Skip to content
Part 7 of 75 in the Series Tana Kasa Tana Dabo by Hadiza Gidan Iko

Kukan ya kwacewa Farida ta Rik’e Hannun Anty lubna tana Fadin “Nifa in taimako na Ake ganin anyi to a mayar Dani gidan miji na Amma Nan gidan kar ku dauka Yana burge ni Wallahi baya burge ni Kuma ni na San manufar Yaya dauda da kawo ni Nan gidan to bana bukatar komai in taimako na akayi aka kawo ni Asibiti ai naji Sauki Kuma ni a gidan miji na Babu Abinda na Rasa tunda kowa ya kalle ni yasan bani da yunwa bani da Rashin sutura to a bari mana Nazo nace ga Abinda yayi mini kafin a Wani kawo ni a killace kamar wata akuya.

“Kiyi Hak’uri to yanzu taho kiyi kalaci nifa Ina ganin kamar duk wannan abun Mai sauki ne Farida kece fa kike Neman zafafa shi shi fa Yayan naki Baki ji Abinda yake nufi ba Kuma bakiyi sati ba bare kiga komawar ki ko hanawa ba.

Suka fito ta tara mata lafiyayyen abun karin mai rai da motsi.

“Sai Wani Tara min abubuwa Ake to Babu bako na a gidan miji na duk wadan Nan abubuwan Ma na wuce da irin su har finsu Ina samu Wallahi wane gidan Aure ne Babu matsala? Sai ni ce za ace Babu iko Babu zarafi aji Wani Abu Wanda Bai Kai ya kawo ba sai anyi tsallen Uwar kuturwa an shigar min lamarin ? Shi wa ya San iyakar matsalar Gidan sa da zai Wani kama mutum ya girke.

Dauda da yake saukowa daga sama ne Farida ta hango tayi maza ta takawa bakin ta burki.

Duk da baiji Abinda take fada ba Amma ya san akan zaman ta gidan take magana.

Ya sauko ta dube shi tana fadin, “Barka da safiya.

Ya zuba Mata ido Ganin ta dauke kanta, Ya amsa Yana Fadin

“Yaya jikin ? Tace da sauki. “Kina da wata matsala ne?

Tayi shiru Bata tanka mishi ba sai ma tura Baki gaba da tayi . Dariya ta so kwacewa Anty lubna Amma ta maze tana Kallon su.

“Baki ji Ina Miki magana ne? Ta juyo tana fadin, “Ina ji Mana…

“Nace kina da wata matsala ne?

“Nifa satin nan da kake magana yayi min yawa. A taimaka mini a sallame ni in koma gida tunda likitan da aka dauko ni don shi ma ya sallame ni to a taimaka mini.

“Yau kwananki nawa ne a yau? Tayi maza tace “Kwana Hudu ne.

“Na zaci anyi bakwai din . To Amma tinda ma kina sane da yau Hudu ne na Kara Miki Wani satin ya zama biyu kenan akan wancan satin da na fada sai Yaya?

Ta juyo da sauri tana kallon shi sai kawai ta wage Baki tana kuka tana Fadin.

“Wallahi ba zan zauna har wannan lokacin ba Yasin tafiya ta Zanyi. “To bari kiyi kukan Mai Dalili don Uban ki.

Ya Figo wayar caja inda ta Mike a guje ta nufi daki antu lubna ta Rik’e shi tana fadin.

“Don Allah ka kyale ta Daddy ni da zaka yarda sai nace ka maida ta Gida tunda ta nuna maka gidan ta da mijin ta take so.

“Ai tunda ta nuna min Hakan Zanga irin kokarin ta da taurin kanta sakarai Dabba marar Hankali. Da haka ya fice ya bar Gidan.

Farida ta garkamawa kofar D’akin ta key don haka ta shaki kukan ta Mai isar ta duk buga Mata kofar da Anty lubna tayi Bata Bude ba Dole ta kyale ta ta dawo ta Zauna.

Da Rana ma da aka gama girki aka doka Mata kofa Anty lubna tayi ta Mata magiya Amma Bata Bude ba .

Dole ta kyale ta don ta San yunwa dai Dole zata fiddo ta.

Tana zama wayar ta na daukar Kara ta duba sai taga Haj ce . Ta dauka da sauri tana Gaishe da Uwar mijin tata suka gaisa Haj tana tambayar sai Kiran wayar Farida take Amma Bata samun ta Yaya jikin?

“Jiki yayi sauki Sosai Haj bari na Kai Mata wayar sai kuyi magana don tace ta baro wayar ne a Gida…

“Yauwa to lubna tunda jikin ma yayi sauki alhamdulillah a bani ita din.

Lubna ta Mike da sauri ta nufi D’akin Farida tana Fadin,

“Ga Haj a waya tana Magana Farida.

Da sauri ta Bude kofar tana karbar wayar ta Kai kunnen ta tana sallama..

“Ameen wa alaikkssalam lallai jiki yayi sauki.

“Haj barka da Rana ya Gida?.

“Lafiya Lau alhamdulillah Farida Yaya jiki Kuma? Nayi ta Kiran wayar ki bana Samu sai dai dauda ya Kira yace min kinji sauki har an sallame ki.

“Haj kiyi mishi magana ni Bama sai na cike satin ba tunda naji sauki shifa na gama Gane nufin shi so yake sai yaja mini Sameer a k’asa kawai Saboda Abinda Saddam ya fada ana kama zancen yaro ne? To ni ki fada mishi Haj na gaji da zama gidan shi don Babu Wani Abu da ke burge ni a gidan in Ma haka yake Gani nawa gidan yafi burge ni akan Nashi.

“Sai Kuwa a kyale ki ki Dawo tunda kinji sauki bari zanyi mishi magana a Sako ki mota kawai.

Sai ta fashe da kuka tana Fadin,

“Kinji fa Haj wai Cewa ma yayi sai na Kuma Wani satin ni Kuma Wallahi ba zan Kuma ba.

“Ke shiga hankalin ki Dani kinji? Yace ga yadda Zakiyi kice ba haka ba? To gaki ga shi nan bari naga idan Zaki iya . Ke ko Yar siyasar Nan Baki iya ba sai kice Dole sai shine zai bi Ra ayin ki? In yace sai sati Zaki koma sai kice kayi hak’uri Yaya akwai Abinda n baro a gida ko Kuma kice mishi makarantar Saddam Amma shi tsaye ke tsaye kina Ganin kina iyawa da shi ne na barki da shi?

Sai kawai ta kuma yage Baki wai kuka Haj ta kashe wayar ta ta barta.

Sai da Yaya dauda ya Kira wayar ta Anty lubna kafin ta Mike ta Kai mata wayar ta dawo tana Lissafin Dokin Rano

Bata Aikin komai sai kallo sai Kuma ta tsala kwalliya ta tule a d’aki ko falo. Kayan da Yaya dauda ya Siya Mata Kam ta San ya kashe kudi sai dai itama ai ta San Sameer Yana Mata fiye da irin wannan gatan Kuma a yadda take jin Sameer fiye da bugun numfashi ai Bata Jin zata yarda Wani dauda ya Raba su ba.

A haka ta Yi kwanaki bakwai Amma dauda ya watsar da Al Amarin ta Bata ga kamar zai Mata maganar tafiya Gida ba. In da ta tabbatar da sai tayi sati Biyun da yace ita Kuma ba zata iya ba Wallahi.

Ta karbi wayar Anty lubna ta Kira Haj tana fadin.

“Don Allah don ANNABI Haj ki Saka Baki bawan Allah Nan ya sallame ni yau dai kwana bakwai nayi.

“Kar ki Kuma Kira na akan wannan maganar Farida . Dole ne dauda yayi Hukunci akan ki Kuma kibi saboda Baku da Uban da yafi shi in nace yayi Hukunci na tayar Babu Ranar da zaku ga GIRMAN shi . Sai in na ga abin Nashi zai Wuce Gona Da irin ne zanyi magana Amma yanzu ya zama Dole ki cika Kwanakin da ya Debar Miki in kin so ku Rabu lafiya sai ki bi shi da Arziki in Kuma kince ke kece to Shima shine in kika bari akayi kwanakin da yace ai ni Zanyi mishi magana Kuma Dole ya dawo da ke..

“Shikenan Haj sai ace sai yadda Ake so za ayi mini shi waye zaiyi mishi haka akan Nashi gidan.

“Ai fa ki neme shi sai kuyi magana ba Gida Daya kuke dashi ba? Taras da shi kuyi magana duk yadda kukayi sai ki bugo ki fada min.

Ta mayarwa Anty lubna wayar ta ta koma sauraren ikon Allah.

Kwana na takwas ne ta fita bakin kofar inda Anty lubna ke tuna Mata kar ta wuce wajen don in ya dawo ya samu ta fita har ita zata jawo Mata.

Bata tankawa Anty lubna ba ta fice Amma iyakar ta bakin get inda tayi tsaye tana ganin sojojin da suke ta shige da fice a cikin jajin komai na ciki Rayuwar bariki ce kowa harkar gaban sa yake.

Tana tsaye sai ga faruk Wani makocin su Yaya daudan ne Uban sa soja ne Shima Kuma ance ya fito a sojan Wanda lokacin da take budurwa tana zuwa gidan saurayin ta ne lokacin da akayi Bikin ta Yana can wurin training sai gashi a yau ya Ganta inda ya faka motar shi ya fito Yana kallon shi ya zama Wani babban ga askin da aka bar mishi wata Suma a Gaba Amma an kwashe sauran sai ta dab da goshi aka bari irin yadda mafi yawan sojojin suke aski.

“Kai wa nake Gani a garin namu kamar wata Farida?.

Tayi murmushi tana Fadin

“Wai Kaine haka ummaru ta fada don ta san ya tsani ace mishi ummaru.

“Na yafe Miki Amma da ba ke bace sai na Saka mutum a gwale gwale saboda Kiran wannan sunan.

Tayi murmushi tana Fadin, “To na Gode ya kake ya Aiki ? In ce dai kayi madam faruk ?

Ya shafi gashin Gaban Kansa Yana Fadin,

“Wallahi banyi ba Farida tunda kika yaudare ni ai ban Kuma yin wata budurwa ba.

“Ban yaudare ka ba Allah ne baiyi Al Amarin ba Amma ai na fad’a maka Ina da wani bayan Kai.

“Ya jingina jikin motar shi Yana Fadin, “Haka dai kika ce Amma ni na sakankance bani da wata Mata sai ke sai dai dawo nayi anty lubna tana fada min Auren ki ni Kam har yanzu Ina Jin a jiki na akwai Rabon Aure a tsakanin mu Kuma ban fidda Rai ba.

“Gara Kuwa ka fidda Ranka faruk Domin kuwa banyi Aure don na dawo ba. Kaima Ina Maka fatan Ubangiji ya hada ka da matar kwarai.

Sun jima ita da shi kafin ta juya ta shuge gida Shima ya shiga nasu Gidan.

Washe gari ta farka da begen mijin ta Sameer don haka da ta tashi ta nemi wayar Anty lubna ta Soma Saka lambar Sameer Amma taji wayar a kashe Abinda Bata sani ba Yana dab da ita ya shigo inda Babu service ne shiyasa Bata same shi ba. Tayi ta Kira Amma Bata samun wayar ba Dole ta mayarwa Anty lubna wayar ta ta Koma tana tunanin ta yadda za ayi ta bar gidan Nan don ba zata iya zaman da Ake son tayi ba.

Misalin Sha Biyun Rana Sameer ya iso jaji ya shigo har kofar gidan Yaya dauda inda suke ta gaisawa da sojoji hadiman gidan kasancewar duk an San juna don haka Bai Sha Wahalar shiga gidan ba.

Anty lubna ta amsa sallamar shi tana mishi Sannu da Zuwa ya zauna Yana gaishe ta Suka gaisa tana Kawo Mishi Ruwa da lemu kafin ta Mike ta Kira mishi Farida.

Ta fito idanun su ya Hadu tayi Wani murmushi tana Fadin “Yanzu kake tafe?

Ya Sakar Mata wani murmushi Yana Fadin

“Kina Nan kin manta Dani Hankalin ki kwance Baki ko tunanin Yaya zan kasance?

Ta dauki lemun ta na Fadin. “Muje D’aki na kawo maka Abinci.

Tayi gaba yabi bayan ta har d’akin ya zauna akan Gadon ta fice ta hado mishi kayan Abinci ta girke mishi ta shiga zuba mishi Yana ta bin ta da ido don ganin a cikin kwanaki Tara ta wani irin sauyawa.

“Ya Ruko Hannun ta Yana Rungume ta Yana Fadin “Bar Abincin nan b shine a Gaba na ba nazo mu koma Gida ne don bana Jin zan iya Rashin ki na kwana kamar Haka in ma Yaya dauda zai dafa ni ne yayi ya bani ke mu koma Gida.

Ta Mike tana rufo kofar ta dawo tana fadin, “Wannan mutumin fa akwai Abinda yake nufi . Sati Daya yace zanyi Shekaran jiya da na tuna masa ma sai cewa yayi sai na Kuma Wani satin.

“Kice kashe ni yake son yayi? Ya Kuma Rungumo ta Yana shafa fuskar ta Yana Fadin, “Kiyi min Afuwa Farida son ki nake shiyasa nake kishin ki. Ki yafe min na taba lafiyar jikin da nake samu nutsuwa da shi jikin masoyiya ta ZUCIYA ta ce take kulafucin ki Bata iya jure Rashin ki don Allah Kar ki bari Yaya dauda ya nemi shiga tsakanin mu.

Tayi kwance a jikin shi tana Fadin

“Ba ma zai fara ba don Haka ni yanzu ma don Kar nace ka tashi mu tafi nayi laifi wurin Haj Amma tunda kazo ka Kira shi ka fada mishi kazo sai Muji Abinda yake nufi.

Ya Kai bakin shi a nata suna kissing din juna daga Nan Kuma sai Al Amari ya sauya.

Yana kankame da ita Yana Jin hakikatan Babu wata mace da zata Kai Farida a wurin shi . Kuma duk Ranar da Farida ta barshi ko ta mutu shi Kam ya SHIGA UKU.

Magana yake Mata Yana Rarrashin ta akan ta yafe Mishi Abinda yayi Mata Kuma kar ta bari Yaya dauda ya Raba su.

“Kar ka Damu bari ya Dawo Muji Abinda zai ce Idan ma ya ce sai nayi sati Biyun zan koma to kawai ka ke zuwa Nan in ya kula da kana kwana wuri na in Yana da kunya ai zai Hak’ura ne . Aure na mutum Biyu ne Kuma munayi to Ina Ruwan shi? Shi zai yarda ayi Mishi wannan wulakancin ne?

Ai kuwa Sameer ya samu karfin gwiwa don haka akayi ta tsinkar furen soyayya har Zuwa la asar inda yaran suka taho suna buga kofar da sauri Farida ta Bude inda su Saddam suka shigo sukayi Arba da Sameer
Hanan da saurin ta ta fado jikin shi ya dauke ta Yana shafa fuskar ta inda Saddam Kuma ya ja ya tsaya sai da Sameer yace mishi “Yaro na bakayi missing Dina bane? Ya Dubi Uban Yana Fadin

“Ni da daddy Babu Ruwa na da Kai tunda ka taka min Hannu da takalmin ka Mai zafi Kuma ka Doki Mami na.

Ya fito da jakar ibon Yana Fadin, “Ai na baka Hak’uri itama mamin taka na Bata hak’uri kazo mu shirya kaji yaro na.

“Indai zaka bani ibon din Nan duka to zamu shirya Amma kar ka Kara taka min Hannu da takalmin ka Mai zafi Kuma kar Kara dokar min Mami.

Ta tura mishi ledar ibon din duka Yana fadin, “Gashi Nan duka ai ni so nake mu shirya na Kuma Daina taka Maka hannu shikenan ko?

Yaron ya cabe ledar Yana fadin, “Shikenan mun Shirya.

Ya sake dauko ledar ibon ya bawa su suhaif Ya’yan Anty lubna kowa dai dai ya Kuma bawa Hanan itama…

Yaya dauda da ya dawo ya Tara’s da motar Sameer a kofar gidan ya tabbatar da shine yazo sai Wani matsiyacin fushi ya sauka a ZUCIYAR shi ya fito Yana shigowa cikin Gidan inda yake Kiran lubna ta Kuma fito tana karbar kayan da yake Rik’e da su a hannun shi.

“Sameer ne naga motar shi a waje? Ta amsa mishi da Eh shine.

Kai tsaye ya wuce D’akin Farida inda yaran suke baibaye shi suna Zuba mishi shirmen surutun su.

Ya Daga labulen d’akin Yana kallon Farida da Sameer kafin cikin fushi ya Soma Fadin.

“Wa ya Kira ka ne yace kazo? Ko kuwa duk cikin Rainin da kayiwa mutane ne? Baka San Hikimar dauko Farida da nayi daga katsina zuwa Nan ba? To bari na fada maka kaji ka Kuma Rik’e. Farida ta gama Auren ka ko da Kuwa Kaine karshen Maza . Na yanke wannan Hukuncin ne don Kar nayi maka Abinda Zakayi nadamar sani na Sameer don Kai ka San ba Farida ba kowacce ban hada komai da ita ba ba zan bari namiji ya cuce ta irin yadda kayiwa Farida ba ai Aure ba bauta bane Kuma a haka don baka da kunya ka iya Tako nan ? To me kake son ce mini ? Inyi hakuri ki Kuwa ita Faridar tayi hak’uri ku koma? To ka Saka a Ranka Auren ku ya kare da Farida Kuma har Abada matukar Ina numfashi Kun Rabu kenan har Abada don haka in Kuma Ya’yan ka ne Suka kawo ka yanzu ne zaka tafi dasu in Kuma na sake ganin kafar ka a gidana zanyi Maka Abinda ba zaka tab’a mantawa ba.

Ya Figo Saddam da Hanan ya dire su a gaban shi Yana fadin.

“Dauke su ka fice min daga Nan Ina jiran ka Rubuto wa Farida sauran saki Dayan da yayi saura a tsakanin ku kaga Kun haramta wa juna don na gaji da Jin wata matsala ta faru a tsakanin ku in Kuma ka Kai Dan iska sai ka kaini kotu ka Nemi hakkin ka Amma manufar dawo da Farida garin kaduna don ku barranta Kai da ita wannan Dukan da kayi mata ka daki Auren ka ! Don haka tashi ka fice min a Nan !

<< Tana Kasa Tana Dabo 6Tana Kasa Tana Dabo 8 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.