kofa da Babu key a wurin shi haka zata wulakan ta yayi kwanan falo.

Tana Rik’e da kumatu tana mamakin Marin da k’arfin Halin sa.

“Wallahi tallahi idan kika kuma zagin Farida a Gaba na Basma zan sauwake miki igiyar Aure na tunda na Gane ni ne nake neman zaman lafiya Dake ke tashin hankali kike nema na dashi to na shirya. Dama nazo ne don na fada Miki ba kwana uku zanyi ba kwanaki bakwai zanyi a D’akin Amarya tunda ni dai a budurwa nake kallon Farida Kuma na yarda da Hakan don Kar ki ga an wuce kwana UKU kice an shiga hakkin ki shine Nazo na fada Miki Amma kina Neman Bata min Rai tunda na SHIGA wurin Farida ko tsaki banyi ba bare Raina ya Baci kullum FARIN CIKI take shayar Dani Amma ke sai hauka da son batawa mutane Rai.

Ya fice Yana masifa ta bishi da kallo tana Jin tamkar tayi bindiga.

Tunda ya bar kofar tata Bata Kuma Saka shi ido ba sai da yayi satin da ya Ambata inda Farida ta mikawa Basma Aikin ta don yace Mata Basma Bata da lafiya ne a lokacin da take sanar dashi budurwa ce akewa kwana bakwai Amma bazawar kwana uku ne Shari a ta bata .

Uzurin Rashin lafiya da ya kawo yasa ta Aminta Amma Kuma ya Hana ta taka sashin Basma wacce tayi nufin zuwa dubawa ko don hakkin makotaka Amma yace ta bari sai ya koma can.

A Ranar da ya cika kwanaki bakwai ne Suka shiga sashin Basma tare da Farida wacce take kallon Basma tayi furgai firgai tamkar wacce aka tsorata.

Basma ta kalle ta ta watsar farida tana Gaishe ta amsa kamar ana Mata Dole.

“Yaya karfin jiki ? To Allah ya Kara lafiya.

Ta Mike don Bata ga fuska ba tana Shirin fita ne Basma tace, “Ji Mana.

Farida ta dawo don taji Abinda Ake son Taji.

“Bana son Ganin ki a sashi na don Babu Had’i in Kuma kika sake Tako kafar ki a nan duk abinda nayi Miki ke kika Siya. Basma ta fada tana nuna Farida da yatsa tamkar Zata kyasta Mata ashana ta Kone ta.

“An gama Ranki ya Dade Amma ni Ina gayyar ki nawa sashin tunda na yarda ni musulma ce Kuma Banga Abinda kikayi min ba da zan katse alaka da ke in don Miji kike Hakan sai Nace kin makara tunda Wanda kikeyiwa ya gama farke miki laya Baki sani ba Amma Kuma ki sani ni Kam ba zan Daina gaishe ki ba sai dai in na Gaishe ki kar ki Amsa na fita hakkin musulunci.

“A Gaba na Basma kike fadawa Farida wadan Nan maganganun? Ke Kam dai Jaka ce Wallahi kinga da yake da mutum kike magana ta fada Miki ba zata Daina gaishe ki ba kinji Abinda yarinyar Nan ta fiki ita Kam taje makaranta ke Kam da kinje da Baki da haka ba shiyasa jahilci yake Wahalar da ke jahilar banza jahilar wofi to ba sai in kin ganta a Nigeria ba ne Zaki ce kar ta Kuma Zuwa inda kike? Kwana Biyun ki tace Nayi Miki kafin mu fita hutun amarci Amma da yake kin Soma haukace wa Baki bari kin ga irin Zaman lafiyar da zatayi da ke ba kike mata muguwar fata to ba ma Zaki ganta a Nigeria ba sai bayan watanni.

Basma ta Dube shi tana fadin, “Billahillazi la ilaha illallahu karya kake Abdullahi kace min zaku fita honey month Kai da matar ka wacce ka Auro a bazawar ni kuwa ai budurwa ta ka same ni Amma baka fidda ni honey month ba sai wacce tazo a Funko Wallahi karya kake sai dai a tafi Dani ko kuwa mu fasa tangararen balaki Wallahi ! . Banda cin Amana ta da satar kwana na da akayi har kwana bakwai shine Kuma za a ce min wai tafiya honey month? To Albarka ban Siyar ba Wallahi.

<< Tana Kasa Tana Dabo 31Tana Kasa Tana Dabo 33 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.