Skip to content
Part 52 of 75 in the Series Tana Kasa Tana Dabo by Hadiza Gidan Iko

Zubaida ta kama wasila tana tayar da ita tana fadin

“Ambaci sunan ALLAH Zaki samu Amincin tashi ta tsayuwa .

“Lah haula Wala kuwwata illah billah

Ta furta sai ga ta a tsaye Zubaida ta kamata.

“Tunda muka Daura aniyar tafiyar Nan Dole mu kasance cikin Ambaton sunan ALLAH Kuma tare da Neman agajin sa don Haka duk ADDU AR da tazo Bakin ki ko kika iya to Yi ta fad’ar ta kina maimaita wa.

Zubaida tana Rik’e da Hannun wasila wacce take takawa a Hankali don iske ma Yana Neman kayar da ita ga tafiyar in tanayi tamkar Zata yage Saboda lillar da akayi Mata a bayan ta.

Suna dab da kofar fita suka ga Uba a bakin kofar Yana tsaye dafe da kugun shi Yana kallon su Kuma ga Alama suna Shirin ficewa ne don haka ya tsaya Yana kallon su .

“Zubaida kina da kokari gaskiya yanzu kina iya fita a gidan Nan a zaton ki?.

“Da karfin ikon Ubangiji zan iya don Ina Jin Hakan a Raina tare da tabbaccin Ubangiji ba zai kunyata ni ba .

“Ok to ga hanya sai nace Allah ya jikan ku duk da ita dai wannan ta Riga mu Gidan gaskiya lokaci kawai take Jira Domin kuwa GAWA ce da Rai Amma saura Taki kad’an a shafe babin Rayuwar ta tunda an bayar da katafun ta kema idanun da Sukayi Miki saura yanzu zan kyautar da su ai sai da su kike Ganin hanya to Zaki Rasa Ganin ta .

Ya wuce su Zuwa Saman benen inda ya dukufa ga son Ganin ya kassara Ganin Zubaida.

Da karfin ADDU AR da take Bakin Zubaida ta Bude kofar gaban ta Yana Sarawa Saboda tuna biran Nan da suke fareti a farfajiyar Gidan Amma da ta k’ara kaimin ADDU AR ta sai Bata gansu a kusa ba sai ma can da taga sunyiwa Wani Abu dafifi suna ta gurnani Abinda ya tabbatar Mata da wani Abu ne Suka dafa ko ma ace mutum ne Suka Rufarwa da yakushi Wanda in suka kashe sau Kuma suyi ta yagar Naman jikin shi suna ci .

Da sauri Zubaida tana Rik’e da wasila suka nufi kofar duk da son suyi sauri kafin hankulan biran Nan ya Kai garesu Amma Kuma wasila Bata iya sauri ita kadai ma ta San yadda take ji a tafiyar nan tamkar Zata yage gashi Kuma ana bukatar gaggawa.

Suka Samu da kyar suka Isa dab da kofar fita Amma sai me?

Gaba Daya suka nemi kofar suka Rasa tamkar ma ba a tab’a Halittar kofar a wurin ba.

Sukayi turus Zubaida tana kallon Al Amarin tamkar a mafarki tasan kadan kenan daga mugun Aikin su .

Ta waiga inda biran nan suke suna ta gurnani akan Abinda suka Rufarwa suna ta badalin su sai kawai Zubaida ta kuma tunkarar hanyar da ta San nan kofar take tana Kara ADDU OIN bakin ta ta tunkari wurin da wani irin tabbacci sai ga kofar tana bayyana a idon ta ta Isa kuwa tana ta maimaita ADDU OIN ta har ta kama kyauren kofar Wanda yake kulle da sakata sama da k’asa da Kuma tsakiyar.

Ta Soma kokarin Zare sakatar ne wacce tayi wata irin k’ara wacce ta jawo Hankalin biran Nan suka juyo inda Zubaida ta Kuma zare sakatar ta tsakiyar k’arar ta Kuma karade gidan duk da haka Zubaida da take yin komai da Hannun ta Daya Mai lafiya bakin ta Bai Daina Ambatar ADDU OIN ta da Neman taimakon Ubangiji ba .

Ai kuwa biran Nan da suka hango mutane a bakin kofar sai suka dauki Wani Uban ihu suka Kuma Bazamo su Duka a tare dauuuuu suka sheko Aguje suna gurnani.

Da sauri Zubaida ta ambaci sunan Ubangiji ta k’arasa zare sakatar k’asa suka auna ita da wasila wacce take Langewa inda Zubaida ta jawo kofar ta makala sakatar waje ta yadda ba zasu iya Bude kofar ba .

Duk akan idon Uba Hakan ta faru . A zaton shi biran Nan ba zasu kyale su wasila ba sai ya Sha mamaki Domin kuwa a Lokacin da kofar ta shafewa Ganin su Dariya ya kama sai Kuma yaga allon computer da take hasko mishi komai ya dauke sai farin haske sai da aka jima ne yaga komai ya dawo har zuwa ficewar su Zubaida.

Da sauri Uba Yan Doma ya dauki wayar shi Yana Kiran tauri.

“Tauri ga su Nan fa sun samu fitowa daga gidan nan ku bi mun bayan su ku dawo Dasu yanzun Nan.

Ya ajiye wayar Yana Dariya.

Zubaida da Babu hannu da kafa lafiyayyu Amma Cikin ikon Ubangiji sai gata da auna Gudu wasila ma tana Rik’e da Hannun Zubaida suna ta Gudun ceton Rai.

Napep ce ta auno Aguje ta Nufo su sai kawai suka Soma tsayat da ita ta kuwa tsaya Suka fada ciki ya auna da su a guje.

Sai kawai Gani Sukayi ya juya kan Napep din ya auna Aguje da su Zuwa baya inda suka baro .

Suka kalli juna Zubaida da wasila saboda ganin Uban Gudun da yake sharawa .

Zubaida ta Ruko Hannun wasila suna kwartsa ihu Domin kuwa sun fahimci manufar shi ta mayar da su Inda Suka baro sai kawai suka kame har suka tunkari kofar gidan Yana ta danna hon har dai ya faka Napep din .

Aguje suka fito suka Kuma kwasawa aguje daidai da Bude kofar inda biran Nan suka Rufu akan tauri suna yagu suna yakushi har ya Kai k’asa.

Da sauri Uba ya sauko don Yana Ganin Akasin da aka Samu .

Zubaida da wasila kuwa tuni suka zage suna gudu inda suka yanki wata hanyar duk da Basu San inda zata kaisu ba. Anan Kam sun yarda nakasa ba kasawa bace tunda gasu a yau duk da a na kashe suke Amma nasu kasa da ceton Rayuwar su ba .

Wani Dan okadan mashin ne da ya auno Aguje inda Zubaida ke fad’in

“Ga shi nan ya biyo mu wayyo Allah .

Yana zuwa inda suke suka ji Yana tambayar su da harshen turanci cewa tafiya ne?

Anan suka yarda ba wancan azzalumin bane.

Da sauri Zubaida ta Haye bayan shi kafin wasila da take dab da daukewar numfashi ga bayan ta da take jin Yana Shirin ficewa.

Suna Hawa Yana tambayar su inda zai kaisu ya bawa mashin din wuta Zubaida ce ke cewa .

“Motor Park line.

Ya kwasa aguje suna like a bayan shi suna sauke AJIYAR ZUCIYA sai a lokacin ne Suka tuna Babu wacce take da kudi a tare da ita bare su biya Dan okadan nan kudin shi bare Kuma kud’in motar Zuwa katsina.

Tafiya Mai Nisan gaske tamkar zasu bar Duniya Yana ta auna Uban Gudu da su Yana daukar overtake ya hau tudu da gangare har kafin ya kawo su motor Park line tashar da motocin zuwa garuruwa suke.

inda suka Sauka suna Raba idanu don Basu San me zasu ce mishi ba.

“9k your cajis.

Ya fada Yana kallon su .

Wasila da take shafa jikin ta Babu ko sisi a tare da ita sai wayar ta bare Kuma Zubaida da Babu komai a tare da ita sai kayan jikin ta ko mayafi Bata Dashi.

“Ehem I will quickly madam.

Ya fada Yana zaro musu jajayen idanun shi .

“You have account nomber?.

Cewar wasila wacce ta tuna akwai kudi account din zata iya Yi mishi transfer.

“I don’t collet transfer money kash an carriyon.

Wasila ta Dubi zoben hannun ta tana fad’in

“Ok please were can na get dew sel Gold? We can go I sel my gold .

Ya kada kanshi yana fadin

“I know dat place go go .

Suka Kuma hawan mashin din yaja su a guje suka nufi kasuwar da Ake siyar da ZINARE har wani katon shago inda aka tarbe su aka Basu wurin zama wasila tace zata siyar da zoben ta ne tana bukatar kud’i.

Ta cire zoben ta bada aka shiga awon gram ama fada Mata nauyin shi da yawan gram din.

Take ta sallama aka Bata kud’in ta Dubu sittin da takwas ta fito tana bawa Mai mashin dubu goma tace nawa zata bashi ya mayar da su Tasha? Yace Ina zasuje tace katsina ya dauke su ya kaisu wata tashar Nan kusa da inda suke suka dauki shatar mota guda wacce ta dauko su daga Legos zuwa katsina.

Kamar sun sani Suka dauko shatar motar Nan Domin kuwa Uba Yan Doma ya tayar da Jami an tsaro binciko wasila da Zubaida musamman da tauri baiyi Rai ba Sakamakon biran gidan shi da suka Rufar mishi sai Al Amarin ya tayar mishi da Hankali ya tayar da Neman su Zubaida Wanda tuni sukayi Nisa da garin Legos.

Goggo da Anty murja da suka nufi Gago wurin iya wacce tace suzo akwai malam kalla Wanda yake Aiki Babu sihiri in dai an kawo mishi abinda ya nema to in Sha Allah ko aljanu ne suka dauki wasila ba Wai tsare ta ba in Sha Allah zata samu kubuta.

Goggo da Anty murja har da iya suka nufi gidan malam kalla Suka karanta mishi Abinda yake faruwa ya gama sauraren su kafin ya ce

“To Abinda ya kamata shine kuje kuyi Sadakar abinci ku Kuma Yi wa k’ananan Yara sadaka ta kosai ko waina in Sha muma zamu Roki Ubangijin Musa da haruna inda Rabo zata dawo in Kuma Babu dama ba mu mukeyi ba Allah ne mai yi sai mu yarda da kaddara Amma kuskure ne Babba mutum ya zo garemu ya jingina Mana imanin sa Bama son haka kawai ku kalli komai daga Allah NE ba Daga wanin sa ba in Kun fahimce ni to in Sha Allah Al Amarin mu duk zai zo da Imani da Kuma sa a amma matukar kuka mayar da ALLAH baya kuka kai Wanin sa Gaba to in Sha Allah Babu Abinda zai Hana a kunyata Kun fahimce ni?

Suka amsa da hakika sun yarda Allah NE Mai yin komai sai dai tashi in taimake ka da ya fad’a Mana.

“To madalla haka nake so Kuma in Sha Allah zamuyi nasara kuje ku abinku in Sha Allah yau zamu fara Rokon Allah Kuma in Sha Allah ba zamuyi kwana uku munayi ba sai ta bayyana da ikon Ubangijin musulunci.

Goggo ce ta aje mishi abin sadaka yace a KUL baya karba ga wadan da za ayi wa sadaka can almajirai a Basu Abinci Yara Kuma a Yi musu ta kosai ko waina.

Da haka suka baro Gago washe gari kuwa Anty murja ce ta dafo Abinci ta kawowa Goggo ita Kuma Goggo dama tun safe ta Yi Sadakar kosai hade da wainar sai Kuma ga Abinci murja ta Aiko wake da shinkafa.

Goggo ta Tara almajirai tana Raba Musu.

Magarubar farko motar ta sauke wasila da Zubaida a garin katsina inda Kuma Zubaida wacce take Sokoto tun s Kano taso sauka Amma wasila tace ta bari ta sauka a Gidan su ta huta tukuna sai ta wuce Sokoton. Don haka a tare suke Napep ya kwaso su daga tashar nartow zuwa gidan Goggo.

Goggo tana Daura Alwalar sallar magaruba taji sallamar wasila ta dago da sauri tana fadin.

“*Wa nakeji kamar wasila?

Alhamdulillah.

Cewar Goggo wacce ta ga wasila .

Da sauri wasila ta Rungume Goggo tana kuka Goggo ma hawaye take tana Fadin

“Alhamdulillah Allah kaine abin Godiya Kai waye a Nan ya Kira min murja yace mata ga Yar Uwar ta ta dawo.?

Da sauri Goggo ta dubi Zubaida tana fadin

“Sannu yarinya tare kuke tafe? Zubaida ta gayer da Goggo tana Fadin

“Tare muke Goggo.

“Masha Allah.

Goggo ta dauki wayar ta ta mikawa wasila tana Fad’in

“Kira Mana murja tazo .

Wasila ta Kira Anty murja wacce tana jin muryar wasila ta Bazamo

Kan kace me? Gida ya cika har da yaya ma aruf inda Ake ta yiwa wasila barka.

Har dare ana ta zarya inda Goggo ta dubi Zubaida tana Fadin

“Baiwar Allah a Ina kuka hadu Naga kamar a tare kuka taho.

Wasila ce ta zayyane wa Goggo da Anty murja ta yadda Zubaida ta shiga Hannun Uba da yadda soyayyar su tazo da yaudarar da yayi Mata aka sato ta aka Kai mishi can gidan da haduwar su da Kuma irin taimakon da tayi Mata har kawo yau din da Suka samu nasarar baro garin Legos suka iso katsina duk da Zubaida Yar Sokoto ce shine tace tazo Gidan su ta huta kwana biyu ko sati kafin ta Isa nasu gidan don a San tana Raye ko hankulan su zasu kwanta.

Haka aka Raba Dare ana fira anty murja tana yiwa Zubaida ADDU A musamman da taga hannun ta da kafarta a shanye irin na Mai Shan Inna ko mutuwar b’arin jiki Amma dai Bata fasa Mata ba

Kwana biyu Zubaida tace zata wuce Sokoto don ta gana da iyayen ta da suka jima da fidda Rai da ganin ta.

Wasila taso Yi Mata Rakiya Zuwa Sokoto to Amma Wani irin ciwo da bayan ta yakeyi ko zama ta kasa sai dai kwanciya Dole tayi Mata kudin mota ta Bata lambar wayar ta tace in ta sauka ta Kira ta su Gaisa Da iyayen ta.

Goggo ma ta Mata Sha Tara ta Arziki haka ma Anty murja da haka Zubaida tayi musu Sallama tana Godewa karimcin su ta wuce garin su Sokoto.

Dawowar wasila gida ne take Jin Kunyar fasa Al Amarin da ya faru a cikin Auren ta musamman bi ta bayan ta da Mijin ta yake har ya Zamo a yanzu Bata iya zama bare Kuma ace tsutsar Nan ta Soma cizon ta Al Amarin Yana damun ta Amma Kuma ta San da kunya Idan ta fasa shi

Maimuna ta iso da katon cikin ta Wanda haihuwa yau ko Gobe don ma ta shanye wata har ta SHIGA cikin na goma .

Ta zube a Gaban wasila tana ta mayar da numfashi don sai da ta matsa ne ISHAQ ya yarda ya kawo ta .

Wasila tabi maimuna da kallo suna gaisawa tana ta Mata Sannu ganin ta zama kayan Nauyi.

Ta wuni a gida har su yusra suka taso makaranta suka biyo gidan Goggo suna Ganin mahaifiyar su sai da yamma ISHAQ ya zo daukar maimuna Banda Yana ganin kimar Goggo da Babu abinda zaisa ya shiga gidan Amma sai ya shiga har ya jajanta wa Goggo ya Mike ya fito waje inda wasila taga yadda ya koma yayi kiba ya zama done Kai ba zaka ce shine ba.duk a lokaci Daya ta kalle shi Amma inda take Bai kalla ba bare yace Mata ci kanki har ya fice Yana hade fuska.

Kwanaki biyar kenan da Dawowar ta Amma Bata ga Sagir ba Abinda Kuma yayi matukar tayar mata da Hankali har ta Soma kuka ita da kanta ta San Bata kyautawa yaron ba Kuma in yace ba zai zo ya duba ta ba bare ya jajanta Mata ba zata ga laifin sa ba Domin kuwa batayi mishi Abinda zai kula ba.

A Ranar da ta cika kwana bakwai ne Kuma ta tashi da Wani babban Al Amari na kasa Rik’e tutu sai dai kawai taga ta sake shi zubut Babu control. In Kuma taji shi kafin ta Mike zuwa Bandaki har ya fice fit duk kokarin ta na son Ganin ta kame da son matse duburar ta Amma ta kasa hakan ita da kanta ta San ta tawaya a nan kuma ba komai yaja Mata Hakan ba sai waccan bak’ar ta adar da akayi Mata a bayan ta Ashe JANHURUN masifa aka jawo Mata.

Kuka take kashirban tamkar wacce akayiwa mutuwar iyaye Biyu Uwa da Uba Abinda ya fito da Goggo kenan wacce taga tutu a gefe k’udaje suna ta gada sun yanyame tutun Wanda ya cika D’akin da wari ga Kuma wasila da take sharbar kuka tana dafe da kanta Alamar jimami da Tashin hankali da Kuma JANHURUN masifar da itace ta jawo wa kanta ba kowa ba.

<< Tana Kasa Tana Dabo 51Tana Kasa Tana Dabo 53 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.