Skip to content
Part 53 of 53 in the Series Tana Kasa Tana Dabo by Hadiza Gidan Iko

Blessing wacce zuwan matar Sameer yayi matukar firgitawa don ta Rasa ta yadda za ayi ta mallaki Sameer tunda har ga matar shi ya kawo a Nan

Kwana Biyu tana Kiran wayar shi Yana kin Amsawa Abinda yayi matukar tayar Mata da Hankali

Wurin Aikin shi dai Bata Isa taje da sunan wurin shi tazo ba saboda ya gargade ta da yin Hakan  Gidan haka ma Gidan shi a Yanzu yafi k’arfin ta sai ta Rasa hanyar ganin shi bare Taji mafitar da ya sama mata don ita Kam Bata ga miji ba sai shi

Tana cikin wannan Yanayin ne Kuma ta tsinci Wani na zazzabi da kwarara Amai kafin Kuma ta Soma jinya har dai suka dire Asibiti ita da mahaifiyar ta likita Kuma ya tabbatar musu da cikin ta na watanni UKU

Mamar ta ta Soma masifa tana fadin

“Kin jawo mini ba? Dama yaushe Ake tarayya da Hausa man Basu cuce ka ba? To ki fada mishi mu ba ayiwa Ya’yan mu ciki sai Wanda zai Aure su don haka ya fito ya Aure ki tunda kince kinji kin Gani

Wayar Sameer ta kasa Samuwa wurin Blessing wacce take matukar bukatar taimakon Sameer din akan cikin Nan Mai laulayi

Sameer kuwa Dukkan damuwar shi a Yanzu Guda Biyu ce Zafafan kalaman Haj akan shi Wanda ta furta mishi akan idan ya Kuma bibiyar Farida da kuma barin Farida tare da mijin ta Wanda ya lashi takobin kisa gareshi Amma Dole Yana Ji Yana Gani ya Hak’ura ya barsu a tare sai dai yaga Farida ta Dora status din su a waya Wanda ya San don shi take yin Hakan

Tunda aka kawo mishi Aisha Bai tab’a duban ta da bukatun gangar jiki ba sai dai tayi girki yaci ya fice ya Kuma Bata umurnin Yi ko bari

Bai tab’a tunanin Wani Abu zaije ya Dawo ba sai da Allah ya Nuna mishi ishara yaga Abinda yake faruwa da kurtun Sojan da ya yarda da shi wato Mustafa

Ranar da Allah ya tona musu Asiri Sameer ya fita Aiki Amma sai Allah ya jarraba shi da Ciwon ciki Wanda ya tilasta shi Dawowa gida a Kuma daidai Lokacin da Mustafa da Aisha suka Saba haduwa suyi Abinda suka Saka kansu na yaudarar Sameer

Takalman Mustafa da Sameer ya Gani a kofar D’akin ne Abinda yaja hankalin sa ya tura kofar D’akin Amma yaji ta a kulle sai kawai ya yi amfani Da key din wurin shi ya bude D’akin inda yayi mugun gani da Mustafa da Aisha a Wani yanayin Da ya tsorata shi har ya kwartsa Wani Uban ihu Wanda ya Ankarar da su Akwai Wani bayan su ba su kadai bane

Sai a lokacin suka ga Sameer Wanda yake tsuma Yana dafe da bango Yana kyarma

Da sauri Aisha take Neman mayafin yafawa ta Rufe tsiraicin ta shi Kam Mustafa sai ya damke filo Yana Neman shigewa acikin filon

A guje Sameer ya fito ya nufi motar shi wacce take a waje inda Mustafa da Aisha suka tabbatar da mugun Aikin na Shirin faruwa sai suka nemi matsera

Da sauri suka fito da son Neman mafaka inda Sukayi kicibus da shi ya Suro bindiga daga motar Yana Shirin shigowa

A guje suka kwasa suna gudu Amma sai da ya sakarwa Mustafa harsashin a kafada ita kuwa Aisha a gefen ciki ya same ta Amma da yake Gudun ceton Rai ne Basu tsaya ba Suka dauki hanyar ficewa daga barracks din inda ya zube a k’asa Yana mayar da numfashi tamkar Mai Ciwon asmh

Sai Kuma ya kike da sauri ya shige motar ya fige ta a guje don Yana Jin yau idan Bai kashe Mustafa da Aisha ba shine zai mutu

Tuni akayi Rabuwar Ruwa tsakanin Mustafa da Aisha kowane ya tarbi abin hawan da zai tserar da Kansa don haka duk yawon Neman su da yayi Bai iya Ganin su ba Dole ya dawo gida da mugun Alwashi a Ranshi

Yana zuwa kofar gidan kuma yayi karo da blessing wacce ta tarbe shi da takardar awon cikin likita da Kuma bayyanar cikin ta

Ya Dube ta cike da Bak’in ciki da Jin haushin Abinda take nufi da shi

“Me kike nufi da bani wannan Banzar takardar? Duk Mazan da kika bibiya Babu Wanda ya dace da ya Amsa Uban cikin ki sai ni? To kar ki Kuma nufa ta da wannan maganar don zan kashe ki ne na kashe Banza

“Kana son kace mini duk mu amalar da mukayi da Kai karya ne kenan? Kana son kace mini Sharri Nayi maka? Wallahi tunda na soma kula ka ban Kuma sauraren Wani Namiji ba na yarda idan na Haihu a gwada jinin shi idan ba yaron ka bane kayi min Hukunci

“Ke ya ishe ki haka kinji ? Ni Zaki kawowa wannan maganar don kina stupid?

“Yaya kake ce min stupid don na zama banza a gareka ne ? To Wallahi zan Kai k’arar ka a wurin Ogan ka tunda na kula kana son wulakanta ni don nayi cikin ka

Sai kawai ya Soma fallawa blessing Mari Yana Shirin taka Mata ciki

Ta kwaci kanta daga hannun shi don dukkan fushin su Mustafa da Aisha akan blessing ya sauke shi

Ya shiga cikin Gidan Yana huci Yana watsi da kayan da cikin Gidan tamkar mahaukaci sabon kamu Allura ta motsa inda ya nemi ciwon ciki ma ya Rasa

Madam gora itace Uwar Blessing wacce ta Saka Blessing kaiwa Sameer takardar awon cikin tace Kuma Daga yau Dukkan dawainiyar ta shine zaiyi Mata kafin ta Haihu Kuma ya Aure ta su dama Namijin da akayi ciki da shi shine mijin Aure a Al adar su duk da madam gora tana ganin blessing ta ja Mata abin kunya tunda tayi ciki da Hausa man Kuma musulmi maimakon Dan kabilar su Kuma yaren su  Shiyasa tun a Asibiti madam gora take yiwa blessing masifa tamkar Zata Kai Mata Duka Kuma suna Zuwa gida tace Maza ta Kai Mishi takardar ta Kuma karbo kud’in Abincin ta da na sauran lalurar ciki Haka ko da blessing din ta fits bata Daina masifa da tijara ba tana Ganin an jawo musu abin fada da abin kunya

Tana cikin masifa Blessing ta dawo fuska a kumbure ga Kuma hanci Yana yoyon jini

Ta Mike tana Fadin

“Kinyi hadari ne?

Blessing ta Sanar Mata yadda Sukayi Da Sameer da irin dukan da ya lakada Mata

“Ya Dake ki kika ce ? Ya kuwa tayar da balaki daga bacci Wallahi ba zan yarda da wannan cutar ba sai ya biya ki Wallahi

Ta fito tana ta masifa tace su tafi can barikin Nasu ta same shi suyi masifa da balaki

“Mama in kika je zai dukan ki sai dai muje wurin Ogan su mu sanar dashi

“To muje ai ni har Uwar sa ma sai na Nemo ba Kuma zai Miki ciki a wofi Kuma ya Dake ki ba Wallahi har kud’in dukan nan sai ya biya ai gashi Nan Ina nuna Miki Hausa man Basu da kirki kina nane Musu gashi Nan Abinda yayi Miki

Haka Suka tafi madam gora tana tana ta tijara har suka Isa office din Ogan Sameer Wanda Suka nemi ganin shi aka aika mishi ya Kuma ce su shigo

Madam gora ta Soma kuka na munafunci tana faduwa a gaban shi tana nuna Mishi blessing da hanci ke ta yoyon jini da Kuma Bayanin Sameer yayiwa yarta ciki Kuma ya kama ta da Duka ya fasa Mata hanci

Ya Kalli blessing Yana tambayar ta Abinda yake tsakanin su da Sameer ta Kuma zayyana mishi cewa saurayin ta ne da yace zai Aure ta har ya kaita gidan shi tana kwana tana mishi girki don ya Auro Hausa girl ne ya Hana ta Zuwa gidan shi inda ta wayi gari da ciki Kuma nashi shine daga ta Kai Mishi takardar likita yayi Mata Duka

Madam gora sai kada Kai take kamar kadangaruwa tana Fadin

“You see my Oga? You see my Oga?

Wasu daga Cikin Abokan Aikin Sameer ma sun Bada shaidar sanin blessing tare da Sameer don haka aka Kira shi Yana gida Yana hadiyar zuciya

Ya iso office din inda ya iske blessing da Uwar ta Oga Kuma ya karanta mishi Abinda suke k’ara akan sa

“Zaka dauki nauyin ta akan komai har ta haihu tunda kayi Mata alkawarin Auren ta Kuma me yasa ka Dake ta ?

“Har ya fasa Mata hanci ma gashi ba? Gashi ba ? Sai jini yake ? Cewar madam gora

Sameer ya Dube ta Yana Jin itama ba zata Sha ba in dai tace Zatayi mishi wannan makircin

“Oga yarinyar Nan Yar iska ce  Haka Kawai ta Rana tsaka tazo tace min wai tana da ciki Kuma nawa ne? Nayi Mata magana tana min Rashin kunya?

“Baka tab’a kwana da ita bane?

Ogan ya tambaye shi ya Amsa da ya Kwana da ita Amma ya jima basa tare

“Anyi Shekara ne?

Ya kada Kai Alamar A a

“Anyi wata UKU?

Yace anyi

To cikin wata nawa ne?

Aka ce UKU

Yace to kaje ka biya su Dukkan kudin da zasuyi caji daga gareka idan ta Haihu za ayi gwajin jini idan ba Dan ka bane ni da kaina zan nema Maka hakkin ka in Kuma Dan ka ne ya zama Dole ka cika Mata alkawarin Auren ta tunda har ka amsa ka kwana da ita

Madam gora tayi maza tace

“My Oga a karbar Mana nan gaban ka in daga ita sai shi ne zaice Mata barazana ya Hana Amma idan aka Amsa sai muzo hannun ka mu Amsa

Haka kuma Akayi sai da Sameer ya direwa madam gora kudin da tace sune ns hidimar blessing abinci da Kuma Asibiti Kuma duk watan Duniya sai ya bayar har ta Haihu da haka aka sallame su

Aisha ta iso katsina Kai tsaye ta zarce gidan Uwar ta sai ganin ta Asiya tayi babu Shiri ga gefen ciki ya mele har Yana fidda Wani irin Ruwa da jini don fatar wurin ce ta yashe Amma Bai Kai ga Cikin nata ba

Asiya ta dauki salati tana kakabi Amma duk tambayar Duniya Aisha taki magana ga tafiya Babu shiri gata tazo da kuka ciki a melee Dole Asiya ta wuce da ita Asibiti aka Bata agajin gaggawa har ta samu kafin Anty Asiya ta Kira wayar Hajiyar Sameer tana tambayar ta ko Sameer yazo ne? Ga Aisha tazo da malolo a ciki Kuma Bata ce komai ga Alama Kuma tafiyar Babu Shiri a cikin ta ko za a tambaye Sameer ne?

“Subuhanallahi Asiya Ina Aishar take ne?

“Gamu a emergency room anyi treat din ta

“To Gani Nan Zuwa

Minti Sha Biyar ya Kai Haj emergency room ta shiga ta hango Asiya zaune yayin da Aisha ke bacci

“Tun yaushe tazo ne Asiya?

“Bayan la asar ne tazo nayi zaton ma tare suka zo da Sameer din shine ma na Kira waya

“Bai zo ba Amma bari na Kira wayar shi yanzu naji

Haj ta Soma Kiran wayar Sameer ya Kuma dauka Yana sallama Haj ta Amsa tana fadin

“Aisha tazo tafiyar da Babu Shiri Kuma Bata ce komai ba ga Kuma ciwo a cikin ta ta Yaya Hakan ta faru? Kuma ka barta ta taho ita kad’ai ko kuwa tare kuka zo?

“Ba tare muka taho ba Haj ni Ina pertercout

“Amma ka San da tafiyar tata?

“Na Sani Haj Amma ku tambaye ta ta San komai Haj in Kuma Bata fada ba munafunci ne don ba zata tab’a fada muku ba

“In ita ba zata iya fada ba kaima da na Kira ka na Zubar da girma na tunda bamu samu matsayi ko Kimar da zaka fada Mana ta taho ba?

“Haj kiyi Hak’uri Amma ba zan iya fadar Abinda yarinyar Nan tayi mini ba sai ta fada da Bakin ta ku tambaye ta zata fad’a

Aisha da ta farka taji Haj na waya ta Zubawa Bakin Haj ido tana Jin abinda Ake magana sai kawai ta Soma fidda kwalla tana nadamar Abinda tayi yayin da Wani sashi Kuma na zuciyar ta baya nadamar Abinda tayi

Haj da Anty Asiya suka Zubawa juna ido cike da Mamaki da alhini

Anty Asiya ce ta dubi Aisha tana Fadin

“Ke kar fa ku mayar da mu wasu Kayan banza ke da kika zo hannu kece wacce Zatayi bayani meye Dalilin wannan Ciwon na cikin ki Kuma me ya faru tsakanin ku da kika kasa fada? Kece kuwa munafukar matukar dai kika bayar da Dalili to karya kuke Wallahi Babu shegen da zai haddasa Mana husuma tsakanin mu da Yar Uwa ta Wallahi sai kin fada Mana Abinda ya faru

Aisha ta Soma kuka tana Fadin

“Ni fa ban San Abinda nayi mishi ba sai Gani nayi ya dauko bindiga Yana Shirin Kashe ni shine na gudu shi Kuma ya harbe ni a ciki Allah ma ya taimake ni na gudu da yanzu sai dai ayi maganar gawa ta

“Karya kike Wallahi kin boye gaskiyar magana babu Abinda akeyi Babu Dalili Kuma munafuncin daga gareki za a same shi da kin shirya gaskiya da kin Fadi gaskiya Amma tunda Baki Shirya gaskiya ba ba zaki iya fadar gaskiya

Cewar Anty Asiya

“A a Asiya kin manta Sameer ne da Bak’ar ZUCIYA? Ai dan Adam Yana kuskure a cikin Rashin sani wata Kil Hakan ne shi Kuma da yake mahaukaci ne

“Haba Yaya Amina bakiji tace Harbin ta yayi ba? Duk haukan Sameer Yana iya duka Amma baya harbi Amma ita ya harbe ta? Na fa San yarinyar Nan Sarai munafuka ce kina nan Kuma in kika ce Zaki goyi bayan ta Wallahi kunya kawai zata baki Kuma ALLAH ya kawo Sameer lafiya zakiji Abinda zai fada

“Ai ya zama Dole Gobe Goben Nan yazo na warware wannan JANHURUN

<< Tana Kasa Tana Dabo 52

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×