Satin Sameer UKU a Asibiti kafin aka sallame shi duk da ba warkewa yayi ba. Yan office din su ne Suka cewa Haj zasu canja mishi Asibiti Saboda yafi yawan kokawa Ciwon ZUCIYA.
Haj tayi mishi fatan Alheri inda Bello ya bisu don kulawa da Dan Uwan shi Kuma yaga Halin da ya kasance. Don haka suke tare a Asibitin da aka canja mishi a can pertercout wacce Kuma Cikin ikon Ubangiji sukayi nasara matuka Gaya har aka ciwo kan Ciwon zuciyar ya dawo hayyacin sa .
Yana kwance akan Gadon Asibitin wacce take ta kud’i ce Kuma an kashe kudi gaskiya Amma Kuma kwalliya ta biya kudin sabulu.
Bello Yana hada mishi Ruwan shayi Wanda yaji Madara da Ovaltine ya kama Hannun shi Yana Fadin
“Yaya Sameer muje ka wanke bakin ka ga shayin Nan
Ya kama Hannun Bello suka nufi toilet din da yake d’akin Asibitin ya wanke baki suka fito ya bashi kofin ya karba Yana Sha sannu a Hankali har ya Sha fiye da Rabi zufa ta Soma karyo mishi Bello ya kunna mishi AC Yana taba wuyan shi don yaji ko Yana da zazzabi ne ya sauka shi yasa shi zufar.
“Bello Allah ya biya ka da gidan ALJANNAH madaukakiya kayi min kokari ka baro Aikin ka kazo ka zauna tare Dani .
“To in banyi Maka meye amfanin Haihuwar mu a mahaifa Daya? Ka kuwa San Dalilin da Ubangiji yayi mu a mahaifa Daya? Don muyi zumunci da ba don zumunci ba sai ayi mu kamar yadda Ruwan sama yake sauka wancan yabi can wancan yayi can Babu Mai Neman Dan Uwan sa . Amma ka Dubi suffar da Ubangiji yayi Mana komai yayi Mana zaka ga Biyu ne ko fin Biyun manufar sa don muyi zumunci. Ka dubi k’aramin misali ko takalmi wari Biyu ne to manufar tana nan a zumunci don mu San komai da Dan Uwa akayi shi Kuma zumunci ake so ayi don haka Allan ya Kara Mana zumunci.
“Ameen Bello kaga Farida ta yaudare ni ko ? Ni fa na fada Mata zan samo Wanda zai Aure ta ya Sako min ita shine ta zabi Wani Dan iska Wanda na tabbatar ba zai Sako min ita ba har tana fada min ta barni har Abada.
“Subuhanallahi Yaya Sameer Auren KISAN WUTA kenan? Ai kuwa shi wannan Auren naji malamai suna fadin Haram ne matukar dai za a Yi wata yarjejeniya akan Auren to wannan Auren ya zama Haram.
“Wannan ba Haram bane Bello tunda zaman da za ayi bayan Sakin yafi zama Haram akan ayi Auren a fito a karya waccan ukun da ta zaga.
“To haka ne Amma dai yanzu Yaya Sameer kana ganin Akwai yaudara a cikin Abinda Farida tayi? Dole fa dama zatayi Aure kaima Haj tace min an gama magana fa akan Aisha da Zaka yarda sai Nace kayi hak’uri kawai ku manta juna Kai da Farida idan Kuma Kuna da Rabon ganawa a Gaba sai kaga Kun GANA.
“Ba zan iya hakuri da ita ba bello wannan Ciwon zuciyar ma da kaga Ina fama da shi Bak’in cikin tunawa da nake Wani Namiji zai kwanta min da ita ne Shiyasa ko naji sauki sai ciwon ya Dawo sabo wannan shine damuwa ta da Ciwo na .
Bello ya zuba mishi ido ya kasa cewa uffan.
Sati Biyu Sameer ya samu Sauki lafiya ta Samu inda Bello yayi mishi sallama ya tawo gida shi Kuma ya koma bakin Aikin shi inda Akayi mishi Karin girma ya samu promotion na karin star Amma duk wannan ba shine Abinda yake damuwar shi ba irin ta yadda zai dawo da Farida Cikin Rayuwar sa.
Gangar jiki ta Soma bijiro mishi da bukatun ta Dolen sa kuwa ya dauki mota ya nufi wurin shakatawar ya Kuma samo macen da yake ganin tayi mishi ya dauko ta Suka zo Gidan Nashi aka Rufe kofar Amma Kuma baiji ya samu gamsuwa yadda yake so ba .
Gwani ne matuka Gaya a harkar ta Neman Mata tun kafin shigowar Farida a Rayuwar sa . Amma samun Farida da Kore mishi kishirwar da tayi akan Mata yasa ya dagawa harkar kafa Amma idan yayi nesa da ita Yana Dan tabawa Amma har yau Bai Kuma samun macen da tayi mishi d’ari bisa d’arin Farida ba. Don haka a Duk Lokacin da ya nemi biyawa gangar jiki butatun ta yaji Bai gamsu ba Bakin ciki ne ke Neman kashe shi.
Ya sallami Yar iskar da kud’in ta ta wuce duk Jin Wani Abu da take akan gayen Mai kama da so irin na ta mallake shi don yayi Mata jaint Kuma Mai k’arfin Da take mutuwa a so Wanda ya san salon siye ZUCIYAR mace.
Ya jima Yana Neman hanyar ganin Farida wacce ya gama yanke Mata Hukunci akan ta .
Ya dauki wayar shi Yana Neman layin ta Amma a kashe don haka ya wuni Neman layin duk ba ya samu Bai San Cewa Farida Bata Nigeria ba . Duk da fada mishin da computer keyi na wayar Bata Samuwa Bai Hak’ura ba kusan kullum sai ya kira Amma ya kasa samun ta.
FARIDA da ABDULLAHI
Sai da sukayi watanni UKU cur kafin suka Dawo Shima Mai gemu Bai so su dawo ba don hakikatan ya murza amarci ya Kuma Kara Jin Farida fiye da kowace mace a Rai da zuciya
A yadda ya tsara sai sunyi wata Tara zuwa goma suna zagaye Duniya tunda ko za a Shekara Babu Abinda zai shalle shi tunda kullum cikin Jin shigowar kudade yake bashi da damuwa. Sai dai Farida ce ta tuna mishi Basma da hakkin da take da shi akan sa. ita Kam Bata shiga hakkin ta kamar yadda ta San ba zata so a shiga nata hakkin ba .
Sun sauka gida Nigeria bayan sun zaga kasashe sama da biyar suna morewa Rayuwar su . Mai gemu Kuma ya kashew Farida kudi kamar Bai San zafin Neman su ba. Ta Kuma Saka shi kashewa Basma da Ya’yan ta irin Abinda ya kashe Mata.
Basma ta tarbe shi da murmushi Babu hargagi Wanda ya zaci Gani daga gareta Amma ta maze kamar babu komai a Ranta.
Ya Dube ta Yana Rungume ta Yana Fadin
“Basma Kinga yadda kika kara kyau kuwa? Ya ya na same ku? Yaya Najwa da Nabeela Babu dai wata matsala ko,?.
“Babu wata matsala Kai din ne ma Naga kayi fresh abinka kana jin Dadi fa kana hutawa.
Ya Kai Mata Sumba a Baki Bata ja ba ta biye mishi har ya zauna ta kawo Mishi Ruwa da lemu tare da dambun Naman kaza Yana tabawa Yana Fadin
“Don Allah ke kanki hakan baki ji kinfi burge kanki ba? Ita fa mace Basma idan ta Gane kanta Namiji zai Sha wuyar ta don zai bita ne yadda take so. Yanzu ni Hakan da kikayi ba k’aramin dauka ta kikayi ba kinyi shiru abinki Babu hargagi Babu Neman Jin Yaya wata take Rayuwa ai haka shine zaman lafiya don Yan magana sunce kazantar da ba a Gani ba sunan ta tsafta . Don haka kema ki shirya nayi Miki alkawarin fita tare da ke da su Najwa da Nabeela mu Yi Hutun mu mu Dawo.
“Nagode Sosai Allah ya Kara daukaka.
Ya amsa da Ameen Yana Bata key din motar shi Yana Fadin
“Kira sadi kice ya bude Mota ya kwaso Miki tsarabar ku duk abinda kika Gani a ciki naku ne ke da Yara itama ta dauki nata .
Ta karba ta wuce ya bita da kallo Yana Mamakin sauyin ta Amma abinda yazo Ranshi Arashin da yayi Mata na in tana haukan kishin ta fita Ranshi take wata Kil shine yasa ta Gyara.
Sadi ya kwaso Mata daga mota ya zube Mata ta na ta Godiya ga Abdullahi Wanda yake duban ta Yana murmushi don mamakin ta yakeyi na yadda tayi Sanyi kalau
Najwa da Nabeela suka shigo sanye da kayan islamiya suna Ganin shi Suka Rugo Aguje suna dafe shi suna Dariya suna Fadin
“Daddy highly welcome sannu da Dawowa.
Ya Rungume su su Duka Yana Fadin
“Thank you my girls Kuna lafiya? To na siyowa kowa sakon da ta bani ga shi nan wurin Mamar ku ta Baku har da Karin wasu ma.
Yana matukar son yaran nashi duk da kowace kamar ta daban tsakanin Najwa da Nabeela Babu wacce tayi kama da shi ko tayi kama Basma haka ma basuyi kama da juna ba duk da farin me Gemu da farin basma Amma Najwa da Nabeela Bak’ak’e ne Basu da farar fata . A haka yake hidimtawa karatun su da Rayuwar su . Kuma komai suka ce suna so zai Basu ko ya sama Musu
Tsayin watanni UKU da Sameer yaga an kwashe ba tare da ya samu layin wayar Farida ba shi ya nuna mishi da gaske ta yaudare shi ne tunda a yadda suka shirya sati Biyu zuwa UKU anyi an gama Amma gashi wata uku Amma Babu wani Labari wayar ta ma ya Daina samu wata Kil Kuma Mijin ta ne ya karbe layin ya sauya mata Wan
A karshen watan Nan ya Shirya zuwa katsina Kuma ya shirya da zai je Gidan me Gemun din ya Samu Farida yaji wane irin wulakanci ta Shirya Yi mishi haka?
Ya iso katsina ya sauka a gidan Hajiyar shi wacce take duban shi tana Fadin
“Haba Sameer shikenan daga wannan Al Amarin ya faru sai ka dauke kafar ka? Ni da Nace zan hada ka da Aisha ai gata nake Maka kaima Idan ka samu matar ka ai Zaka manta ne da wata Farida.
Yayi murmushi Yana Fad’in
“Kiyi Hak’uri Haj yanayin Aiki ne tunda Akayi min promotion din Nan sai ayyuka Suka karu ba Wai wannan abun ne ya Hana ni zuwa ba .
“To na yarda Allah ya Kara taimako Amma fa ka sani magana tana Nan Babu inda ta tafi tunda ma ka zo sai ka leka ta ita Aishar ku Gaisa don ta San dai Aiki ne yayi maka yawa.
Ya Mike don har ga Allah baya son maganar Aisha Amma ta Yaya Haj zats Gane Hakan ?
Ya wuce gidan shi Farida inda su Saddam da Hanan Suka Dafe shi suna mishi oyoyo ya cabe yaran Yana Daga su sama Yana sumbatar su suna Dariya.
Yana Gaban Haj Yana gaishe ta ta Amsa Yana tambayar shi Aiki kuma kwana da yawa . Yace yanayin Aiki ne .
Yayi ta baza idon ganin ko zaiyi sa ar ganin Farida Amma Bai Yi sa ar ganin ko takalmin ta ba.
Tamkar ma Hanan ta San Abinda ya ke sakawa kenan tace
“Daddy kaga Mami tayi tafiyar ta Taki Dawowa?
Ta fada cikin gwarancin maganar ta. ya Soma shafa kan yarinyar Yana Rarrashin ta .
“Kiyi Hak’uri zata zo ne Hanan ko Kuna son Zuwa ganin ta ne?
Saddam ya amsa da kargi Yana sakala hannun shi a wuyan Sameer yana fad’in
“Daddy’ ko zaka Kaimu ne ?
Ya Dubi Haj da take kallon su da sauraren su Yana Fadin
“Haj ba a kaisu wurin ta bane har yanzu?.
“Yaushe zan kwashe su Sameer na Kai su gidan Uwar su a Yanzu? Gidan da take ba ita kadai bace Kuma ka San Halin yaro ba a Sha mishi Alwashi Kuma duka yaushe Akayi Abun? Mata Bama Raina abin magana Kuma ta yuwu mijin ta baya bukatar Zuwan Ya’yan ta. Kuma ba su k’asar ne kusan watan su UKU sai Shekaran jiya suka Dawo ta Kira tana tambayar su har tana Fadin a aika Mata su ni kuma Ina ganin ba yanzu ne ya kamata su fara taka kafar su gidan ba sai Ranar da shi da kanshi yaga kamatar suje .
Gaban Sameer yayi matukar Sarawa Jin Haj na Fadin wai Farida Basu k’asar sai Shekaran jiya suka Dawo.
Zufa ta Soma wanke fuskar shi Yana hango yadda fita k’asar ya kasace yadda ya San Mai gemu da naci Akan Mata baya ko shakka ya tab’a mishi Farida.
Ya Mike Yana ajewa Haj Kayan da ya Ruko musu da Kuma kayan su Saddam.
Ya Mike zai Wuce Hanan ta dafe shi tana Fadin zata bishi Shima Saddam din ya biyo su ya na Fadin zai busu Shima.
Dole ya kwashe su a mota suka nufi ber Birch ya Siya musu ice cream da kayan kwalam ya maido su gida suna murna Amma Hanan sai Fadi take
“Daddy yaushe zaka kaini wurin Mami?
Ya zubawa yarinyar ido Yana kallon ta don yaji Lallai sai ya Nemo Farida a Yanzu.
“Kiyi Hak’uri kinji my girls zan kaiki idan na dawo kinji?
Ya lallaba su ya wuce Yana Kiran wayar Farida kuma cikin sa a ya samu ta shiga har yaji ta dauka tana Fadin.
“Yanzu nake Kiran wayar ka Sameer Yaya jikin ka Ina ta Kira wai a Kashe?.
“Farida Dama kinyi nufin wulakanta ni dama ? Yau watannin ki uku Ina Neman wayar ki ma a Kashe?.
“Yaya Zanyi da Kai Sameer? Duk yadda nake kokarin Naga na faranta Maka Amma Kai kullum zuciyar ka son nuna maka Wani Abu take Akaina . Ni Kuma na Gaji da wannan Halin naka gaskiya shine kawai na kyale ka na Rik’e mijina tunda Naga Abinda Babu shi a wurin ka.
“Kina nufin Shegen mutumin Nan ya kula ki Farida? Dama kinyi nufin ganin GAWA ta ?.
“Gani Nan Zuwa gidan ki Farida Dole nazo Naga halin da kike ciki don Wallahi a yau idan ban ganki Naga Halin da kike ciki ba mutuwa Zanyi.
Ya tsinke wayar Yana huci idon shi ya kada jajir tashin hankali muraran ba ba don komai sai don tabbaccin da yake da shi akan Mai gemu ya tab’a Farida don ya San ya tabbatar da ba zai zuba Mata ido ba Dole ya nemi Wani Abu wurin ta.
A take ya tuna da Duk Matan Duniya Babu wcce ke samar mishi da nutsuwar da yake gamsuwa irin Farida sau Kuma ga Wani can wai suna tarayya da shi.
Ya Soma tari don in tashin hankali ya same shi yanzu ne tari zai turnike shi tamkar zai Suma sai ya Sha glucose yake samun relief don haka ne ma baya Rabuwa da shi a mota in har Saddam ya Gani yake ambama.
Ya jawo gwangwanin Yana afawa ya bi da Ruwa ya hadiye kafin ya samu Sauki ya tashi motar a guje ya nufi gidan Mai gemun da yake karkanda .
Ya Isa kofar gidan Yana Jin idan Kuma suka hade da me Gemun yace me ya kawo shi? Sai ya tuna a yanzu ba ya Gida.
Ya tsayar da motar a can bakin hanya kafin ya Tako kasa ya iso Bakin kofar wacce akwai Mai gadi Amma ga mamakin shi Babu Mai Gadin . Ya tsaya Yana kallon sashi sashi na gidan ya Rasa Wanda zai shiga Amma sai ya lura da Wanda yake da Sabon fenti ya Kuma Fi kayatywa sai kawai zuciyar shi ta Bashi Nan ne sashin Farida ya Kuma wuce kanshi tsaye Babu ko dar bare shayin komai.
Farida tana Zaune a gaban mirror tana shafa inda take daure da tawul ta aje wayar tana mamakin Abinda Sameer ya fada . Tana daure gashin ta da band sai kawai taji an turo kofar falon ta juyo don taji daga Nan ne Amma Bata kawo wa Ranta shine ba . Sai da ta Ji wayar ta ta dauki tsuwwa ta duba taga sunan Sameer Amma Bata dauka ba sai kawai taga yana turo kofar idon su ya Hadu inda taga girman da ya kara shi ma Kuma ya zuba Mata shanyayyun idanun shi Yana hango ta cikin tawul din.
Yana Rik’e da Hannun ta Yana Jin yadda Ake Jan shi zuwa gareta sai kawai ya Rungume ta Yana Kai Mata sunbuta a Rikice ita da shi Suka manta da halakar da suke shirin afkawa .
Tuni kuwa suka fada Al Amarin da Babu Shiri har ya Kai ya cire Mata tawul da yake daure a kugun ta ya Rungume ta tsam a kirjin shi Al Amarin da yaja su har katafaren d’akin baccin Farida a kan gadon ta Wanda Sameer ya baje tamkar Yana gidan shi baya Kuma tunanin Abinda ka iya Zuwa Kuma ya Dawo.