Labuda ta iso Gidan yayar tata wacce tace tazo tana son Ganin ta yanzu .
Basma ta fito da takardar manubar da take Shirin Yi ta Rattaba Hannun shaidu ta na nunawa Labuda.
“Kinga wannan takardar?
Basma ta fada tana Duban Labuda wacce ta zuba Mata ido tana sauraren Abinda zata ce.
“Ranar Sha takwas ga wata zamu koma kotu Ina so idan munje kice kina daga Cikin shaidun da Abdullahi ya bawa su Najwa gidan shi don an Soma zalunta ta ana bawa shegun Ya’yan Farida kudin jirgin da Abdullahi ya biya musu wai tunda kyauta ce sun ci kyautar su shine Nima na kulla nawa Makircin Nace ya bawa su Najwa gidan shi duka shine akace na kawo shaidu to na Saka da sunan ki da na lawisa da jafaru don haka ki Zamo cikin shiri in munje kotu kice kina shaida .
“Haba Yaya Basma meye na wannan Abun Saboda Allah? Don Allah kiyi Hak’uri ki kawar da kanki akan komai gado fa Toka ne Mai shi ma ya bar shi bare Wanda aka Bawa? Ni Banga abin jawowa Kai wannan JANHURUN masifar ba har kina hada wasu shaidun zurrrr.
“Ke kar ki kawo min maganar banza kinji ko? In ba Zakiyi ba kice min ba Zakiyi ba sai na sauya da batula tunda kin zama matsiyaciyar da Bata son kowa ya Samu bare ita ta Samu. An fada Miki a kyauta Zakiyi min hakan ne ? Biyan ki Zanyi bance kiyi min Alfarma ba .
“Gaskiya to ki Saka batular ni Kam ba zanyi shaidar Abinda ban Gani ba ban Kuma San anyi ba don Ranar Alkiyama zai zamo min JANHURU .
“Tashi ki tafi don Uban ki tun Baki sa na b’are Miki Kai ba.
Da sauri Labuda ta Mike tana Fadin.
“Amma kiyi Hak’uri Yaya Basma wannan Rayuwar Mai Hankalin cikin ta ne kawai yake iya tuna yau da gobe da Kuma sauyin da take kamar yadda ta sauyawa Mai gidan Nan yau Babu shi kema da kin tuna inda ya tafi kema Zaki je yanzu ko anjima da Baki Wahalar da kanki akan Abinda ya bari ba Rahamar Allah tana da yawa ba Lallai a gado Rabon yake ba .
A fusace ta biyo bayan Labuda wacce ta auna Aguje ta fice daga gidan.
Ta jawo wayar ta a fusace tana Kiran wayar lawisa wacce ta dauka tana Fadin.
“Yanzu nake Shirin Zuwa kika kira Gani Nan Zuwa bani minti Sha Biyar.
“Yauwa kamar kin San dama Ina bukatar ki lawisa sai kinzo din.
Ba a Rufe minti Sha Biyar din da lawisa ta Kira ba ta iso bayan sun Gaisa ne Basma ta Karantawa lawisa Abinda akayi mata na bawa Salman da Sulaiman kudin da Abdullahi ya biya musu da Kuma Yaya lami wacce itama akace kyauta ce Kuma Dole a Bata basa daga cikin kayan gado shine fa suka je har Gaban alkali Shima ya tabbatar da Hakan shine itama tace ai Abdullahi ya bawa su Najwa gidan shi shine akace ta kawo takardar shaida da Kuma shaidu shine ta bayar da sunan ta.
“Ni ?
Lawisa ta fada tana Duban Basma.
“Haba ta Yaya Zaki saka ni cikin wannan manubar Basma? Ban fa San anyi Hakan ba kema son ZUCIYA kika Saka da kin Hak’ura kin barwa Allah da yafi.
“Biyan ki zanyi lawisa ni Baki ga Abinda akayi min ba akace kyauta ce Bata cikin kayan gado? To Suma kyauta ce ya Basu Kuma Dole a Basu tunda an bawa wadan can shegun ma.
“Au to to Babu damuwa yaushe ne za a koma kotun? Ai na dauka haka taka Haye ne Amma tunda biya Zakiyi ai ko wasu ma kika ce na kawo suyi shaidar ai zan kawo su.
“Yauwa Basma ki samo min mace guda wacce zata maye gurbin Labuda wacce ta watsa ni tana fadin ba zatayi ba .
“Amma kuwa ba ta kyauta ba labuda Halan baki fada Mata Wani Abu zata samu ba? .
“Kamar Labuda ma don Zata Yi min wannan Aikin sai na biya ta lawisa ? Banda dai yau din da komai ya zama a BARWA RAI kema Banda kinji Wani Abu ne zai shigo ai da kina Nan kina min zayyana wata Kil ma fiye da Labuda.
“Ke kar ki Wani Damu kin San yadda abubuwan suke Dan abin Rage zafi ne k’arfin.
A Ranar kuwa lawisa ta samo wata Mata Mai suna ladi Amma an fada Mata sunan da zata fada a kotu idan an tambaye ta sunan wato labuda Kuma tace tana shaidar kyautar da Abdullahi yayiwa su Najwa Idan tayi Hakan zata samu kyautar Dubu Biyar.
Jafaru ma da ta Kira wayar shi Bata same shi ba tuni aka sama Wani Wanda zai hau sunan nashi .
Ranar da aka koma kotu Basma ta gabatar da takardar bogin ta ga alkali Wanda ya karba ya duba kwanan wata ya Kuma bukaci ganin shaidun ta inda lawisa ta fara fitowa ta gabatar da kanta da Kuma Rubutun Da akayi na takardar shaida har da Saka Hannun ta.
Aka bukaci ganin jafaru na bogi Wanda ya bayar da shaidar yayi gadi a gidan ne Kuma Shima Yana daga Cikin shaidun.
Shaida ta karshe itace labuda matar Nan Kam Bata taba Zuwa kotu ba don Haka a Rikice take matuka Gaya itama dai ta Bada tata shaidar har aka gama inda alkalin ya Dubi lauyan Basma Yana Fadin
“An gabatar da takarda kumw shaidu sun amsa sai dai ta Yaya akayi wannan kyautar Babu Ahalin Mai kyauta Babu Ahalin Wanda akayiwa? Kuma a nan ga Saka Hannun masu shaida Ina so su sake Saka min Hannun su a wannan takardar Don na hada Wanda Sukayi Yanzu da Wanda Sukayi a baya.
Alkalin ya Bada takarda da biro inda jikin shaidun zurrrr ya dauki Rawa. Amma lawisa da jafaru Suka Rattaba duk da Bai zo Daya ba Amma Labudar bogi Kam cewa tayi .
“Allah ya baka nasara ni Kam zan Fadi gaskiya cewa akayi nazo Nayi shaidar zurrrr a bani Dubu Biyar to ban iya Gane wacece zurr din ba wacece Kuma Ake son nayi? Ni dai an karanta min yadda zan fada Kuma sunana na Gaskiya ladi ba Labuda ba.
Kotun ta dauki Dariya hatta da shi alkalin sai da yayi Dariya yace
“To madalla ladi ai kinci kud’in ki tunda dai kinyi Abinda aka Saka ki Kuma tun a Saka Hannun na Suka yada kari don kowanen su yayi daban da Wanda yake jikin takardar don haka ke malama ladi Zaki iya tafiya Gida kotu ta sallame ki Amma sun biya ki Dubu Biyar din ki? .
Tayi Maza tace
“An biya ni ALLAH ya gafarta malam.
“To jeki kotu ta sallame ki su Kuma jafaru da lawisa kotu zata Rik’e su har sai tayi bincike akan su ta Gano gaskiya akan Abinda suka fad’a matukar kotu ta kama su da zambar marayun Allan to Hukuncin su zai biyo bayan Zaman Nan .
Jafarun bogi ya Mike Yana Fadin
“Allah ya gafartarwa malam Nima zan Fadi gaskiya Wallahi Nima biya na akayi Wallahi ban San komai a Kai ba wannan azzalumar ta gayyato ni ya fada Yana nuna lawisa wacce tuni idon ta ya Raina fata don itama Kam tuni tayi nadamar Abinda tayi.
“Ka makara malam jafaru Domin kuwa sai da Asirin ka ya tonu ne kake fadar gaskiya don haka ba za a ja wani zance ba Hakan ya nuna Mai Kara ta shirya Wani zalunci ne tunda ta gayyato mutanen da Basu da alaka da Wanda ta kawo Hakan ya nuna zalunci take son Yi da dukiyar marayu don haka idan wakilan su Duka sun iso a hakarto da lissafin dukiyar marayu ayi musu Rabon gadon su.
Baba isuhu Wanda yake cike da Mamaki shi da garba da Kuma Gali yayan Farida Wanda yazo a matsayin wakilin ta suka fito ana gabatar da komai na dukiyar marigayi Abdullahi.
Farida na Zaune aka Soma da Kasa dukkan Dukiyar takwas aka fiddawa matan Aure kaso daya bisa bakwai a matsayin tumunin takaba yayin da kaso bakwai Kuma ya zama Salman da Sulaiman ne suke kaso Hudu da Rabi yayin da su Najwa Kuma Suke da kaso Biyu da Rabi.
Abinda ya tabbatar wa Basma cewa gidajen Nan duka sashi uku su Salman ne Suka cinye su inda Kuma Basma ta Mike tana Fadin.
“Ban yarda da wannan kason ba ya Mai Shari a Wallahi ban yarda da shi ba Domin kuwa wadan Nan Ya’yan ba na Abdullahi bane Ina da shaidar Hakan Kuma Idan kotu Bata yarda da magana ta ba Ina so ayi gwajin jini ta haka ne za a Gane Dukkan Ya’yan Farida ba na Abdullahi bane na tsohon mijin ta ne da take gayyatowa gidan ta .
Yaya lami ta Mike tana Fadin
“Ya Mai Shari a ni Kam ina nemawa Ya’yan Dan Uwa na da take shegen tawa hakkin su don na tabbata Abdullahi idan Yana Raye take wa yaran Nan wannan wulakancin ba zai yarda ba to ni ma Kuwa ba zan yarda ba don Babu Rayuwar shi ba zan tab’a b’ari a wulakanta su ba Wallahi Ina Neman hakkin su a bi mini KADI.
Alkalin ya Dubi Yaya lami Yana Fadin
“Kina iya shigar da Kara idan mun kammala wannan Shari ar don yanzu cikin Shari a muke.
Baba isuhu ya Mike Yana Fadin
“Allah ya gafarta malam tunda har kotu ta Gane wanna yarinyar da irin yadda take son ta karbi hakkin wasu ya zama nata mu dai mun gamsu da wannan kason don Haka yazo a cikin Aya a Kuma Yi wa Yaran Nan tsakani don ta tab’a bawa yaron abokiyar zaman ta guba da son ta kashe shi to yanzu Idan taji anyi haka Komai zai iya faruwa to gara ayi musu tsakani tunda ta nuna Rashin yardar ta komai zai iya faruwa.
“Mai Kara tana da ikon daukaka Kara zuwa kotun gaba idan har Bata gamsu da anyi Mata Adalci ba Amma Kuma ya zama Dole ta biya yaran nan da take batawa suna Tarar Bata musu suna haka Kuma zata biya kotu tarar yin wasa da hankalin ta wurin yaudarar kotu da ta kawo Mata shaidan Karya sannan su wadan da suka zo bayar da shaidar zurr zasu biya Tarar Dubu Sha Biyar ko Kuma zaman gidan sarka na wata UKU ita Kuma Mai Kara zata biya Yara kudin Bata suna Dubu d’ari Biyu da Hamsin ga kowane yaro Daya Dukkan su Kuma Dubu d’ari biyar sai Kuma Tarar kotu Dubu Hamsin ko Kuma zaman gidan sarka na shekara UKU Mai Tara Yana da zabi ta biyan Tara ko kumw zaman sarkar.
Basma tace Bata da zabi Dole ta biya Tara inda Kuma aka wuce da lawisa da jafarun bogi zuwa Gidan sarka In sun biya Tara Nan da sati a sake su In Kuma Babu kud’in Tara suyi zaman sarka kawai Amma Kuma lawisa cike take da Mamakin Basma da Bata biya Tarar ta ba ta barta a wakafi.
Basma Kam Bata yarda da wannan Hukuncin ba Dole ta daukaka Kara tun a Ranar don taga ana Shirin fidda ta gidan Abdullahi da sunan Salman da Sulaiman ne Suka ci gadon su? Wallahi ba zata Sabu ba Wai bindiga a Ruwa.
Farida kam kuka take sai a yau ne tayi nadamar hada Miji da Basma yayin da baba isuhu da Yaya lami suke Bata Baki Akan tayi hak’uri ta Daina kuka duk inda basma zataje yawo zataje Kuma sun shirya Binta da dukkan Abinda take nufi Abinda Bata so ma dai shine zai faru.
Gali da su garba da Kabir Suma Mamakin suke Amma dai sun san karshen MAKIRCI nadama.
A Ranar Kam Farida tayi kuka har kanta yayi Ciwo ta kumayi kaicon Sanin Sameer a Rayuwar ta Wanda Abinda yayi mata sai dai Allah ya Saka mata . Gashi ana mata barazana da shegen ta Mata Ya’ya akan zaluncin da yayi Mata.
Tun a wannan Rana zazzabi ya Rufe Farida Wanda ta tabbatar na damuwa ne da Bak’in ciki .
Kwananta UKU a kwance inda Yaya lami tazo duba su Dama duk bayan kwanaki UKU ko biyar take Zuwa duba su inda ta iske Farida a kwance Babu lafiya duk ta Rame .
“Subuhanallahi Farida kar dai kin Saka damuwa a Ranki?
Ta tashi Zaune suna gaisawa da Yaya lami tana Fadin
“Ban Saka damuwa ba Yaya lami ai na San Basma Bata Isa tayi Abinda Bai zamo zanen kaddara ba. Kawai dai na tashi da zazzabin ne .
“To ai Asibiti ya kamata mu tafi ba za a zauna da Ciwo gida ba.
Yaya lami ce ta dauke ta tare da Yaran suka nufi Asibiti inda aka Soma auna ta a gwada ta sai ga ciki ya bayyana har na sati Sha Biyu Yaya lami sau hawaye ya goce mata tana Fadin
“Ikon Allah yau ga Abdullahi baya Duniya Amma ga wata baiwa da Ubangiji yayi mishi Sannu farida Allah ya Raba lafiya Masha Allah Allah ta ala ya sa Abdullahi ne Zaki Haifa Mana kai wannan Duniya kuncin da yake cikin ta yayi yawa.
Farida kam sai ta SHIGA Mamaki har ta manta da batun Wani Bak’on wata da Bata Gani ba Amma sai ta tuna magagin mutuwar Abdullahi ne ya mantar da ita komai sai fa yanzu da taji bayyanar cikin sai Kuma ta hango Wani katon kalubale musamman basma taji Abinda take yiwa din ma Kuma Dole ta saurara Domin kuwa TANA K’ASA TANA DABO.
Da haka suka baro Asibiti Yaya lami sai murna take tana Fadin
“Allah Mai iko ni lami Ashe ZURIAr Abdullahi suna da sauran zuwa Duniya bayan shi Uban nasu ya jima a kiyama Allah ya albarkaci Abinda ya bari Farida Allah ya Raba ku lafiya yayiwa ZURIAr ki Albarka.
Haka suka dawo gida Yaya lami ta shiga wurin Basma suka gaisa inda Basma take fadawa Yaya lami sammaci na Nan Zuwa Ranar litinin don tuni ta shigar da Kara a wata kotun wacce Farida zata Yi bayani da yaren hausa don zata yaga Leda ko da biredi Bai Dadi ba.
“To Basma Muna jiran sammacin duk lokacin da alkali ya neme mu zai gan mu Amma da zan Baki shawara ki dauka sai nace ki canja su Najwa daga jinsin Mata ki mayar da su mazaje Ina ganin idan kikayi hakan Zakiyi nasarar Samun Abinda kike so Amma matukar dai suna a Matan su sunan su Kuma Bai sauya ba daga daga Najwa da Nabeela Zuwa Salman da Sulaiman ba to Akwai matsala don har gaban Abada k’asa kike in dai baki da Sulaiman da Salman sai Najwa da Nabeela to Biyu kadai kike dashi a cikin takwasa don yanzu ma TANA K’ASA TANA DABO Domin kuwa ga Farida can tana Laulayi kinga TANA K’ASA TANA DABO tunda Abinda zata Haifa Shima Dole ya karbi nashi kason ko da Kuwa mace Farida ta Haifa itace dai a Saman ki in kuma Ubangiji ya so nuna Miki ishara sai ya Kuma Bata namiji ya zamo kaso Tara ne Bata ke Kuma Daya to wa ya Isa Banda ALLAH?