Mamman ya Sauke AJIYAR ZUCIYA Yana Dafe goshi da yaji Yana Shirin tarwatsewa yayin da Haj Baraka da Haj kulu Baba isuhu da Yaya lami har da Garba suke Duban bakin mamman din Wanda yake zayyano kowaye shi a wurin Basma da irin ta asar da suka shuka shi da ita har sakamakon ya bayar da Najwa da Nabeela. Kafin yaci gaba daga inda ya tsaya.
“A wannan Lokacin ne Kuma na Samu matsala da Hukumar jami an tsaro ta Yan sanda Saboda Samu na da akayi da wani laifi na hada Kai da ni wurin safarar miyagun kwayoyi har aka sallame ni Kuma DAMA Akwai harkallar da Dole zata sa na Gudu na bar katsina shine na cika wando na da iska na shalle sai shagamu a can ne Kuma nayi wata ta asa wacce na zambaci Wani basarake Shima na gudu daga shagamu na wuce ilesha . A katsina kuma ban Kuma marmarin zuwan ta ba saboda Abinda na bari a garin na yiwa matar makoci na ciki Saboda tana Kawo min kukan na taimake ta saboda mijin nata baya iya ciyar da su ita da yaran ta shine nake zagawa idan mijin nata ya fita na Bata dan Abinda zasu siyi Abinci har dai Ashe Wani tela a Nan layin Yana kula da yawan shige da fice na ya Kuma kwarmatawa Mai gidan Nan Ranar har ya fita ya dawo Ashe sun Dana mini tarko sai gashi Kuma sun cika hannun su dani suka Kuma kama mu turmi da tab’arya Amma na samu na sulale shine fa na gudu zuwa shagamu . Daga can Kuma na yaudari Wani basarake Wanda ya yarda Dani ya damka min Amanar kula da gidan gonar sa wacce take cike da kaji da agwagwi jimina da talo Talo har da dawisu da dawaki. Shima sai da na siyar da komai na gidan gonar Nan na kulle kudi na na gudu tun farar safiya Zakara ya bani sa a na bar shagamu zuwa ilesha inda acan nake Yan buga buga na harkar ZINARE. Na San zaku tambaye ni inda kudin da na zambato sukayi? To Babu Wanda yake ci min kudi sai Mata don ko taba bana Sha bare kayan Mayen Zamani dama Wanda haramcin su ya zama abin kyama tun Fil azal a zuciya ta.
Haka nake zagewa nayiwa macen da nake so asara kafin na gama da ita na nemo wata .
Ina Nan a ilesha ne Muna ta buga buga da son Allah ya kawo Mai tsautsayin da zai shigo Hannun mu mu gyara shi Amma shiru SA A tayi Nisan kiwo sai kwatsam na samu Labarin mutuwar Mijin Basma . Don haka na Yi nufin zuwa na Gani idan ta samu kason gadon Ya’yan ta na yaudare ta na Kuma Debo Ya’ya na musamman Najwa da na nunawa mahaifiya ta hoton ta Gani ta Kuma ce daga Ina take ? Nace Mata Diya ta ce don nayi Mata karyar nayi Aure shine fa mahaifiya ta ta matsa min da Lallai Lallai na karbo Diya ta na kawo mata ita don tun Ranar da taga hoton ta kaunar yarinyar ta tsaya mata a Rai shine daga Nijar na shigo ta jibiya na iso katsina da Niya guda Biyu. Ta dauke Najwa da Nabeela da Kuma tattare komai na Basma . Sai dai na Fara kokarin Ganin na kammale komai ta hanyar Bata shawarar siyar da kaddarorin Mijin ta ta Kuma yarda ni Kuma na nuna Mata nafi ta zalama na Fara da karbe Mata mota Kuma Gidan Da ta Siyar ma ni na Fara saida shi na Kuma ce ta nuna min sauran kaddarorin da suke waje Suma duk ta nuna bayan na kula da farko zatayi min gardama sai kawai na karbi kwallin kifil na shafa Wanda ya zamo Dukkan Abinda nace Mata ba Zatayi gardama ba har dai aka zo kan filin da MTN suke haya Wanda shine naso Siyarwa kafin na dauki su Najwa mu gudu Allah da yake almusauwuru ne sai ya kawo karshen komai Ashe duk Wahalar da kamu kawai muke Al Amarin NASA Zane ne Wanda Baya gogewa Kuma tabbatacce sai Gani a yau da nake Ganin nafi Basma wayo da manuba Gani tana Shirin Kashe ni bayan ta fasa min goshi sai gata da WUKA zata caka min lallai Dan Adam Mai wauta ne shine yake barin Abinda yake Gaban shi yaje Yana ganin na gaban Wani Gani dukkan Abinda na aikata Babu Wanda zan daga nace naci Riba sai gashi duk na gama kashe Maza Amma mace tana dab da kashe ni . Hakika na zama asararre da yau Gani Ina fallasa abubuwan da nayi Wanda ni da kaina na San Babu Daya na Azo a Gani Kuma ban tsira da komai ba sai tarin zunubin da na tabbatar da shi kadai ya Isa ya Hana ni kwanciyar kabari in da na mutu a wannan Halin.
Akayi tsint duk mutanen cikin d’akin yayin da Haj Baraka mahaifiyar Basma Kam kuka take marar sauti sai dai HAWAYEn da suke gudu akan fuskar ta.
Hatta da Yaya lami ta kasa motsi.
Baba isuhu ne yayi k’arfin Halin magana Yana Fadin
“Amma dai yaro baka yiwa kanka Adalci ba . Banji haushin yaudarar da kayiwa mutane ba irin yadda ka keta haddin Ubangiji akan Matan Auren Nan da ka tabbatar da igiyar Auren su akan su ka kuwa San girman azabar Wanda ya Yi Zina da matar Aure? Azabar da Ubangiji zaiyiwa Al Ummar ANNABI lud’u da suke Neman jinsin Maza dukkan yawan Al Ummar to Rabin ta ne akeyiwa Wanda ya keta haddin matar Aure shi Daya tal? Me yasa Ake samun wannan matsalar ne a Yanzu ta keta haddin Matan Aure da sunan taimakon Halin da suke ciki ga Maza marasa tsoron Allah? A yau kotuna ma case din da zaka Tara’s kenan wane yayiwa Yar makocin sa ciki? Wane yayiwa matar makocin sa ciki? Mace Mai Aure da take bibiyar Maza ? Maza masu bibiyar Matan Aure da sunan waye wai har anzo Zamanin da Maza ke fadin basa son Yan Mata ko zawarawa a lalata sai Matar Aure? Kai tur da wannan mugun Zamani Wanda yake cike da mugayen kaba irai Wanda dole zasu Hana Al Ummar Zamanin jin dadin Zamanin. Ni Kam da za a ce mini zan riski wannan Zamanin da Rayuwa ta da na karyata ko kuma nace ba Baki ba. Yanzu inda ta samu nasarar kashe ka Kai kuwa me zaka cewa Ubangiji?.
Abdullahi ya dago Yana Duban Baba isuhu Yana Fadin
“Ai baba ko tanadi abin fad’a ba zai Nemo shi tunda Babu inda Ubangiji ya bar bawa ya Rayu Kara zube . Kuma Wani Abun mu da kan mu me muke jawo shi dukkan Abinda kayi sai anyi Maka Nima ai nayi Wani Abun da Dole za ayi min haka ta Yaya zan nemi na shakata ko na huta Amma ace ba za a Bude min kofar da zan kulle ba? Nima giyar kudi taja ni na nemi na huta tun lokacin da na Rasa Auren Farida Wanda duk macen da ta mallaki Abinda ya ke burge ni zan Taya to Ashe kuwa Wani Abun ma nine da kaina na kawo shi. Sai dai in na so kaina ne zanji zafi don haka ban ga laifin Basma ba tunda nayi Mata KISHIYA itama batayi laifi ba in tayi mini. Kuma Babu wani mataki da zan dauka akan su ita da mamman matukar dai Adalci ne a zuciya ta sai dai kawai mu daura Aniyar gyara abinda muka San kuskure ne don ni Kam tun lokacin da Allah ya mallaka mini Farida na yafe Rayuwar morewa na Kuma kama hanyar da Allah zai tsare Mini Ya’ya na da ba zan so da wannan Rayuwar ba Amma Kuma ai Dole na biya Bashi gashi Kuma Basma ta biya mini . .
“Sai tari abubuwan da Ake aikatawa kuskuren kuruciya ne Wanda in akayi yayin kuruciya sai girma ya zo anyi hankali sai ayi ta nadamar Abinda aka aikata Amma dai muke sani Allah Bai bar mu sake Kara zube ba yace mu nemi ilimi . Haka Kuma iyayen mu sunyi kokari matuka Gaya wurin tarbiyar mu da son Ganin Goben mu tayi kyau Amma sai mu watsar mu kama son zuciyar mu yanzu me gari ya waya?.
Haj baraka mahaifiyar Basma ta dago tana fadin
“Ni Kam bani da idon duban ka Abdullahi. Yau da malam Yana Raye da ya hadiye ZUCIYA ya mutu saboda Bak’in cikin yarinyar Nan. Amma ni Kam Ina Dab da yin Hakan Domin kuwa malam yayi maka Hakan ne da nufin wanke Maka zuciya Ashe Bak’an ta Maka zuciyar Zatayi . Ni Kam ban San me zan ce Maka ba? In baka Hak’uri? A a Wallahi Abinda duk zai Sanyaya ZUCIYAR ka kayi shi ka Kuma nemi zama lafiya.
“Ai Haj Babu Abinda zan iya yiwa Basma wallahi in laifin ta ya Fi wannan taci ta cinye lafiya.
“Ai kuwa ko yarinyar Nan zataci lafiya sai an biwa yaran Nan da tayi ta shegatawa kadin su Wallahi .
Cewar Yaya lami.
Baba isuhu ya Dube ta Yana Fadin
“Ke Kam kar ki zama babbar kawai Mana. Ita fitina waye yake son tayar da ita in ba shaidani ba? Ko ni Naji zafin kazafin Nan Amma a yanzu da Al Amarin ya fito fili Bata zamo Miki abin tausaya ba? Sau tari k’etar gwaiwa Mai ita take kashewa yanzu dai a da Bakin wancan Mutumin ya tabbatar da Cewa Ya’yan ta NASA ne Kuma Mai awon da ta dauko ba ya fada ba cewar jinin su ya Sha banban ba? Duk Mai son yaga ya tona Asirin Dan Uwan sa to Sha Allah nashi Asirin ne zai fara tonuwa. Kamar yadda fara ta gari ta zama lamiri dukkan Abinda kake son Ganin Wanin ka to akan ka zai fara sauka Alheri ko Akasin sa don ka Gane shi Allah ma ya haramtawa Kansa zalunci ya Kuma Saka shi Haram a tsakanin Yan Adam .
Garba Kam sai zufa yake sharcewa Domin kuwa Shima maganganun Abdullahi sun Saka shi tsoro da firgici musamman da ya zama Shima ya na Daga cikin masu son morewa da Matan da suka zamo na Aure ma don a Cewar su Matan Auren ne Suka dadin harka fiye da yan Mata da zawarawa. Idan kuwa haka ne Shima kuwa ba zai tsallake wannan siradin ba idan har kayi da na wasu kaima sai anyi da naka Yaya kenan ?.
“Ni Kam Ina cike da yadda akayi wannan haihuwar Ragayar aka ce Mana ka mutu Abdullahi Amma sai gaka akan kafafun ka bayan duk mun gama koke koken mu . Shin dama don kaga Ruwan hawayen mu ne yasa akace mana ka mutu ko kuwa mutuwar ce tayi Maka Dadin da ka tafi sai da kaje ne ka dawo Kuma don ka bamu LABARIN Abinda ka Gani?
Cewar haj kulu inda Kuma Basma taji cikin ta yayi bala in kartawa k’ugi Yana Rarakar ta har tana Shirin sakin zawayi don ta tabbatar da yanzu ne Kuma zata Kuma Shan wata Kunyar Domin kuwa dai abin da yake Rufe ne zai bayyana Wanda yafi na baya muni. Musamman da ta tabbatar da Zancen gawa Dubun da ta zuba mishi a Nama ya fito tunda Bata manta ba Garba ya fada musu cewa an Gano yaci guba ne a cikin labal milk ko Dambun Nama da tuffa Wanda yaci Amma a yanzu ita da kanta ce zata yankewa kanta Hukunci tunda har suka Rufe maganar tsakanin su shi da Abdullahi komai Kuma ai ya gama bayyana yanzu ne zasu k’arasa tsiraita har su Baba isuhu da Yaya lami Haj kulu da mahaifiyar ta su tsine Mata irin tsunuwar da zasuyiwa wanda Sukaji yayi irin Abinda tayi.
Abdullahi ya Dubi Haj Yana Fadin
“Haj Garba ya kamata ya bayar da Bayanin Nan .
“Ai Kuma garba ya zama makaryaci tunda ya San kana Raye yace Mana ka mutu haka na kwana Ina mafarkai da tunanin munyi Hannun Riga da Kai sai dai ko a kiyama kaga ba zan Kuma yarda da Garba ba tunda Yana sane da gaskiya yake barin Muna matsar hawaye.
Sukayi Dariya Abdullahi Yana Fadin
“Kuma da gaskiyar ki Haj Amma nine nacewa garba ya Fadi duk abinda kukaji daga Bakin shi ba shine ya kirkira ba ayi Mishi afuwa ni din ne ya kama ta na Fadi komai da Baki na Haj tunda ance Waka a bakin Mai ita tafi Dadi .
Ya Soma da fad’in