Skip to content
Part 49 of 75 in the Series Tana Kasa Tana Dabo by Hadiza Gidan Iko

Wasila ta dubi sanato Uba Yan Doma da idanu cike da wani irin tsoro da firgici Jin Yana fadar Yana da tafiya Alhalin gata sabuwar Amaryar da take bukatar tarairaya da kulawa.

Tana Kallo ya taka step up din bene ya haura Saman d’akin tabi shi da Kallon tsoro da wata irin nadama..

Tana Kallo ya shige d’akin ya maido kofar ya Rufe har Yana murza key.

Ta dafe kirji tana Ambatar hasbunallahu Wani imal wakeel Wala haula Wala kuwwa ta illah billah.

Ta sake daga kanta ta zube idanun ta akan bangon Nan da akayi Zanen taswirar biri Mai kayan sarki har da sandar sarki

Ta Soma neman hada biyar da uku Wanda zasu Bata takwas akan alakar gidan da birai..

Tana Nan zaune tana faman tufka da warwara har taji ana Bude kofar tayi maza ta Kai ganin ta Saman benen inda yake saukowa..

Ya sauya Kaya Zuwa kansnun Riga t shirt da wando tree seater sai Kuma hular pacing Cap. Sai dai Abinda ya Kuma jefa ta a firgici da Tashin hankali shine Rigar jikin shi ma hoton birin ne Mai sanye da kayan sarki. Sai hular pacing Cap din itama a Gaban ta akwai hoton birin nan Mai kayan sarki..

“Inna lillahi wa Inna ilaihir Raju un.

Ta fada tana Jin Bata ko shakka wannan birin da Ake ta ado da taswirar sa akwai wani BOYAYYEN MAKIRCI akan sa . Meye abin burgewa a biri da har Ake ado da mummunar fuskar da har Ake kawata gida da ita? Tambayar da takeyiwa kanta kenan..

Ya aje jakar shi Yana dafa kafadar Wasila..

“Ga dakunan ki Nan Guda Biyu duk abinda kike so kiyi gidan ki ne Kuma dakunan a shirye suke haka Kuma komai akwai na bukata. Kiyi ko ki Saka ayi Miki gidan ki ne.

“Amarya zan tafi sati Daya zanyi na dawo ki kula min da kanki akwai hadimai a gidan komai kike so zasuyi Miki zan kira ki naji Yaya kike zan tafi sai na Dawo take care my dear. Ya fada Yana shafa fuskar ta..

Ya dauki jakar sa ya wuce Bai Kuma ce mata komai ba tabi shi da Kallon tsoron da shakka..

Ta Mike tsaye tana wars ido a katon falon Wanda Bata ji motsi komai ba bare taga hadiman da yayi maganar Akwai su..

Ta Dubi kofar D’akin da ya nuna Mata yace dakuna Biyu duka nata ne akwai komai ..

Ta shiga D’akin Wanda yake tarwai da Haske ga kawar Duniya an Zuba komai akwai hakikatan Babu ce kawai Babu a D’akin tun daga kujerun falon da kafet kafet Wanda aka Malala zuwa labulen da aka Rufe bangayen d’akin ..

Gaban ta ya kuma ya Kuma Sarawa a lokacin da taga Zanen birin Mai kayan sarki a Saman Rufin d’akin Wanda akayi da wasu Gold docoraition Abinda ya Kuma Bata Mamaki shine meye alakar biri da mutum da har Ake ado da shi a Gidan?..

Ta fito da sauri tana leka Dayan D’akin Wanda Shima dai an Zuba komai a ciki Babu ce kawai Babu Amma Shima sammakal dai akwai zanen taswirar birin .

Ta jima a zaune tana dauke kwallar idon ta don ta saduda ta Kuma gama Gane kuskuren ta da ta tafka a yanzu Kam Godiyar Allah ce da batayi ba take Godewa Akasin Godiyar don ta Gane a yanzu ga kudi dai har kudi Amma Kuma ita da kanta ta San Akwai Wani babban kalubale da damuwa tunda ita da kanta ma tana zargin gidan da Mai Gidan..

Kiran sallar magaruba ne da akayi yasa ta mikewa ta nufi D’akin Daya Wanda ta shiga tana k’arewa zanen taswirar birin kallo har ta wuce zuwa kofofin da ta Gani a dakin Wanda Suka kasu Biyu tana turawa tana ganin store ne Dayan Kuma shine toilet don haka ta shiga ta daura alwala ta zo tana sallah har ta k’are tana Rokon Allah ya kawo Mata Abinda yake Alheri ne a cikin wannan Aure Wanda ta Gane izina Mai ywwa ce a ciki yanzu ga Abdullahi can ya samu kudi na ban mamaki Kuma ga maimuna kanwar ta tana ta hutawa har tana Shirin Haihuwa ma..

Ta gama dogon lazimin ta fito inda taga an jera Mata kayan Abinci Wanda tayi ta Mamakin Wanda yake gidan da Bata ji motsin sa ba har ya gama abinda yake

Ta Bude abincin tana Gani lafiyayyen abinci ne da nama manya manya a Saman farar shinkafa wacce taji taji Kara’s da tsanwan wake na turawa da wani ganye Shar ..

Ta mayar ta Rufe don gaskiya Wani irin kyankyamin gidan da Duk Wani Abu take ji musamman biran da ta gani a waje da kuma zanen taswirar birin da akayi ta mannawa a bangayen d’akunan gidan ..

Ta koma ta Zauna ba tare da taji tana son cin Abincin ba don har ga Allah kyamar Abincin take ji .

Ta zauna da son taga waye hadimin gidan Wanda ya kawo Mata Abinci? Amma har goma ta buga Bata ji motsin kowa ba Abinda ya Kuma d’arsa Mata tsoro da shakka

Dole ta Mike ta wuce d’aki tana karanto ADDU OIN Neman tsari tana tofe kusfa kusfa na KUSURWAR D’akin kafin ta daura alwala ta kwanta

Ta jima batayi bacci ba tana ta faman tufkawa da warwara..

Bacci na daukar ta ta soma jin Abu a jikin ta inda taga goggon birin nan mai kayan sarki ne rungume Da ita yana shafa jikin ta da wani kakkausan hannun sa Inda ta so ta kwace kan ta amma ta kasa tana ji tana gani birin nan mai kayan sarki yana Romantic din ta har ya yi mata rumfa yana kaiwa kirjin ta dumbula amma bata iya wani motsi ba da zata kwaci ksnta hat taji ya keta ta yana shigar ta..

Wani irin zafi da radadi suka shuge ta kuma ta kasa yin ihu har sai da share lokaci mai tsayi bata san lokacin da ya barta ba.

Ta farka cike da wani irin tsamin jiki da radadi yayin da raga jikin ta duk gashin birin nan mai kayan sarki abunda ya tabbatar mata ba mafarki tayi ba gaske ne sai kawai ta rushe da kuka kukan nadama da bakin cikin. Dama goggon biri aka aurowa ita? Dama manufar kenan? Tashin hankali ya rufe ta ta kasa gane gaba da baya n ta ta baro mutum kamar ishaq ta kare da kwanciya da biri? Yau ta shiga uku ta lalace in haihuwa ta kama ta ta hsifi goggon biri? Sai ta kuma shekewa da kuka tana fadin ta shiga uku ta lalace.

Haka ta wuni babu sanin abinyi sai hangen makoma wacce ita da Kanta takewa kanta hisabi da karshen abunda ta shuka..

Kwanan ta Biyu a gidan tana fama da kunci da bakin ciki kuma matukar zata kwanta sai goggon birin nan mai kayan sarki yaxo mata a mafarki ya keta ta ya barta da tsamin jiki da bakin ciki. Kullum kuma ana ta faman aje Mata kayan kalaci na safe da Rana Amma daidai da Rana Daya tak Bata tab’a Katarin ganin Mai faman ajewa da daukewa ba sai dai tazo taga an Aje. Tun tana kawar da Kai tana kin cin komai saboda kyama har dai ta Hak’ura ta Soma ci Saboda taji yunwa na Shirin kassara ta..

Kuma har zuwa yau din uba bai kira ta yaji ya ts kwana ba

A Wani dare tw farka kishin Ruwa ya ishe ta ta nufi Wani fridge da ta Gani a falon ta nufe shi da fatan samun Ruwa tana Budewa kuwa tayi Arba da wata Roba wacce take cike fal da wani Abu jajir Wanda ta tabbatar da jini ne..

Ta mayar da fridge din ta Rufe da sauri jikin ta Yana kyarma..

Al Amarin da ya Kuma gigita tunanin ta da Hankalin ta kenan

Tsafi? Tsafi da shirka

Zuciyar ta ke ta nanata Mata ..

Ta koma ta makure tana Jin tsoron Al Amarin gidan gaba Daya .

Ta jima kafin ta Samu bacci ya dauke ta baccin da Bata ji Dadin yin sa ba don da ta San Abinda zata Gani kenan da Bata yarda ta Yi shi ba..

Wani irin katon biri ne sanye da kayan SARKI har da sandar shi ta Jan karfe Yana zaune a kan wata kujera ta sarauta yayin da Uba Yan Doma yake gurfane a Gaban shi cike da wani irin ladabi tamkar Mai Neman gafara ..

Sai kawai taga Wani mutane sun dauko Wani mutum Wanda yake ta Shure Shure Amma Basu dire shi ko Ina ba sai a gaban katon birin nan Wanda ya fito da WUKA ya yanke mutumin Nan da aka kawo Yana Shure Shure jini ya Soma zuba birin nan mai kan sarki ya tarba bakin shi jinin mutumin Nan Yana zuba a bakin shi Yana shanyewa..

Sai taga tawagar wasu biran sun zo sun ja gawar mutumin Nan da biri Mai kayan sarki ya yanka suka wuce da shi suna cizgar Naman jikin shi suna ci suna gurnani..

Ta farka jikin ta yayi sharkaf da zufa sai kyarma take tana tunanin Abinda ta Gani Wanda ya Soma fassara Mata kowa ye birin nan. Amma Kuma MAFARKI ya Isa zama shaida?

Ta jima Bata koma bacci ba har garin ya K’arasa wayewa ta SHIGA toilet..

Sai da ta fito ne taga an Jere Mata kayan break inda taji a yau Kam tana son Ganin Mai wannan hidimar har ta Soma zagaye gidan da sunan neman Mai hidimar Nan Amma ko kwado Bata Gani ba. Haka Kuma tayi ta zaga ko Ina da sunan neman kitchen Shima ba d’akin ta kawai ta iya Gani Amma Bata ga Wani bayan wannan ba .

Ta dauki wayar ta tana Kiran Anty murja suka gaisa tana tambayar ta Goggo da maimuna tace kowa Yana lafiya sai dai mugayen mafarkai da suke tayi da ita..

Gaban ta ya Sara tace

“Mafarkai Kuma Anty murja wane irin ?

Anty murja tace

“Uhum Wallahi Goggo ce ta fara fada min tana yawan MAFARKI da ke a tsakiyar jeji wasu birai sun kewaye ki suna ta yagun ki tun dai tanayi jifa jifa har nima dai Wallahi Shekaran jiya nayi wasila gashi Kuma wayar ki ba a samun ta ..

Sai kawai wasila ta fashe da kuka tana Fadin

“Anty murja don Allah ki cewa Goggo tayi Mini ADDU A Wallahi gidan da aka kawo ni cike yake fal da birai manya da k’anana Wallahi na San SHIGA UKU ce ta same ni Anty murja ko Kuma nace Allah NE yake sakawa ISHAQ ta adin da nayi Mishi..

Anty murja ma ta fashe da kukan tana Fadin

“Inna lillahi wa Inna ilaihir Raju un wasila Gaya Mana a Ina Gidan ki yake..

“Wallahi Anty murja ko a Legos din ba zan iya fiddo kaina ba ni dai kicewa Goggo ta yafe mini don naji a jiki na Wanda gidan da na shigo mahallaka ta na shiga don Allah don ANNABI ku yafe mini Anty murja ki nema min gafara wurin ishaq da sagir na san ko Alhakin su kadai ya ishe ni . Kuma wannan biran da kuke Gani Wallahi gidan mutumin Nan cike yake da birai manya da k’anana ni kaina a tsorace nake da gidan ..

“Inna lillahi wa Inna ilaihir Raju un wasila bamu ga ta zama ba bari na tashi naje na samu Goggo a Nemo waliyyan mijin ki don mu Nemo gidan ki tun Al Amarin baiyi Muni ba..

Anty murja ta fad’a a Rude tana kashe wayar ta .

Kuka kashirban wasila take tana Fadin ta shiga uku..

Wata zuciyar ta fada Mata ta nemi honorable Gona Wanda ya kasance Abokin Yan Doma ne don taji Wani Abu daga gareshi ..

Ta jawo wayar ta tana dokawa gona Kira Amma har ta tsine Bai daga ba ta sake Kira dab da zata tsinke ne ya dauka Yana Fadin.

“Amaryar mu kin Sha kamshi ya ya amarcin?..

“Honorable don Allah tambayar ks zanyi me ka Sani akan Yan Doma? Na fara nadamar Auren shi tunda har Ahali na sun fara MAFARKI Dani a mummunan yanayi..

“Ni Kuwa me na sani akan shi Amarya? Ai in da akwai Wanda ya bayar da shaida akan sa Ina Ganin kece ko kuwa?.

“Don Allah ka kar ka Rufe mini tunda ban manta ba ka Kira ni kana fada min ba sa ar Aure na bane Amma banji ba..

“Au to yanzu ne da masara taji Wuta take Shirin fashewa da kanta? Me ya sa baki fahimci Wani Abu nake son Sanar da ke a wancan Lokacin ba? Ke da kanki fa kika ce min na makara karshe ma sai kashe wayar ki kikayi sai yanzu ne kika ga kamatar kiji Wani Abu? Da kin bari na fada Miki tun a wannan lokacin da Baki kawo yanzu kina nadama da Dana sani ba. Ni da Kaina na fada Miki kar ki Auri Mutumin Nan Amma kika ce min na makara Ashe kece kika makara to ni yanzu me zanyi Miki? Me kike son sani akan sa?..

“Kayi min Afuwa don girman ALLAH Wallahi a da can ban fahimce ka ba Amma a yanzu ni da kaina ne nake son sanin waye shi tunda Naga abubuwan Mamaki ..

“Ai Baki fara Ganin abubuwan mamaki ba tukuna tunda gaki nan da Ranki da lafiyar ki ai me ma kika Gani? Ki bari tukuna ki fara Ganin abubuwan mamaki sai muyi magana dama Mai Rabon Shan duka baya Jin kwab’a tunda dai kinji kina son mijin ki Kuma ba Zaki fasa Auren shi ba ai kiyi Hak’uri kawai da Duk Abinda kika Gani kar ki damu kiyi Hak’uri Zaman Aure ai dama haka yake In dai ibada ce kalubalen ta yawa gareshi Lada ma zaki Samu Amma ki sani Baki fara Ganin komai a cikin mugun Aikin Yan doma ba sai kin fara zama da kyar tashi da kyar ko kuwa kin Rasa ido Daya ko kafa Daya sai na fito Miki da komai a faifai ta yadda Zaki Gane ita bari ba shegiya bace da Uban ta a ci gaba da istigifari da salatin ANNABI MUHD S A W don kuwa kin Kai kanki inda Babu mafita sai wacce Allah ya kawo Miki ai kinga birai a gidan ko? To madalla dai .

Ya tsinke wayar shi ya bar wasila da Tashin hankali Mai yawa Wanda ya Saka ta mikewa tana zarya a falon tana tariyo maganganun Gona. Ya San da zaman biran Nan,? Meye manufar zaman su a gidan? Me yake nufi da sai ta Rasa ido ko kafa ko zama da kyar tashi da kyar?.

Ta Kuma danna Mishi Kira don tana Jin a da can bataji tashin hankali ba irin na Yanzu wanda ya gama kad’a Mata ganye..

Ta danna Mishi Kiran har ta tsinke Bai daga ta Kuma danna Mishi Kira tana kallo yayi rejected karshe ma da ta sake Kira sai taji wayar a kashe..

Haka ta wuni kiran wayar Gona amma a kashe ta Kuma kasa Hak’ura da kiran Amma ta kasa samun shi .

Tana nan zaune wayar ta ta dauki tsuwwa tana dubawa taga Shama ce ta dauka inda tajiyo shama na Fadin zasu shigo Garin Lagos ta tura Mata address din gidan ta don nan zasu sauka..

Bata iya Cewa Shama komai ba ta kashe wayar inda ta Soma neman layin Yan Doma Wanda tayiwa kira biyar kafin ya dauka murya can k’asa yace mata..

“I’m busy I will call you back..

Ya katse Wayar shi ya barta da sakin Baki. Yau kwanankin shi Hudu da tafiya ko da wai Bai Kira ta ba bare yaji Yaya take sai ma Amsar da ya Bata wai Yana Aiki zai Kira ta Daga Baya..

Ta Soma zarya tana neman zarewa

Ta nufi waje don tunda ta shigo Bata leka waje ba

Tana fita kuwa ta hango biran Nan suna guje guje a farfajiyar Gidan suna ta gurnani Babu Arziki ta juyo da sauri tana fadin..

“Na SHIGA UKU…

<< Tana Kasa Tana Dabo 48Tana Kasa Tana Dabo 50 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×