Skip to content
Part 37 of 66 in the Series Tana Kasa Tana Dabo by Hadiza Gidan Iko

Shama ta kyalkyale da dariya tana fadin

“Wai tsinuwar ce har Dubu Ashirin Haj ta? Ta kuma kyalkyalewa da Dariya irin ta iya Shege kafin tace…

“Abin naki ne da mamaki Yan Mata . Ni fa Banga Dalilin wannan JANHURUN masifar da kike jawowa ba har da Wani munafukin koke koken ki . Miji ne kince ba Kya Yi Kun Rabu kowa ya kama tashar sa to in ba tsegumi ba Ina Ruwan na goye da gwalo Saboda Allah ? Ko kuwa kina nufin kishin Auren sa kike?”

Wasila ta Kuma Jin kuka na shirin kece Mata don har ga Allah wannan Zancen Auren ISHAQ yayi Mata ba zata matuka Gaya Bata zaci ishaq da Auren maimuna ba.

“Ban za ci hakan ba har ga Allah Shama. Maimuna fa? Kanta ce kusan ta hudu akwai mutum uku a tsakanin mu don dai Allah yayi musu Rasuwa wasu ma Basu zo da Rai ba. Itace autar mu yarinya ce k’arama Shama da kadan fa ta girmi Sagir ana dab da Yi min Aure aka haife ta Kuma saboda Allah sai ace itace wacce ISHAQ zai kwabe a Gaban ta? Shi Kuma da yake Dan akuya ne duk Matan Duniya ya Rasa wacce zai Aura sai kanwa ta don ya tura min Bak’in ciki? Yanzu fa Yana iya Cewa kwana zaiyi da ita? Ta tambaya idon ta fal da kwalla.

Shama tana Rik’e da Baki tana mamakin kalaman Wasila.

Shama ta cabe tambayar Wasila tana Fadin.

“Sai dai kar a kuma don ba na Jin zai Zuba Mata ido tunda ba don Hakan ya Auro ta ba.

Wasila ta cije Baki tana jin Bak’in cikin wannan Aure Wanda ta tabbatar Goggo ce ta assasa shi da sunan maye girbi tunda tayi Imani Goggo tana girmama ISHAQ Idan kuwa haka ne Goggo ta darsa Mata Bak’in ciki marar yankewa don idan anyi Hakan da manufa to Kuma hakika anyi nasarar Hakan don a yanzu ne ta gane ISHAQ Yana Nan makale a zuciyar ta Kuma ba son sa ta Daina ba kawai dai Babun sa ce Abinda ya taka Rawar Rabuwar su . Sai dai Kuma gashi a yanzu ta samu kudin da takewa mayata Amma Kuma wannan bak’in cikin da ya darsu a zuciyar ta a yau ya shafe mutuncin kudaden da take Homa da barazana akan su Domin kuwa tunda ta baro gida Bata Yi karo da kunci da Bak’in ciki da damuwa irin yau ba. Bata nadama irin ta yau ba.

“Kinga fa Hajiya kar wannan ya zame miki damuwa ita fa duniya da kike gani Inna arari wasi an ce tana da yawa da Fadi shi fa wancan mijin Naki ba komai bane akan wasu Mazan in kika Saka Al Amarin su a Ranki Wahala kawai Zakiyi tunda ke da kanki dai yanzu kin San yayi Miki Nisa tunda ya dauko Yar yarinya danya shakaf Kuma dai Dole ki janye jikin ki gara kawai ki fuskanci Abinda yake mafita a gareki shawara ce wannan kuma a kyauta.

Wasila tayiwa Shama Wani matsiyacin kallo don tafi ganin wannan maganar a matsayin Arashi ba Wai shawara ba . Zuciyar ta a kufule tace.

“Wallahi Nayi kaico da Ranar da na Fara haduwa da ke Shama na tsinewa wannan azal da ta hada mu Yafi sau D’ari da Hamsin.

“Ayya Haj ai ko kafin haduwar mu ai kin tafasa kin kone ba Shama ce ta kangarar Dake ba Dama can a bushe kike.

“Wa ye ya bani shawarar kashe Aure na?

“Ai ni taimakon ko nayi don nasan zunubi Biyu kike dauka in kika ce da Auren ki Zakiyi wannan yawon gara kiji da Guda Daya Amma in kika ga laifi na akan wannan Al Amarin Baki da Adalci. Ko ni na Baki shawarar kashe Auren ki ne ke kuwa wane irin tunani ne da ke da Baki auna Abu a mixanin Hankali? Ai ke ba yarinya bace Uwar Yara ce Amma Baki San Abinda ya dace da ke ba? To kaddara ma ni na Baki shawarar kashe Auren to yanzu Kuma shawarar da nake Baki itace ki koma ga Auren ki shikenan ko kuwa da saura? Ta fada tana kallon wasila da ke kuka bil hakki da gaskiya don idan Akwai wata damuwa a Ranta yanzu to maimuna ce da ishaq Wanda take hango Rayuwar su da sunan Aure.

Shama taja tsaki tana Fadin, “Wallahi Dan Adam dai butulu ne duk yadda kayi mishi abin Arziki sai ya nuna maka Uwar ka dai Baka ce Bata hada hanya da farare ba. Kin manta yadda kika zo Abuja Hajaran majaran kin manta yadda na hada ki da manyan mutane kika samu kud’in ki Amma yau ni kike tsinewa sau fin Dubu Ashirin saboda na Baki masauki nayi Miki hanyar ganin manyan mutane shine tukwici na ? In Banda Dubu d’ari Biyun da kika bani sau biyu kin Kuma bani kudin ki? Idan nace haya Zakiyi a Gida na nawa kike zaton zan karba ? Ko kuwa don Ahalin ki sun tura Miki Bakin ciki da Auren Yar Uwar ki ga Mijin ki sai ki Rufe ido ki manta da wanda yayi Miki kirki? Ni Wallahi in ma iyayen ki ne sukayi Hakan sun burge ni don sun San dattako. Kuma ni da kaina na fada Miki ba a wanye lafiya da ja da iyaye ko da Mijin Aure. Kinga Idan kin San kina da matsala da Dayan su Wallahi gara kije ki gyara tsakanin ku don ni da Kaina na Gane Akwai matsala a tare da ke wasila tunda a yau kina cikin wata na tara a garin Nan Amma banji kince Zaki Gida ba . Ko Baki da iyaye ai ba Zaki Rasa madadin su ba bare Kuma Yan Uwa. Wallahi kyauta nake Baki wannan shawarar bana son ko sisi.

Cewar Shama da ta Mike ta wuce ta bar wasila da share HAWAYE tana bin bayan Shama da kallo har ta fice daga falon tana Jin Wani irin turirin Bak’in ciki.

Har anzo gab’ar da Shama ke Mata Gorin Dan Gidan da ta Ara Mata ? Me Shama take nufi da maganganun ta?

Ta Soma safa da marwa a falon tana Jin Lallai ya zama Dole ta barwa Shama Gidan ta don ba hak’uri gareta ba wata Rana za a iya yin Abinda bashi da kyau.

Kwanaki Biyu da samun wannan Labarin na Auren ISHAQ da maimuna Wanda ya haddasa mata zazzabi da Ciwon Kai har ta kasa fita ko Ina ta Kuma Ji bariki ta ishe ta haka kudi dai Kam gasu Nan a account din ta lode Kuma duk Wanda ta samu ta hanyar bayar da jikin ta . A yanzu Kam ta gama da bariki don ta Gane Ba kudi ne jigon Rayuwa ba. Rayuwa na Nan tare da FARIN CIKI Amma a yau Kam gata da kudin da sune suka zama jakadun Raba ta da mijin ta Amma Kuma bakin cikin da kanwar ta ta samu mijin nata ya dusashe Mata girman kudi da take Gani . a yau sai soyayya ta nuna Mata ita din daya ce Bata da Kari.

Sai dai kuma Dukkan Wanda tayi tarayya da shi a bariki babu Namijin da ya dasa Mata soyayya a ZUCIYA irin Mai gemu shine Namijin da zata iya Aure a yanzu Domin kuwa kaf Mazan da ta Sani a Mazan bariki shine ta kasa mantawa Kuma take Jin Zatayi komai don shi.

Ta jawo waya tana Kiran wayar Mai gemu wanda sai da ta jera mishi kira biyar Bai dauka ba. Ta kasa hak’uri da Kiran har dai tayi sa ar da ya dauka.

“Shikenan Kuma Mai gemu ka yada ni? Ta tare shi da fad’in Hakan…

“Yi Hak’uri haj ban fa Gane Mai magana ba?

“Wai da gaske baka Gane ba? Ya amsa da fad’in.

“Naga dai wayar Babu suna Amma kamar na san lambar.

“Wasila ce Yanzu ka Goge waya ta kenan Mai Gemu?

“Au ! Wai Mai shawarma ce ? Yi Hak’uri Wallahi da yake kaina yayi zafi yi Hak’uri to ya kike?

“Lafiya Lau alhamdulillah Gani nayi kwana biyu Babu nema shine nace bari ni na neme ka.

“Ayya na kuwa Gode Sosai Haj Amma don Allah Ina Rokon ki Goge lamba ta a wayar ki don yanzu Kam na sauka Daga layin nan Kuma ni a yanzu ma nayi Aure na Wanda Rashin samun Abinda nake so ne ya kaini ga biye biye to Allah ya bani macen da ta mallaki komai don Allah ki Goge lamba ta kar ki Kuma Kira na don bana son Abinda zai batawa matata Rai.

Ya datse wayar Bai Kuma Bata Damar tankawa ba. Wani Abu ya tsaya mata a zuciya har taji idon ta Yana yaji yaji.

Ta jima tana kukan zuciya tare da na ido. Gaba Daya Rayuwar bariki ta fice mata Aure kawai take son tayi ta huta da wannan Al Amarin Amma Kuma maganganun Shama suna Mata yawo a Rai musamman Gorin Bata zuwa gida Ashe tana Nan tana Ankare da ita ta Kuma gano akwai gagarumar matsala a tsakanin ta da Ahalin ta tunda har ta Saka Mata idon Bata tab’a zuwa gida ba tsayin wata Tara.

To Amma yanzu da wace fuskar zata je gida? Saboda taji maimuna ta Auri ISHAQ? Saboda ta Gaji da Rayuwar bariki?

Ba zai yuwu ta tafi Gida a yanzu ba sai ta tabbatar da ta samu mijin Aure Amma Kuma waye zata Aura din? Babu Wani da take Jin shine ajin Auren ta irin Mai gemu shi Kuma ga karshen wulakancin da yayi Mata har da gargadin kar ta sake Kiran wayar shi.

Duk yadda taso kaucewa hada kanta da honorable Gona Dole shine wanda take da sauran dama akan shi don ta tabbatar ta gama kama shi.

Don haka taja waya ta Kira shi tana Fadin.

“Honorable kana gari ko Ka koma kebbi ne? Ya amsa Mata da Yana kebbi Amma yau din zai taho tunda tana son Ganin shi.

“Ok to Ina jiran ka.

“Akwai wani Albishir ne sweetyn honorable?

“Eh Amma sai ka zo din.

A Ranar kuwa honorable Gona ya biyo jirgi daga birnin kebbi zuwa Abuja ya Kuma turo Da mota aka zo aka dauki Wasila.

Yana rungume da ita akan katon cikin shi Yana tarairaya yake tambayar ta meye damuwar ta?

“Babu wata damuwa kawai dai na ga kamatar muyi Aure don na fara gajiya da wannan Rayuwar. Shine nake so muje da Kai can gidan mu ka tura magabata a tsayar da magana.

Yayi Dariya Mai sauti Yana Fadin.

“Me yasa ki yin wannan tunanin? Ai ni yanzu Babu ajandar Aure a tsari na mata na Biyu suna can birnin kebbi kuma su ma din Banda sun Tara Ya’ya da na sauwake musu don ni bana son takura nafi son na Yi Rayuwa ta a Bude ba a Rufe ba don Haka gaskiya ba zanyi Aure a yanzu ba me na Rage ki da shi ne irin na matar Auren? Ina gamsar da ke Ina Baki kudi ga kuma gidan Nan na yarda kiyi komai kike so me kike so bayan Hakan ? Ko kema irin na wadan can sakarkarin masu fadan in na mutu wance ce Mai gida da kaso Mai yawa tin da Rayuwa ta ana min kasafin gado? To ni ko zanyi Aure ma sweety ai ba zan yarda a Kuma min haihuwa ba bare ma ba zan Kuma Aure a Yanzu ba.

“Ina ganin kuwa Rabuwar mu ita tafi tunda Nima ba zan Kuma wannan Rayuwar ba kamar yadda ba zaka sake Aure ba kaga kunyi Hannun Riga Ina Maka fatan Alheri.

Ta Mike daga jikin shi Yana Fadin.

“Ji Mana sweetie? Me kike nema a cikin Auren ne? Kar kiyiwa kanki katan katana mutuwar bakin almuru ni Ina ganin in dai ba Lallai kema gadon kike son Soma lissafin lokacin mutuwa ta ba gara ki tsaya kudin da Zaki samu suna iya fin tumunin takabar ki tunda zan iya Baki ko nawa kike so Amma Kuma kina da Damar ki ni dai ba zan iya Wani Aure ba yanzu gaskiya.

“To mu Hak’ura da Juna mana? Ni ma ba zan iya wannan Rayuwar ba a yanzu kawai mu saki hannun Juna honorable Nagode tunda har zaka iya son mu amular banza Dani Amma ba zaka iya Aure na ba na Kuma San Dalilin da ya sa Hakan shine tinda Ina ne baka Sani ba a jiki na? Kana kallo na gallafirin Duniya.

“Kwarai kuwa har da wannan ma kawaici nayi Miki Amma yaushe Zanyi Hakan?

Ta Mike a fusace tana daukar Jakarta duk Kiran da yake Mata Bata iya tsayawa ba ta fice tana Kara jin Lallai maganar Shama gaskiya ce irin mai dacin Nan wacce take da Ciwo a lokacin da ake Fadawa mutum ita Amma idan masara taji Wuta ita da kanta take fashewa.

Ta fito kenan daga gidan inda lurwanu ya taso wato Direban da yake faman sufurin Kai ta da dauko ta.

Ya taho da Sauri Yana Bude mata kofar Motar Amma tayi maza ta daga mishi Hannu tana fadin.

“Nagode lurwanu Amma Yi Zaman ka zan tafi a k’asa Allah ya biya.

Tana shirin ficewa ne kuma motar senator Yan doma ta shigo gidan wanda ya gigice a kan Wasila wacce ya yiwa gani daya yaji tayi mishi irin yin da ya tabbatar da Babu nadama.

Tana Shirin fita shi Kuma ya danna Mata hon Amma Bata iya tsayawa ba ta tsayar da Napep ta shige inda Yan doma Kuma ya koma mota ya Rufa mata baya dama don yazo ya samu lirwanu ne don ya Kai shi inda suka mayar da ita a lokacin da Gona ya Hana ya Ganta Kuma yayi ta Mishi nacin ya bashi lambar wasila Amma yana mishi rawani Ya Hana shi ..don haka sai ya tuna ai lurwanu shine ya mayar da ita a Ranar don haka yazo don ya tambaye lurwanu Ina ne inda suka maida ita? Sai Kuma gata ya Gani wata sa a don haka ya faka motar ya fito Amma Kuma Yana fitowa tana shiga Napep ya dawo Shima ya dauki motar ya Rufa mata baya.

Sai dai kafin ya yi kokarin kamo Napep din tuni ta shige cikin go slow ta bacewa Ganin shi duk kokarin shi na Ganin ya kamo ta Amma ya kasa samun ta Dole ya koma gidan gona ya tambaye lurwanu wacce ya fada mishi wacce fa fita a lokacin da ya shigo inda lurwanu ya Gane wasila ce don haka ya fada mishi a garki take ya Kuma bashi full address har da sunan Shama Mai gidan.

Wasila da ta sauka Napep ta biya shi kudin shi sai ta yanke shawarar komawa Gida ta koma gida ta Rungumi Rayuwar da zata fuskanta..

Shama ta Dube ta tana fadin, “Da dai kin bari har ki samu Wani da zaku daidaita in yaso sai ki tafi da shi ki nuna a matsayin Wanda Zaki Aura Al Amarin zai Fi zo miki da sauki.

Tayi shiru tana auna zancen Shama Amma Kuma ta Gaji da zama a gidan Shama Dole ta siyi nata gidan in ma ba zata iya kowa gida ba tunda Shama tayi Mata Gorin Nan taji Lallai wata Rana zata ce mata ta fita ta sallame ta.

Knocking din da akayi ne ysa Shama fita don taga ko waye yake nocking inda wasila ta bi bayan ta da kallo cike da Bak’in ciki.

Shama na budewa tayi karo da senator Yan doma Wanda ta San shi Sosai Amma Kuma baya harka da Mata shi Kam yafi harkar sa can.

Tayi saurin sakin fuska tana Fadin, “Barka da yamma distinguish shigo daga ciki Mana?

Yayi murmushi Yana Fadin, “Na gode Amma na biyo wata ne Mai suna wasila ko tana Nan?

“Kwarai kuwa tana nan distinguish ko na sauke ka a masukin Baki Mana sai ta same ka a Nan kamar Babu Sirri ko kuwa?

Ya bude kofar Motar ya fito Yana Fadin, “Na gode”.

Da sauri Shama ta Bude mishi kofar masaukin Bak’i ya shiga ya zauna ta wuce ciki tana fadin zata kira mishi Wasila.

<< Tana Kasa Tana Dabo 36Tana Kasa Tana Dabo 38 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×