Skip to content
Part 55 of 55 in the Series Tana Kasa Tana Dabo by Hadiza Gidan Iko

Abdullahi ya shigo Yana Rungume da Sulaiman yayin da Salman Kuma yake biye a Bayan shi Saboda wata irin shak’uwa ce Mai tsanani a tsakanin su idan ya jima Bai dawo ba sun kama kuka kenan suna fadin daddy Zasu don haka a kowane sashi yake Salaman da Sulaiman suna like da shi don Shima Wani irin so yake musu Wanda har Basma ta Gane yaran sun Sha gaban nata Ya’yan Najwa da Nabeela duk da shi Uban Baya nunawa Amma Kuma tuni soyayyar yaran ta bayyana kowa ya Sani ba tare da ya furta ba.

Basma ta Dube shi Yana yiwa Sulaiman wasa a ciki Yana Dariya Shima Salman Yana cewa Daddy Nima kayi mini ..

Wani haushi ya kashe ta Daga Zaune don sai ya Raba Dare Yana wasa da su wani Lokacin har da su Najwa sai fa in sunyi bacci ne zai mayar dasu kafin ya dawo ya Bata nata lokacin don haka taji wata irin tsanar yaran nan a Ranta tamkar kuwa zata zuba musu fetur ta Kone su ..

Ta Dube shi a fusace suna ta Dariya shi da yaran .

“Wai Hakan da Ake mini ana mini Adalci? Uwar yaran Nan ce kishiya ta duk kissar ta da dauke hakkkin da take min Ina kawar da Kai duk ba a Gani ba sai an Kuma hada ni da yaran Nan Suma sun zama kishiyoyi na mun zama Hudu kenan? Ga Uwar su a gefe da muka Raba kwana da ita Suma wadan Nan a Ranar kwanan nawa ma sai sun shiga hakki na ?..

Ya Dube ta yadda ta kirne fuska tana kallon shi cike da masifa da son ta fashe..

Yayi murmushi Yana Fadin

“Yanzu yaran Nan ma sun tsone Miki ido Basma har kike furta kalaman Nan ? Gaskiya kin bani Mamaki idan har kika ce Abinda nakewa yaran Nan kike kallo har ya zama abin tsegumi . Me kike nufi to da Maganar Nan? Su Daina takowa nan ko kuwa na Daina kula su? In kince kin Raba mu a sashin nan alakar mu ta ni ne Uban su Kuma fa? To ki dai tsaya ga Uwar su wannan itace daidai da ke Amma su wadan Nan jini na ne ko Nisan tazara Muka samu da su Ina ji a jikina su ma haka bana son kowace irin magana ce in dai akan wannan Banzan Ra ayin naki ne . Ina Jin ma zanyi kokarin samawa Uwar su ko da jirgin yawo ne su tafi Saudi don ba zan iya jure Rashin su har a gama Aikin hajjin nan ba Kwana Daya ma idan bangan su ba Ina Wahala to zan San yadda za ayi ko a jirgin yawo ne Uwar ta taho min tare da su.

“Kace Balaki kake Shirin tayawa da kud’in ka Abdullahi. Wai kana nufin itama Faridar tayi Aikin Hajj tare da yaran Nan Amma ni Ina gida Gani ga Najwa da Nabeela Muna gida Kai Kuma Kuna Saudi da Ya’yan so? Kai Wallahi karya ne in ma MAFARKI kake to ka farka don Wallahi ka Kira tashin hankali a gidan Nan. Ina cikin Gidan ku fice Zuwa Saudi har wadan yaran da suka zo a jiya sune da tafiya Saudi Amma ga Najwa da Nabeela ko Dubai Basu je ba Amma Saboda Rashin Adalci ka tsallake su don kawai kana son nuna min su Mata ne ba son su kake ba sai wadan Nan da suke Maza? To don Allah ayi Hakan ba Gani .

Basma tayi ta Zubar da Ruwan tijara tana masifa shi Kuma Yayi Shiru Yana kallon ta da sauraren ta inda Kuma yaji kaimin biyan kudin jirgin yawon da zai kwashi su Salman da Sulaiman tare da Farida don yaga kokarin da Basma zatayi akan wannan JANHURUN da take mishi duk da ya fahimci akwai Rashin Adalci a cikin Abinda yake kokarin yi Amma don ya nuna Mata shine jagora Kuma Wanda ba a Isa a Saka shi ko a Hana shi ba.

Ya Mike Yana Rungume da Sulaiman Yana mishi Salman kuma ya Mike ya bi bayan shi Suka fice daga sashin Basma wacce har yanzu batayi shiru da d’umace d’umacen da take ba

Ya shiga sashin Farida wacce take Shirin kwanciya ya Mika Mata Sulaiman tana fad’in

“Yau baya Jin bacci ni Kuma gashi bacci nake ji Wallahi zai Bata min lokaci..

“Zan nemi ko da jirgin yawo ne ku taho ke da su don Ina Jin ba zan iya jure har a gama Aikin hajjin nan ba tare da Naga yaran Nan ba ..

“Mu taho mu duka har da Basma da su Najwa ko kuwa ni da Sulaiman da Salman?..

“Banda Basma da su Najwa su sai azumi sai su tafi Umrah.

“Bakayi Adalci ba derling gaskiya. In dai haka ne gaskiya sai dai su Basma su fara binka in yaso ni na tafi Umrah..

“Ba zan tsara yadda nake so a gida na bane Farida sai an tsara min Kuma kema kibi bayan Hakan? Ya fada a fusace ..

“Zaka tsara Mana Amma idan kayi Adalci. Ni Kam zan fada Maka gaskiya Kuma ba zan yarda na shiga hakkin matar ka ba tunda Nima ba zan yarda ta shiga nawa ba. In kace hakan da ka fad’a ai Kai kanka ka San Babu Adalci a ciki. Ta Yaya ma ni da nazo daga baya na Yi Abinda Basma batayi ba? Ta Nan sai dai idan Wata husuma ta fito gaskiya derling Kai ka hada ta Kuma Kai zaka kawo Rashin zama lafiya a cikin Gidan ka sannan Kuma ka jawa yaran Nan Bak’in jini a wurin yan Uwan su Kuma bana so sunan ka ya Baci wurin matar ka har ta Rik’a ganin Ina yin Wani Abu Wanda yake tauye Mata hakki. Idan har dai Adalci zakayi sai ka fara tafiya da ita ko Kuma ka tafi damu gaba Daya. Itace ya kamata ace tana farawa kafin ni ba Wai ni da nazo a baya ba Kuma a matsayin ta na Babba sai ace k’arami ne zaiyiwa Babba overtaken? Ai ko ni ba zan so Hakan ba..

“Kenan Baki yarda da Abinda na fad’a ba?

“Na yarda Mana Amma kar kayi Abinda zai zama zalunci don Allah kayi Abinda matar ka zata yarda Kai adali ne Salman da Sulaiman ko kana can zaku iya magana kuma ka gansu in kace zaka fiddo son da kake musu a Fili to Wallahi matsala kawai zaka ja musu ka Kuma jawowa kanka don Allah ayi Hak’uri da tafiyar nan ko Kuma ka hada mu duka har da Basma da su Najwa din sai mu taho Kawai.

“To shikenan tunda kema kin fara takewa Basma baya in fada ki karyata ni in ke ban Isa nayi iko da ke ba ai na Isa nayi iko da Ya’ya na zan nemi Yaya lami ta daukar min su tazo min Dasu..

“To gara Hakan Kam Yaya lamin sai ta zo Maka da su Amma ko ita Yaya lamin ai ta San Gaskiya ko ita ma din sai na fada Mata ta hada da su Najwa su tafi tare..

Ya juya ya fice a fusace Yana Jin haushin Abinda Farida tayi mishi..

Basma taga ya shigo a fusace ta Dora da fadin

“Allah dai Yana Gani Idan ma ana satar kwana na ana bawa matar Nan Ranar Alkiyama dai mutum da b’arin jiki zai tashi a shanye ..

Bai tanka Mata ba ya wuce toilet yayi Wanda ya Fito ya kwanta

Sati Biyu ya Rage a maniyyata Aikin Hajj su fara tashi na garin katsina inda me gemu yake ta fafutukar Neman jirgin yawo Wanda zai tafi mishi da yayar shi lami da Kuma Salman da Sulaiman ba don komai ba sai don ya debe kewar su ta tsawon Lokacin da zai dauka a Saudi

Yaya lami da ta iso gidan Saboda Kiran da kanin nata yayi Mata akan tafiyar don ya gama musu komai ya kums biya kudin komai.

Yaya lamin ta fara shiga sashin Basma wacce ta karbe ta da mutunci tana kawo Mata Ruwa da lemu suka gaisa Abdullahi ya fito da yake Nan yake

“Au Ashe kana Nan baka fita ba?

Ya zauna suna Gaisawa yake fada Mata ya gama Mata komai itama zata tafi Saudi ne tare da salman da Sulaiman Suma don Yana son ya debe kewar su adadin kwanakin da zasuyi su Duka zasu takura..

Yaya lami ta kame Baki tana Fadin

“Kai Abdullahi in ba son b’arnatar da kudi ba wadan Nan yaran suje Saudi suyi me Saboda Allah? Gaskiya bakayi tunani ba Kuma Yanzu haka akeyi su dangin nasu Kuma fa? Ai su ya kamata ma ace ka biyawa ba Yan Yara irin Salman da Sulaiman ba..

Basma ta Soma kuka tana Fadin

“Gara dai ki fada mishi Yaya lami . Ni ban San a me yake kallon su Najwa ba don kawai suna Mata yake nuna mini shi fa Ya’ya Maza sune masu muhimanci a wurin shi komai ya Rakito sai yace Salman da Sulaiman tun Ina kawaici har na fada mishi Amma ya Rufe ni da masifa Yana min Gori to na barshi da fitar Rana da faduwar ta gashi ga Allah Nan..

Yaya lami ta ce

“Ba haka akeyi ba Abdullahi shi fa Mai gida Dole sai Yana Adalci gaskiya ni bana son Rashin Adalci..

“Ai kuwa ina ganin Rashin Adalci a gidan Nan Yaya lami tunda ya Auro matar Nan yake ta nuna min komai nayi ban iya ba itace ta iya Komai bare Kuma da ta Haifa mishi Mazan nan sai ya zama kishiyoyi na sun zama uku ga Uwar su Suma yaran gasu ta ko Ina dai Bak’in ciki nake hadiya sai kawai gashi wai zasu tafi da Farida da Ya’yan ta Saudi Amma ni Bai tuna da Ina da nawa hakkin ba to na yafe Yaya lami su tafi in da akwai gaba da Saudi Arabia ma sai sun dawo in ma sun tafi su dauwama a can .

“A a ba za ayi haka ba sai dai a San yadda za ayi..

“Nifa haka na tsara Yaya lami Kuma haka zanyi tunda su a matsayin su na Mata na ban Isa nace ga yadda za ayi suyi ba ai Suma karya ne wata tace min ga yadda take so ayi. Ita Basma sau nawa Ina biya Mata Umrah? Har makka dai taje sai ace sai yadda take so Zanyi ni ban Isa nace ga yadda nake so ayi ba?

Yaya lami tayi Shiru kafin tace

“Eh to haka ne kuma ke Basma kiyi Hak’uri tunda kinje itama Farida sai taje in yaso gaba in zai iya sai ya biya muku ku tafi tare..

“To Yaya lami ai ni kadai naje ita Kuma harfa da yaran ya biya anyi mini Adalci kenan? To suje ma na yafe Allah ya tsare hanya ni ko ya biya min ma Bana so Wallahi.

“Bama zan biya ba Yaya lami da ke nake so ayi tafiyar don ko ita Faridar ba zataje ba tunda nace ta shirya a tafi da ita tace min sai dai na Fara biyawa Basma tana son nuna min tafini sanin daidai to ko ita din na soke tafiya da ita daga ke sai Salman da Sulaiman..

Yaya lami ta Soma bashi magana Amma yace ya Rufe babin su Wallahi tunda su Duka Babu wacce ya Isa yace tayi tayi..

A haka ayiwa Yaya lami shiri ita da Salaman da Sulaiman Wanda Abdullahi sune zasu fara Isa kafin su Yaya lami su biyo jirgin yawo.

A Ranar da zai tafi Yana sashin Basma wacce ya kawo kajin da Zatayi mishi dambun Naman kaza Wanda zai tafi da shi ta Kuma daka mishi yaji . Amma Kuma Abinda yazo zuciyar Basma shine ta Saka mishi guba a cikin dambun Naman ta Wanda har s cikin yajin sai da ta Zuba don a gaskiya Abdullahi ya fita a Ranta tunda yayiwa Salman da Sulaiman wannan tafiyar Amma ga Najwa da Nabeela Basu samu wannan tagomashin ba. Kuma bayan hakan ma tana son kawo karshen shegun yaran Nan da Uwar su . Hakan Kuma ba zata tab’a Samuwa ba sai bayan Babu Abdullahi don Haka Basma ta zagaye kayan Abdullahi da Dukkan gubar ta wacce ta tabbatar da ba zai tab’a tsallake Daya Daga cikin kayan tafiyar da ta zagaye da gubar ba .

Karfe Hudu na yamma zasu tashi don haka tun kafin uku ya gama shirin shi inda garba Abubakar Wanda zasu tafi tare ya iso a motar shi inda shi Kuma Abdullahi yake Rungume da Najwa da Nabeela suna bankwana Yana musu alkawarin shekara Mai Zuwa tare da su zai tafi suna ta mishi ADDU A inda Basma take kallon su fuskar ta murtuk tamkar hadarin gabas.

Ya gama sallama da su Najwa ya Dubi Basma wacce ta hade Rai Yana fad’in

“To Uwar gida mu zamu tafi sai Allah ya kaddara saduwar mu a yafe Mana ..

“Allah dai ya yafe Mana

Ta fada Bata kalle shi ba ta juyar da kanta gefe ya shafa fuskar ta ya Mike don ya kula da irin sallamar da yake so suyi ya fice sashin Farida Salaman da Sulaiman suna jikin shi Yana sumbatar su inda Farida Kuma take kallon su har ya dire su Yana kallon ta Yana Fadin

“Derling mu fa mun Daura niyar tafiya Muna bukatar ADDU A sai Allah ya sake sadamu .

Suna Rungume da juna tana mishi ADDU AR samun Rabon DUNIYA da LAHIRA da Kuma yin Aiki karbabbe Kuma makabuli..

Sun jima kafin ya fito Farida ta biyo bayan shi tana Fadin

“Haba dai duk yawan mu a gidan Nan derling ace Babu wacce Zatayi maka Rakiya? Gaskiya ni zan Kai ka har naga tashin ku ..

Ta dauko key din motar ta ta fito Salman da Sulaiman suna biye da ita har mota inda Basma ta Saka su Najwa da Nabeela suka fiddo kayan Abdullahi suka zube a bakin kofar ta inda garba Abubakar yake jiran shi sai Ganin Farida yayi ta fito suna like da juna inda suka gaisa tace sai dai yayi dakon kayan Abdullahi Amma ita zata Kai shi da kanta har ta ga tashin sa..

Yayi Dariya Yana Fadin

“Wato ma dan dako na zama? To na Gode..

Ya Dubi Abdullahi Yana Fadin

“Wai Amarya ita kadai Zatayi Rakiya banda Uwar gida? Kai bari na Kira ta taxo ayi Rakiyar Nan da ita ..

Ya shiga sashin Basma ya fada Mata Banda a Rakiya? Ta fito tana Ganin Farida a mota ita da Abdullahi da yara tayi Wani Banzan murmushi tana Fadin..

“To Kai garba ai ba a gayyace ni ba ni Kuma banayin Abinda ba zanyi kwarjini ba Allah ya tsare Muna ADDU A.

Ta fada tana mele Baki kamar wacce akayiwa Dole..

Garba Abubakar ya shiga motar Yana Fadin

“Dan daure ki zo muje Mana a Raka shi ..

“Ba zanje ba garba ku sauka da Nauyi wai Dan daudu yaga Mai kayan gwaiwa..

Ta juya ta koma sashin ta inda Najwa da Nabeela suka shiga motar Farida tare da Daddyn su aka nufi Filin jirgin Wanda Babu wata tsaya wa aka Soma Kiran suna har aka zo kan Abdullahi Wanda yake Rungume da yaran duka dole ya barsu ya tafi Yana daga musu Hannu inda Sulaiman kuwa ya Soma kuka shi sai ya bishi. Ganin kukan Sulaiman Shima Salman ya kama Kiran Daddy Yana kuka duk suka Ruda Farida wacce take ta faman Rarrashi Amma Basu yarda sunyi shiru ba sai da suka ga dagawar jirgin su Abdullahi ta tashi motar Zuwa gida inda Kuma Basma ta nemi Najwa da Nabeela ta gane sun bi motar Farida zuwa Rakiya Abinda Kuma ya Kara fusata ta Soma tsumayin zuwan su . In Banda yaro da Bai San komai ba meye Nasu na zuwa inda ba a bukatar su?..

Ta Soma safa da marwa tsakanin kofar ta da farfajiyar Gidan har ta Ji shigowar motar Farida ta kuma ga fitowar Nabeela dauke da Sulaiman ai kuwa cikin Wani irin matsiyacin fushi ta damko Nabeela tana auna Mata Ashar marar tsarki.

“Shegiya shaidaniya har kece da daukar wancan shegen yaron ? Ban Hana ku kula su ba shine saboda samun wuri kike damukar shi har da shiga motar Uwar sa? Ta Soma jibgar yarinyar tamkar wacce ta kar zomon.

Farida ta Isa gare ta tana fadin

“Ba akan yarinyar Nan Zaki huce ba Basma Ina ganin ba laifin ta bane..

“Ke dakata da Allah malama Uban wa ya Sako ki a cikin Abinda ya Shafe ni ni da diyata? Kar ki Kuma shiga SHIGA harka ta bare ki bawa Ya’ya na shegun yaran ki suna damuka in kuma kika ce ba haka ba Wallahi Nayi nufin wulakanta ki irin wulakancin da Baki tab’a zato ba Wallahi don na gama bacci da ido Biyu so zo ki shige ki saurari zuwa na ..

Farida tayi murmushi tana Fadin

“Wulakancin kawai Zaki iya Basma Kuma in kin iya wulakanci to Akwai Abinda Baki iya ba Ina jiran koman ki.

<< Tana Kasa Tana Dabo 54

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×