Skip to content
Part 35 of 60 in the Series Tana Kasa Tana Dabo by Hadiza Gidan Iko

Sagir ya yi murmushi yana Fadin

“Abba Na gode Allah Ya ja da rayuwa na ji dadi da kake fahimta ta ka kuma ba ni dama a rayuwa. Hakika na duba wani abu ne shi yasa nace ka nemi Anty maimuna ko babu komai Goggo tana fahimtar ka kuma ko babu komai Anty maimuna itace za ta iya rik’e maka su Yusra ba tare da ta duba ba itace Uwar su ba.

Kuma Goggo zata ji dadi saboda ta fahimce ka Kuma ita Anty maimunar zata fahimce ka . A yanzu Abba duk wacce zaka Auro Akwai yuwuwar kalubalen zaman ta da su yusra tunda zaman Uwar Wani da Dan wata sai an Kai zuciya nesa Amma Anty maimuna dama ta Saba da su Yusra ba zasu samu wani kalubale ba.

ISHAQ yayi murmushi Yana dafa kafadar sagir Yana Fadin. A’a”Na yarda da Kai sagir tunanin ka Mai kyau ne matuka Gaya. Kai din Yaro ne Mai Albarka Allah ta ala yayi Ruko da hannayen ka yasa Albarka a Rayuwar ka na baka WUKA da nama Sagir.

“Ameen Abba a Ara min mashin na tafi gidan Goggon yanzu.

ISHAQ ya dauko makullan mashin din ya bashi Yana Fadin

“Na San dai sai na ganka Sagir in ka samu mashin sai ka zagaye garin Nan Allah ya tsare..

Sagir yayi murmushi Yana karbar makullin mashin din ya wuce Yana Fadi

“Allah Abba iyakata gidan Goggo kawai ba zan matsa daga can ba.

Ya tayar da mashin din ya wuce inda ishaq ya zauna Yana tunanin Nisan Hangen Sagir da Kuma irin yadda Goggo zata Karbi maganar kafin ita maimunar.

Maimuna itace autar su wasila a wurin Goggo Mai suna hurera .. Ya’yan Goggo biyar ne Mata Hudu sai namiji Daya . Ma aruf ne babban sai karima wacce take can Lagos tana Aure . Sai murja sai wasila sai maimuna.

Maimuna kuwa yarinya ce Mai Hankali da tunani don sau tari ta Fi wasila tunani Wani Abun ma sai ta nuna Mata ko zata Gane.

Maimuna Yar islamiya ce ta Sosai don zaiyi Wahala kaga maimuna cikin Yan Mata ana sharholiya ko shargalle. Ita ko kawayen ta ka Gani ka San Allah yayi Mata wata Karishma ta Hankali. Hatta da shigar maimuna ta mutunci ce ba irin ta Yan Matan Zamani ba daga makaranta sai gida sai Kuma zumunci hakika akwai ta da zumunci matuka Gaya har ta Samu wannan yabon daga Ahalin su hatta da Goggo ta Yaba mata akan zumuncin ta.

Har Rana an sakawa maimuna ita da wani sayyadin makarantar su da ya Yaba akan ta ya Kuma shiga wurin ta Suka daidai ta har Magana tayi Nisa Bai wuce wata uku ya Rage ayi bikin ba iyayen sa suka Aiko cewa sun fasa Kuma Babu wani Dalili. Aka mayar Musu da kayan su Nan ba a nemi Jin Wani Dalili ba inda Goggo take tambayar maimuna ko Wani Abu ya faru tsakanin ta da sayyidin Wanda har ya fusata shi yace ya fasa? Maimuna tace Wallahi Babu Abinda ya hada mu Goggo kar ma ki damu kanki shi Aure dama nufin Allah NE Wani baya Auren matar da ba tashi ba haka ma mace Bata Auren mijin da ba nata ba mu dauka shi din ba Mijin bane da mijin yazo Goggo sai kiga anyi an gama. In ma nayi mishi Wani Abu Ina ganin idan Akwai uzuri sai a fara Jin ta baki na kafin a yanke mini Hukunci Amma Tunda fasawar ce maslaha Allah yasa hakan ne Alheri don Allah Kar ki damu Goggo Babu abin damuwa a Nan ciki.

Goggo ta kada kanta cike da jimami tace
“To maimuna Allah ya kawo Miki Wanda ya Fi shi ai Rahamar Allah yawa gareta ba ga Yar Uwar ki ba tunda ta balle ta wulakanta Aure sai fa kayan ta turo mini ita Kuma ta shiga Duniya ni na Rasa Abinda wasila take Gani a cikin Rayuwar da ta dauka wai ace mace batayi karuwanci da kuruciya ba sai da ta zama mace ? Wannan Abu ya dame ni maimuna ni Yaya Zanyi? Sai hawaye ya balle Mata ta Soma kuka Abinda ke motsa zuciyar maimuna kenan ganin HAWAYEn Goggo. Duk da ta san wannan maganar ta fasa Auren ta itace damuwar ta sai Kuma ta hada da damuwar wasila sai abin yayi Mata yawa Dole Kuma tayi kuka.

Maimuna ta Soma share mata hawaye tana Fadin, “Kiyi Hak’uri Goggo ai kin San musulmi da Kuma wanda Allah yake so shine Ake jarrabawa don aka Imanin sa a Kara mishi daukaka kiyi Hak’uri kiyi kuma ADDU A in Sha Allah dukkan Wani Bak’in ciki da kikayi sai ya zama FARIN CIKI Goggo.

“To Allah yasa maimuna ni kadai na San yadda nake ji idan na tuna wasila da Abinda tayiwa yaron Nan ISHAQ don kawai tana ganin Babu ta same shi Amma Babu komai Allah ya shirye ta ke Kuma Allah yayi Miki zabi mafi Alheri ni Banda ma don Kar nayiwa yaron Nan ISHAQ shisshigi ko kuma ace Abinda Yar Uwar ki tayi Mishi yasa ya yiwa Ahalin wasila Bak’in fenti ai da nace yazo ya nemi Wallahi Amma ba Zanyi Hakan ba don zai ga ko kema zakiyi mishi Abinda yar Uwar ki tayi Mishi duk da ni Ina da tabbas akan ki maimuna.

“A a Goggo shi namiji ma ai ba ayi Mishi haka da dai shi yaji ya Gani ana iya yin Hakan Amma in akayi Hakan ko don girman ki da yake Gani ba zai Musa ba Kuma wata Kil a Ranshi yaji ya cutu Amma ba zai iya musu ba Kinga an Saka Shi a cikin damuwa ADDU AR nan DAI da na Rok’e ki ita Zakiyi Mana sai kiga ni da shi Allah ya kawo Mana mafita wacce bamuyi zato ba.

“Wannan ma gaskiya ne maimuna ALLAH ta ala ya kawo Muku mafita ta Alheri Kuma in Sha Allah za a ga daukakar da Allah Zaiyi muku wacce kowa Zaiyi Mamaki.

Tunda Goggo tayi wannan hasashen na Auren ISHAQ ga maimuna sai Al Amarin Yayiwa maimuna tsaye a ZUCIYA ta Soma Jin Wani Abu akan ISHAQ Mai kama da son Aure Wanda Bata hango aibi ko Babun shi ba.

Duk yadda ta so ta fidda Al Amarin daga Rai da ZUCIYAR ta yaki barin ta Amma sai tayi ADDU A Allah ya zaba Abinda yake Alheri

Abu kamar wasa maimuna ta kasance cikin Wani hali Wanda Bata ma fatan ko Goggo ta San da zaman shi a zuciyar ta don tana ganin ya zama abin kunya.

Kwanaki da yawa ta kasa samun sukuni Amma dai tana ta boye abinta a Ranta.

Watannin Biyu Ranar sai ga ISHAQ ta dawo Daga makaranta ta samu a gidan Yana durkushe a gaban Goggo ya kawo Mata sabulu da omon kilin har da shimfaka.

Wani irin duka da taji a kirjin ta Saboda afirgita da ganin ishaq da tayi Amma tayi ta danne Abinda yake Ranta ta duka tana Gaishe shi Yana Zolayar ta da malama dama haka yake ce mata malama.

Ta wuce d’aki tana murmushi don tana Jin Wani Abu a Game dashi tunda Goggo tayi sub’utar bakin hada su take cikin wani irin hali Wanda ko sayyadin makarantar su Bata ji irin Abinda take ji a game da ISHAQ ba Amma tayi kokarin danne abinta

Kwanaki biyar da Zuwan ISHAQ a gidan har ma ta manta sai kawai taji Goggo na Fadin

“Ni Kam jiya nayi Wani MAFARKI maimuna Wanda ya tsaya min a Rai har nace ko don na sakawa zuciya ta ne shiyasa ya zauna min a Rai har nake MAFARKI Dashi ? Wai sai Gani jiya Ina mafarkin wai an Daura Auren ku da yaron Nan ISHAQ Ina ta murna . Ai kuwa Ina farkawa nace ALLAH ka Amsa in dai da Alheri ka kaddara Auren Nan ko don naga nayiwa yaron Nan halaccin da wasila batayi mishi ba . Ni dama Ina tsoron wacce zai Auro ko don Yan yaran Nan su yusra duk da yace min suna hannun suwaiba.

Maimuna tayi sak jiki a Sanyaye tana kallon Goggo irin FARIN CIKIN da take Yi akan MAFARKI kawai da tayi . Shin idan Goggo taji Halin da take akan ISHAQ Anya ba zata Kira shi tace taho na baka Auren maimuna ba? Idan akayi Hakan kuwa anya anyiwa ISHAQ Adalci musamman da aka San ba zai iya mayar da kyautar baya ba saboda kimar Goggo da yake Gani ?

Sai Al Amarin ya Zamo wa maimuna sabo Wanda ya zama Bata da burin da ya wuce taga ISHAQ yazo gidan amma shiru sai ta Kuma mikawa Ubangiji Al Amarin tare da Neman zabin Ubangiji.

Tunda Goggo tayi Mafarkin Nan sai abin ya zama kullum maganar ta kenan . Babu Ranar da zata fito ta komawa Ubangiji Goggo Bata ce
“Oh ni hurera wannan Abu Yana Nan a Raina Allah Kai kadai kasan Dalilin zaman sa a Raina Amma Allah Alheri muke nema Daga gareka duk inda Alheri yake Allah ka Kaimu ko bamu shirya zuwa ba. Duk Kuma inda babu Alheri Allah ko mun Daura niyar tafiya Allah ka kawo Silar da tafiyar zata watse mu ma manta da tafiyar.

Tun Goggo na laguda maganar har dai yau da gobe ta sa ta Daina tayar da ita ba don ta manta da ita ba.

Manema masu yawa suka shiga zarya wurin maimuna Amma duk Wanda yazo sai taga baiyi Mata ba. Idan Goggo tayi Mata magana sai tace

“Goggo baiyi min ba ne. Sai Goggo tace, “Babu dole kuwa maimuna Allah ya kawo Nagari.

A yau laraba maimuna tana Shirin fita makaranta sai ga Sagir Yana murza mashin Yana Kara inda Goggo ke fad’in

“Wannan kuwa sagir ne shi da hanyar sa shaida ne da ita in dai ya samu mashin sai ya cikawa mutane kunnuwa.

Maimuna tayi murmushi tana Fadin, “To Goggo Lokacin Abu ayi shi ai tunda ya iya gyara ai ya murza da kyau tunda ya San Kan tsiyar.

“Ai ke dama yaushe Zaki kwarewa Sagir baya ?

Sagir ya shigo Yana Fadin, “Goggo taho na Kai ki anguwa daga Nan har Gago ko bindawa ga mashin a Hannu na. Goggo tayi maza tace

“Allah ya tsare ni Hawa tuk’in ka Sagir in dai ba Ina son Rasa yan Hak’ora na ba ga dai Uwar ka Nan dauke ta ka Kai makaranta.

Suka kyalkyale da Dariya Yana Fadin

“Ai Anty maimuna Bata shakkar Hawa kece dai kika kasa yarda na goya ki. “Ba Kuma zan yarda ka Goya ni ba don na San Rami zaka afka ni koma nace kabari salamu alaikum.

Maimuna ta ce, “Muje ma sagir ka sauke ni makaranta tunda Goggo ta kasa yarda ka iya tuk’i ni Kam ai na jima da yarda ka iya tunda na hau Kuma na Gani.

Ya dago Yana Duban maimuna Yana Fadin

“Wannan tafiyar fa anty maimuna Taki ce muje D’aki mu Saka labule Goggo kin yarda muyi Sirri? Kin San sai ka fita hakkin mutum in dai ka samu mutum Biyu Dole ne ka Nemi izinin ganin Dayan.

“To ni na Isa na SHIGA tsakanin Uwa da danta ne?

Suka shiga d’aki sagir ya Duka Yana Gaishe da maimuna tana tambayar shi yaje wurin su yusra kuwa? Yace yaje suna lafiya.

“To Allah yasa dai lafiya Sagir? Ta tambaye shi tana kallon shi.

“Lafiya Lau Anty maimuna Dama Abban mu ne ya Aiko ni don Allah ki fahimce shi na San kin San komai Allah NE yake yin sa ni dai na gamsu don Allah ki fahimce shi yace Nazo na same ki na fada Miki Yana son yazo ku daidai ta Amma Bai san yaya zaki dauki Al Amarin ba shi da Goggo yace na Fara yiwa magana sai naga kece ya kamata a fara yiwa kafin ayiwa Goggo don in har Baki Aminta ba kar Goggo ta tursasa Miki don haka kar ki Cuci kanki Anty maimuna ni dai na gamsu da ke ko don adalcin ki na Kuma tabbatar da Zakiyi mishi Adalci ki Kuma yiwa su yusra shiyasa ma na karfafa maganar.

Wani irin Abu da maimuna Taji Yana Sauka a ZUCIYAR ta Mai kama da ganin MAFARKI har dai ta tabbatar ba MAFARKI bane gaske ne ta Zubawa Sagir ido Shima Yana kallon ta da son yaji Abinda zata ce.

“Baki ce komai ba anty maimuna idan har kinji Al Amarin baiyi Miki ba don Allah Kar ki Dubi ni na kawo Miki maganar ki Dubi maslahar ki wallahi zan fahimta Kuma Shima Abban zai fahimce ki.

Ta Sauke AJIYAR ZUCIYA tana Fadin
“Sagir naji Abinda kace Kuma na yarda Amma ka sani bani da Bakin magana sai Abinda Goggo tace. Ba zan iya yanke Hukunci kaina tsaye ba Alhalin ga Goggo da Sona da k’i na matukar Goggo na Nan sai Abinda ta yanke a Kaina don Haka ka samu Goggo ka fad’a Mata na tabbatar da zatayiwa Abban ku Adalci ni Kuma Zanyi mata biyayya akan Dukkan Hukuncin da ta yanke Koda kuwa bana so . Idan tayi na am da Al Amarin Nan sagir Nima nayi idan kuwa batayi na am ba to dole Nima Zanyi don Haka ka same ta ka fad’a Mata komai idan na dawo makaranta Zanji Komai.

Ta Mike tana daukar Jakarta Shima ya Mike Yana Fadin, “To Anty Nagode Kuma in Sha Allah na San Goggo zata yarda kome kenan zan kira ki na fada Miki.

“To shikenan D’ana na kaina. Ta fice tana yiwa Goggo sallama tana fad’in “Har Kun gama Sirrin ne ?

“Ai gashi nan Goggo kema ai kin shiga cikin Sirrin Sako ne aka bashi ya kawo min ni Kuma nace ya same ki ya fada Miki idan na dawo zanji Abinda kika yanke don Kar nayi latti.

Goggo ta dubi Sagir tana Fadin “Gashi ta yi tsami har zamu ji.

Ya zauna Yana Fadin. “Bata yi tsami ba fa Goggo kinji kinji Abinda Abba ya turo ni don ni da kaina naga dacewar su na Kuma kawo mishi shawarar ya Kuma yarda shine yace Azo a same ki ni Kuma sai naga kafin ke ita Mai Yi ya kamata a fara tuntuba Kinga Idan tace ba tayi ba ma sai magana tazo gareki ba don ma kar ki tursasa ta . Amma da Nazo mukayi magana sai tace ba zata iya Cewa komai kina Nan ba sai abinda kika ce ba zata yanke Hukunci Kai tsaye ba sai In kin yarda don ko Bata so kika ce kin yarda to itama ta yarda shine tace Nazo na fada Miki ni Kuma na San Goggo daga gareki ba za a Samu matsala ba Kuma na Kara lura da Cewa Anty maimuna itace daidai Abban mu Domin kuwa ta nuna zatayi biyayya Goggo ni Wallahi da ace nazo Duniya ma da ba zan yarda ya Auri Mamar mu ba in dai ga Anty maimuna Amma kaddara ta Riga fata Amma Goggo ga ni a gaban ki ni Kuma Nazo da yawun Abban mu na Kuma San ba Zaki juyawa Abba baya ba ki dauka ma Abban ne a gaban ki me Zaki ce?

Goggo da take Duban Sagir da idon ta Kur ta kasa kiftawa tana son ta Gane shin da gaske ne Abinda take ji ko kuwa ire iren mafarkan da ta Saba Yi ne? Ta Kai Hannun ta kan Sagir ta shafa ta tabbatar da ba mafarkin take ba sai kawai ta fashe da kuka.

<< Tana Kasa Tana Dabo 34Tana Kasa Tana Dabo 36 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×