Skip to content
Part 39 of 75 in the Series Tana Kasa Tana Dabo by Hadiza Gidan Iko

Tunda Wasila ta shiga dakin ta zauna wata irin muzanta ta same ta ba don komai ba kuwa sai Kalmar karuwancin da Goggo ta Kira mata. Wallahi Bata taba kawowa Ranta Jin kalmar daga Bakin Goggo ba. Kai ko Wani Can Banza wofi Bata zaci Jin Hakan ba . Sai Kuma zuciyar ta ta shiga Bata Aikin fassara Mata sunan Abinda tayi idan ba karuwancin ba?

Ita da ta San gaskiyar magana kenan karuwa ce ita. Gaskiya Bata tab’a yin kama da karya ba ko da an Yi Mata kwaskwarima kuwa.

Amma kuwa in Banda Goggo da ta zama ita har ta furta Mata kalmar Nan taci ta cinye lafiya Amma Wani banza a Banza can taka Haye Wallahi Bai Isa ya fada Mata hakan ya wanye lafiya ba zai Gane barno ba gabas take ba tana can arewacin Nigeria.

Ta kuskuta tana tuna maimuna da taji ana maganar wai laulayi take wai har ISHAQ ya iya duban maimuna da wannan harkar.

Wani matsiyacin Duka ya naushi zuciyar ta tana Jin tamkar tayi Aman ZUCIYAR. Idan tana hango irin Hakan a zuciyar ta shine take Jin tamkar tayi bindiga ta fashe ISHAQ ya cuce ta . Haka maimuna ma taci Amanar ta da har ta yarda aka hada su Aure don a tura Mata Bak’in ciki.

Ta Mike ta fito don tayi alwala Tayi sallar la asar wacce ta kubce Mata har gashi ana dab da Kiran magaruba.

Ta fito taga Goggo tana kwashe tuwon ta tayi Mata sannu da Aiki Amma Bata Amsa ba sai ma Kara tamke fuska da tayi tana kwashe tuwon ta.

Ta nufi butar Goggo ta Kai Hannu zata dauka Goggo ta katsa mata tsawa.

“Kar ki kuskura ki taba mini buta.

Ta janye hannun ta tana kallon Goggo cike da Mamaki.

“Ai ni banyi zaton ma kina salla ba Wallahi don mutumin da yake Kallon gabas bana zaton zai iya aikata zunubi irin naki Domin kuwa sallar sa zata Hana shi aikata alfasha to koma kina yin ta Sha Ruwan tsuntsaye kike yi.

Tayi tsaye sake da Baki tana kallon Goggo da fututtuke tana masifa.

“Haka Kawai sai ki kama min buta da kazantar ki ki Goga min JANHURUN masifa? Ai ni Wallahi kyankyamin ki nake tun Ranar da Allah ya nuna min Abinda kike naji a Raina kin zama kayan kazanta to a na me da Zaki kama min kayan amfani? Ke da kanki ki sun suna jikin ki zakiji Karni kike Wallahi.

Jiki a sanye wasila ta koma d’aki idon ta Yana fidda kwalla ta dauko mayafi ta fita siyen fiyo wota ta dawo da Leda ta dauki Daya ta shiga bandaki ta kama Ruwa ta fito tayi Alwala ta gama ta ja sallayar Goggo zata shimfida Nan ma Goggo ta fige abinta tana Fadin.

“Wai ni Kam wahayi akayi Miki da taba mini Kaya na ne Halan? Nace kyankyamin ki nake ko Baki Gane bane? Nan gidan fa don ya zamo naku da nawa Wallahi wasila ba zan Baki masauki ba Amma Ina so ki Gane muhallin zaman gidan kawai kike da shi Amma Dukkan Wani Abu da kika San nawa ne kar ki Kara tab’a shi in Kuma kika tab’a Wallahi wulakanci Zanyi Miki.

Kuka ya kwacewa wasila ta zube a Gaban Goggo tana Fadin

“Don girman ALLAH Goggo ki yafe mini kuskuren da nayi Miki Wallahi banyi da niyar na bata Miki ba.

“In ma kinyi da niyar ai Baki Bata min din ba kanki kikayiwa sai Kuma Ubangijin ki Amma ni me kikayi mini ? Ai ni Baki yi min komai ba kima Daina Roko na wata gafara wacece bani da ita Nima nake a wurin ALLAH. Kar ki Kuma Roko na kinji na fada Miki.

Kuka wasila take tamkar Ranta zai fita Bata tab’a zaton Hakan daga Goggo ba Amma Dole ta kiyaye.

Kwanan ta Biyu a gidan inda duk abinda wasila ta taba zataji masifar Goggo Amma sai dai ta Bata hak’uri. Kuma da ta tab’a Abu ko da Akan kuskure Goggo zata jefar da abin wai ta gama da shi.

A Cikin kwanaki Biyun da tayi Dole tasa ta mallaki kayan amfani da kudin ta don Abinci Kam Goggo na Bata Amma fa a kwanon ta haka gaisuwa In ta Gaishe ta zata amsa daga Haka Babu komai a tsakanin su sai ma in Goggo taso masifar ta zatayi ta fada tana Arashi da da bace bacen ta

Yayan su ma aruf yazo gaishe da goggo ya kawo Mata kayan Abinci don Yana Aiki da gidan kifi na sauki fish Kuma Yana Samun kud’i don haka shine jigon Goggo komai shi yake Yi Mata. Duk kwana biyu yake Zuwa yaji Abinda Goggo take bukata a kawo Mata don haka a yau da yazo ya samu wasila ya kalle ta Yana Fadin

“Yaushe kika zo garin? Ke kuwa wace irin lalacewa ce ta same ki wasila? Kina mace Uwar Yan Mata Kuma idan Ya’yan ki sukayi haka kice musu me?

“Ku yafe mini Yaya ma aruf ai na bar Abinda nake yanzu ma Aure zanyi shine na dawo gida Wanda zan Aura din zai zo ya ganku.

“To ni dama me zanyi Miki wasila ? Ai sai dai nayi Miki ADDU A Amma gaskiya nayi Mamaki kwarai da akace kinyi Abinda kikayi yanzu har ISHAQ yaci irin sakamakon da kikayi mishi? Amma da yake Allah ne kina barin shi tamkar dai ace kece Mai farar kafar da ta Hana shi Arziki kina tafiya Al Amarin ya sauka.

Taji Wani Abu Yana sukar ta a ZUCIYA me yake nufi da tana tafiya? ISHAQ din ya Samu kudi kenan yanzu? Tambayoyi ne fal a bakin ta Amma Bata da Damar yin su. Goggo ta fito tana fadin
“Kai Dan Nan taho mu Gaisa kaji wannan fa ai tayi hannun Riga da Aminci ai barin mutum Ake da Abinda ya zaba ba Duniya bace? Wanda bai shigo cikin ta ba ma jiran shi take.

Ma aruf ya zube a Gaban Goggo Yana gaishe ta Suka gaisa Yana tambayar Abinda take bukata tace komai akwai sai dai ya siyo Mata buta da sallaya don wasila ta taba Mata nata har ta sallama Mata su don kyankyamin ta take.

Yayi murmushi Yana Fadin. “Hak’uri Zakiyi Goggo ita dama haihuwa haka take dole sai an jarrabe ku a cikin Ya’yan ku ko a cikin dukiyar ku ko Abokan Zaman ka ADDU A dai itace Abinda za ayi

“To Allah ya shirya ya Kuma shirya muku naku ZURIAr.

Da haka yayiwa Goggo sallama ya na aje Mata kud’i.

Ranar da ta cika sati da Zuwa gida a Ranar ne Kuma Yan Doma ya iso katsina ya Kuma Sanar da ita zaizo inda ta fadawa Yaya ma aruf Wanda ta sauke shi a can don ta San idan ta sauke shi a gidan Goggo kunya zata Sha shiyasa ta Kai shi gidan Yaya ma aruf akayi mishi tarba ta Sosai Sukayi magana da shi ta fahimta Kuma da yake sanannen mutum ne ma aruf din yayi mamakin inda suka Hadu da wasila har suka shirya maganar Aure.

Yaya ma aruf ya jagoranci Kai senator har bindawa wurin dangin Uban su akayi magana aka gama sati Mai Zuwa.

An Zubar da kudi a bindawa Domin kuwa senator yayiwa iyayen wasila kyauta ta girma ya Raba kudi kafin aka dawo gida ma Yaya ma aruf ya kawo shi gaban Goggo wacce take kallon shi a kaikace suka Gaisa cike da mutunci ya Aje mata kudin masu auki tace ba zata karba ta Gode Allah ya sa Albarka. Duk nacin shi da son Goggo ta karbi kudin bata karba Abinda yasa shi Jin Lallai har gobe akwai irin Goggo Wanda Basu da zalama akan kud’i.

Tuni aka shiga Shirin Biki duk Babu Abinda wasila ke so irin taga ISHAQ da Halin da yake ciki.

Ranar juma wasila ta fita da nufin zuwa gidan Anty murja don tunda tazo Bata yawan fita don yanzu ne Goggo zata ce mata

“Yawon ta Zubar din Zaki fita? To ba a Nan gidan ba gara ki koma can gidan magajiyar ku ki Kama daki ni kam ba Zaki Bata min mutunci da sauran yaran Nan masu Kima ba. Tunda dai kinji kin Kuma Gani kiyi duk yadda kike so Amma ba Nan ba.

Dole take Hak’ura da fita sai fa yau juma a da Roki Goggo zata je gidan murja.

“Ba gidan murjar kawai Zaki tsaya ba Zaki dai fake ne da gidan murja Amma Akwai inda zakije Kuma Allah ya kiyaye ai Duniya ce gaki ga ta nan

Ta fito idon ta da kwalla sai kawai taga motar ta faka a kofar gidan su inda ta ga Sagir ne ya tuko motar yusra da Zainab suka fito suna Ganin ta Suka Dafe ta inda maimuna Kuma ta fito daga gaban motar tayi fari Dan cikin ta da ya turo Riga shine Abinda ya kusa Sumar da wasila wacce take Rungume da Yusra da Zainab yayin da Sagir yake cikin motar Yana kallon mahaifiyar tashi wacce ganin ta ya dawo Mishi da wani dadadden Miki har ya Soma kwalla.

Maimuna ta Rungume wasila tana Fadin, “Shikenan Anty wasila kin tafi kin bar mu Babu ko waya?

Ta Dubi maimuna da wani matsiyacin kallo Wanda ta kasa boye zafin maimuna da take ji Amma ta amsa tana yake.

“Maimuna Amarya Yaya amarci? Kunya ta kamata Bata Amsa ba tace, “Unguwa ma Zaki tafi ko?

“Gidan Anty murja zanje ai har zan dawo na same ku ko?

Ta fada tana Duban su yusra da Zainab da girman su ya Bata Mamaki ga kulawa ta musamman da ta Gani a tare da su hatta kayan jikin su tamkar Ya’yan wani Mai kud’i.

“Idan Abban mu Bai zo da wuri ba mama zamu Jira ki dawo Amma kar ki Dade.

Cewar yusra.

“To Yusra ba zan Dade ba in Sha Allah, Suka wuce Cikin gidan Goggo inda wasila ta Dubi sagir da motar da yake ciki abin ya Bata Mamaki yanzu sagir ne yayi wannan girman a cikin shekara biyu ?

Ta Dube shi tana Fadin

“Sagir yanzu kana kallo na Amma ka Kasa Yi min magana?

Ya Dube ta ta kasan ido kafin yace

“Na Gaishe ki ai Baki Ji ba, Yana fadar Hakan yaja motar a guje ya bar wurin saboda kukan da ke Shirin kwace mishi.

Tabi k’urar motar da kallo har ya bacewa ganin ta.

Ta juya tana Jin Wani Abu Mai kama da nadama Yana saukar mata Domin kuwa ta San sagir Yana kallo Abinda ya Gani ne a tare da ita.

Ta bi ta kofar gidan ishaq don taga ko zata iya Ganin shi Amma Tasha Mamaki da ta ga yadda aka mayar da gidan Wanda aka kawata da ginin dutsi har da bene ma an Dora a sama . Tayi mamaki matuka Gaya da Ganin sauyawar gidan Wanda take kokonton ko ba Nan bane? Amma Kuma Dole ta yarda da Nan musamman da ta tuna da leshin da yake jikin maimuna da Kuma kulawar da ta Gani a tare da Yusra da Zainab..

Ta wuce zuwa gidan Anty murja wacce ta karbe ta da mutuntawa Akasin yadda tayi zato karbar irin wacce Goggo tayi Mata Amma sai ta Gane jinin yan Uwan taka Bai bari murja ta kyamace ta ba sai dai tayi Mata fad’a matuka Gaya musamman yadda ta Zubar da yayan ta Mata ta tafi Kuma tana tafiya Al Amarin ISHAQ ya zama daga Cikin baiwar Ubangiji ta KUN FA YA KUN ya kudance tamkar abin Nan da Ake cewa Dare Daya Allah kanyi bature inda Kuma sagir ne ya nunawa Uban sa ya nemi Maimuna ya Kuma yarda ya amsa gata nan da nata Rabon tana Shirin Haihuwa.

Kuka wasila take tana Fadin, “Nayi kuskure Kam Anty murja ga dai kudi na samo Amma Kuma ta hanyar da ni da kaina na San Haram ne . Amma Nima Zanyi Aure na na zauna Amma ki sani Anty murja da wani Miki da Bakin ciki zan mutu.

Sunyi magana Sosai Anty murja ta nuna Mata ba kuskure ne tayi ba sai ganganci da gadara da Kuma izgili.

Ta dawo gida daidai da ISHAQ yazo daukar su maimuna. Tun daga nesa take hango yadda yake Rik’e da maimuna wacce ya Budewa mota ta shiga ya mayar ya Rufe.

Ta iso tana ganin yadda ISHAQ yayi clean ya cika yayi kiba ga Wani gashin saje da ya aje ya zama done…

Ya SHIGA motar tana isowa maimuna ta leko tana Fadin, “Anty wasila har mu gamawa Goggo wunin juma a Baki dawo ba don Allah kizo mini wuni Goggo tace sati Auren ki?

“Ba zan zo gidan ki ba maimuna sai dai in kinzo Ranar satin.

Ta fada idon ta akan ISHAQ wanda ya hade fuska Yana tashin motar ko gama magana basuyi ba ya figi motar a guje duk da fad’in da Zainab take tana fadin, “Abba tsaya na Kara Ganin Mama Amma sai yaji tamkar ya Rufe Zainab da duka saboda wannan maganar Amma kuma baya son dukan su ba tare da babban Dalili ba sai Bai kula yarinyar ba har suka Isa gida Bai Kuma tankawa ba duk yawan maganar da Yaran keyi sai dai maimuna ta amsa musu

Wasila tayi tsaye tana kallon yadda ISHAQ ya figi motar a guje tamkar Wanda zashi sama ta bakwai.

Ta share kwallar da taji tana bin idanun ta ta juya ta SHIGA gidan tana yiwa Goggo sannun da gida ta Kuma fada Mata ta Dawo.

“Duk wannan dadewar da kikayi kina cab ne gidan murjar? Ta Amsa Mata da Wallahi tana can.

“Hutar da kanki doguwar Rantsuwa ba kinji kin Gani ba? Ai Duniya ce Wanda Bai zo ba ma tana Jiran shi bare ke da kika gama sanin komai a Cikin ta.

A cikin kwanakin nan wasila ta fuskanci matsin lamba daga Goggo Amma ya ta iya?

Ranar asabar aka Daura Auren ta da senator Uba Yan Doma duk da Babu wasu mutanen shi da ya gayyato Asali ma shi kadai yazo Babu wani Aboki ko Dan Uwa na kusa don haka ana gama daurin Auren yace tare da Amarya zai Wuce duk da Yaya ma aruf yaso ya hada ta da murja da Hafsat matar shi don suyiwa wasila Rakiya Amma yace Babu komai Suma jirgi zasu hau zuwa gidan sa da yake Lagos Amma daga baya idan Akwai Mai son Zuwa zai turo tikitin jirgi su zo

Da haka wasila tayiwa Goggo sallama bayan ta gama ta da girman Ubangiji ta yafe Mata Abinda tayi ko akan Auren ISHAQ da maimuna ta Gane kuskuren ta Kuma yanzu tayi Aure ne don Allah ba don Wani Duniya ba.

Anty murja ce ta Taya ta Rokon Goggo ta yafe Mata idan bawa yace ba zai yafe kuskuren da akayi mishi ba Goggo Anya da yanzu Ubangiji Bai kife Duniya ba? Don Allah don ANNABI ki sakawa Auren ta Albarka.

“Shin ni me nace anyi mini murja? Ai nace na yafe in ma anyi mini Allah fa tayiwa laifi sai Kuma mijin ta Kinga su ya kamata ta tsaya Kai da fata ta nemi yafiyar su ni Kam ai ba a mini komai ba.

“To Alhamdulillah Goggo sakawa Auren Albarka ta Damu da fushin ki ne akan ta yafe Mata Goggo sai Allah kema ya yafe Miki.

“Murja na yafe muku ku duka Allah ya muku Albarka ya shirya muku ZURIA ya tsare su daga sharrin Zamani Allah yayiwa Auren ta Albarka tare da aurarrakin Ya’yan musulmi Baki Daya.

Da haka wasila ta baro gaban Goggo Yan Uwa suka Mata Rakiya har zuwa filin jirgin Saman malam Umar Musa Yar Adua Wanda jirgin max Air ya dauke su sai garin Legos Abinda ya Soma bawa wasila mamaki don tayi zaton Abuja zasu zauna sai gasu a Lagos

Da yamma suka Sauka inda mota tazo ta kwashe su Suka nufi wata unguwa da Bata San sunan ta ba . Sun dai Yi tafiya mai Nisa kafin suka iso Wani katafaren Gida Mai girman gaske Suka Soma tafiya har suka iso inda mazaunin gidan yake

Babban Abinda ya Fara Bata Mamaki shine biran da ta Soma Gani suna faman tsalle da son su iso ga motar . Biri Kuma irin Goggon Nan Wanda Ake cewa gurilla kartaka kartaka.

Ta Ji tsoro Mai tsanani ya kamata Amma ta koma Bayan shi tana lafewa yayi murmushi Yana Fadin

“Babu Abinda zasu Yi Miki maraba Suke Miki Basu hannu ku Gaisa hadiman ki ne.

Ta Dube shi a tsorace tana fadin, “Hadimai Kuma? Birin ne hadimi na? Ai ni kyamar biri nake Wallahi gara kare da biri a wuri na.

“Muje ciki ki huta Amarya ni Ina da tafiya a Gaba na karfe Tara na dare zan bar k’asar Amarya da fatan Zaki gafarce ni.

Ta Dube shi a tsorace tana fadin, “Zaka bar k’asa a yau din? Ya kada Mata Kai suna shiga wani kayataccen falo Wanda yaji komai na kayan more Rayuwa Amma Kuma Abinda zai baka mamaki shine zanen taswirar Wani katon biri da aka zana a Saman bangon falon Wanda da ka shigo Zakayi Karo da Zanen na birin Wanda yake sanye da kayan sarki har da wata hula ta Jar AZURFA Yana zaune akan wata kujera irin ta sarauta Yana Rik’e da sanda ta jar AZURFA itama . Babu kyan Gani akan wannan zanen bari don duk da yake Zane Amma ya fito tamkar na gaske idanun shi jajir Babu kyan kallo. Abinda ya fadar Mata da gaba kenan musamman da ta tuna da manyan biran da suka Gani a waje wai suna musu maraba sai ta hada biyar da uku suka Bata takwas sai taji Wani matsiyacin tashin hankali na taso Mata. Meye alakar wannan mutumin da biri Kuma har yake zuba su a gidan shi irin zubin da akewa awaki har Yana zana taswirar sa da Saka mishi kayan sarauta?.

<< Tana Kasa Tana Dabo 38Tana Kasa Tana Dabo 40 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×