Skip to content
Part 62 of 62 in the Series Tana Kasa Tana Dabo by Hadiza Gidan Iko

Wani irin matsiyacin Duka ne ya naushi zuciyar Basma Jin Abinda Yaya lami take fada Mata.

“Banji me kika ce ba Yaya lami? Don Allah maimaita mini sai Naji kamar kince ciki ga Farida? Wace Faridar? Wane irin ciki Kuma?.

“Ashe ma kinji Abinda na fad’a Basma kike son na sake Wahal da Baki na. Ciki Nace Miki Farida tana da shi yanzu muka Dawo daga Asibiti likita yace ciki ne na sati Sha Biyu Kinga an yanka ta tashi kenan TANA K’ASA TANA DABO.

“To in ciki ne da ita Yaya lami ke Kuma me kika ce? .

“Yo me zance Banda Allah ya inganta ya Kuma Raba lafiya?.

“Amma dai Kam Yaya lami anyi faduwar Bak’ar tasa Wallahi ke yanzu In banda an mayar da ke mahaukaciya ko wacce ta zama Sha ka tafi har kike b’are b’aren jikin SANARWA wai Farida na laulayi? To Naji tana Laulayi me take nufi da wannan munafuncin? Banda kudin da ta danne Wanda kema kika danne hakkin marayu shine yanzu take fadar ciki? Wai ma don Allah Yaya wane kalar tunani gareki ? Wai Cikin ma da Ake magana na waye take nufi? Na Abdullahi ne? Tabdijan Amma kuwa Yaya lami kinyi banza da kanki Wallahi in na Neman ki Akayi an same ki .

“Yo ke har sai kin tsaya batawa kanki Lokacin Neman ba asin ciki ko na waye? Na Abdullahi ne ko kuwa kina musun Hakan ? To in ma ke kina Yi ni bana musu tunda bana fatan jawowa Yar Wani JANHURUN masifa tunda ni ma na Haifa kema da Zaki yarda sai na tuna Miki Ya’ya Mata kika Haifa da kin Hak’ura kin karbi irin Rayuwar da Ubangiji ya nufe ki da Yi Babu Abinda bashi da karshe sai ikon Allah.

“Yanzu Duk abinda nake fada Bai zama matashiya ba Yaya lami? Ni fa da idona nake Ganin tsohon mijin matar Nan ya na shigowa k’arewa da karau ma bari na dauko Miki shaida ki Gani.

Ta Mike da sauri tana dauko hotunan Nan da ta dauka ta Kuma wanke ta kawowa Yaya lami tana Fadin.

“Yanzu wannan Bai Isa zama izna da Darasi ba? Yanzu dai ai gata ga tsohon mijin nata kingan su a fit haihuwar Uwar su Ina Kuma maganar ki Yaya lami? Shine yanzu Kuma Abdullahi Yana Neman wata uku a kushewa shine ya dawo yayi Mata cikin ko kuwa?.

Yaya lami tayi maza ta Runtse idanun ta saboda ganin da tayiwa hotunan Babu ko Kyan Gani musamman tsiraicin da ta Gani.

Tayi saurin mayarwa Basma hotunan tana Fadin.

“To ni me kike so na fahimta a cikin wannan hoton? In ma kina son ce min farida tana Kawo Maza ko tsohon mijin ta Basma ai ke yanzu Allah Daya kawai Zaki ce min na yarda tunda anyi walkiya ta haska ki. Wanda yayi hayar Yan shaidar zurr Kuma meye ba zai aikata ba? Kuma yanzu meye computer batayi ? Kana daga wata Uwa Duniya ma sai tayi Maka editing ta hada ka da Wanda kake ko ta Raba ka to meye Abin mamaki a wannan hotunan? Ai yadda kika nunawa yarinyar Nan tsana komai ma ni ya fito daga gareki to sharri ne Basma ko da Kuwa Zakiyi ta hadiyar alkur anai Wallahi Babu sauran Aminci a tsakanin mu da ke Kuma ko daga waje farida tayi Cikin Nan tace na Abdullahi mun yarda mun Amince tunda bamu taba samun ta da manuba ko ha inci ba in ma daga kushewar mijin ta yayi Mata cikin Duk anayi in ma Kuma yadda kike zaton ne duk mun dauka kema in kikayi Naki cikin a yanzu Wanda Bai Gaza kwanakin nata ba kema Muna maraba.

Cewar Yaya lami wacce take ficewa daga sashin Basma.

Basma ta Mike tana faman safa da marwa a falon ta kafin ta dauki gyalen ta ta fice Zuwa gidan baba isuhu.

Goggo Amu ta ganta kamar an Koro ta taja tsaki don yarinyar Nan ta gama fice Mata a Rai . Ko da wasa Bata tab’a zaton samun Basma a matsayin da take a yanzu ba.

“Baba kaji Abinda yake faruwa a yanzu kuwa?

Ya Dube ta Yana Fadin

“Koma me zai faru ai ba zai Wuce k’arar da Zaki shigar ba ko akwai wani Abu bayan Hakan?.

“Eh akwai baba Domin kuwa an yanka ta tashi.

Baba isuhu yayi Maza ya amshe da fad’in .

“To kaza ko akuya ne aka yanka ta tashi?.

“Yanzu Yaya lami take fada min wai ga Farida can tana Laulayi sunje Asibiti ance ciki ne har na sati Sha Biyu. Yanzu Baba ka yarda Farida sharholiyar ta takeyi tare da tsohon mijin ta? Ta Yaya miji ya mutu yau kusan wata uku Kuma don a Raina mutane ace wai ga ciki ya bullo? To bari na fada maka gaskiya baba ni da idona na kama Farida da tsohon mijin ta fit haihuwar Uwar su ga hotuna ma ka duba shiyasa nace Maka ban yarda da Ya’yan ta ba Kuma in yanzu za a kawo maka tsohon mijin nata da ka dubi Salman zaka San sun hada hanya shi kuwa Sulaiman farin Abdullahi kawai ya dauko Amma duka sammakal.

“To da wannan kika dogara?

Ya fada Yana watsa Mata hotunan a jikin ta saboda haushin da yaji na ganin tsiraicin.

“Yanzu ke in Banda Baki tsoron Allah ta Yaya kika samu hoton Nan ? Ko kuwa duk cikin ki kulla Mata munafuncine kika shirya Hakan ko kuwa a gaban ki sukayi Hakan ne? Na tabbatar da ba zasuyi Hakan a kan idon ki ba duk Rashin kunyar su Kuwa ba zasu yarda Kuma a dauke su hoto Hakan ba . Kinga ni zan iya Cewa ma kinyi Hakan ne don ki batawa yarinyar Nan suna Kuma mu a idon mu Bata da aibu Domin kuwa mun gama Sanin ko wacece ita ke dai da tsoron Allah ya zama akwai ya Babu wurin ki shine har kika Rik’e wannan ya zama hujja to Allah ya fiki Kuma in Farida tayi ciki a Yanzu kina nufin Shima shegen ne kamar yadda kika shegen ta Mata Ya’ya? To kije kiyi lissafin Cikin da aka fada ki Kuma lissafa kwanakin Abdullahi sai ki yanke Mata Hukunci tunda ke dai na lura Baki Je makaranta ba. Shine kika kwaso tab’ai tab’ai kina b’are b’are kinzo ki kawo sharri? .

“Wai baba a Cikin Hankalin ku kuke ne? Yaya lami ma ta kasa fahimta Kai ma ka Kasa fahimtar Wani Abu ga matar Nan na son sai ta Gaje komai na Abdullahi? To Baba tunda Kun ki ku fahimta dama ni koto ni zanje Wallahi Dole ne a gwada jinin yaran Nan Kuma wancan cikin sai dai ta San yadda Zatayi da abinta Amma maganar tace na Abdullahi ne karya ne Wallahi taci Uwar karya ta kwana da yunwa.

Ta Mike ta fice daga gidan tana sambatu.

Goggo Amu ta Rik’e Baki tana Fadin

“Uh uhum wannan Kam malam bana zaton tana da Hankali Wallahi tun Ranar da tace ta Saka mawaki ya rerawa Abdullahi wakar mutuwa nace Bata da Hankali ko da yake in ka Raina Mutane ma kana iya yin fiye da haka ita Kam duk gadon Nan ya sa ta zarewa.

“Iskancin dai shi yafi yawa amu tunda ta San ta kalawa kishiyar ta sharri ? Yanzu ma tazo ne tana Fadin wai Farida ce ke laulayi to kwana nawa da mutuwar Abdullahi? Ai takaba kawai zata fita ba a karbi Wani ciki daga Dukkan su ba tunda ita jahila ce da ka take yin Abu ai musulunci Bai bar komai ba . Ai yarinyar Nan tayi ba zata Wallahi .

“Ni fa malam Ina tsoron kar ta cutar da yarinyar Nan don tunda ta futo ta nuna maitar ta a fili Allah zata iya yin Komai.

“Allah ya fita amu Kuma idan Farida ta bar Mata Gidan ai ita burin ta ya cika Babu inda zata je sai ta haihu ta karbi kason gadon da ba a so ta karba tunda yanzu baya ta haihu Kuma ai Dole a jingine maganar Rabon gadon har sai an ga Abinda matar shi ta Haifa mace ko Namiji ta yadda Shima za a ware mishi nashi kason matanta ko mazantaka.

Basma ta Kira barrister ya zo har Gida ya same ta tana fada mishi Halin da Ake ciki yanzu.

“To gaskiya sai mun hada da kudi wurin Aikin Nan don gaskiya a yanzu Babu wani alkali da ba zai duba kudi ba duk da akwai Wanda Babu Ruwan su da kudin Amma dai a fara siye su tun daga waje kafin a Mika misu Al Amarin.

“Duk wannan Mai sauki ne shiyasa ma na neme ka wane alkali kake ganin zai yi accept din Al Amarin mu ?.

“Akwai su da yawa in kin bani WUKA da Nama Zaki ga Aiki. .

“Na baka har da Dukkan Kai da kafafun Dabbar da ta zama Naman ga wannan Dubu d’ari biyar ne a Bawa alkalin a kuma Rubuto Mana sammaci in yaso sai ka karanta mishi yadda Shari ar mu ta farko ta Kaya Ina son a Karbo min kudin da aka bawa Salman da Sulaiman da Yaya lami haka Kuma Ina so ace sai mun gwada jinin Ya’yan mu don kawo results ka dai san komai barrister ka Kuma san yadda zaka tsara Zancen a lauya shi .

Shima Yana jiran yaji tace mishi ga nashi income din Amma yaga ta maze Bata ce ko uffan ba sai ya tuna Mata don har waccan Wahalar da yayi Mata Dubu Hamsin din dauka kawai ta bashi dag ma su Bata Kuma duban shi da wani Abu ba don Haka ya tuna Mata Shima Yana bukatar na Shiga Amma tace ya bari sai an Kare komai zata sallame shi

Da haka suka Rabu Yana kulla Mata nashi makircin Wanda Bata sani ba ya fita iya Tasha idan Shari ar ta batayi nasara ba shikenan ba zata sallame shi ba zatayi ta Ganin ma shine baiyi kokarin komai ba don Haka sai kawai ya bi ta kan wadan Nan kud’in da ta bayar a kaiwa Alkali cin hanci ya dai yanko sammacin ya kawo Mata ta mikawa su Baba isuhu da Yaya lami

Hajiyar Farida kam ta so Farida ta dawo gida musamman yanzu da take cikin laulayin Nan duk da wannan karon Bata Wahala irin sauran Laulayin da tayi a haihuwar Salman da Sulaiman ba shiyasa baba isuhu yace Haj tayi hak’uri Farida ta Haihu a D’akin mijin ta in ta Haihu aka Raba musu gadon su sai ta komo gida har Allah ya fito mata da miji tayi Auren ta.

Ranar da aka shiga kotu Alkali ya nemi Mai Kara da Wanda Ake Kara wato Basma da su Baba isuhu da Yaya lami suka fito aka biya magana inda aka fara sauraren Mai kara da akan Abinda take kara na kwashe kudade daga cikin kayan gado aka baiwa Yaya lami da Ya’yan Farida.

Alkali ya Dubi su baba isuhu da Yaya lami Yana tambayar su Yaya akayi Hakan?.

Suka mayar da magana tun daga farko ta yadda aka biya kudin zuwa Rasuwar Abdullahi da ya biya kudin inda aka bawa wanda ya biyawa din .

Alkalin ya Dubi Basma Yana Fadin

“Haka akayi ?

Ta Amsa da haka ne.

“To in dai haka ne kyauta yayi Basu daga cikin kayan gado idan Kuma kika ce za a dawo Miki da su to daidai yake da kice dukkan wata kyauta ko sadaka da yayi sai an dawo Miki da su don haka ba zalunci bane hakkin su ne da ya Basu tunda ai inda Yana Raye ba Zaki ce kar yayi ba ko kuma Basu Isa su karba don Kar a tab’a kayan Mijin ki.

“To Amma Allah ya gafarta malam Nima ya tab’a yiwa Ya’ya na kyautar gidan da Muke ciki Amma akace ba a yarda ba.

“Me yasa lokacin da yayi kyautar Baki karba ba? Ai da tun a lokacin Zaki karba Amma in ya zama Babu shaida Kuma sai da ya mutu ne kika fito da wannan ko a kotu ba Zakiyi nasara ba tunda kinyi kuskuren barin Damar ki don Haka Wanda mijin ki yayiwa kyauta kyautar su ta bayu .

Lauyan Basma ya Mike Yana Neman a Raba musu gadon su da mijin su ya bari.

Baba isuhu ya mike yana Fad’in

“Allah ya gafarta malam su biyu ne Matan da mijin nasu ya bari ita Kuma gudar yanzu tana tare da juna Biyu ne .

Alkalin ya Dubi lauyan Basma Yana Fadin

“Babu Rabon gado ga matar da take da juna Biyu sai ta haihu ne za a Raba da Abinda ta Haifa don ba zai yuwu ba Dole masu hakki ko Kuma magada suyi Hak’uri har a haifi jinsin da zai San kason da zai dauka mazantaka ko matantaka .

Da wannan kotu ta tashi Abinda Kuma baiyi wa Basma Dadi ba har ta Soma tuhumar barrister kudin da aka kawowa alkali ya Kuma fada Mata ya amsa .

“Amma Kuma yake min son Ranshi? .

“Su fa Dama haka Suke mafi yawan su karbewa mutum kudi suke su kuma ajiye Shari a a inda suka so .

“Amma ai ba zai ci kudin Nan ya nutsar da ni a wofi ba in ba a kwado da yaro sai a bashi gayan shi.

“Ai sai dai hak’uri kawai Amma dai mu bar shi zuwa Lokacin da matar can zata Haihu ta haka ne zamu Gane inda ya Dosa.

Da haka suka Rabu Basma tana Kallon barrister Wanda Bata ji ta yarda da shi ba don Haka bayan sun Rabu da barrister ta nemi address din alkalin Wanda ya karbe ta da son yaji Abinda ya kawo ta inda ta Dora da fadin.

“Allah ya gafarta malam an turo Sako ko ya iso kuwa? Ya Dube ta da fushi a fuskar shi Yana Fadin.

“Wani ya ce Miki ki turo Sako ne? To bana karbar irin wannan Al Amarin don ba don shi nakeyi ba kar ki fara bana karba in ma kina son bacin Rai ne to sai ki turo.

“Ayi Hak’uri Allah ya gafarta malam dama ba wani Abu bane bamu San za ayi laifi ba tunda har an tura Amma ba za a sake ba.

“Babu Wanda ya bani Komai don an San bana karba ki dai je ki tuhumi Wanda kika bawa.

Ta Mike tana Fadin

“Nagode Allah ya gafarta malam a huta lafiya.

Ta Isa gida da Mamakin cutar Nan da barrister yayi Mata Dubu d’ari biyar Amma ya bi ta kansu? Kuma shine ya Rufe Mata Bai fada Mata gaskiya ba Yana nufin ya dafe kudin Nan kenan ?.

Ta iso gida tana tunanin ta inda zata fitowa barrister Amma ta tabbata ba zai ci kudin Nan siddan ba Wallahi tunda ya munafunce ta sai ya amayo su Wallahi.

Ta wuto Bak’on da yake ta Zaman jiran ta ba tare da ta kula da shi ba. Ta fito motar ta ta wuce ciki inda Najwa ta taho tana Fadin

“Mama Baki ga Wani mahaukaci a waje ba? Tun da kika fita yazo Yana Fadin ke yake Nema har Nabeela tana Kai mishi Abinci ya karbe Yana Fadin wai Ina Najwa Ina Nabeela? Shi har sunan mu ya sani Amma ni tsoro yake Bani Wallahi.

Basma ta dubi Najwa tana Fadin

“Mahaukaci kika ce Najwa? .

K’arar kwankwasa kofar tare da yage murya Yana Sallama.

Aguje Najwa ta koma bayan Basma tana Fad’in

“Wallahi Mama ga shi nan ya biyo mu Nan Wallahi tsoron shi nake.

Aka sake doka kofar da karfi tamkar za a jijjige ta Yana Fadin.

“In shigo ko kuwa na Jira a Nan ?.

Muryar shi ta so tunaww Basma Wani Mutum da Bata fatan Gani a yanzu Domin kuwa.

Ta fita da Sauri ta na Fadin

“Wai waye haka da yake Mana kwararato?.

“Nine Nan a bari na shigo Mana sai a ga kowaye Mana?.

A Rikice Basma ta tabbatar wa kanta Wanda Bata son Ganin ne yake Shirin bayyana . Ilai kuwa tana fita bakin sashin Nata taja tayi turus tamkar wacce tayi Gamo da damisa a dokar daji.

<< Tana Kasa Tana Dabo 61

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×