Dukan kofar da akayi da karfi ne yasa Farida ta dubi Abdullahi da yake kankame da ita tana fadin
“Sulaiman ne yaron Nan Yana da hayyata fa.
“Mami a Bude Mini kar Daddy ya sake guduwa ya barni.
Sulaiman ya fada Yana Kara Dukan kofar da son a Bude mishi.
“Mami kizo ki Bude mini.
Ta Mike tana zura hijabin ta nufi kofar da sai doka ta yake.
Ta Bude ya shigo Yana wara idanu Yana fad’in
“Mami Ina Daddy?.
“Yana Nan d’aki BACCI yake Amma ka bari ya tashi kar ta she shi kaji.
Bai Jira ta gama Bayanin ta ba ya sheka d’akin Yana hango shi kwance ya fada akan shi Yana Fadin
“Daddy kayi BACCI?.
Dole ya tashi Yana Rungume da shi Yana Fadin
“Banyi bacci ba Sulaiman.
“Na dawo don kar ka sake tafiya ka barni zan bika mu tafi tare.
Dole dai aka Hak’ura da wannan kulawar saboda Sulaiman ya kasa ya tsare .
Yayi wanka ya fita Yana Kiran wayar garba Amma Bai same ta a kunne ba sai kawai ya zarce state C I D don ance a can Case din yake.
Mamman Kuma da Basma ta Kira tana tambayar Yana Ina ? Ya amsa Mata da Yana MTN branch Alhalin Yana can ana cinikin gidajen da Basma ta nuna mishi a matsayin kaddarar Abdullahi inda ya Riga ta don Yana son sai ya tattare komai ya siyar ya kammale kudin shi ya shalle don yanzu MTN office din can yake so ko Rabin kudin su bashi ya tsallake ya bar garin don haka ya gayyato Wanda zasu Siya su bashi kudin shi inda Kuma aka bukaci ya kawo takardun su ya amsa da Akwai. Ya Kuma bazama nemo su inda yaje ya Hado na bogi ya kawo har da shaidun karya.
Aka kashe ciniki kudi masu Nauyi ya Kuma sallama aka tura mishi kud’in shi a account ya wuce ya Fara Neman Visa don ya San matukar ya hada kud’in Nan to ya gama kasaye Nigeria sai dai wata k’asar ba Nigeria ba Nijar ko Sudan kamaru ko chadi.
Don haka ya nufi benen da suka da Alhakin Samar da visar fita tsallake k’asa ya Soma Neman Visa Amma Babu visa a k’asa ya Soma cuku cukun yadda za ayi ya same ta .
Yana cikin Yaya za ayi ne wayar shi tayi Kara Yana Dubawa yaga Basma ce ya dauka Yana Fadin
“Ya akayi ne madam ?.
“Kana Ina ne nazo baka Nan?.
“Ina Nan Wani cuku cukun kin Gano min sign din marigayin mijin ki? Don sunce sai da shi Amma ko kallo Daya nayi mishi zan iya yin irin shi .
“Ai shine na nemo Kai Kuma kayi Wani wurin sai kace baka San Halin da Muke ciki ba.
“Gani Nan Zuwa Gani Nan Ranki ya Dade ai abinda Naso kiyi mana kenan tun kafin yanzu kika tsaya Jan jiki.
“Kina Ina yanzu kin koma Gida ne ko kuwa kina Ina?.
Gani Nan MTN branch din .
“A a koma gida don in Suka gan mu tare zasu zaci kunji kunjin yayi yawa mu Hadu a gida Kawai sai muyi komai cikkn Sirri.
“Ok to Ina jiran ka
Ta kashe wayar suka juyo Gida.
Basma a motar Jami an bincike C I D sai Raba ido take inda jami in daya yake tsare da ita a motar Yana kallon ta tana waya da mamman Wanda Suke son suji Ina yake Amma yace sai dai yazo gida don haka suka jiya daga MTN branch din Suka koma don ajiye motar ma aikata suka dauko wacce take ta gida ce don in ya tunkaro yaga motar ma aikata zai iya guduwa
Basma da take cike da Mamakin mamman da irin zalamar da ya nuna Mata wacce tafi tata. Har ya San ya siyar da gidan Nan ne ita tana gefe Kuma Bai sanar Mata ba? Sai a yanzu ma taji Lallai motar ta da yace tana gareji taci kuturus karya yake akwai lauje cikin Nadi Wallahi Bata ko shakka ya kad’as Mata da mota tunda yau kwana Biyar kenan wane irin gyara ne da har za a Kai wannan lokacin ba a gama shi ba?.
Suka iso gida Basma ta fito daga mota zata shiga cikin gida yayin da Jami an bincike suka Kasu Kashi Biyu wasu suka tsaya a inda motar su take nesa kadan da gidan yayin da wasu Kuma suka takowa Basma Baya har cikin sashin ta Suka tsaya a bakin kofar da mamman zai shigo .
Tana SHIGA ta Tara’s da Yaya lami ta fita zuwa gida ta bar su Najwa da Nabeela da Salman da Sulaiman Wanda Yaya lami ko da ta gansu an turo su sai ta dauki Hannu ta Kuma Rik’e Sulaiman din wurin ta inda Salman da su Najwa Kuma Suke wasan su Amma ko da Yaya lami ta tafi Gida ta dawo sai Sulaiman ya so komawa wurin Daddyn shi Amma Salman ya Rik’e shi suna game a game din su Najwa shiyasa ya jima Bai koma ba sai da Sulaiman yaga dawowar Basma wacce yake masifar tsoro saboda Wani duka da ta tab’a Yi mishi yasa yake tsoron ta Kuma baya son ta zaro mishi ido ita Kuma tafi Gane ta zare musu ido shiyasa Yana ganin ta ya fice daga sashin nata ya koma nasu Yana buga kofar .
Ta dubi Salman da wani matsiyacin haushin yaran zatayi Magana ne Nabeela ta tarbe ta da kayan kwalam din da Uban su ya Basu tana nuna Mata .
“Mama Kinga kayan da Daddyn mu ya kawo Mana wai mama ba kince Daddy ya Rasu ba?.
Ta Dubi yarinyar tana Hararen ta Bata Kuma tankawa Nabeela ba Domin kuwa Abinda yake Gaban ta yafi k’arfin ta ita Kuma tana mata wata Banzar magana.
“Mama Daddyn mu fa ya zo har mama lami ta fita tana kuka ya kawo Mana sweet din Nan Mai yawa.
“Ke ya ishe ni da Allah bana son surutun wofi wane Daddyn ne Yazo?.
“Daddyn mu mama .
Ta zauna akan kujera tana Duban yaran.
“Wai Nan gidan ya zo ko kuwa Ina kuka ganshi?.
“Can wurin maman su Salman muka ganshi Yana can ma Bai zo Nan ba .
Sai a lokacin ne taji Wani Abu yana Dukan kirjin ta ta mike zata nufi sashin Farida sai Kuma ta koma ta Zauna tana jin tamkar wacce ta zare don ta kasa samun nutsuwa duk da ta kasa gasgata yaran sai Kuma kasa karyata su .
Mashin ya Sauke mamman a kofar gidan Abdullahi inda idon jami an Nan yake kan Mai shiga da Mai fita har suka ga mashin ya Sauke mamman Wanda kallo Daya sukayi mishi suka Gane shine Wanda Suke tsumayin.
Wanda Suke cikkin motar suka dafe mishi baya zuwa bakin kofar gidan suka tsaya.
Mamman Kuma da yake ta sauri Yana Rungume da wasu takardu Wanda ya gurzo duk cikin manubar da za ayi zamba Cikin Aminci.
Bai iya kula da mutane Biyun da suke gefe ba saboda yadda ya afu da son ya karbi sign din marigayin mijin Basma in yaso sai ya je ya Kai da ya salhe su Suka Soma zuba kud’in su zai lallabe su ko da Basu biya kudin duka ba ya samu ya karbi kudi masu Nauyi ta yadda zai cuce su ya sulale ya Gudu ya bar su da Allah ne yayi Abin.
Ya tausa Kanshi cikin sashin Basma Yana Fadin
“Dauko min sauri nake da Allah gara muyi mu gama da wuri .
Ta fito tana fadin ai gasu na kammala Maka Kai nake Jira .
Jami an bincike suka shigo su Hudu inda mamman yaga sun kewaye shi suna nuna mishi ankwa.
Ya Dubi Basma wacce take kallon shi cike da nadamar sanin sa Shima Yana kallon ta da Neman Karin Bayani .
“Zasuyi Maka bayani kar ka Damu mamman muje zakaji komai daga garesu.
Aka tasa keyar mamman gaba Yana Sanye da ankwa yayin da Basma ma aka tasa ta GABA suka SHIGA motar Jami an bincike suka koma state C I D mamman Yana fadin
“Ni kika yaudara Basma? Zaki ga Abinda zai faru Wallahi har Wani shigo shigo kike min don Nazo ki kulla min Sharri.
Suna zuwa Kuma mamman ya ga Wanda ya Siyarwa da gida Wanda ya tabbatar da ta tashi Shiyasa aka farauto shi.
“Yauwa ga Shegen Nan Wallahi na fasa siyen gidan tunda Kai dai Shege mayaudari ne Wallahi kudi na kawai za a mayar mini in yaso bangis ya kare kalau da wacce ta siyar mishi.
Aka Soma tambayar mamman ya San mutumin da Nan? Ya amsa da Cewa Bai San shi ba duk ma Abinda ya fada Sharri ne Kawai aka ja Mishi.
Ana cikin Hakan Kuma sai ga wasu mutanen da suka biyo mashin din mamman Wanda mota ta dauko suka iso Nan Suma suna Neman mamman din aka gidan da ya siyar musu sai daga Baya suka Gane takardun bogi ya Basu.
Suma mamman yace Bai San su ba.
“Ana cikkn Hakan Kuma ma aikatan MTN suka kawo Kabir Wanda Shima yaga mashin dauke da mamman ya nuna shi a matsayin Wanda zai siyar da Filin da suka karba haya .
Mamman dukkan su ya karyata su Cewa Bai San Maganar ba shi Sharri suke mishi .
Aka karbi takardun da yake tare da su ana dubawa same irin Wanda ya bawa Wanda ya saidawa gida Amma gashi Yana karyatawa.
Basma tana sakaye a Wani wuri da aka kebe tana kallon mamman da ya murje idon shi yace Bai San komai ba.
Aka Soma Rarrashin mamman akan ya Fadi gaskiyar Abinda ya sani in ya karbi kudin mutane ya biya su kawai kar yaja zance tunda ga gaskiya a hannun shi ta takardun da ya bayar ga wadan Nan mutanen. Amma yace Bai San da maganar ba .
Daya Daga cikin ma aikatan ne ya Karbi wayar shi Yana cewa ya bude mishi account din sa ta haka ne zai Gane Abinda Ake Magana.
“Bani fa Aiki da banki ni malam bani da ma account.
Aka karbi wayar sa sai ga alert din da akayi ta tura mishi na kudin da ya zambata.
“Kace baka Aiki da banki ga Kuma shigar alert a wayar ka? Tunda munga bankin da kake yanzu zamu Bude account din naka muga Abinda ke cikkim ka sauwake wa kanka kar ka kawo taurin Kai don zaka Wahala ne kawai don yadda mutanen Nan suka zo Nan karbar hakkin su sai fa ka biya su tunda ga gaskiya ma ta bayyanar da kanta.
Aka Saka code din banking na mamman wato first bank ana Neman checking balance din sa har aka zo kan pin aka ce mamman ya Saka pin ya Saka shi daidai sai ga account ya bude Wanda yake kwance da kudi masu bayar da tsoro.
“Wadan Nan kud’in kenan kidnapped kayi ka same su tunda kace baka San da maganar da Ake tuhumar ka ba? To laifin ka ya juya daga na zamba Cikin Aminci ya koma na irin mutanen da Muke farauta don haka ka zo hannu in yaso su wadan Nan mutanen da ka ce baka san komai akan su na zamu karbi details din su duk Ranar da muka samo Wanda Suke nufin shine ya zambace su zamu nema musu hakkin su .
“A a Ranka ya Dade na San su wallahi Kuma na karbi kudin su Amma ni Wallahi ba Dan kidnapped bane ban ma tab’a hada hanya da su ba.
“Ai Kuma ka makara in Kai bakayiwa kanka matsaya ba mu munyi Maka tunda ka karyata Cewa Kai ba macuci bane to Dole ka Amsa kidnapped tunda kudin da suke cikin wayar ka in ba kidnapped ba ko zamba Babu ta yadda zaka same su haka taka Haye dai irin ka Wanda kallo Daya za ayi maka a Gane alkiblar ka.
“Wallahi Ranka ya Dade da gaske ne na cuce su Kuma wadan Nan kudaden su ne har ma da Wanda Bata tashi suka Gane zambatar su nayi ba.
Abdullahi ya faka motar shi a kofar farfajiyar ma aikatar ta state C I D ya fito ya shiga cikkn inda garba ya ganshi Kabir ma ya ganshi sai ya dauko kabbara.
Basma Kam k’iris ya rage fitsari ya subuce Mata ta ta makale tans shirin kifewa sabodsa rudani kyarma ta kwsce Mata Tana
agwalalo idanu tana kallon shi ta kasa kiftawa inda yake ta bawa ma aikatan hannu suna Gaisawa har ya kare ya Dubi mamman Yana Fadin
“Mamman dama kana Nan?
Garba ya Dube shi Yana Fadin
“Ya akayi ka zo ba a Kira ka ba?.
“Kar ka Damu garba Naji ance basma tana Nan ne shine nazo na fanshe ta kud’in da ta karba mu koma Gida.
“Ai gama Wanda ya Karbi kud’in Nan Kila ma ka San shi ko ?
Abdullahi ya Dubi mamman Yana Fadin
“Wane irin ma na San shi ? Dan Uwan Basma ne.
Abdullahi ya fito da wayar shi Yana fadin
“Waye za a turawa kud’in?
Mamman da yayi k’asa da kan shi.
“Ga kudin su Nan ma sun fito fa Abdullahi bari a mayar Musu da kud’in su itama Basmar ai zata maida musu da kudin su ne tunda an yanka ta tashi Kuma tana k’asa TANA K’ASA TANA DABO.
A take Wanda mamman ya karbi kudin su Suka karanto account akace ya mayar Musu da kud’in su ya Kuma mayar sai Wanda Suka siyi gida Suma aka mayar Musu da kud’in su Abdullahi Yana zaune Yana kallon duk abinda yake faruwa yayin da Abdullahi ya nemi karbar Basma wacce itama akace ta mayar da kud’in da ta karba ga Wanda ta saidawa gida ta mayar mishi da kud’in shi aka kashe case Amma mamman Kam ance sai an Rik’e shi don Akwai yuwuwar Wani jagwal din da ya Fi wannan tunda ya zama mazambaci.
Shima sai da Abdullahi ya karbi belin sa ya kuma dauko su a motar shi shi da Basma wacce take Jin tamkar kasa ta tsage ta fad’a a cikk . Ba komai take tsoro ba a yanzu irin yadda mamman ya shaka ta San Dole zai FASA KWAI ne akan Abinda yake boye .
Tana cikin wannan zancen zucin ne taji mamman Yana Fadin
“Ina da magana Alh a yau zan fada Maka Wani Abu da baka sani ba.
Bai bari Abdullahi ya amsa ba ya zarce da fad’in.
“Ni ba Dan Uwan Basma bane kamar yadda ta fada Maka karya take Maka ni din saurayin ta ne Wanda take gayyatowa har cikkn Gidan ka Kuma akan Gadon ka.