Skip to content
Part 46 of 75 in the Series Tana Kasa Tana Dabo by Hadiza Gidan Iko

“Me ya kawo ka Gida na? Waye Kai da Zaka Rik’a keto mishi haddi gida kana shigowa kanka tsaye tamkar gidan ku? Ko kuwa ka zo ne ka k’arasa kashe shi tunda Allah ya Nuna Maka ikon ba a Hannun ka yake ba Yana Hannun ALLAH? To sahun ka a likkafa ka fice daga gidan Nan in Kuma ba haka ba Wallahi zan ja Maka Abinda baka tab’a zato ba Sameer ! Nayi kaicon Sanin ka a Rayuwa ta fiye da yawan Shekarun Uwa ta da Uba na Kai ba Alheri bane a tare Dani sai yanzu na Gane Hakan. Kai Sharri ne a gareni tunda baka nema na da Alheri.

Ya Mika hannu ya Dauki Salman da ta aje a cikin kujera Yana tsotson yatsun hannun shi

Ya Daga yaron sama Yana sumbatar shi Yana Jin wata irin kauna da soyayya akan yaron Wanda sai da yazo ya ganshi ya tabbatar da yafi Saddam kyau don shi Kam fari ne tas Mai yalwar sumar Kai Bak’a Kuma Mai Wani irin kwarjini Wanda Mai kallo zaiji Yana son yaron.

Ya Rungume yaron Yana shafa Sumar kanshi shi Kuma Salman din sai bangala mishi Dariya yake.

Ya zauna Yana Duban Farida wacce take Jin tamkar ta maka mishi mabugi.

“Kina iya Rufe kofar nan muyi magana idan Kuma Bako da damuwa akan Hakan ni bani da matsala ke kin San bana shakkar Wani.

Da sauri kuwa ta dannawa kofar key ta Rufe don tana Jin tamkar Basma tana Nan tana ganin Abinda ya shigo .

Ta tsaya daga Bakin kofar tana hararar shi Yana Rungume da Salman Yana Jin tamkar ya hadiye yaron.

Ya Dube ta kafin ya Soma Magana

“Kika ce na zama Sharri a Rayuwar ki? Amma ke kuwa meye Naki sunan na ta addancin da kikayi min? Ta Yaya kike zaton zan zama Alheri a gareki bayan kin cuce ni kin munafunce ni? Eh tabbas Nazo ne don na k’arar da numfashin shegen mijin ki don na Gane sai ya bar Duniya ne ko zan sake mallakar ki a karo na Biyu.

“Har Abada ! Wallahi har Abada Sameer ni da Kai munyi Hannun Riga ko Babu ran Abdullahi na Fi k’arfin Komen Auren ka saboda na Gane Wani Abu Guda Daya da baka da shi. Gara kawai ka Rik’e matar ka ka bar mafarkin zan dawo gareka don Wallahi ko Babu Ran miji na Wani Namijin zan Aure ba Kai ba gara ka Rik’a kallo na a haramiyar ka Domin kuwa na Gane tazarar da take tsakanin mu tana da Nisa Zaren Sam ba kalar yadin bane Wallahi .

Ya ajiye Salman akan kujera ya Mike ya Isa inda take Yana zuba mata ido kafin yayi Wani murmushi na takaici.

“Dukkan maganganun ki suna dafa min zuciya suna Kuma ci gaba da kashe ni Daga tsaye Farida. Na Gane nine kawai nake Miki so Guda Daya Amma ke kin Raba Mana shi biyu koma nace Kai tsaye yaudara kikayi tunda Naga yadda kike Dora status Wanda bana ko shakka don ni kike yin Hakan Amma kina Ganin Zaki iya yaudara ta a wofi Salim alim? .

“Wallahi karya kake kace Sona kake akwai coge a cikin wannan maganar. Naji na yaudare ka Kaine farkon yaudara a Duniya ko kuwa zaka zama karshen yaudara? Duk ma yadda kaji a Ranka Hakan ne Amma ni Sona ma ban Raba shi da Kai ba Wallahi gaba Daya na bawa Abdullahi don Kai kanka ka San irin Rayuwar da nake dashi ban tab’a yin irin ta da Kai ba don ka Gane na kulle ka na jefar da Dan makullin a maliya.

“Ai kuwa kinci Uwar karya kin kwana da yunwa Wallahi sai kin SHIGA maliya kin dauko makullin Nan don banyi kama da Wanda Zaki kulle ki jefar da Dan makullin a maliya ba Wallahi ba.

“Kaga don Allah zo ka shige Kuma daga yau kar ka Kuma dawowa Nan gidan in Kuma ka Kuma dawowa wallahi zan SANARWA manya Zuwan ka gida na Kuma Miji na na Rantse Maka da Allah kayi na farko Kuma kayi na karshe Amma da na Kuma jin Wani Abu Mai shigen irin wannan har pertercout zan iske ka na tuhume ka tunda ka nuna min Kai ko waye.

“Ai Babu inda zanje a yau Nan gidan zan Kwana sai na nunawa mijin ki iyakar sa wuri na don a yanzu Kam na shirya kashe Miki Aure da kaina tunda na Gane kin yaudare ni da sunan Auren KISAN WUTA Amma kinzo kin mike kafa har ana miki ciki kina haihuwa to cikin Biyu Wallahi Daya za ayi ko dai ki fito Baki alaikum ko kuwa na nunawa Duniya Cewar ke din tawa ce Kuma duk Wanda ya dauke ki Dole ya aje min Kaya na. Domin kuwa zan nunawa Duniya Cewar Baki yaudare ni a Banza ba don Haka ki gyara min makwanci a gidan Nan har nayi kwanaki na Biyu ko UKU ya danganta da yadda Zaki Raba Mana kwana tunda kinfi son Hakan ai Kuma na Gane kin Kuma Samu .

Ido waje take Duban shi da Mamakin Abinda ya fad’a.

Ya Soma balle botiran gaban Rigar sa Yana Shirin fincewa tayi maza ta ce

“Meye haka ? Kar kayi zaton zan iya barinka a yanzu wancan ma da kayi na Kai k’arar ka ga Ubangiji ne Kuma duk in nayi sallah sai na fadawa Ubangjji ya sakawa miji na akan keta haddin da kayi min .

“Yanzu ma sai ki k’ara kaimi don na Gane Hakan ne kawai zanyi Miki ki fahimci yaren da nake magana da shi tunda nayi Nayi kin kasa fassara.

Tayi baya zata kwasa a guje ta dauko key yayi Maza ya Rik’e ta Yana Fadin

“Gara kawai ki tsaya mu fahimci juna in Kuma kince A a Ina ganin Wahalar da kanki kawai Zakiyi don ni dai ba zan iya kyale wannan yaudarar da kukayi min ke da mijin ki ba Kinga Idan ya dawo ya same ni Dole kiyi mishi bayani da yaren da zai fahimce ki.

Ya Rik’e ta Yana Shirin Kai Bakin shi a nata Amma ta kauce tana Kai mishi Duka da duka karfin ta Amma tamkar ba dukan shin tayi ba Bai ko motsa ba sai ma daukar ta da yayi Dan das ya wuce da ita tana kuka tana dukan shi Amma Bai ko tsaya tuna Salman da yake kwance akan kujera yana tsotson yatsun hannun shi bawan Allah bai san bikin da Ake ba .

Ta Soma kokarin kwacewa Amma ta Gane Bai mata Rukon da zai saki ba shiyasa ta Soma Galla mishi cizo Amma tamkar ba fata da tsokar jikin shi ta ciza ba sai kokarin cimma Bak’in kudirin shi yake inda ta Gane in ta bar shi ya cimma kudirin shi a Yanzu itace Mai laifin farko da ba zata tab’a fita ba har ga Allah. Don ta jawo kofin gilashi ta kwantara mishi a ka Amma ko gezau Baiyi ba .

Ta Soma jawo abubuwa tana kwantara mishi don’t ta gane babu tsoron Allah a tarw da shi . da karfi ta buga mishi murfin kwanon tana fadin.

“Wallahi sai na kira haj na fadawa Hajiyar ka wannan ta addancin da kayi min na Rantse da Allah ba zan yarda ba. Nayi nadamar sanin ka a Rayuwa ta Allah ya Saka min wannan zaluncin da kayi min ba . Ba zan iya fadawa Abdullahi ba Amma Wallahi Dole na Kira mahaifiyar ka don ta Sani ban taba sanin baka tsoron Allan ba sai yau da kake shirin min fyade.

Ta Mike tana jawo wayar ta ya dai Gane da gaske take zata Kira Hajiyar.

Ya Mike araza ne Yana balle botiran gaban Rigar shi Yana Fad’in

“Wallahi Idan kika fada Mata wannan maganar Wallahi ni Kuma zanje na fadawa Hajiyar ku cewa kina Kira na Nazo har Gidan ki . Kinga in Baki iya Sharri ba Zaki ga kazafi.

Yana tsaye Yana kallon ta don Bata ma saurare shi ba sai Neman layin Haj da take har tayi ringing ta yanke ba a dauka ba ta wurgar da wayar ta na kuka .

Yayi murmushi Yana shafa fuskar ta .

“Kar ki damu my dear shawarar da zan Baki kawai ki Rabu da mutumin Nan mu koma Auren mu Amma in kika ce saboda yafi ni kudi ne ba Zaki dawo gareni ba to ni Kuma irin haka Zanyi ta zuwa kina sallama ta Kinga har ya Gane da kanshi Muna tare ya sallame ki Amma tunda kika ce ma ba Zaki dawo gareni Kai tsaye ba Wallahi tallahi ba zan bar garin Nan ba sai Naji ana kukan mutuwar gayen Nan don kin ja mishi Dole na kashe shi don naga Idan da gaske kina son nashi ai zani bishi can kuyi soyayya ni Kuma idan kika bishi dole na Hak’ura tunda na Gane kina son shi .

Wayar ta ta dauki tsuwwa tana dubawa taga Hajiyar Sameer ce ta dauka ds sauri tana kuka tana Fadin

“Haj don Allah don ANNABI kiyi min iyaka da Sameer Wallahi gashi Yana Fadin zai kashe Miji na Yana mini zalunci Haj .

Da sauri ya dafe kanshi don baiyi zaton zata tona Mishi Asiri haka ba .

“Sameer Kuma Farida? Yazo garin ne?.

“Yazo Haj har Gidan Nan fa ya zo Yana Mini ta addanci way zai kashe Abdullahi.

Da sauri ya fincike wayar daga kunnen ta Yana kashe ta ya Dube ta idanun shi jajir.

“Na Rantse Miki Da Allah idan kika bari maganar nan ta fita har Haj ta Yi mini Wani Abu to a bakin Rayuwar Shegen mijin ki don haka ya Rage gareki ki gyara abinda Kika Bata ko Kuma ni da ke muyi mutuwar kasko.

Ya fice da sauri don Yana hasaso tashin hankali idan Haj ta aika aka duba gidan shi aka Samu motar shi .

Yana Bude kofar ne zai fice sukayi taho mu gama da Basma wacce take duban shi da idanu irin Duban Nan na bari na kalle shi yadda zan Gane shi a ko Ina ne .

“Kai wannan fuska tayi kama da Saddam Wallahi duk inda akaje aka Dawo akwai Jini Mai k’arfi kuwa?

Cewar Basma wacce tayi maganar tana Jiran amsa Amma Bai kula ta ba ya wuce abin shi Yana ta zuba sauri don Farida ta kad’a mishi ganye musamman da ta Sako Hajiyar shi a maganar ko da wasa Bai zaci zata iya Sako Hajiyar ta shi ba shiyasa yake saurin ya koma Gida ya dauki motar shi ya bar garin Nan tun Haj Bata Gallo mishi sabon Aiki ba.

“Haba wannan kama da yawa take tunda ya shigo nake ta ganin kamar na San fuskar Nan Ashe da Saddam ne yayi min kama shine na kasa tunawa Anya wannan ba Daddyn Saddam bane?.

Farida ta jiyo wannan zayyanar da Basma take Yi gaban ta yayi masifar Sarawa .

Kafin ma ta kirkiri karyar da zata lullube Basma da ita tuni Basmar ta shigo tana Fadin

“Farida Amma wannan shine baban su Saddam ko? Kai wannan kama tasu har ta Baci. Shine fa na Gani kwanaki yazo gidan Nan nake ce Miki naga Wani ya shigo nan Wallahi shine na Gani .

Farida ta Yi Wani bisasshen murmushi Wanda ya ke na Tashin hankali ne .

Basma ta bi ta da kallo ganin ta a yamutse tamkar wacce ta tashi daga turaka .

“Idon ki kuwa kamar kinyi kuka Farida lafiya dai ko?.

“Lafiya Lau Wani Abu aka sanar Dani ne Wanda Hankali na ya tashi.

“Ayya ai sai hak’uri Amma kamar wacce ta ta fito daga turaka kanki ya yamutse ga Babu Yan kunne a kunnen ki .

Sai a lokacin Farida ta tuna da Halin da take ciki na fyaden da Sameer yayi Mata .

Ta Soma laluba kunnen ta da tab’a kanta taji gashin kanta ya yamutse sai tayi maza taja hular ta ta Saka .

Basma tayi murmushi tana Fadin

“Ai sai hakuri haka Mazan nan suke Basu da M kar ma ace Wanda ya tabbatar da wani yayi mishi overtake to sai mace tayi matukar kokari in ba haka ba kuwa yanzu ne zasu juyar Mata da Hankali.

Wani irin matsiyacin firgici ya shigi Farida Jin tana mata tafinta tamkar wacce ta leka taga Abinda ya faru.

Basma ta Mike tana murmushi tana Fadin

“Sai Anjima Amarya yaushe su Saddam zasu Zo? Saddam dan Gida na ashe duk Baban sa ne Dama ance like son like father.

Farida ta Raka Basma da Kallon takaici da mamaki.

Sameer kuwa Yana zuwa gida ya Dauki motar shi ya hau hanya wayar shi ma sai ya kashe ta don ya San Dole ne Haj ta kira shi akan maganar da Farida ta fada Mata .

A matukar Rikice Farida take akan wannan ta addancin da Sameer ya nuna mata Wanda bashi da maraba da fyade.

Ta dauki Salman Wanda yayi bacci akan kujera Yan yatsun hannun shi a Baki Yana tsotso . Ta dauke shi ta Rungume tana kuka saboda Bak’in ciki.

Haka Abdullahi ya same ta a Rikice ya Rude matuka Gaya ya Rungume ta Yana faman Rarrashi da Neman ba asi.

“Me ya faru ne Farida Baki lafiya? Ta Soma share HAWAYE tana Fadin.

“Wancan mutumin ne yake min barazana don na Aure ka .

“Waye shii?

Ya tambaya Yana kallon ta.

“Baban su Saddam. Ni Kuma Wallahi idan ya Kuma ko kiran waya ta zan sanar da iyayen sa tunda su ba Zai kasa fahimtar su ba.

“Wace irin barazana yake Miki ne? Don ba zan yarda ya cutar mini da ke ba.

“Yana yawan Kiran waya ta ne ni Kuma bana so na Kuma ce mishi in us sake kira na zan fada Maka .

“In don Kira ne Farida kamar Babu damuwa Ina ganin ke da shi Kun zama daya ko don Saddam da Hanan Amma Kuma in baki so Dole na taka mishi burki kiyi Hak’uri.

Tana kwance jikin shi Yana Rarrashin ta har ta wartsake ta shiga Hidimar ta.

Haj da ta sake Kiran wayar Farida don a lokacin da ta Kira taji wayar a kashe tayi ta Kira Amma bata samu ba don Haka sai ta juya ga Kiran wayar Sameer Nan ma Bata iya Samun shi ba Dole ta tashi ta nufi gidan shi da kanta Amma ta Tara’s da gidan a Rufe don haka ta shiga gidan maman Umar wacce ta karbe ta Suka gaisa tana tambayar ta ko makocin ta yazo garin kuwa? Maman Umar tace Eh Taji zuwan shi jiya da Dare Kuma Babu jimawa taji fitar motar shi.

Da haka Haj ta fito daga gidan maman Umar inda taso zarcewa gidan Farida don hankalin ta a tashe yake matuka Gaya musamman da taji kukan Farida tana son taji Abinda Sameer din yayi Mata don ta tabbatar da Zuwan nashi dama kwanani taji tana son zargin shi da Harbin mijin Faridar sai gashi yanzu Yana Shirin fitowa a Wani sunkurun . Sai dai bata iya zarcewa gidan Farida ba saboda yamma tayi sai kawai ta wuce gida inda zata Kira farida

Tana zuwa kuwa ta Kira wayar ta ta same ta Suka gaisa tana fadin.

“Wai Farida me ya faru ne ? Kar ki boye min komai don Allah.

“Haj Sameer Yana zalunta ta da son Lallai sai ya kashe min Aure na koma gareshi don Allah Haj kiyi mishi magana ya Daina bibiya ta tunda Al Amarin Nashi ya zama zalunci har Yana Neman .

Sai Kuma tayi shiru tana jin nauyin Fada.

“In Sha Allah kuwa Gobe goben Nan Farida har can zan iske shi Naji Dalilin shi na zuwa ya takura Miki tunda shi dai baya tsoron Allah gara da kika kira ni kika sanar Dani.

Washe gari kuwa Haj ta yanki tikitin jirgi ita Bello suka nufi pertercout sai Ganin su Sameer yayi kamar daga Sama Abinda Kuma ya tayar mishi da Hankali matuka Gaya don ya San karshen maganar dai ba zai wuce Abinda Farida ta Fadawa Haj ba. Don haka sai yayi matukar Shan jinin jikin shi ya tarbe su haj wacce take auna mishi Wani mugun kallo

<< Tana Kasa Tana Dabo 44Tana Kasa Tana Dabo 47 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×