Skip to content
Part 66 of 66 in the Series Tana Kasa Tana Dabo by Hadiza Gidan Iko

“Kamar yadda gwajin DNA din ya Nuna a takardar sakamakon Ina fatan kowa ya gamsu da Abinda takardar kowane yaro ta bayar da kalar jinin sa duk da Gaba Daya yaran jinin nasu ya Kasu Kashi Kashi .

Gwajin jini na ciwo daban yake da gwajin gane alaka irin ta kusanci wato DNA . Amma dai ga gwajin kowanen su.

“Ai likita kar ka rufawa kowa Asiri ai dama sai da na fad’a aka karyata ni gashi tun ba a bayyana ba Anji cewar jini ya banbanta to aci gaba da gashin kawai Muna Jin ka likita kar ka Rufe komai ka fad’a shiyasa aka Tara kowa da Ahalin sa.

Cewar Basma wacce take mayar da wannan Zancen .

“To wannan takardar ta yaron farko ce wacce aka fara gwada jinin sa ce wato Abdullahi Abdullahi ga group din jinin sa Nan wato A sai a Taya ni Dubawa.

Dr arwan ya mikawa alkali Shima ya Gani ya mikawa Baba isuhu har ta zagaya zuwa ga Farida..

“Alhamdulillah yanzu shi Abdullahi ya zama Dan Uban sa kenan tunda jinin shi yazo Daya da Uban sa? Cewar Yaya lami.

Dr arwan ya Amsa.

“Sai a tambaye ita wacce take musun Hakan shin ta YARDA?

Baba isuhu ya Dube ta Yana Fadin

“Kin yarda da Hakan kenan?

Basma da ba haka taso ba ta amsa da

“Na yarda .

Aka matsa ga takarda ta GABA ta Abdurrahaman Abdullahi Shima bashi jinin Yana layi Daya da na Dan Uwan sa Shima group A yake..

Nan ma Yaya lami tace

“Kin yarda da Hakan? Duk Wanda aka zo kanshi in kin yarda ki ce kin yarda in Kuma kina da ja sai kiyi Magana dama dai kece Mai in Karin Hakan ..

Basma ta Amsa da ta YARDA.

Aka wuce kan takarda ta GABA ta Salman wacce ta fito Shima nashi jinin group A ne Amma da sauri Basma ta cafe da Cewa

“Ban yarda da wannan ba Kam sai an sake shi Wallahi..

A take kuwa Dr arwan ya sake gwajin jinin Salman Amma dai yadda sakamakon farko ya bayar na yanzu ma haka ya bayar..

“To Alhamdulillah Shima dai jinin nashi irin Na Yan Uwan sa ne ko?

Cewar Baba isuhu Dr arwan ne ya amsa mishi har aka zo kan takardar Sulaiman Shima dai a layin group A yake Nan ma sai da Basma taja tace sai an sake Dr arwan Kuma ya sake ya Kuma sake Amma dai kamar farko..

“Wai tsaya ma Dr shin ka kuwa kware a Aikin Nan ko kuwa practical kake? Ni fa Wallahi ban yarda da wannan gwajin ba ko don kaji nace Mai takardar Nan jinin shi group A ne shiyasa kake ta min jaye jayen masu group A? ..

Dr arwan yayi murmushi Yana Fad’in

“Eh to ba zance na iya ba tunda Babu Mai iyawa face ALLAH SARKI Amma ki tuna Ina kika dauko ni? . kuma ba wai gwajin jini nayi ba DNA nayi Wanda yake nuna alaka ta kusanci Relationship. Asibitin Sha ka tafi kika dauko ni ko kuwa federal? Ai Baki tsaya kinji na sauran ba tunda ai ba duka nace Miki duk a group A suke ba su wadan Nan sauran ai nasu jinin ya Sab’a da A din?..

“Me kake nufi da wannan maganar?

Ya dauko takardar Mai dauke da sunan Najwa Yana fad’in

“Najwa Abdullahi group din ta A ne ita kuma Nabeela Abdullahi group din ta O ne ..

“Karya kake Kai k’aramin Dan iska me kake nufi da jinin yata group O ne akasin na yar uwar ta?..

“A a kar ki zage shi akan Aikin shi gara Da Ubangiji ya nuna wannan izinar Basma wallahi Nima a yanzu ban yarda a Raba gadon nan da Ya’yan ki ba don Wanda yake aikata Alheri zaton Alherin yakewa kowa Amma ke sai gaki da fatan Sharri kuma Wallahi sai nabi kadin batawa yaran Nan suna da kikayi Kinga Allura ta tono garma TANA K’ASA TANA DABO kenan ..

Cewar Yaya lami wacce take kallon Basma wacce ke Shirin kaiwa Dr arwan Duka.

“Kai Wallahi ban yarda da iyawar Aikin ka ba bani kudi ne kaje na Samo Wanda ya iya Kai Kam nafi zaton practical kake Wallahi ..

“Duk wannan Aikin da nayi ya zama na Banza kenan? Ai sai kin biya ni ma awon da na sakewa yaran Nan da Wanda..

“Kaci Uwar karya ka kwana da yunwa Wallahi tashi kaje..

“A a kar ya tafi Dr Don Allah akwai Yara Biyu da suke gida zan dauko su a gwada Mana jinin su Saboda Uban su ne matar Nan keyiwa Sharrin cewa wadan Nan yaran nasa ne to Ina son na San idan group din jinin su ya zama daya to zan iya yarda nasa ne Amma idan ya zama ba group Daya duke ba to ni zanbi kadin Yar Uwa ta da aka batawa suna aka zarge ta akan Abinda ba ta aikata ba..

Cewar Gali Wanda ya mike Yana cewa zai dauko Saddam da Hanan Ya’yan Sameer Wanda Basma tace su Salman Ya’yan sa ne idan jinin su Suma yazo group A din to zai yarda duka Ya’yan Sameer ne..

Yaya lami tayi maza tace

“Kwarai kuwa Gali kaima ka kawo Hikima Nan Yi Maza ka dauko su .

Farida kam ta zuba tagumi tana Jin in dai haka wasu mutanen Duniya suka zamo to Aminci yana dab da k’arewa..

Da sauri kuwa Gali yazo gida ya kwashi Saddam da Hanan zuwa gidan Farida Dr arwan Kuma ya Soma gwajin jinin su har ya kare ya Kuma fidda sakamakon su inda jinin su Yazo a group O Wanda hakan ya nuna su a Ya’yan mutum Guda kamar yadda Salman da Sulaiman Abdullahi da Abdurrahaman suka zamo Suma na mutum Daya ..

Farida ta Ji wasu hawaye suna sauka a Saman bakin ta tayi maza ta share su tana son ta tambaye Dr arwan shin shi jini da Ake gado Dole sai na Uba kawai Ake gado ba a Gado na Uwa? Amma Kuma maganar da Gali yake ya Hana tankawa..

“To Alhamdulillah tunda abinda matar nan take fada Sharri tayiwa Farida Kuma Bata mata suna take nufin Yi ni Kuma Wallahi ba zan yarda ba tunda ga gwaji anyi Uban yaran Nan da take zargin Farida da shi har da wasu hotunan Sharri jinin su ya zama daban da su Salman da ace jinin su duka ya zama iri Daya Babu yadda zamuyi tayi nasara akan mu to gashi allah ya kunyata ta jinin su Saddam da Hanan daban na su Salman da Sulaiman Abdullahi da Abdurrahaman Shima daban Kuma muma a yanzu muke da ja tunda jinin marigayi Abdullahi group A ne to sai jinin Ya’yan ta ya zama group A ko zamu yarda Suma Ya’yan sa ne in Kuma ba haka ba Muna da ja Wallahi..

“Kwarai kuwa Gali Nima Ina da wannan Jan Wallahi da matar Nan gaskiya ta shirya da Bata shegenta yaran Nan ba sai gashi ana zaton wuta a makera sai gata a masaka don haka Nima sai jinin Ya’yan ta ya Zama irin na Dan Uwa na ko zan yarda da ita. Najwa dai na yarda tawace amma nabeela kan ban yarda ba wlh. Abinda kakeyi ne sai kayi zaton kowa Ma shi yakeyi don Haka Muna da ja.

Cewar Yaya lami.

“Karya kenan ai Kuma in har nayi Muku Alfarmar bari a Raba gadon Nan da Ya’yan Farida Wallahi Banga Uban da ya Isa yace min Kala ba bare ma wannan likitan na bogi ne Bai iya komai ba sai shirme Dole a sauya gwajin jinin Nan don ni da idona ganau ce naga Abinda na Gani Kai Kuma da kake fadar kana da ja mu hade a kotu ma na sai ka Nemi hakkin naku?..

Sameer ne yayi sallama a farfajiyar Gidan inda su duka suke ..

“To ba gashi ba? Gashi Nan Yanzu ma ya Kuma Zuwa? Yanzu Kuma Shima da yazo Allah ya tona Asirin shi akan idon ku yanzu Kuma me ya zo Yi? To gashi dai Kun Gani yazo yayi Abinda ya Saba Yi tunda har da Auren ta ma Yana zuwa bare Kuma yanzu ko me Kuma za a ce mini yanzu? Sai ku tambaye shi me yake kawo shi gashi Nan ai gashi Nan Allah ya kama shi akan idon ku.

Sameer ya Duka Yana Gaishe da baba isuhu da Yaya lami tare da alkali Wanda ya mutu a Zaune ya kasa cewa uffan..

Baba isuhu ya Dubi Sameer Yana Fadin

“Yaro Kaine Baban yaran Nan?

Ya fada Yana nuna Saddam da Hanan..

Sameer ya amsa da kwarai shine ..

“Don Allah kayi Mana wata Alfarma Mana a duba Mana jinin ka ko wane group yake don matar Nan tace ba zata bari a Raba gadon Nan ba sai anyi gwajin jini inda tace Bata yarda Ya’yan Farida na marigayi Abdullahi bane wai naka ne duk da anyi gwajin jinin..

“Babu komai baba a gwada.

Ya fada Yana mikawa Dr arwan Hannun shi aka zuk’i jinin shi aka Soma awo Shima har aka gama inda gwajin ya fito da nashi group din wato O. Sameer Kuma ya Amsa da Dama ya san group din jinin sa O ne ..

Yaya lami tace

“To Alhamdulillah da jinin bawan Allah Nan ya zama A da Basma kamar daga can zata koma tace Ya’yan Farida nashi ne.

“Ai yanzu Kuma ba ta gwajin jinin ya kamata kiyi ba Yaya lami ta Abinda ya kawo shi ya kamata kiyi tunda na nuna muku Amma Kun kasa Ganewa Mutumin Nan Neman matar Nan yake Zuwa tunda ni na kama su ba sau Daya ba..

“Mu Kuma ba ta wannan din muke ba ta yadda aka Samu Sab’anin Jinin Najwa da Nabeela da Abdullahi muke..

Mutanen suka shigo Gidan kimanin su shida suna auna Ashariya..

Su Baba isuhu suka juyo suna kallon su inda Daya Daga Cikin mutanen ya Dubi Basma Yana Fadin..

“Ehem ga ta Nan algungumar shegiya macuciya ..

Basma taja baya Domin kuwa ta Gane shi Wanda ya siyi gidan Nan ne sai Kuma wasu da Bata Gane su ba..

“Kira min Hukuma ta kama min shegiyar matar Nan don barin ta a haka ma criminal ne tunda ta San ta Siyarwa mutum Abu ta Kuma zagaye ta Siyarwa Wani..

“Ni fa ba itace ta siyar min Wani dan mamman ne ..

“Wai ku dakata bayin Allah me yake faruwa ne haka kuka shigo Gidan mutane Kuna hayaniya?

Cewar Baba isuhu..

“Baba Wannan matar ce ta Siyar Mana da gidan Nan muka biyata kudin ta Amma Kuma sai ga wannan mutumin Shima ya kawo Mana tallar gidan inda muka Gane bayan mun siya Kuma sai aka siyarwa Wani to mu dai ita wannan ce tare da Wani mutum Mai face mask suka siyar mana har takardar ma sun bamu Amma shi bangis yace Basu cika mishi takardu ba..

Sai Baba isuhu da Yaya lami suka dauki salati suna sanar da Ubangiji..

Kan kace me? Kofar gidan ta cika dankam da motocin Hukuma Wanda Suka shigo ana nuna Basma wacce ido ya Raina fata tana Shirin guduwa don Allah yayi ta da tsoron Hukuma..

Amma Ina tuni aka damko ta aka maka mota Mai jiniya Wuce da ita garba da Kabir ne Suka bi bayan su inda Yaya lami sai Fadi take..

“Yau na SHIGA UKU ni lami wai Muna Nan sake da Baki baba har Basma ta Soma siyar da gidan Nan bamu sani ba? In Banda Allah ya Tona Mata wannan Asirin da sai dai a zo a cewa Farida ta fito zasu kulle gidan?..

Baba isuhu ya ce

“Ni Wallahi tsoro na ma kar ya zamo ba Gidan Nan kawai matar Nan ta siyar ba tunda ta afu da son mallakar Dukiyar Nan har ta San ta kewaye ta kad’as da Dukiyar Abdullahi ta kulle kudin ta to Amma Kuma shi Allah baya zulunci gashi Kuma ya nuna Mata kayan marayu ba zai bar Mai zalunta su ya Zauna lafiya Kuma sai ya tona musu Asiri..

“Ni Kam ba zai yuwu na koma gida ba baba isuhu Dole na tsaya tare da Farida don Kar Wani Abu yayi waiwai da Baya ga Kuma su Najwa da Nabeela da Uwar su Bata gida ..

“Nima bari na bi bayan su don ba zai yuwu na barta ba Dole cikin ido ayi tsawurya..

“A a Baba kar Kaje tunda ga garba da Kabir sun Isa suyi komai Kawai in ta mayar Musu da kud’in su ai zasu sake ta tunda fa ta saka kanta wannan masifar ai Kuma ta SHIGA UKU ..

Baba isuhu ya fita ya wuce gida Yana Fadawa su Goggo Amu Abinda ya faru na gwajin jinin da Basma ta gayyato likita Amma Kuma k’etar gwaiwa tana Shirin Kashe Mai ita Domin kuwa reshe zai juye da mujiya Domin kuwa Abinda take son Ganin Bai faru ba sai ma ita da Ake Neman yadda akayi jinin Ya’yan ta ya zama daban da na Uban su kuma ana cikin hakan sai ga wasu mutane da suka ce wai ta Siyar musu da gida kuma Wani ma yace an Siyar mishi wai wannan Gidan Nasu fa wai har yarinyar Nan ta San tayi Bak’ar kasuwar shi ta kulle kudin ta? To gashi dai can har da hukuma suna ta Kai kawo sai kace wacce tayi KISAN Kai Yanzu dai Kabir da garba suna can sai mu saurari Dawowar Kabir ..

Goggo Amu ta Saka salati tana sallalallami..

“Ni fa malam na Daina mamakin yarinyar Nan komai akace tayi ba Zanyi Mamaki ba tunda ta fara Cewa wai ta Saka anyiwa marigayi Abdullahi wakar mutuwa nace Kai matar Nan ta fita zakka har gobe Ina Mamakin yarinyar Nan akan wakar Nan da tace anyi sai kuma shegenta yaran Nan da tayi tun daga Nan na saki da Al Amarin ta sai gashi wai har ta iya kulla wannan makarcin ni Amu yanzu me gari ya wayar Mata? Yanzu irin haka ke da Dadi Abu ya Kare a hukuma ai kuwa Asiri ya gama tonuwa Kuma dai girma ya Fadi wai Rakumi da shanye Ruwan Yan tsaki..

A can state C I D kuwa inda aka Kai Basma tambaya ce tamkar taje Kiyama har dai ta amsa ta Siyarwa Ado gidan ta ta Kuma karbi kudin ta Amma Bata San Wanda ya saidawa bangis ba inda ya fad’i Dan mamman ne ya Saida mishi gida ..

Jin wannan maganar ne Kuma ya tayar wa Basma Hankali don ta tabbatar da mamman ne ya Saida musu gidan Nan Kuma Abinda take tsoro kar ya zama ba ga gidan Nan kad’ai mamman ya siyar ba..

Don haka aka Soma Kiran wayar mamman Amma yaki dauka ..

Aka tambayi Basma ko ta San Dan mamman ? Tace Eh ta san shi..

“Kira shi da wayar ki wata Kil ya dauka Amma nan ya San ya kasaye Nan Shiyasa Bai dauka ba..

Basma ta Daga wayar ta tana kiran mamman sai gashi ya dauka Yana Fadin..

“Yaya ne ? Gani Nan wurin kamfanin MTN zan tsara su akan sign din marigayin mijin ki da suke nema so nake ko Wani Abu na karba kafin na San yadda Zanyi na salhe su ..

“Yanzu kana can wurin MTN din?

“Ina can Taya mu da ADDU A na samu na shiga Gaban su..

Ta kashe wayar inda jami in C I D yace Basma ta tashi ta Kai su kamfanin MTN din da shegen Nan yake yau sai ya shigo Hannu tunda ga shi can ma Yana Shirin yaudarar wasu ..

Haka Aka Dauki Basma a motar Jami an tsaro C I D zuwa damko mamman …

Basma tace kuci nama a sannu gudun zawayi gidan iko bata da flajin🥰😂

Fatan kowa yayi sallah lfy

Wai duk yawan mabiyan tana kasa tana dabo a kasa yiwa wasila karar bata ragon layya

<< Tana Kasa Tana Dabo 65

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×