Tun a mota Sameer yake jaraba Kiran wayar wasila Amma har yanzu baiji wayar ta shiga ba sai ma shegiyar matar Nan Mai kaifin muryar tsiya da take ta fada mishi wannan layin a kashe take sai dai ya sake Kira Lokaci na gaba.
Haka ya iso majalisar tasu inda ya iske duk mutanen su sun hallara motoci ne fal a wurin na mate din su Wanda Suke cikin garin katsina wanda Ake haduwa ayi fira a Sha shayi na Yar buta kasancewar kowanen su Yana da Aikin Yi Mai kwari . Kuma Masu budewar ido akan Rayuwa musamman ga mata. . .